← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 152

Sashe 115

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haba mana! A iya sanin da ka yi min ya kamata ace ka san ba zan tab’a fallasa tsaraicinka ba, kawai dai na san za ka yi mini abunda nakeso idan ka ji na fad’i hakan shiyasa..kuma na san hakan shine kad’ai abunda zan yi in iya controlling d’inka wanda controlling ɗin naka danayi a yau ɗin ne ma kaɗai dalilin da ya sanya na ajjiye video d’in dama tun farko, saboda ban san me gobe ta k’unsa ba.
amma daga yau ba zan k’ara ba, tunda na ga ranka ya b’aci sosai!!na ma
goge video d’in!!ka yafe mini.
Pretty please!!”
Ya fad’i hakan cikin had’e hannuwansa biyu waje d’aya sannan ya yi kalar tausayi da fuskarsa.

K’ura masa ido Junior yayi
shima Yassir d’in shi yake kallo da serious face kafin dariyar da ta taso masa ta samu nasarar kufcewa bayan ya fara fesar da ita a hankali
a hankali da farko.

Kauda kai kawai Junior ya yi cikin fushi ya juya ya nufi k’ofa zai fita.Da sauri Yassir ya bisa ya rik’o hannunsa
yace”Pls mana!!
Da gaske nake, na ji ba daɗi nima ka yi haƙuri..so sorry

Mun shirya???
Ya fad’i hakan yana mik’o masa hannunsa alamun su yi musabaha.
Juyowa Junior ya yi kafin ya kalleshi yace
“Na san ba ka goge ba!.
Kana son mu shirya?”
Ya yi mishi tambayar yana kallonshi.

Da sauri Yassir yace
“Yes,Wallahi.”

“Inaso ka goge.
ba ma na buk’atar dole sai na ganka ka goge ɗin dan na san za ka iya sake yin kamar ka goge bayan baka goge d’in ba,kawai inaso ka goge tsakanin ka da Allah da kuma darajar friendship d’in da yake a tsakani na da kai!
Iyakar abunda nake so daga wajenka kenan Yassir…

A wajenka hakan abun tsokana da wasa ne,
Amma ni a wajena! Wannan ba abun wasa bane ba.”

Numfashi Yassir ya fesar, ya zura hannuwanshi duka biyu a cikin aljihu, cikin yin serious sosai da fuska shima yace
“Maganar gaskiya junior, nima ɗin wannan ba abun wasa bane ba a wajena!!! I’m morethan serious, da gasken gaske na ke.
Sannan video d’inka is safe Junior, babu mai ganinsa dan na killacesa a wajena
Ni kaɗai! Har zuwa lokacin da za ka yi gangancin faɗawa Mutane gaskiya.…..”

Yadda Junior yake ji kamar ya rufe Yassir da duka ya b’ata komai ne ya sanya shi juyawa kawai da sauri ya fice daga d’akin ya banko musu k’ofar ransa a mugun b’ace.

Yana fita Kausar tace”ka san dai Abotar ku ta lalace harabada ko?”

Sai a lokacin Yassir ya juyo,inda take ya nufa ya zauna a gefenta ya ruk’o hannunta a hankali yace”I don’t give a f**k(ban damu ba)!.
Ki manta da shi kawai, mu duba kanmu sannan mu saka kanmu a farkon komai! a ko da yaushe,
In ba haka ba akwai matsala.”

Numfashi ta fesar tace”yeah nima ba wai damuwa na yi da shi ba, kawai dai gaya maka na yi, sannan ko komai ya yi settling ya wuce to kar ka taɓa sake yarda da shi har abada, saboda zai iya cewa shima zai rama.”
Cikin kawar a zancen Junior d’in ta d’aura d’ayan hannunta a kan nasu ta damk’e da kyau tace
“Thankyou Yassir”
Murmushi ya yi kafin yace
U re welcome
Sweetheart…ai saboda mu nake yi, ba ke kaɗai ba…”

Ajiyar zuciya ta sauk’e, ganin ta kusa kwafsawa ya sa ta d’an yi murmushi ta kawar da zancen tace “ya akayi da Yaran grenade?”
Sai da ya fesar da iska tukunna yace “da farko 5m suka buk’ata, da kyar muka tsaya a three, na tura musu 2 gaba d’aya kud’in accnt d’ina kenan, yanzu saura 1.
Sun ce dai sun ma riga sun goge amma kin san halin Irinsu.
2 hours suka bani akan in tura musu cikon ko kuma su sake yi mini b’arna.
Gyara zama ta yi tace “a drawer chan akwai sark’ata, ka d’auka ka saida sai ka cika musu, a samu a wuce wajen.….”

Jinjina kai ya yi, yana jin babu dad’i kafin ya ce”inshaaAllah zan siya miki dozen d’in ta.”
A hankali ta yi wani d’an guntun murmushi ta zuba mishi ido ba tare da ta ce komai ba.
Shima itan yake kallo kafin ya fesar da numfashi yace”bara in tafi… kafin ma wani ya shigo
d’akin nan a ganmu tare a san ba haushin ki nake ji ba!”

Murmushi duk sukayi, shi yana jin tsananin k’aunarta tana ratsashi ita kuma tana jin tausayinshi kad’an dan ba ta san ya zai ji ba idan ta auri Yashjub…..

Sark’ar ya d’auka har da receipt ɗin duk ta haɗa ta bashi, suka rabu bayan yace mata duk abunda take buk’ata ta kira shi …..

Yassir yana fita Yadira ta kira Kausar ɗin ta ce ”Junior yana jiranta a k’asa, Daddy yace scanning mai kyau yake so a yi, dan haka ta fito su tafi…”

Hakanan ta shirya ta fito, bayan sun yi waya da Yassir ya ce”ta je,ba komai..shi har ya kama hanya yana so ya gama da Yaran grenade ɗin da wuri.”

Har suka k’arasa office d’insa babu wanda ya cewa wani uffan…Yassir kam ya tura masa messages sun fi biyar kuma duk barazana…
sun ci sa’a, dan colleague d’insa ba ya nan, dama office d’in nasa na cikin asibitin su biyu ne kawai shi da wani d’an India.

Rai a b’ace haka ya yi scanning d’in…dan yana fara scanning ya ga cikin ya fi 2 months kamar yadda ya yi lissafin d’azu a gida.
Gashi dai ciki k’ato amma ya na ji yana gani ya dank’ara 2 weeks a jikin report da conclusion amma ya san tabbas ko Yasmeen in ta gani wata rana sai ta gane…shi
kuma da gangan ya bar shi a hakan bai ɓoye scanning ɗin ba ya bar komai b’aro b’aro!
Ya san ko ba komai ya bar hint kuma ko ta kwab’e zuwa wannan lokacin ya san ba shi da case da Yassir, in sha Allah.

Suna gama scanning d’in ya mayar da ita gida, shi kuma ya komo domin ya kammala had’a result d’in jinin da ko tab’a jinin bai yi ba saboda kamar yadda Yassir ya fad’a babu buƙatar jinin tunda k’arya zai rubuta.

Har dare gidan shiruu, kowa ya tsit, ko
dinner yau kam babu wanda ya tab’a dan kowa da abunda ya damesa…
su Mommy kuwa kamar an yi musu bushara da gidan aljannah, dan haka suka sake k’aimi wajen aikin da suka saka a gaba kwana biyu, inshaaAllah yau za ta tunkari su Daddy da maganar auren Yash da Kausar tunda gashi komai ya zo musu da sauk’i sun samu hujja….a da tace ba za ta bari Kausar ta auri Yashjub ba amma Manubiya ce ta farkon da ta fara fusatata dole ta yi using Kausar ta taimaka musu su kawo k’arshen Manubiya inyaso sai ta san yadda za ta yi da Kausar daga baya, dan ba kaɗan ba kalaman Manu na aaibiti da ta ji tana gayawa Yash suka bada gudummawa wajen kammala hautsinata…dalilinta na bari Kausar ta auri Yash na biyu kum shine da ta zauna ta yi tunani duba da yadda Daddy ya chanza mata, abubuwa suka fara rinchab’ewa ya sa ta ga dole fa ta tsaya a kan Kausar d’in ta auri Yashjub, ko ba komai su samu su samu abunda suke so in yaso daganan ba sai Kausar d’in ta san me suka shirya ba cikin sauk’i za su zagayeta su yi abunda ya dace ga Yash ɗin ba tare da ta san su d’in ne suka aikata ba, kuma ta san a yanzu idan ta taimaki Kausar to za su shirya komai zai gyaru tsakaninsu za ta daina ganin kamar ba ta so ta taimake ta ne.
Daganan sai ta taimaka mata itama dan akwai aikin da take so Kausar d’in ta yi mata bayan ta auri Yashjub a kan Daddy, ta hakan ne kawai take ganin abubuwa za su gyaru a yadda ya birkice kwana biyun nan…………

Yashjub kuwa waya ya yiwa Manubiya yace mata”wani abu ya rik’esa…ta yi hak’uri idan ya dawo zai yi mata bayanin komai.”
Sam bai ji alamun ta ji haushi ba, instead ma addu’ar fatan alkhairi da samun nasara ta yi ta jera masa, daga haka suka yi sallama dan ta ji yanayin sa kamar yana gaban su Daddy…shi kuwa tunda ya shiga side d’in nasa wani Irin zazzab’i ne ya lullub’esa.
Suna gama wayar ya lumshe idanunsa daganan wani Abu kamar bacci kamar suma ya dannesa ba shi ya samu kanshi ba sai da gari ya yi duhu sosai….yana duba time ya ga har an idar da sallar isha…dan haka ya mik’e da sauri ya nufi bathroom yana istighfari…zazzab’in da ciwon kan sun sauk’a dan gashi har yana iya tafiya saɓanin d’azu da ya kasa tashi ma, amma fa sharkaff yake jinsa cikin gumi shiyasa yana shiga bathroom d’in ya sakarwa kansa shower yana jin yadda zuciyarsa ta shiga dagulewa dan tashi d’aya komai ya dawo masa sabo…….

Sai da ya idar da sallolin yana cikin karatun Al’Qurani,kiran Daddy ya shigo wayarsa, yqna ɗauka ya ce “ya zo yana son ganinsa kafin ya wuce gida.”

Sama sama hayaniya ta fara tashi a cikin gidan kafin ta karad’e ko’ina.
Ko ba a fad’a ba ansan Kausar ce dan ga muryarta ana ji
dan haka duk suka firfito parlourn saman….

Akwatuna wajen ashirin suka gani a jejjere…

Dafe Kai Hajiya mama ta yi,
kafin ta k’arasa inda suke tsaye Yassira rik’e da jakar hannun Kausar ɗin dan ta hanata tafiya ne, ita kuma Kausar tana k’ok’arin kwacewa tana kuka tana cewa”ki bar ni in tafi,
kowa ya samu salama.”

Hajiya Mama tana zuwa ta fincike jakar daga hannun duk su biyun ta yar kafin tace “Yanzu ke ashe rashin tsoron Allah n naki har ya kai haka?
Bayaga tashin tashin hankalin da kika saka mu a ciki throughout
shine kika sake cin wani burin hana kowa bacci??.
Ki wuce ki shige ciki kafin gobe da safe a san yadda za a yi da ke!”.
Ta fad’i hakan tana mai juyawa za ta koma inda ta fito.
Chapter 115 · 0% Book details