Sashe 77
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ji matuk’ar mamakin yadda k’awar tata ta amsa wayar hankali kwance har da y’ar tsokana a ranta tace”to ko dai ta fita ba ta gidan ne”
dan haka a hankali a fili tace mata “kina ina?”
Sai da gaban Yasira ya yanke ya fad’i da ta ji k’awartata ta ce mata”Ina gida mana, za ki zo ne?”
Zaro wayar ta yi ta kalla ta tabbatar da k’awar tata ta kira tukunna ta mayar kunnenta kanta tsaye tace’’ji na yi ance gobara fa ya tashi a estate d’innaku!yanzunnan aka kira Yash aka ce masa ga wuta yanata ci an gagara kashewa”
A rikice matar ta rafka salati kafin tace “to inaga gaskiya mak’iya ne, wani ne yake so ya jaa shi ya fito da shi domin a samu ya fita a kama shi!! ko dai wani Abu makamancin haka, dan mu kam nan ko k’aurin wuta babu a nan gaskiya, ki yi maza ki kirasa kice ya juya…..”
ai tun kafin ta rufe bakinta Yasira ta yi maza ta kashe wayar a gigice ta shiga kiran Yashjub…ta jera masa miss calls sun fi takwas amma bai d’auka ba, shiyasa hankalinta ya sake tashi dan zuwa yanzu tabbas ta gama gasgata maganar wannan k’awa tata!!
tashi d’aya ta fashe da wani Irin kuka a ranta ta gama sakawa ‘shikenan an kashe Yashjub’……..
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 29*
..Ko kuma an yi kidnapping d’in sa!.
A rikice ta afka d’akin, suna nan a yadda ta bar su, su uku, Manubiya a gefe tana ta faman hawaye.
Cikin rikici Yasira ta k’arasa gaban Mommy tukunna tace
‘’Mommy Ina ga magauta ne suka kira Ya Yash!
Dan yanzunnan na kira frnd d’ita ta estate d’innasa, tace ‘babu wani gobara,’
shi kuma yanzu haka inata kiran sa a waya ba ya d’auka! Inaga sun sace shi ko sun yi masa wani abun….’’
Ta k’arashe maganar tana mai sake fashewa da wani irin kuka.
Manubiya kawai tsintar kanta ta yi a gaban Yasira a rikice tace
‘’Ki sake gwada kira, InshaaAllah babu abunda ya same sa, bara nima in kirasa, idan bai d’auka ba mu yi message, na san in ya gani zai ki kiramu” ta fad’i hakan tana mai juyawa ta nufi wayarta.
Sai a sannan tukunna Mommy ta tashi ta tsaya a d’an rikice tace ‘’ikon Allah, to Allah dai ya sa lafiya…babu komai ma ki kautata zato….”
Kafin minti sha biyar gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi,
dan babu kalar kira da sak’onnin da ba’a yi an tura masa ba amman sam ba ya d’aukar waya kuma bai yi responding messages d’in ba.
Banda kuka babu abunda Manubiya take yi, tana kuka tana aikin kiran waya ba’a amsawa abun tausayi…
Suna a haka Daddy ma ya kira wayar Yasira yace “da shi da Yassir sunata kiran sa suma amma baya d’agawa but ga su yanzu suke barin gida za su je su duba estate d’in na sa..”
Yassira ce ta yanke shawarar ta sake kiran friend d’in tata inyaso ko mai gadin su ne ta sanya ya tayasu ya bincika ko Yashjub d’in ya k’arasa chan…gaba d’aya ta gigice haka ta shiga kiran k’awar tata.
Matar tana d’auka tace ‘’ya ake ciki Yasira? kun yi magana da shi?”
A tare da matar da Yasira suka fara jiyo hayaniya da ife-ife…ta cikin background d’in Yasira take jiyo k’ara ta ban mamaki kamar ana fasa abubuwa da kuma na bindigu da ihun bayin Allah suna neman ceto….
A hankali jikinta yana wani irin karkarwa ta ji matar tace”Innalillahiwa innalaihirrajiun,Yasira kina jin abunda nake ji?bara in duba…”
Sai kuma a rikice taji tace”y’an bindiga ne suka shigo mana sun fi mutum d’ari…..”
K’arar harbin da Yasira ta ji ne ya tabbatar mata da k’awartata aka kashe dan a tare ta ji k’arar wani abu ya fashe kamar k’ofar aka fasa da kuma harbin….
K’amewa ta yi ta kasa cewa komai,tana sauraron yadda mutanen suke magana wani a cikinsu yana cewa”a sake duba gidan sosai, idan babu kowa mu yi sauri mu kunnawa wannan ma wuta mu tafi next house bamu da isashshen lokaci…mu yi mu yi mu tafi,yanzu Grenade ya yi min waya yace mu yi retrieving dan sun riga sun kashe gayen, sun k’ona motarsa ma tun a bakin gate….“
K’afafuwan Yasira ne suka shiga kakarwa tashi d’aya ta gagara ci gaba da tsayuwa dan haka ta durk’ushe a wajen ta fashe da wani irin kuka.
Daidai nan Manubiya ta matsa kusa da ita kusan a tare ita da Ya’isha suka ce mata “m-m mai ya f fa rru!??’’
Suka yi mata tambayar a tsorace dan yanayin ta ya yi matuk’ar sake firgita su.
Da kyar ta iya d’agowa ta kalli Ya’isha ta yi mata bayanin abunda ta ji ya faru sannan ta d’aura da cewa”na ji yana cewa Grenade ya ce sun kashe sa sun k’ona motarsa tun a gate,Ya’isha Ya Yash suke nufi, shi ake so a kashe dama shiyasa aka yi k’arya da gobara aka ja sa wajen saboda su b’adda track d’insu kar a gane manufarsu.
Ba y’an fashin gaske bane Ya Yash d’inmu aka shirya kashewa dama Wallahi…”
‘Sululululu’ haka Manubiya ta tafi ta fad’i a wajen sumammiya…
Mommy ce ta kira Daddy, wanda ta ji muryarsa a rikice shima, cikin tashin hankali ya ke ce mata“gasu nan sun zo shiga layin motocin sojoji sun taresu, wai y’an fashi sun kaiwa estate d’in hari, an hana su shiga sun ma rufe gate d’in layin gaba d’aya. amma ga su nan dai ana ta k’ok’arin shiga ciki, motocin sojoji biyu sun kutsa kai yanzunnan…”
Yadda su Yasira suka ji muryar Daddy yana yi wa Mommy bayani ta wayar yana kuka ne ya sanya suma suka fashe da wani irin kuka.
Sun san Daddy ba lalle ya so su je wajen ba shiyasa ba su ce masa za su je d’in ba, maimakon hakan kawai suna gama wayar da shi suma suka fice dan hankalinsu gaba d’aya ya yi wajen….a nan suka fice suka bar Manubiya a yashe a k’asa suka nufi estate d’in suna kuka gaba d’aya su ukun..
…..
A Chan suka tarar da Daddy da Yassir, suma duk hankali a tashe. lokacin har an bud’e gate d’in layin, wajen taff cike da sojoji da y’an kwana kwana dan kusan kaff gidajen sai da suka cinna musu wuta tukunna suka gudu ba a kama ko d’aya ba.!
Yadda estate d’in ya k’one ya koma wani abu daban dole ya bawa Mutum al’ajabi, sannan ya sanya ɗan Adam ya sake ka’daita Allah ya kuma tabbatar da cewa abun duniya da duniyar kanta gabaɗaya ba a bakin komai suke ba.
Su Yasira suna hango su Daddy suka k’arasa wajen su, suna kuka. shima Daddyn hawaye yake yi, cikin sharar hawayen yace “akwai hope! ga dai motarsa chan a k’one da mutum a ciki, amma gaskiya ba shi bane ba inaga kamar driver d’insa ne, kuma shi har yanzu wayarsa tana shiga, amma wayar mutumin ciki ta k’one da na duba ba ta aiki.
Sannan munata dubawa har ciki amma kamar ma shi d’in bai zo nan ba kwata-kwata.
Cikin jinjina kai Yasira ma tace “Nima Inada hope Daddy,
dan yanzu ma na kirasa wayar tasa tana shiga, Allah dai ya sa ba wani abun ne ya same shi ba.
dan gaskiya bai zo nan ba.”
Daddy ne ya kira asibiti,
dama ga polisawa da sojoji a wajen, dan haka ambulance suna zuwa aka fara fitar da deceased da injured…abun ba dad’in gani, dan mutane sunfi talatin waenda suka rasu
injured kuma wajen mutum goma……
Bayan kamar awa d’aya wajen ya cika taff da jama’a, dan har su Baba larai duk sun k’araso suma kowa in ka kalla hankalinsa a tashe.
Dukda cewa zuwa wannan lokacin sun tabbatr da cewa Yashjub ba ya wajen, dan kaff jama’ar da ke yashe a harabar wajen da gefe gefen titin a lokacin da abun ya faru an shaida identity d’insu, amman kuma rashin amsa wayar tasa ne ya fi komai d’aga musu hankali a halin da ake ciki.
Dan haka Daddy ya kalli Yassir wanda duk hankalinsa ya gama tashi da rashin ganin gawar Yashjub…cikin dafa kafad’arsa yace ‘’ka kwantar da hankalinka Yassir, inshaaAllah babu abunda ya samu d’an uwanka, ka nutsu ka yi addu’a ka ji ko? dan ni kam zuwa yanzu inda hope ‘’
Ahankali Yassir ya had’iye wani k’ululun tashin hankalin da ya toshe masa mak’ogwaro kafin yace ‘’To Daddy’’.
Cikin fesar da huci Daddy yace ‘’d’an sake gwada kiran sa mu gani”
Still yanzu ma a hankali ya sake cewa “to Daddy”
Daganan ya matsa gefe k’irjinsa yana dukan uku-uku dan baya k’aunar ya kira a yi rashin sa’a ya ji muryar Yashjub safe and sound!..Hatta seconds da komai sai da aka k’irga daga inda yake zuwa estate ɗin, sannan ya bada numbobin motocinsa duka incase ma
Idan ya chanja mota, kuma sai da suka yi waya da mutanen suka ce masa gashinan ya shiga estate d’in yanzu tukunna suka fara aikin amma bai ga alamun sa a wajen ba!sai driver d’insa wanda yanada tabbacin bai cika yawo da shi ba,mai ya faru???yana ina????
Ya yi wa kansatambayar ba tare da ya san wa zai basa amsar ba…
adduarsa d’aya Allah ya sa a wani wajen suka danna gawarsa shiyasa ba a gani da wuri ba!…Allah ya sa a nemota yanzunnan a duk inda take a cikin estate d’in a fito da ita, dan tabbas zuciyarsa za ta iya tarwatsewa idan akace Yashjub ya fita daga cikin wannan abun da ya haɗa masa lafiya ƙalau babu abunda ya same sa….
Da kyar ya samu ya d’an nutsu tukunna ya zaro wayarsa daga aljihu, hannunsa har karkarwa yake yi haka ya danna kiran Yashjub..bugu biyu a na uku ya d’auka yace ‘’Yassir! kuna Ina??’’
A hankali Yasir ya lumshe idanuwansa wasu zafafan hawayen bak’in ciki da na tashin hankali suka shiga silalo masa…
Sai da Yashjub ya sake cewa ‘’Yassir ba ka jina ne?kuna Ina??”
tukunna da kyar da mugun kyar ya samu ya iya had’a kalmar ‘’ga mu nan duk, a estate d’inka’’
‘’Okay gani nan zuwa amma fara bawa Manubiya wayar yanzu, Inata kiran ta ba ta d’auka! Lafiya dai take ko??”