← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 152

Sashe 93

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya sake yin k’asa da kansa kafin yace”ya k’arfin jiki?”
ya fad’i hakan a hankali.
“Alhamdulillah”Baba yace daga haka ya maida dubansa ga Ya Nafi’u yace”Nafi’u na tura maka kud’in,ka je ka siyo gadon,kaka mallan kai yake jira tun d’azu ku kai gidan.”

A hankali Ya Musbah yace”Baba ba za a hak’ura da maganar nan ba,ka yi hak’uri dan Allah ka….”

Cikin fushi Baba yace”kai har yaushe ka zo ka ji halin da ake ciki da har za ka tsomo mini baki a cikin al’amurana?Kar fa ka kaini bango Musbahu, kulaka da ka ga na yi ba shi yake nufin na manta abubuwan da ka tafka ba!”
Da sauri kaka mallan ma ya tsomo baki,dama d’azu ma saboda Yash ne ya yi magana shiyasa bai tanka ba, dan haka yanzu ya samu bakin magana harda cewa “a cikin duhu aka kama Jidda da Al’ameen, amma shine saboda rashin sanin ciwon kai still suke da bakin k’orafi ga Yusuf wanda ya ji ya gani ya rufe ido zai aureta a hakan.”

“Yashjub mu je ciki”
Baba ya ce, daga haka ya juya, har Yash zai bisa sai wayarsa ta d’au k’ara, ganin sunan Daddy yasa yace”Daddy yana kirana bari in je in dawo kafin d’aurin auren.”
“To”kawai Baba yace, daga haka ya shige cikin gidan dan yana so ya yi wanka ya shirya da wuri gashi har 9:00 ta yi.

Su Ya Musbah sun san shawo
kan Baba ba abu mai sauk’i bane, dan ransa ba a b’ace ba ma idan ya turje babu mai sa shi ya bari, ballantana yanzu da yake a fusace, shiyasa gaba d’aya hankalinsu ya sake tashi suka cigaba da addu’a kawai..dan tunda har Yashjub ya sa Baki ya k’i yarda to addu’a kawai za suyi ta yi su jira Ubangiji ya yi ikonsa ya ceto rayuwar Jidda.

28 September 1994
….zaune take a tafkeken parlourn gidan, wanda ya ji kayan alatu mabambantq…a cikin shekarun da ba su fi hud’u ba Mijin nasu bud’i yake samu ta ko ina Alhamdulillah..sun chanja gida, ya gina musu bungalow guda biyu tafkatafka iri d’aya a cikin gate da compound d’aya, ko wacce da b’angarenta, sai kuma boysquaters babba shima a ta gefe…ya siya musu gwala gwalai har motoci ya siya musu guda biyu iri d’aya, zani kuwa mafi tsada na wannan zamanin shi suke d’aurawa ita da Abokiyar zamanta!
Sai dai fa ita duk wannan daula da ake ciki sam hankalinta ba a kwance yake ba, zuciyarta babu dad’i, nutsuwarta ba ta tare da ita!! sakamokon juya mata baya da Mijinta masoyinta abun k’aunarta ya yi tun lokacin da ta haihu shekaru hud’u kenan.
Tashi d’aya ya chanja mata ba tare da ta san laifin ta garesa ba.
A yadda yake nunawa kamar har yanzu yana k’aunarta tunda yana masifar kishinta har yanzu kishi mai tsanani ma kuwa, amma kuma ko kusa da shi baya so ta je..hantara kyara da tsangwama ne kawai yake shiga tsakaninta da shi, gashi tsabar kishi ya maida ita kamar prisoner ko baranda ta fita indai mai gadi ko mai wanki wani ya ganta to fa ta shiga ukunta a ranar, hakanan tana ji tana gani Abokiyar zamanta za ta tambayi fita a barta amma ita ba ta Isa ba!
kitso kawai ta san tana zuwa bayan layi shima tare ita da Abokiyar zaman nata su ke zuwa. Ita sam ta kasa gane kan Imam kwata-kwata, dan kamar ma zarginta yake yi haka take gani, watak’il saboda ya san ba ya sauk’e hakkin ta da ya rataya a wuyansa ne shiysa yake zargin za ta je ta nema a waje…
A take hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarta,
‘shin wannan wacce iriyar rayuwa ce??’
Ta aiyyyana tambayar a cikin ranta!!
gashi ba ta da gurin zuwa, bata da kowa!! dama Imam d’in shine Uwa shine Uba kuma Masoyi a gareta, yanzu kuwa abubuwan da yake nuna mata ita kanta ta san kora da Hali ne k’arara yake yi mata, ya gaji ita ne..!!!
A da tana tunanin ta yi sa’ar Miji yanzu kam tabbas ta san ba ta yi ba, maimakon sa’a Ubangiji ya had’ata ne da mugun Miji Mugu ajin farko!
“Khadija wai har yanzu ba za ki bar kukan nan ba?na gaya miki addu’a itace mafita…wallahi Imam har yanzu bai yi miki rabin abunda ya yi mini ba,haka yake, zai daina wata rana, dan Allah ki yi k’ok’ari ki cire damuwa a ranki mana.”
Muryar Abokiyar zamanta wadda shigowarta cikin b’angaren nata kenan, ta katse mata tunani.
A hankali ta d’ago ta kalleta daidai tana zama da Yaronta a hannunta.
Cikin sharar hawaye tace”ba komai Mommy,kar ki damu, nima na san wata rana sai labari.”
Cikin son kawar da maganar dan zuwa yanzu ko rarrashi ba ta so a cika yi mata gaba d’aya sai ta sake zama emotional, dan haka ta d’an k’ak’alo murmushi ta ce ”Yassir! Ina ka baro Yasira? ko tana chan tana sana’ar?”.
Ta fad’i hakan tana mai mik’awa Yaron Hannu alamun ya zo gareta.

“Kamar kuwa kin sani..tun da Baba larai ta yi musu wanka ita da Yahanasu suka koma bacci har yanzu ba su tashi ba..”
Murmushi ta yi tace”Allah ya yi albarka, ya had’a kawunansu”

“Am khadija ko za ki yi wa Hajiya Mama magana, a samu Yashjub ya dawo..ya yi k’ank’anta a zuwa Hutu ya dad’e haka a wata k’asar, gashi an koma makaranta.”

Dariya ta yi kafin tace”yanzu Mommy sai in kira Hajiya Mama in ce mata Yashjub ya dawo ya yi k’ank’anta?
ai sai a ga rashin karar mu..ki yi hak’uri, ita kanta na san nan ba da jimawa ba za ta dawo da shi..ke da ya kamata ace yanzu fafutukar ta yadda za ku shirya ma kike yi!? idan ta ji mun ce Yash ya dawo ai bak’in jini za ki sake gogawa kanki har ni sai ta shafa….”

Shiruu Mommy ta yi kafin ta sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya tace”Allah ya sa mu dace”
“Ameen”Khadija ce, sannan ta fara yiwa Yassir wanda ta karb’a wasa shi kuma yana dariya.

“D’azu dai Daddy ya kori mallan lawal,ai dama na gaya miki yadda ya sakawa Yaron nan k’ahon zuk’a ba zai barshi ba.”
Shiruu Khadija ta yi kafin tace”yanzu kenan ta tabbata Daddy zargin na yake yi?”
“Ba zarginki yake yi ba Khadija masifar kishi ne kawai, ke dai ki yi ta addu’a, sannan kamar yadda kika fad’a wata rana sai labari..
Ki yi ta sallar dare kina gayawa Ubangiji, na san kina yi amma ki k’ara,jikina yana bani inshaaAllah yana dawowa daga Abuja za ku shirya komai ya zama labari…”

A hankali Khadija tace”Au ya tafi?”.
Jinjina kai Mommy ta yi kafin tace”bai yi miki sallama ba?”
Sai kuma ta kawar da zancen tace”bari in je in had’o y’an kud’ad’e in bawa mallan lawal, Yaron yana bani tausayi wallahi, bashi da kowa fa maraya ne gaba da baya.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e ta bar mata Yassir ta nufi k’ofa tana cewa “bari na je na d’auko.”
Daga haka ta fice….

Tana fita itama ta mik’e ta nufi bedroom d’inta da Yassir a hannunta…wajen ajjiye kud’ad’e ta d’aga ta zaro masu nauyi da niyyar idan Mommy ta dawo ta bata tace ta bawa mallan lawal d’in, dan ko ba komai shima maraya ne kamarta kuma saboda ita a ka koresa….tana d’aukowa ta jiyo kenan suka yi ido biyu da shi, da farko tsoro ya bata saboda ta san mallan lawal d’in da ta sani ko giyar wake ya sha bai Isa shigo mata har cikin bedroom ba, ganin yana magana yana matsota ne ya sa ta fahimci tabbas fa shi d’in ne dan haka cikin tsoron gudun a gansu fushi da hargowa ta fara ce masa”ya fice mata daga d’aki”
Ba tare da b’ata lokaci ba.
Gadan-gadan ta ga ya nufo ta
daga haka bata sake tuna komai ba…sai farkawar da ta yi
wadda ta ji inama da ba ta farka ɗin ba inama wucewa lahira kawai ta yi da ya fiye mata kwanciyar hankali.
Daga ita sai under skirta kwance a gado d’aya lullub’e cikin bargo d’aya da mallan lawal wanda shima wando ne kawai a jikinsa yana kwance yana sharar baccinsa peacefully.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”
Ta shiga ambato ba k’ak’k’autawa, tana jin wani irin bak’in ciki da tashin hankalin da bata tab’a jin kwatankwacin irin sa ba.
Tashi d’aya ta fashe da kuka, ta fara k’ok’arin tashi amma sai ta kasa motsi kwata kwata saboda wani masifaffen tashin hankalin da ya sake mamaye ta sakamokon muryar Daddy da ta ji a parlournta yana cewa”har fa na kama hanya kuka saka ni na dawo saboda takardun! ke da kika gansu a hannun Yarinya ai kamata ya yi ki amshe ki kawo mini.”
Cikin kwantar da murya ta ji muryar Mommy tana cewa”to ai Daddy ban yi tunanin naka bane, ni na d’auka na Maman nata ne da na ga ta yo
nan d’in da su,ba dan yanzun ka gaya mini kalar envelope d’in ba ma da yanayinta da ba ganewa zan yi ba….”

A hankali Khadija ta koma ta kwanta ta ja bargon ta lumshe idanuwanta kawai, saboda ta san no way out, dan a halin da ake ciki ma key ta ji Daddy yana murzawa ta waje zai bud’e k’ofar ya shigo yana cewa”yau kuma Khadija rufe kanta ta yi ta ciki kenan!Allah ya kyauta!”.Gashi ba ta ga makulli a jikin k’ofartata ta ciki ba.
Chapter 93 · 0% Book details