← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 152

Sashe 61

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa ya yi da kyau kafin yace
“Tun ba yau ba? Kenan tun ba yau ba kuke waya kake zuwa???”
Bai basa damar cewa komai ba yace
“Am Musbahu…
ba zan baka goyon baya ba, sannan ba zan hanaka ba.
Gwargwadon shaƙuwarmu da kuma sanin da na yi maka ni dai na san kanada hankali da sanin abunda ya kamata, dan haka ka yi
duk abunda ka ga dama.”
Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice kai tsaye ya wuce cikin gida, ya bar Ya Musbah a nan zaune shi kad’ai.

Ya jima sosai a cikin motar, tukunna ya zare makullin ya rufe motar shima ya nufi cikin gidan.

A zaune ya same shi suna raha wasa da dariya shi da su Inna,
yana shigowa Ya Nafi’u ya mik’e ya yi wa su Inna sallama suka wuce shi da iyalinsa…ko ba a fad’a ba tashi d’aya za a fahimci Ya Nafi’u haushin Ya Musbah yakeji, shiyasa dukkan su suka shiga al’ajabi dan abu ne wanda bai tab’a faruwa ba.

Su Ya Nafiun suna fita Baba ya kalli Ya Musbah yace
“Tashi ka bi sa ku sasanta.”
Zai yi magana yace
“Jeka”
Saboda dama shi tunda aka ce masa suna waje suna magana ya san akwai wani abun, yanzu kuma da ya ga hakan sai ya fahimci tabbas sab’ani suka samu…wataƙila ma shiyasa kwana biyu yake ta ganin Musbahun a cikin damuwa…

Ba su jima da fita ba Baba ma ya mik’e ya fita bayan an tabbatar masa da cewa ‘su Manubiya suna lafiya’
daganan Muhsin yace “bara ya je d’akin su” Jidda kuma ta tafi raka Siyama…
Suna fita Siyama tace “ni kam ina ma ace Ammi za ta
hak’ura wallahi…kinga d’azu fa dakyar ya iya jan motarsa ya shiga gida!
Ko ba ki lura da shi a time d’in da muke shirin shigowa gida ba?, lokacin shima yana k’okarin shiga gida.
Kinga yadda ya rame kuwa a cikin kwana hud’u gask…..”

Kukan da Jidda ta fashe mata da shi ne yasanya Siyaman yin shiru, kafin da sauri tace “Innalillahi, yi hak’uri Jidda, mai ya yi zafi??”

Cikin kuka tace
‘’Siyama dan Allah ki daina min maganar Ya Al‘Ameen, dan Allah!
Kin san Amminsa ba za ta tab’a amincewa ba, ko ta amince ma su Ya Musbah suma yadda suka zuciya na san ba za su bada goyon baya ba.
Ki daina yi min zancen sa ki taimaka min in samu in fitar da shi a raina dan Allah.”

Shiruu Siyama ta yi tana mai jin tausayinta yana sake rufeta…
rana d’aya tak ta d’an samu moment da Najeeb ta kuma fahimci k’udirin sa a kanta amman ba k’aramin Namijin k’ok’ari take yi wajen dannawa calls d’insa reject ba.
Shiyasa ta ke ganin k’ok’arin Jidda na hak’ura da Al’ameen da ta yi bayan shekaru wajen hud’u da suka yi a tare suna soyayya kawai yanzu tashi d’aya an raba su, tabbas abun da ciwo.

Rarrashin ta ta shiga yi tare da bata baki….dakyar Jiddan ta d’an dawo dai dai dan a kwana biyun nan ita kad’ai tasan halin da take ciki..kwanakin baya ta ji haushi ta ji takaici amman kuma tunda ta gansa gaba d’aya sai ta ji ta yafe masa.
Kuma tabbas a yadda ta ga ya yi ta san yana da uzuri sannan uzurin nasa mai k’arfi ne…so take kawai ta ji ta Bakin nasa, bayan nan ta yafe masa sannan ta mantar da komai daga nan ta kasance a tare da shi!!!….

Tana wannan tunanin suka fara takawa towards wajen su Siyama, kowa ta yi shiru da abunda yake damunta a haka suka k’arasa…Siyama ta zaro makulli daga jakarta ta bud’e
Parlourn, dan maman nata
bata nan ta tafi gidan suna.

Suna shiga ko gama zama ba su yi ba
Siyama tace
“Kina ganin mu kira Manu mu yi magana, ko mu je gidanta bayan kwana biyu?”

Shiruu Jidda ta yi kafin tace
“Sai dai zuwa anjima mu kirata, dan kinsan tafiya za su yi tace jibi ne da asuba.
Amman zakice na gaya miki dangin mijin nan nata ne suka sakata kuka babu ruwan Ya Yash,
kinga yadda jikinsa yayi sanyi
ai, ba laifin sa bane.”

A hankali Siyama ta nemi guri ta zauna sannan tace
“Ina fatan ya zamana su ɗin ne, dan ba na so su fara samun matsala da shi. Allah dai ya sa ta gaya mana.”

Cike da tabbatarwa Jidda tace “za ta fad’a inshaaAllah..idan na bayar da shawara ne sai mu bata, idan kuma munga ya fi k’arfin mu sai mu sanar da su Innaa, dan ba zai yiu mu zuba ido ba…kwata-kwata fa yau ne ta yi 4 days a gidan.”

Ahankali Siyama tace
“InshaaAllah ma k’aramin abu ne, Allah ya sa ba wani babban issue bane ba.”
..
Ya Musbah yana fita daidai motar su Nafi’u tana tashi, sarai ya san ya gan sa amman haka nan ya murza giya ya ja sukayi gaba.
Shiruu ya yi kawai ya fad’a duniyar tunani a hankali ya nemi guri ya zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan, ya buga uban tagumi…Bai tab’a samun matsala da Nafi’u ba tunda yake sai a kan Baraka, shiyasa ya ke jin tsoron tunkarar su Baba ma da maganar dan ya san suma akwai matsala,
shi kuma a yadda yake jin Baraka in har aka hana shi ya maida ita to tabbas akwai matsala Babba…..
Ya jima sosai yana tunani a wajen, ya ga motar Yashjub ta yi parking a daidai k’ofar gidan.
Dama tunda suka nufo sa ya gane su dan haka ya d’an k’urawa motar ido kafin ya mik’e tsaye bayan sun gama parking d’in.

Murmushi ya yi ganin yadda Manubiya ta fito har tana d’an tuntub’e, shi kuma Yash d’in yana cewa ‘ta yi a hankalin’
yana mai zagayawa da sauri inda take.

Yana gani Yadira ta bud’e k’ofa ta fito, dan haka ya d’auke Kai ya maida hankalinsa ga Yashjub yana mai ce masa “Ashe kuna tafe, barka da zuwa, mu shiga daga ciki mana”
murmushi Yashjub ya yi yana mai jin dad’in yadda Ya Musbah ya amshesa sam bai rik’e kukan da ya baro Manubiya tanayi a rai ba.
Cikin jin dad’i ya cewa Ya Musbah “ya gajiyar ku”

“Alhamdulillah”
yace, kafin cikin yanayin sigar zolaya ya cewa Yash ɗin ”A k’aida fa sai Mace ta yi watanni uku tukunna take zuwa ganin gida, daganan kuma ita da ta dawo sai ta haihu”
Wani kallo Manubiya ta yi masa kamar za ta yi kuka,
sai kuma ta fara bubbuga k’afa tana cewa “dan Allah kar ka fad’a ya ji, Allah ba zai d’auka da wasa kake ba”

Da sauri ya tsare gida yace
“Au ke a naki tunanin wasa ne?”
Sai kuma ya kalli Yash yace
“Dagaske Yash ba a zuwa sai bayan watanni uku”

Jinjina Kai Yashjub ya yi, sannan shima cikin tsare gida yace
‘’ai ban sani ba, yanzu kam mun riga mun zo dama kuma shima saboda za mu yi tafiya ne shine muka zo yi muku sallama, amman daga wannan zuwan kam inaga sai in ta haihu d’in kenan’’

Kan Ya Musbah Manubiya ta yi ta na cewa”Allah bana so ka daina”
Ganin ta na shirin fara kuka ne yasa duk suka saka dariya wanda hakan ne ya sanya ta fahimci zolayar ce dan haka ta koma gefe ta chuno Baki gaba.
Murmushi Ya Musbah ya yi yace”yi hkr mana”ya fad’i hakan kamar yana rarrashin wata y’ar Yarinya.
Yadda ya yi d’in ne ya sanya murmushi sub’uce mata ba tare da ta shirya ba.
Daganan ita da Yadira wadda ko kallo Ya Musbah bai isheta ba balle ta gaida shi sukayi cikin gidan, Ya Musbah da Yashjub kuma suka nufi masallaci…ba ya son case ko ta kawo masa raini a gaban mutane shiyasa kawai ya rabu da Yadira, yana addu’a a cikin ransa Allah ya sa in sun shiga ta gaida su Inna, a d’ayan b’angare na zuciyarsa kuma yana mamakin ta yadda Daddy ya kasa gani da fahimtar how wrong and rude behavior d’insu Yadira yake.

A fanfon masallacin sukayi alwallah duk da masallacin yanada matuk’ar kyau amma yana alwallar yana aiyyana yadda zai sake gyara masallacin duk da inshaaAllah ya san su Baba sun kusan tashi dan ya gama siya masu gida amman yanaso kawai ya gyara masallacin saboda yana daga cikin tarihin rayuwarsa.

Ba su dad’e da shiga ba Baba ya shigo kusan a tare shi da su Baba Habu….
Da mutuntawa Yashjub ya gaida su, ba yabo ba fallasa suka amsa shi, daga haka suka koma gefe shi kuma da shi da Baba suka d’an gaisa sama sama suma dan ba su wani tsananta magana ba sakamokon a masallaci suke kuma Allah ya taimakesu babu Kaka Mallan wanda kwana biyu yake fama da zazzab’i da sai gaisuwar ta fi haka.
Cikin nutsuwa aka gabatar da sallar Magrib d’in
Ko da aka idar bayan an gama gaishe gaishe.
Yashjub a masallacin ya zauna dan yana son ya yiwa Ya Musbah magana…..

Sam bai ji dad’in yadda Ya Musbah shima ya k’i amincewa da maganar tashin nasu ba, dan kamar yadda Manubiya ta ƙi yarda ya chanja musu gida hakanan shima Ya Musbahn ya ƙi amincewa bayan Yash ɗin ya gaya masa, amman dai ya ce zai sanar da su Innaa su saka masa albarka but ya san suma bazasu tab’a yarda ba.

Sun jima suna kai ruwa rana kafin daga baya Yashjub ya hak’ura kawai, ya rabu da shi, ba wai dan ya hak’ura ba sai dan ya basa lokaci ne ya yi nazari kafin ya sake zuwa masa da zancen.
Chapter 61 · 0% Book details