Sashe 83
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Daddy ka yi shiru”
D’in da tace ne ya katse masa tunani…
A hankali yace”yanzunnan ya rasu”
Wata zabura ta yi tace”innalillahi wa inna ilaihirrajiun,
Daddy dama chan bai rasu ba??me ya faru?kiranka ya yi?”.
Ta fad’i hakan ita kanta ba ma ta san ta fad’a ɗin ba tsabar rashin sanin tudun dafawa, tsoro take yi kar ta yi shiru ya zargeta shiyasa ta zab’i ta yi duk maganar da ta zo mata.
Wani kalar mahaukacin bugawa zuciyar Daddy ta yi, dan tabbas Mommy ta k’ulle kanta da kanta..ta ya aka yi ta san kiransa ya yi?
Jinjina mata Kai ya yi kawai, yana mai jin kamar ya shak’e ta ya kashe ta a take a wajen, da kyar ya iya cewa”kira na ya yi, ya ce in yafe masa, yana buk’atar gani na da gaggawa.”
Zuwa yanzu yadda Mommy ta fara gumi ya gama tabbatar masa da komai, dama abunda ya zo tabbatarwa d’in kenan shiyasa ya zo mata a haka, cikin son sake ganin reaction d’inta (yadda za ta yi) yace”tun lokacin da ya kira ni ya fara magana gaba d’aya hankalina ya karkarta ne a kan watak’ilan Khadija (Amarya) itama tana raye.”
A take ya ga idanuwanta sun fara ciccikowa da hawaye kamar za ta yi kuka…da kyar Bakinta yana wani irin karkarwa ta samu tace”Noo Daddy, it can’t be(hakan ba zai yiu ba ai), idan shi ya rayu ita ba zai yiu ta yi rai ba, ko ka manta yadda ita d’in da hannunka fa ka c….”
Yadda taga idanuwansa sun yi jaaa a take ne ya sa ta had’iye maganarta ta sunkuyar da kanta,kafin da kyar ta sake d’agowa tace”amma ban sani ba, sai dai mu fara bincikenta,watak’il itanma she made it out alive(ta samu ta fita da ranta)..saboda ka san dama na gaya maka wajen yadda ya koma ba mu iya detecting(gane) ko da biro ba ballantana gawa, dan komai ya kone k’urmus, ruwa kawai muka yayyafa aka yi musu salla a haka…..”
Wuff kawai ta ga ya juya ya fita, zuciyarsa ta na wani irin tafarfasa dan ya san tabbas idan ya ci gaba da zama to zai iya aikata abun ban mamaki ga Mommy…Mommy ta yi masa abubuwa daban-daban tun daga kan yadda ta tilasta masa aurenta har kawo yanzu, kullum a cikin b’acin ranta ya ke, amma bai tab’a tunanin za ta iya aikata hakan ba, sannan gashi still k’ok’arin b’oyewa take yi ya san ba zata taɓafaɗin gaskiya ba!!!
amma shi ya san ta yadda zai kamata dumu-dumu! Ta yadda zai k’ulleta da jijiyoyin jikinta, ya tona mata aisiri kowa ya ganta…hacking wayarta kawai zai yi ta yadda ko typing take yi sai ya gani.
A nan ne kawai zai ji komai da take yi, ya kuma ga komai sannan ya kamata dumu-dumu…ya tabbatar da zarginsa a kanta.
He really can’t believe this!he can’t believe (kansa ya kasa ɗauka! Sam ya kasa yarda da cewa) ‘Mommy ta saka shi ya kashe Khadijah da hannunsa, ba tare da laifin ta ba’
dan kamar yadda ita ma Mommyn ta ce yanzun ‘idan mallan lawal ya samu ya fita da ransa to ita Khadijah ba ta Isa ta fita da rai ba, ba za ta iya ba.’
Tabbas hukuncin kisan kai ya yi wa Mommyn sauƙi…shi kansa yana jin tsoron abunda zai yi mata, Wallahi.
…….
Kasancewar Yassir a napep ya taho ya sanya sai yanzu ya samu ya shigo cikin gidan…..
Yana zuwa a fusace ya haye sama ya nufi d’akin Kausar,zuciyarsa tana wani irin tafarfasa.
Kausar ta na wani kalar kuka haka nan ta shiga d’akinta ta fad’a kan gado…..ta yi kuka a wannan rana kamar ranta zai fita kafin ta mik’e ta fad’a toilet ta shiga wanke fuskarta a ranta kuwa ta gama aiyyanawa “wallahi,
daga yau!! itama ta kanta za ta yi, farin cikinta kawai za ta duba! Kowa ya yi ta kansa….inshaaAllah sai ta mallaki Yashjub ko ta halin yaya ne, daga nan za ta nunawa Mommy wacece Kausar, sai ta san ta yi betraying d’inta, wallahi daga kanta ko d’an aiki ba za ta sake cin amanarsa ba.”
Tana wannan lissafin ta fito daga toilet d’in…a d’akin ta tarar da Yasira, cikin rashin kwarin jiki Yassirar ta mik’e ta k’arasa ta ruko hannunta kafin tace “Kausar na zo ne akan in yi miki gargad’in ki bi Yassir a hankali, kar ki bari ya fahimci wani abun, saboda gudun kar yaje ya yi miki kwab’a.
Dan yadda ya yi miki d’azu a asibiti ni kaina na d’an tsorata gaskiya”
da “to” kawai Kausar ɗin ta bi ta, daganan Yasirar ta juya ta fita dan ta fahimci kamar Kausar d’in ta na buk’atar sarari.
Tana fita Kausar ta girgiza kai a ranta tace’’kwab’a kuma ta nawa?bayan abunda ya aikata,’’
wannan shine karo na biyu da ya so ya kashe Yashjub kuma ta lura Mommy ma ta fahimci wani abun amma ta ga kamar k’ok’ari ma take yi ta b’oye…
A hankali tana jin kanta yana wani irin mahaukacin sarawa
ta nemi guri ta kwanta.
Lumshe idanuwanta ta yi
atake hawaye suka shiga sintiri a kan farar fuskarta!!!
Wannan wacce irin rana ce ta risketa?…ga ciki tana d’auke da shi, ga Mommy wadda ta juya mata baya ga kuma Yassir wanda take zargi da wannan
shirmen a karo na biyu,
sannan bata Isa ta tunkare sa da maganar ba, dan ba ta so ya
fahimci wani abun…
Sannan ga rayuwar Yashjub dake a cikin hatsari, ga Manubiya, ga shi Yashjub d’in ma kansa har yanzu ta kasa samun sa!
ta Ina za ta fara ne? dan abubuwan sun yi mata yawa…..
K’arar bud’e k’ofar d’akin nata ta ji da mugun k’arfi, dan haka ta tashi a d’an rikice duk da kuwa da ma ta riga ta san waye ne.
A tsaye a bakin k’ofar ta gansa yana huci, kafin ya juya ya rufe k’ofar ya murza key tukunna ya nufota gadan-gadan…
Duk tsaurin idon Kausar sai da ta tsorata, dan haka tun kafin ya k’araso ta mik’e tsaye tana mai gyara doguwar rigar jikinta ta hau inda inda cikin in’ina tace’’Yassir I’m sick dan Allah ka bar….’’
Mahaukacin marin da ya d’auke ta da shi ne ya sanya ta gagara k’arasa maganar tata, sai da numfashinta ya d’auke na y’an seconds tsabar tsananin shock d’in da ta shiga, a rikice ta d’ago fuskarta wadda ta yi jajir sannan ga shatin y’an yatsunsa sun fito rad’o rad’o a fuskar tata tace ‘’Yassir ni ka mara??’’
Cikin karsashi yace‘’somin taɓi ne ma wannan ɗin, kar ki damu, in kinga dama ki bari in yi miki tambaya ki yi mini k’arya…’’
Ya fad’i hakan yana mai kunce belt d’in wandonsa.
Cikin fushi tace “dukana za ka yi?baka da hankali ne? Duk abubuwan da ka yi basu ishe ka ba???’’
Dakatawa ya yi daga nad’e k’asan belt d’in da ya ke yi around his fingers, kafin ya d’ago jajayen idanuwansa ya zuba su akanta tukunna yace ‘’abubuwan da na yi?me da me na yi kenan?’’
Ya fad’i hakan cikin matsowa daff da ita yana mai tsare ta da dara daran idanuwansa waenda suka yi jaaa!!! hatta fuskarsa ta yi jaa tsabar bala’i.
Ahankali ta d’an ja da baya dan a mugun tsorace take dashi!
Sai da ta d’an kauda kanta gefe tukunna ta yi k’asa da murya tace’’ Wallahi zan tona maka asiri,in har ka tab’a lafiyata sai kowa ya san kai ne ka tura y’an fashi estate d’in Yashjub yau’’
Cak!haka ya k’ame, kafin ya sa Hannu ya juyo da fuskarta cikin karsashi yace ‘’Kausar ni za ki yi wa sharri da borin kunya saboda kinga na kama ki dumu-dumu?’’
Ganin yadda jikinsa ya yi sanyi kuma ta ga ta d’an samu galaba a kansa ne yasanya ta fincike fuskarta tace’’ba iya wannan ba ma, Wallahi har tayar motarsa da ka cire kwanakin baya sai na fad’a kowa ya ji, tunda dama son da nake yi maka ne yasanya nake rufa maka asiri amma in har zaka iya d’aga Hannu ka mareni to na san ka daina sona dan haka nima ban ga amfanin ci gaba da son ka Ina bin bayanka ba,’’
Ta fad’i hakan tana mai rushewa da wani uban kuka wanda yayi tsananin tasiri akan Yassir.
Ganin kamar so take ta bugi cikinsa sannan kamar wayo take so ta yi masa ne yasanya ya dake yace’’ke!Kausar bana son hauka da shirme da sharri…idan ba so kike in yi miki fiye da abunda na yi niyyar yi ba to kawai ki bani amsoshina da na zo k’arba, mu yi ta ta k’are.
‘’How dare you! Ta ya ma za ki k’ala mini sharri wani wai ni Ina so in kashe Yashjub! baki da hankali ne?kuma wa kike tunanin za ki gayawa wannan maganar ya yarda?. bari ki ji ko Mommy idan kika gayawa wallahi ba za ta tab’a yarda da ke ba, za ki sha mamaki idan ta juya miki baya har abada, dan babu uwar da za ta yarda wata tazo ta ce mata d’anta yanaso ya kashe d’anta!’’.
Goge hawaye Kausar ta yi ta d’ago ta fuskance sa tukunna tace’’Yassir cewa na yi ‘zan fad’awa kowa kaine ka cire tayar mota sannan zan fad’awa kowa kaine ka tura ƴan fashi estate d’in Yashjub’.
A kaff cikin maganata ka ji ta inda nace ‘kana so ka kashe Yashjub’?’’.
Cikin fushi hargagi da hargowa yace’’Kausar zan illataki fa! ni za ki yi wa wasa da tunani? ai indai aka ji kince na cire taya to an san kashe sa nake son yi kenan!’’
Tsit!haka muryarsa ta tsaya chak!yana mai recalculating (son fahimtar) abunda ya gama faɗa yanzun a cikin kwakwalwarsa’’
Kafin ya yi cilli da belt d’in hannunsa tukunna ya d’aga hannu kamar zai damk’i wuyanta, kamar kuma wanda ya tuna wani abun sai ya tsaya chak!! kafin ya juya mata baya yana wani irin huci kamar mayuncin zaki….