Sashe 107
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba k’aramin dad’i Hajiya Mama ta ji ba da ta ga Yashjub ɗin ya zo, haka itama Siyama…saboda dama tana ta addu’a Akan Allah ya sa ba fushi ya yi ko ya k’ullaci Manu ba.Ta san dole da zafi shiyasa ta d’aga masa k’afa ya d’an huce gudun kar ta yi magana ta jagula abun, hakanan ta yi ta addu’a sai gashi kuwa yanzu ya zo…..
Shi ya tarar da su Hajiya Maman, su Ummi kuwa ba su same su ba iyaka Yashjub d’in suka tarar.
Suna zaune, Manubiya a kan gado shi kuma a gefenta ya rik’e hannunta ya sunkuyar da kansa k’asa, ita kuma tana video call da Jiddah wadda Manubiyan ta ji matuk’ar dad’in ganin yadda k’anwar tata ta yi k’iba ta yi fresh a cikin kwanaki k’alilan, alamun Hankalinta a kwance yake.
Yadda su Ummi suka ga walwala da murmushi a kan fuskarta ya sa suka fahimci ba ta ji komai ba, tukunna.
Gaisawa suka yi da Yash, daga haka ya mik’e ya k’arasa ya shiga had’a mata Breakfast, Yayinda ita kuma suka yi sallama daJidda bayan Jiddan sun gaisa da su Yaha, Manu ta ajjiye wayar suka shiga gaisawa da su Ummi.
Yana gamawa ya k’arasa ya ajjiye mata abincin, sannan ya fara k’ok’arin bata…
Cikin nutsuwarta tace masa”ai Likita yace akwai allurar da zai yi mata kafin ta ci abinci”
“Okay”kawai Yash yace, ya d’an yi mata murmushi, kafin ya mik’e ya fita domin kiran Doctor d’in.
Yana fita Yaha ta zauna a wajen da ya tashi tace”MashaaAllah, Jidda ta yi fresh abunta,Al’ameen ya iya kiwo”
Dariya duk suka yi har Ummi, kafin Manubiya ta kalli Yahanasu tace”Adda Yaha akwai abunda yake damunsa ne bayaga al’amarin da ya faru da ni? Na ga yanayinsa gaba d’aya ya sauya.”
Shiruu Yahanasun ta yi ta d’an k’ura mata ido kafin tace”za mu yi magana anjima,ki kwantar da hankalinki”
Daga haka ta yi sauri ta mik’e ta fice, ba itace Yashjub ba amma yunk’urin sanar da Manu da ta yi kad’ai a yanzu tashi d’aya k’irjinta ya fara dukan uku-uku.
Kusan karo suka yi da shi, dan tana fita shi kuma yana shirin yin knocking.
“Ina Doctor?”
Ta tambayesa.
“Yace yana zuwa”
Ya bata amsa yana kallonta.
Ajiyar zuciya Yahanasu ta sauk’e kafin tace”Yash Inaga gara mu bari ta warke garau, tukunna mu sanar da ita, sannan har ga Allah bana so in yi lalata walwalar da na gani a kan fuskarta.”
Jinjina kai ya yi kafin yace”abunda nima nake tunani kenan, da na shigo d’azu ta yi matuƙar farin cikin ganina, dan har kasa ɓoye murnarta ma ta yi a gaban kowa…
Ba na jin nima ɗin zan iya lalata farin cikin da nake gani a kan fuskarta, ba zan iya fad’a mata ba Wallahi, shiyasa dama kema tun ɗazun na shirya akan zan ce miki ki yi shiru, to Alhamdulillah tunda tunanin mu ya zo d’aya.
Dan haka Mu bari mu koma gida inyaso sai a san abunyi, dan tabbas kam ba zan b’oye mata har abada ba.”
Yahanasu ta bud’e baki za ta yi magana kenan suka jiyo k’arar fad’uwa sai kuma salatin Ummi…kafin ta fara cewa”Yashjub Yahanasu kuna Ina Ina likitan?!”
dai dai ta bud’e k’ofa za ta fito a gigice suka yi kicib’is da su, dan haka ta juya ta koma ita a tunaninta ma tare suke da likitan…
A rikice suma duk suka yi kan Manubiya wadda ke zube a k’asa yashe a tsakar d’akin…
Kasa tab’ata Yashjub ya yi, tsabar tashin hankali da tsoro!!!
a mugun rikice ya rarumo gorar ruwa ya shiga shafa mata a hankali da hannunsa wanda ya ke wani irin karkarwa…ganin ta k’i motsi ne ya sa ya mik’e a gigice ya nufi k’ofar da niyyar sake kiran Likitan amma sai suka yi karo da shi….ba ma ya iya cewa komai dan ya kasa, kawai Manubiyan yake nunawa Doctor d’in hankali a mugun tashe…da hanzari shima Doctor d’in ya k’arasa gareta…
da taimakon Yahanasu suka kinkimeta suka d’aurata a kan gadon ya shiga bata taimakon gaggawa…Yashjub kam ya ma kasa motsi ko magana, hawayen ma sun k’afe, in banda karkarwa babu abunda ilahirin jikinsa yake yi musamman ma k’afafuwansa,
dan har zuwa wannan lokacin ba ta farfad’oba!
Luu haka ya tafi zai fad’i a wajen, da kyar ya rik’e kansa, ya samu ya zauna a kan kujerar bayansa yana ganin bibbiyu.
An kai ruwa rana kafin da kyar aka samu ta farfad’o….ruwa Dr ya sake jona mata ya fita ya je ya kwaso wasu allurai ya yi mata har da ta barci…Sai da bacci ya yi awon gaba da ita tukunna ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya ya juyo ya kallesu yace da Ummi”jiya jiya na gama ja muku kunne akan d’aga mata hankali ko?za fa ku ja wa yarinyar nan stroke da k’arancin shekarunta idan ba ku yi wasa ba!,jininta maimaikon ya sauk’a hawa yake kuma yi, ku kiyaye fa!.”
Cikin d’aurewar kai Ummi tace”lafiya fa muke zaune da ita muna magana,na ga ta fara duba wayarta , sai kuma na ga ta mik’e to daga haka ne ta tafi ta fad’i a k’asa.”
Numfashi ya fesar kafin yace “idan ta farka ku kira ni, Allah ya rufa asiri”kawai,
Daga haka ya sa kai ya fice.
Shiruu duk suka yi suka zubawa Manubiya ido, kafin Yash ya mik’e da kyar ya k’arasa ya d’auki wayar tata wadda har zuwa wannan lokacin take a k’asan gado inda ya ga ta fad’a ,matsawa Yahanasu ta yi saboda itaama wayar tata take shirin dubawa….
Yana bud’ewa ya ci karo da sms daga bak’uwar number ta inda aka sanarwa Manubiya abunda ya faru jiya tsakaninsa da Kausar tiryan tiryan tun daga farko har k’arshe….
Jifa ya yi da wayar cikin fushi yace”enough is enough!!!”
Sannan ya fara k’ok’arin fita.
Da sauri Ummi da Yahansu suka tare sa, dukda Ummi ba ta ga message d’inba amma itama zuwa yanzu kwakwalwarta ta bata me ya gani.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka iya tsayar da shi, dan ya zuciya matuk’a, ransa ya b’aci….
Cikin muryar fushi yace”Ummi ki barni in je in same su komai ma ya ishe ni,Wallahi sai na sauya musu kamanni tunda basu san dai dai ba!”
Cikin rarrashi tace”Yash wa za ka tunkara? Me za ka yi musu?”
Ba tare da sanin inda ya dosa ba ma yace”na san a tsakanin su Yadira so
just let me…..”
Hawayen da suka shiga zubo masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana, sai kuma ya nemi guri ya zauna ya dafe kansa
A ransa ya shiga aiyyana “me na yi musu da zafi har haka?me yasa y’an uwana suka tsaneni suka tsani farin ciki na?”
Sai da Ummi ta share hawayen da suka zubo mata itama, tukunna ta k’arasa gefensa kan sofar ta zauna, cikin sanyin murya tace”kar ka ce haka Yashjub,ba ka ta tabbaci…”
Cikin katseta yace”Ummi su ne!idan ba su ba wa ya san maganar in ba y’an gidanmu ba?yaushe aka haifi Yaran nan da za su zama mugaye makirai kamar haka?me na tab’a yi musu da za su yi mini haka?”
Shiruu Ummi ta yi dan ta ma rasa bakin magana.Ahankali Yahanasu ta matso tace”Kamar yadda Ummi ta fad’a Yash ba lallai su ɗin bane ba,ka bi komai a hankali kamar yadda na gaya maka jiya…”
Dan ta san ko da ace su d’in ne to Mommy ce ta zuga su suka aikata kamar kullum, amma kuma still ba ta jin a tsakaninsun ne, ita ta fi tunanin Mommyn ce da kanta ta aikata wannan d’anyen aikin.
Itama cikin katseta ya mik’e yace”Yaha to
waye idan ba su ba?Daddy wanda ya haifeni?ko kece?ko Ummi?ko kuma Mommy?….”
Shiruuu ya yi, kafin a hankali ya sunkuyar da kansa k’asa yace”damn it!!”
Sai kuma ya koma ya zauna ya yi shiruuu kawai.
Kasa ci gaba da zama a d’akin Ummi ta yi, dan ba ta san ta Ina za ta fara ba..ba ta so tana shigar musu Irin wannan case d’in.
Shiyasa ta kalli Yahanasu ta ce”bari in je, Allah ya rufa asiri,Yash k’addara kowa da kalar tasa, ka yi k’ok’ari ka cinye jarabawarka.”
Daga haka ta d’au Jakarta ta fice…ba ta da tantama wannan aikin Mommy ne.
Tana fita yace”ki je kema,idan ta tashi zan ji da ita,I can face her(zan iya fuskantarta)…”
Cikin tausayawa tace”Yash ka yi hak’uri”
Wani kalar murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi kafin yace”Yaha hak’urin nake yi a ko da yaushe, amma wani abun dole aga rauni na!…tunda nake a rayuwata ban tab’a jin labarin uwa irin Mommy ba,bani da tabbaci tukunna Akan abubuwan da ta yi mini, sannan ta saka su Yasira suka yi mini amma Yahansu tashin hankalin da nake a ciki ba kad’an bane ba, saboda Ina jin tsoron ranar da zargina zai tabbata Yaha ban san ya zan yi ba.
Ina jin tsoro in ji sunada hannu a case d’in estate d’ina!
Ina jin tsoro in ji sune suka yi chatting da Abbakar suka bawa Manubiya magani….shiysa nake ta k’ok’arin gocewa amma message d’in nan da aka turo tabbas na san su ne wannan kam ba ni da tantama, kuma hakan ya sanya na sake yarda sune suke yi mini abubuwan da na kasa fahimtar ribar su idan sun tarwatsa ni!”
Ya fad’i hakan yana mai sakin hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa,
rungumesa Yahanasu ta yi, itama a take wani irin kuka ya kufce mata…Tabbas ta san zafin da Yashjub ya ke ji a yanzu da ya fahimci Mahaifiyarsa ba ta son sa, sannan ba ta damu da shi ba, kuma ba ta damu da farin cikinsa ba! saboda itama ta fuskanci wannan kalubalen kuma har gobe tana rayuwa ne a cikin azabar raɗaɗinsa….