← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 152

Sashe 120

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali jikinta da kwakwalwa da zuciyarta har yanzu suna kan karb’ar azaba tace”a yi mata adalci,na yarda ta zo nan ta zauna da mu har zuwa lokacin da za ta haihu…daga nan idan Babynta ya yi wayo zan rik’esa kamar ni na Haifa da zuciya d’aya, ba na son Kausar amma na yarda ta zo
ta zauna da mu zan jure!
zan jure komai banda kasancewar wata mace matarka Ya Yash!!!”
Ta k’arashe maganar cikin fashewa da kuka…

Wani irin sauk’i Yash ya ji, dan ya san su Daddy idan suka ji wannan shawarar da Manubiya ta bayar Hatta Mommy duk za su ji sauk’i suma kuma an yiwa Kausar ɗin adalci tunda har za ta zauna a gidansa ya d’auki d’awainiyar ta har ta haihu ai kuwa an yi adalci, kuma itama Kausar d’in ya san tunda ba ta riga ta san su Daddy suna shirin had’asu aure ba tsaff za ta yarda da shawarar Manubiya….ko dan ta zo ta zauna gida d’aya da shi.
ya san za ta so ta yi abubuwa da dama idan ta zo d’in amma InshaaAllah shi kuma ba zai bata fuska ba, kuma zai taka mata burki, ba zai bata dama ba.

Cikin samun sauk’I ta b’angaren case d’in Kausar ya sake rungumo Manu ya sumbaci goshinta sannan ya share hawayenta tukunna yace”inshaaAllah ke kad’ai ce mace d’aya tak
Matar Yashjub,inshaaAllah.”

Ajiyar zuciya ta shiga sauk’ewa kafin ta d’aura kanta a k’irjnsa ta yi shiruuu.
Dukda tana jin tsananin tashin hankali idan ta tuna Kausar tana d’auke da ciki amma ba
ta kishi da Yaro ko
Yarinyar da za ta haifa tunda ba laifin sa/ta bane ba,InshaaAllah zata rik’e da zuciya d’aya dan ba ta Isa ta tsani d’an Yash ba, ta san ba ma za ta iya ba….amma Kausar kam!wani kalar zafin kishinta ne yake azalzalar zuciyarta ji take yi kamar ta je ta sameta ta shak’eta!.

Sun jima a haka kafin ta ji yace”na san da maganar binciken da kuke yi ke da Yaha a kan case d’in estate d’ina…na gode sosai Allah ya saka muku da alkhairi, na ji dad’i matuk’a da na ji batun kuma na yi farin ciki amma daga yau ku dakatar da komai ku daina.”
Ya k’arashe maganar muryarsa tana kakkatsewa kamar zai fashe da wani kukan.

A hankali ta d’ago ta kallesa tace”meyasa?”

“Saboda na riga na san waye”
Ya bata amsar hawaye suna masu saukk’o masa kafin ya zaro wayarsa ya shiga chat d’in ya kunna mata ya mik’a mata, ita kuma ta karb’a…
A hankali ya sa hannu biyu ya dafe kansa yana mai zubar da hawaye….da d’an sauk’i da ya kasance ba Mahifiyarsa Mommy bace ba,amma fa dukda haka masifa da tashin hankalin da ya shiga da ya fahimci Yassir ne babu sauk’i.

Tabbas dama Manubiya tunda akace insider ne (na jikinsa ne)
Yassir ta zarga a karon farko, amma dukda haka itama sai da ta shiga shock ba na wasa ba.

Kasa ma magana Mannubiya ta yi, gaba d’aya tausayin Yashjub ya rufe ta tun bama da ya fara magana cikin d’acin zuciya abun tausayi ba!”amma ni kad’ai ne mai irin d’an uwan nan ko?babu wani d’an uwa da na tab’a jin labarin ya aikata hakan ga d’an uwansa uwa d’aya uba d’aya!!babu shi.
Ji nake kamar zuciyata za ta fashe!!shiyasa fa case d’in farko na k’i yin bincike saboda in gujewa wannan tashin hankali da azabar da binciken nawa ka iya haifarwa…!!!
Abun da matuƙar azabar ciwo sannan bashi da daɗi kwata kwata, ace wai naka ne yake son ganin bayanka!
me na yi wa Yassir haka! Ya za a yi ya tsaneni to this extent??? me ya yi zafi har haka?.”

A hankali Manu ta rungumesa itama tana hawaye ta shiga shafa bayansa alamun rarrashi.
Suna zaune a haka wayarsa ta d’au k’ara!!
Sai da aka kira sau uku tukunna ya zaro wayar Da kyar! Da kyar ɗin ya iya karanta sunan Ummi tsabar masifar da yake ciki, a hankali ya amsa ya kara a kunnensa yace”Hello Ummi”
Cikin hargitsi da b’acin rai ya ji Ummin tana cewa
“Yashjub kana Ina?ka zo yanzunnan,Daddynku yanzu suka gama d’aura maka aure da Kausar.”
Kashe wayar kawai ya yi ya ajjiye a gefe ya runtse idanunsa da mugun k’arfi yana jin kansa kamar ba a jikinsa ba!

Yana cikin wannan yanayin ya ji k’arar fad’uwa…
A mugun rikice ya bud’e ido yana kallon Manubiya da ke yashe a k’asa kan kafet.
Sai da numfashinsa ya d’auke, da kyar ya dawo, a take jikinsa ya d’au wani mahaukacin karkarwa.
Tabbas ya san abunda aka fad’a ta ji dan wayar tasa tana da murya sosai!!shiyasa tashi d’aya wani sabon tsanar Kausar ya lullub’esa…haka kurum Yarinya ta bi ta d’aga musu hankali babu gaira babu dalili!!!!
bai san lokacin da ya shiga tsinewa Kausar albarka ba!.

Da hanzari ya rufarwa Manubiya…wadda sai da ya k’ura mata ido sosai tukunna ya lura Ashe ba suma ta yi ba tsabar tashin hankali ne ya sanya ta yanke jiki ta fad’i.

Shafa fuskarta ya yi a hankali ya mik’ar da ita ya rungume, ya ce”kar ki bari hakan ya d’aga miki hankali dan Allah saboda Abu ne wanda ba zan tab’a aminta da shi ba”
Daga haka ya sa hannu ya d’auki wayarsa…da kyar ya nemo number Kausar a wani group na y’an gidan nasu…
A take kuwa dan bai ɓata lokaci ba ya tura mata message daga garesa mai d’auke da saki guda biyu kwarara!
Ta watsapp da ta sms duk ya haɗa ya tura mata, da niyyar gobe da safe zai ce ya mayar da ita sannan atake ya sake sakinta, shikenan!!!
Ya san idan ya yi uku lokaci guda tsaff za a mayar masa da shi d’aya.

Lokacin da Yashjub ya yi sakin, su Kausar suna zaune ita da su Yasira suna zab’ar gado a wayartata messge d’in ya shigo, ta sama duk suka gani amma ba sosai ba dan kad’an suka gani…cikin tsananin tashin hankali Yasira ta amshe wayar ta bud’e gaba d’aya saƙon dan Kausar ta kasa bud’ewa…da kyar ta lek’a suka karanta a tare su duka…..
tashi d’aya ta zube a kan gadon ta fashe da wani irin kuka.

Salati duk sukayi, Yasira ta mik’e ta k’arasa ta nunawa su Mommy waenda suka mik’e tsaye a tare suma sakamokon salatin da suka ga suna yi da kuma kukan Kausar da rikicewar da suka ga duk sun yi.

Suna gama karantawa Mommy ta kalli Ya’isha da Yasira tace “su biyo ta” kafin ta kalli Baba larai tace”bari mu je mu dawo,incase idan Daddy ya tambayi ina ina kice na sha magani na kwanta, Idan kuma sun ji an fita sun tambaya ku ce su Yasira ne suka tafi siyowa Kausar magani…”
Tana gama fad’in haka suka saka kai suka fice su uku, ragowar kuma suka ci gaba da rarrashin Kausar.

Ya’isha ce ta biya side d’inta ta d’auko musu hijabai, dan Mommy ba ta da kuzarin wannan,daganan ta taho da makullin motarta ta mik’awa Yasira…daga haka suka sauk’a k’asan.
Dama Yasira ta san gidan Yashjub suka nufa aikuwa tana kunna motar Mommy tace mata”gidan Yashjub za mu je.”
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 39*

Lokacin da su Mommy suka isa gidan, su Yashjub suna chan sama d’akinsa, shi yana wanka Manubiya kuma tana zaune a kan sofa ta fara jiyo k’arar door bell!.

Kusan minti biyu suna a tsaye ba’a zo an bud’e ba, dan haka suka fara danna masa call ta wayar Mommy…

Wanka yake yi alokacin shiyasa Manu ta d’auko Hijab d’inta ta sauk’o.
Sai da ta lek’a ta y’ar b’ular jikin k’ofar, tukunna ta sa Hannu ta bud’e k’irjinta yana wani irin bugu dan tana ganinsu Hankalinta ya tashi zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa.

Har k’asa ta durk’usa tace”Mommy Ina wuni”
Ba tare da ta kalleta ba ta wuce kawai ta nufi sama tana mai cewa”Ya’isha duba mini k’asan ko yana nan, in baya nan ki hawo mu duba sama”.

Tana gani Ya’isha ta k’araci dube dubenta ta zo ta haye saman suka barta nan bak’in k’ofar a durk’ushe dan tun d’azu ta kasa tashi.
Da kyar ta samu ta mik’e, ta tura k’ofar ta mayar ta rufe, daga haka ta shige d’akin bak’i na nan k’asan, tana shiga ta fashe da wani irin kuka….A yadda ta ga Mommy ta zo a zuciyen nan ta san ko dai ta saka Yashjub ya mayar da Kausar, ko kuma ta sa itama a sake ta.!

Ya fito kenan d’aure da towel kawai ya ga sun shigo su duka ukun.
“Subahanallah” ya ambata, daga haka ya juya ya koma cikin closet d’in da sauri hankalinsa a tashe ransa a mugun b’ace….ita kanta Mommy yana da tabbacin ba ta tab’a ganinsa a haka ba da girmansa ballantana su Yasira,
sannan yadda ya ganta a gidansa a cikin bedroom d’insa haka ya san ba alkhairi ne ya kawo ta ba, amma fa yau sai dai duk abunda zai faru ya faru dan shima a high yake….
Yana wannan tunanin ya zura jallabiya bai zare towel d’in ba ya fito fuskarsa a mugun murtuke kamar bai tab’a dariya ba.

Idanuwansa waenda har yanzu kalarsu bai daidaita ba ya zubawa su Yasira kafin yace”ku fita ku bani guri!!!”

“Ba inda za su fita su je!!
Ai idan za a yi tsinuwa ana buk’atar wasu a wajen, saboda su bayar da sheda!!!”

Zuwa yanzu jikin Yashjub ya fara karkarwa…ya zubawa Mommy idanu kawai ya gagara cewa komai, kafin ya yi taku biyar zuwa shidda ya k’arasa ya tsaya a daff da ita har tana jin hucin numfashinsa yace”Mommy saboda na saki Kausar shine za ki tsine mini????”
Chapter 120 · 0% Book details