Sashe 145
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Aslam ya yi da mugun gaske, shima ya nuna musu k’arfin iko suka fahimci wayene shi ɗin!
Tukunna suka hak’ura bazasu tafi da Manu ba!
Dai-dai nan Hajuyar tasu (k’awar Kausar) tace”to a yi binciken sark’arta tunda an gama case d’in jariri…..
Haka kurum da Manubiya ta juya ta hangi Jakarta chan a yashe wadda bata san ya aka yi ta fad’i ba, tashi d’aya sai ta ji jikinta ya bata nan ma an gama k’ulleta ne, aikuwa ana fara bincike na jakankuna da akazo kan tata aka duba tashi d’aya akaga dankwaleliyar sarkar k’awar Kausar a ciki ta asalin ɗanyen gold…
Suna tamabaya batayi musu ba tace musu “jakarta ce”
Aslam ya san sharri aka yiwa Yarinyar, amma kuma duba da yadda mai sark’ar take influencial ya sashi kawai yin shiru, dan ya san bata da mafita, amma inshaaAllah zai san abunyi…..
Huda tana kuka kamar ranta zai fita itama Manu haka, hakanan suka kaita har office d’insu a motarsu, dan Aslam ya nemi alfarmar su bari su kaita da kansu su kuma sun yarda!
Ba wai kukan sharri ko arresting d’inta da akayi manu take yi ba…tana kukan yadda aka wuce da ita ta gaban Yash amma bai ce komai ba, bai tab’uka komai ba….
…
Babu yadda Aslam bai yi ba, amma duk inda ya zaga ya zagayo sai ya ga ba fa zai iya fitar da Manu ba, ga Hudan ta d’aga masa hankali sai kuka take yi, ko magana ma ta kasa yi duk ta gigice……
Shi kansa tausayin Manu d’in ya addabesa kunyar kallon ta ma yakeyi, shiyasa kawai yace mata “bari ya mayar da Hudan gida(dan zuwa lokacin dare ya yi sosai),
kar ta d’aga hankalinta zai san abunyi….”
Huda ta so ya barta tare da Manubiya har a san abunyi amma yace mata “A’a su tafi gidan”
Hakanan ta bata kwarin guiwa, daga haka suka fita suka tafi suka barta ita kad’ai a wajen cikin masifa tsoro da tashin hankali, dan ma a office aka ajjiye ta ba a cell ba.
Ana tafiya da Manu k’awar Kausar ta yi mata waya ta sanar da ita.
A gate su Mommy suka ajjiye Kausar suka wuce…su kansu Mommy da Kausar d’in sun sha jinin jikinsu dan yadda su Yasira suka had’e rai suka k’i kulasu ya ishi ya sanya su fahimci ba su ji dad’in abun ba….
Tana shirin shiga ita da mai aikin ta da jaririnta kawai ta ji an fincikota ta yi baya kamar zata fad’i! sai kuma ya mayar da ita ya buga mata kanta da jikin gate d’in yana huci….suna had’a ido da shi ta kalli mai aikin nata tace”wuce mini ciki da Yaro”
Sai da Yarinyar tagama shiga tukunna ta kallesa tace”Yassir!ban yi tsammanin ganinka a nan ba”
Sake matsowa daff da ita ya yi tukunna yace”na ji labarin abunda kika aikata a Yarona saboda baki san ciwon sa ba ko?
Wallahi wallahi Kausar ko da wasa kika sake yunk’urin cutar mini da ɗa ba zaki sake ganinsa ba! Mahaukaciya kawai!”
Daga haka ya sake bugata da jikin gate d’in har sai da ta yi k’ara tukunna ya juya ya wuce, dan a mugun zuciye yake dama…har yau Daddy ya ma k’i ya sauraresa, duk ya bi Abokan Daddyn ya roƙesu akan “su yi masa magana, ya yi laifi ne, a shirya su dan Allah”
amma dukda haka ko saurarensa Daddyn bai yi ba, gashi he’s broke!!! Gaba ɗayansa Bashi da kuɗi! Infact bashi da ko sisi!.
Motarsa tana barin wajen Kausar ta yi tsaki,a ranta tace”na dai kusan ya da kwallan mangoro in huta da k’uda!”
Saboda ta gama shawo kan su grenade ta basu miliyan huɗu cif cif! gobe inshaaAllah za su saki videos d’in Yassir a polisawa, sojoji, dss duk sai sun turawa kowa!!….
Yassira ce ta sanar da Yahanasu halin da ake ciki!
Ita kuma Yaha ta sanarwa su Daddy, Ummi da su Ya Musbah…
Abbakar da Ya Musbah ne suka fara zuwa dan a lokacin suna tare aka kira Ya Musbahn.
Suna shiga suka ganta a zaune ita kad’ai ta yi shiruu ta zabga uban tagumi, waani irin tausayinta ne ya lullub’e Abbakar bai san lokacin da Hawaye ya zubo masa ba!!
Tana d’agowa da ta gansu kawai sai ta fashe da wani irin kuka, ta tashi ta k’arasa ta fad’a jikin ya musbah tana kuka abun tausayi fad’i takeyi
“na hak’ura da Ya Yash, na hak’ura da shi har abada…
A gabansa aka tafi da ni, amma bai ce komai ba!
Ina sonshi kamar Raina amma wallahi na hak’ura da shi, mak’iya ba za su tab’a barinmu tare ba!”
Sosai Abbakar ya ji guilty conscious ya lullub’esa, dama shi tunda aka ce masa an kama Manubiya hankalinsa ya tashi dan hakan baya cikin tsarinsu…kwata kwata bai yi tunanin abun zai iya cutarda ita ba, amma kuma ta ya yi tunani mai zurfi a ransa, a take sai ya fahimci to ai duk abubuwan da ya ke ta yi ɗin cutar da itan ya ke yi a baɗini kawai dai wannan a zahirance ne an ga an yi arresting ɗina amma ragowar abubuwan da ya yiyyi mata tabbas nauyin cutarwarsu idan aka auna ya ma fi na kamata ɗin da aka yi a yau…..
A ransa ya shiga cewa”Tabbas na biyewa sharrin zuciya, na cutarda wadda nakeso da sunan so…
Tabbas Manu bata chanchanci hakan daga gareni ba, dan idan na ajjiye soyayya a gefe ko dan friendship d’inmu sam bai kamata in yi mata haka ba….
What was i even thinking? ta ya akayi na bari shaid’an ya rinjayi zuciya da kwakwalwata har haka???
Ta ya na kasa gane Manubiya ta Yash ce, ta ya na kasa gane ko da na aureta to fa zuciyarta ba tawa baceba!
Ba zan tab’a samunta yadda nake so ba, sai dai na wahalar da kaina da ita na lalata mana rayuwa da farincikinmu gabad’aya…kallifa yanzu a halin da take a ciki amma cewa takeyi ‘tana son Yash kamar ranta!!!’
How can i be this selfish to the person who stood by me through thick and thin(ta yaya zan zamo mai son kai haka ga Matar da ta tsaya min a lokutan wahala da lokutan sauƙi na rayuwata..)
my first sannan kuma last love?!”
Bai yi auni ba kawai ya ji hawaye sun wanke masa fuska, da sauri ya juya ya fita zuciya fall danasani!…….
….
Kusan duk a tare su Anty Umma, Baba, Daddy, Yaahanasu suka isa wajen har da Duputy Governor saurayin Yahanasu wanda tana gaya masa ya taho…ai kuwa yana saka Baki a al’amarin aka saki Manu tare da bata hak’uri…..
Sai a lokacin ne kuma Yash suka ƙaraso suma, shi da Aslam wanda ya je ya ɗadd’akosa a event centre d’in bayan ya ajjiye Hudan a gida.
(dan kowa ya watse amma shi ya kasa tafiya,yana inda suka barshi)
A hanya Aslam ya gaggaya maasa abunda Hudan tace…ta inda ya sanar masa ‘duk sharri ne, gashi-gashi, Hudan duk ta gaya masa komai, ta tabbatar masa ‘ita Kausar ɗin ce ta saka d’an nata a buhu, ita maid d’in bakinsu d’aya da Kausar, sannan jakar Manu babu komai a cikinta da farko! Huda ta gani.
saka mata sarkar aka yi daga baya lokacin da wajen ya hargitse….”
Sannan ya ɗaura da cewa
“Amma yanzu su fara zuwa wajen nata dai, idan abu yak’i ci yak’i cinyewa sai su je su d’auko Huda ta bada shedar sarƙar….”
Suna zuwa suka tarar an sake ta, har suna ma shirin tafiya!
Sai a lokacin Yashjub ya ji kamar ya rufe kansa da kansa da duka!!!.
Da mugun kyar ya samu ya d’aga k’afafuwansa ya nufe ta, yana zuwa dai dai inda take ta juya ta kamo hannun Ya Musbah tace masa”take me home, dan Allah, pls…”
Zai yi magana tace masa”plsss”hawaye suna masu bin k’uncinta
Su Ya Musban za su yi mata musu, Daddy yacewa Ya Musbah ya tafi da ita…..dan shi kansa ya ji mugun mugun haushin abunda ya ji Manu tana gayawa Yahanasu Yash d’in ya yi mata…ko a wanne irin Hali kake a ciki ai bai kamata ka bari a tafi da matarka a gaban idanunka ba!.
Duk watsewa suka yi, aka bar shi da Aslam a wajen…sai a lokacin Aslam ya dafa kafad’arsa yace”Allah ya kare gaba”
daga haka shima ya juya ya wuce ya tafi, dan tabbas Yashjub yana buk’atar space!…ya san menene damuwa da k’unci, shiyasa tun ɗazu suna yin ido biyu da Yash ɗin kai tsaye ya fahimci ‘Yasjub yana cikin masifa..’
dan haka ya tafi yana mai yi masa addu’ar ‘Ubangiji ya yi masa maganin damuwarsa……’
Shi Yash bai ma lura da Abbakar ba, sai da aka gama watsewa tukunna ya hangesa a chan nesa zaune shi kaɗai ya yi shiruu ya yi tagumi..kafesa kawai Yashjub ya yi da idanuwa, kamar an ce ya ɗago shima Abbakar ɗin ya ɗago dan hakansuka yi ido biyu…suna had’a idanu Abbakar ya mik’e ya nufosa,a zuciye Yashjub shima ya nufi Abbakar d’in yana jin ‘tabbas yau kam ko shi ko Abbakar…..’
…..suna zuwa kusa da juna Abbakar ya yi sauri ya durk’usa a gaban Yash ya rik’e k’afafuwansa da hannu bibbiyu, kawai ya fashe da kuka…
Da farko Yashjub ya d’auka wani sabon plan d’in Abbakar d’in ne yin hakan, shiyasa a zuciye ya fara k’ok’arin wafce k’afarsa amma sai ya ji Abbakar d’in yana kuka yana neman yafiyarsa sannan ya shiga zaiyyano masa dukkannin abunda suka yi shi da su Yasira da Kausar!..
Dan haka Yash ya fahimci nadama ce ta zowa Abbakar,wanda hakan ya sanya zuciyarsa ta d’anyi sanyi jikinsa ma haka…..
Babu abunda Abbakar ya b’oye bai gayawa Yashjub ba, ya kuma nuna masa proof a wayarsa, sannan ya gayamsa yadda suka yi da Manu d’azu..
komai dai duk sai da ya fad’a masa, tun daga farko har zuwa k’arshe…
Dare ya yi sosai amma hakanan Yash ya tisa k’eyar Abbakar suka nufi gidansu Manu…….
Da farko cewa ta yi bazata saurari Yash ɗin ba, Allah ya so Baba ya ji lokacin dan haka ya fatattake ta zuwa parlourn Bak’i wajensu…
Ta yi mamakin ganinsa tare da Abbakar, amma sai kawai ta zauna ta juya kai ba tare da ta kula ko wannen su ba….