← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 152

Sashe 31

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mamaki Yashjub ya d’an d’ago ya kalle ta kafin ya ce ”ai all the rooms are full(ai koina a cike ne)”
Sai kuma ya kalli Manubiya ya d’an matsa Hannunta wanda ke a cikin hannayensa har yanzu kafin ya ce”Baby ba mun riga mun gama shirya komai da ke ba? me ya kawo zancen kaya kuma??”
Ya yi mata tambayar yana murza Hannun nata dake a cikin nashi.

Ita kam Manubiya kasa ma cewa komai ta yi, dan yadda yake yi mata da Hannu gaba d’aya ya burkita mata lissafi, shiyasa duk yadda ta so sai ta gagara cewa komai.

Wani shu’umin murmushi Yashjub ya yi mai had’e da dariya kafin ya sake cewa”
Babyn Yashjub, kin yi shiru….”

Dariya Sir Najeeb ya yi tukunna ya ce ”Keys d’in suna Hannuna, za mu iya barinka anan ko??”

“Yeah,”
kawai yace, ba tare da ya kalleshiba, dan har yanzu idanunsa suna kan Manu yana murmushi sannan ya ƙi ya daina murza hannun nata.

Sai da Najeeb ya sake sakin murmushi tukunna ya kalli Siyama ya ce “mu je, za a san inda za a saka kayan”

“Dagaske Najeeb ba waje ka sani kuma”
Yashjub d’in ya fad’a still ba tare da ya kallesa ba.

Cikin sigar zolaya Aisha ta ce
“kai dai ka ji da Amarya ka barmu da jere”

“Yauwa abunda nima zan fad’a kenan”
Siyama tace hakan tana d’an dariya.

Murmushi Najeeb yayi kafin yace “Ashe kin iya magana”
Ya fad’i hakan yana kallonta
wanda ya sa ta d’an ji kunya.

Yashjub ya yi tunanin Yassir zai zauna da shi, amman sai ya ga shima ya mik’e yana cewa”bari mu je gidan, sai anjima”

“Okay”kawai Yashjub ya ce,
a ranshi yana aiyyana
“In dai har Yassir ya nuna yana son d’aya a cikin Yaran nan to
InshaaAllah shi kuma zai tsaya mishi har sai ya ga ya aura”
dan ya lura da yadda suka nutsar da shi a cikin awa d’aya kacal. Ya san tunda har so ya chanja shi ya maida shi mutum mai walwala raha da dariya to ya yi imanin inshaaAllah so zai iya chanja Yassir shima ya nutsar da shi ya shiryar da shi.

Yash bai ma san sun fita ba sai da ya ga d’akin ya k’ara haske tukunna.

A hankali ya d’an cika hannun nata tukunna ya kamo k’asan vail din ya yi sama da shi…ko a kan kafad’unta bai bar sa ba sai da ya kai chan k’asa tukunna ya ajjiye shi akan kujerar kawai,
ya shiga kallonta.

Ahankali tana mai jinta duk a takure ta d’an juyo ta kallesa kad’an…..d’inkin babbar riga ne a jikinshi na wani irin yadin da bata tab’a ganin irin sa ba tunda take a rayuwarta.
Yanayin kwalliyar d’inkin anyi sa ne da bak’in zare mix with white (mai haɗe da fari), da d’inkin da yad’in da kwalliyar d’inkin sunyi mugun tafiya da imanin ta…..ba ta san yanayin d’inkin maza da kyawunshiba asalima ba burgeta yakeyiba amman wannan kam ta yi declaring nashi as the best!!! Dan ya matukar yi masa kyau, wankan nasa ya bi jiki.
Ya murza bak’ar hula kamar zanna bukar ita dai bata san ko akwai hula zanna bukar kuma bak’a ba amma yau ga ta anan, sannan hatta cuff links da agogonsa ma duk bak’ake ne ga kamshin mayataccen turarenshi wanda tun lokacin da ya shigo cikin parlourn
shi ya fara yi mata sallama….kallonshi take yi sam
ta gagara d’auke idanunta a kansa(ba wai cikin idanunsa ba dan ta ƙi yarda su sake haɗa ido, amma shi ɗin kawai take kallo), wani irin kyau kwarjini da haiba ta ga ya k’ara…..ahankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata moments d’insu tun daga farkon had’uwarsu a office d’in sir Najeeb, har kawo yanzu da yake zaune a kusa da ita a matsayin mijin aurenta…ahankali ta lumshe idanunta a cikin zuciyarta ta shiga godewa ubangiji dan tabbas idan akwai Mace mafi sa’a a duniya to ita kuma ta naɗa kanta a matsayin wadda ta fi ta sa’a, dan ba kowa bace take samun dama ta auri wanda ya ke sonta so na haƙiƙa sannan kuma first love ɗinta, amma itakam gashi ta samu…har ila yau, kalli kyan Yash, kud’i, aji, ilimi da komai ma nashi duk marar aibu, amma ita ya zab’a, ita ya so, ita yakeso ya yi rayuwa da……….da kyar ta ɗan buɗe idanuwan nata ta ci gaba da kallon abunta.

“Na yi kyau har haka ne???”
Muryar Yashjub ta dirarwa dodon kunnuwanta…
Wanda shima ɗin dakyar ya nemo numfashi da nutsuwarshi ya sakawa gangar jikinsa dan tun lokacin da ya bud’e fuskar tata ya neme su ya rasa…..ta yi wani irin kyau wanda tsayawa fad’a ma b’ata baki ne,tabbas Manubiya itace rayuwarsa, shiyasa ya kasa daina tasbihi hamdala da hailala ma Allah subahanahu wata’ala da ya mallaka masa ita a yau.
“Yahayyu ya Kayyum ka bamu tsawon rai mai amfani ka sa mu tsufa tare kasa kar Manubiya ta riga ni mutuwa
dan ban san ya zan yi rayuwa idan babu ita a duniyar nan ba”
Ya yi adduar a cikin ransa yana mai ci gaba da k’are mata kallo!.

Ahankali ya ji tace”Ina wuni…”
Bata samu damar d’aura komai ba sakamokon sallama da shigowar Muhsin a tare hannunsa d’auke da lemuka.

Kunya ce ta kama Yashjub…shi da yake Ango amma ya zo ya shantake gashi har an kawo masa lemo!shiyasa ya cewa
Muhsin d’in “ya maida, shi kam
tafiya ma zai yi.”

Muhsin yana fita, ya janyota jikinshi ya rungumeta wanda hakan yasa duk sukayi shiru……
Sai da ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya tukunn a hankali dai dai cikin kunnenta yace”Allah ya bamu zaman lafiya”
Wanda hakan ya sanya ta ji numfashinta ya yi sama kamar zai ɗauke,
Cikin tsantsar kulawa da bege ya ɗago ya yi kissing forehead d’inta sannan ya ce ”thankyou”
tukunna da kyar ya daddage ya yi kokawa da zuciyarsa ya cikata ya mik’e da sauri, dan ya san idan ba da saurin ya mik’e ba tou tabbas sai ya k’ara jan lokaci…….Ahankali yace mata “sai Allah ya kaimu anjima”
Daga haka ya sa kai ya fice.
Allah ya so shi babu mutane sosai dan sai da ya fito ɗin tukunna wata sabuwar kunya ta lullub’e shi, ya ji kamar ya nutse a wajen.

Earlier (awannin baya da shuɗe) (11:45am)
Tun k’arfe goma lokacin da aka sallamo Kausar, suka dawo gida gabad’ayansu! suka gaza sukuni, kamar wasu masu zaman makoki haka suka koma, Kausar kam k’arshema d’aki ta mik’e ta shige ta rufe kanta.

Hankalin Mommy bai sake tashi ba sai da ta kira Daddy ya tabbatar mata da an d’aura auren….tashi d’aya ta gaza nutsuwa k’arshe ma kawai sai ta kama hawaye, ba ta yi tunanin za ta shiga damuwa kamar hakan ba, duba da yadda suka hak’ura suka tsara dakatar da komai har sai Manubiyan ta shigo tukunna su d’aura daga inda suka tsaya.

Suna zaune a d’akinta itada Baba larai Yassira ta shigo ta same su…
Numfashi Yassirar ta fesar kafin ta k’araso ta zauna a kusa da ita tukunna tace “Mommy, idan Ina ganin ki a haka za ki sa in je in yi shirme a wajen d’auko Yarinyar nan, ku ne kuka ce mu kwantar da hankalinmu amman ganinki a haka gaba d’aya yana nema ya dawo min da komai sabo.
“Ta ya kuke so mu tarbeta Hannu bibbiyu mu yi maraba da ita bayan gashi muna ganin yadda ta zama silar kukan ki!”

Ajiyar zuciya Baaba Larai ta sauk’e, kafin ta kalli Yassira ta ce ”dan Allah kar ku dawo mana da Hannun agogo baya, mun riga mun gama magana, yanzu ki bar jan lokaci mu samu mu je mu yi abunda za mu yi a cikin gidan kafin ta tare….na riga na gaya muku idan har ta tare ba’ayi ba to gaskiya akwai matsala!
Ki yi sauri ki je ki cewa Yahanasu ta baki makullai da frames d’in da suka siyo ita da Ummi a kasuwa za ku had’a ku kai gidan tare da flasks d’in da kuka siya kuma…..na ji d’azu Ummin tana ce mata ya kamata a kai a kafa kafin zuwan Amaryar, dan haka ki yi sauri ki karɓo mana komai.”

Sai da Yasirar ta fesar da wani bahagon numfashi tukunna tace”okay Baaba”
daga haka ta sa kai ta fice.

Sai a sannan Mommy tace “ni kam da kun yi abun nan tun a jiya…”

“Ai dole sai a ranar da za ta tare tukunna za’ayi, kar ki damu ba za a samu matsala ba…..”
Baaba Larai ta bata amsa.

Shiruu Mommy ta yi, tana tunani, kafin a hankali cikin mutuwar jiki ta ce ”kin tabbatar zuwan nata ba zai taɓa surrukana ba dai ko?”

Sai da Baaba Larai ta sauk’e numfashi tukunna ta ce ”na gaya miki ai…ita Manubiya tana tafe ne da fad’uwar ki a bayanta, muddin ta zo ta zauna ta daɗe da shi kuma ta zauna a cikinmu to komai naki sai ya tab’arb’are, a hankali a hankali za ki yi ta shiga bala’i kala-kala kuma babu ranar farin ciki….amma inshaaAllah, da izinin Allah mu kuma ba zamu bata ikon dad’ewa a cikin gidan nan ba! Ba za mu bari ta samu kwanciyar hankalin son zama da mu ba! Sannan ba zamu bata damar kasancewa a tare da shi ba!
Ballantana har ta samu gindin zama da shi idan ciki ya samu ko shaƙuwar da ta fi ta yanzu ta wanzu a tsakaninsu…..
Ballantana har matsala ta fara tasowa…kuma dukda haka still Ina ta add’ua inshaaAllah babu abunda zai taso har ta zo ta yi ɗan zaman da za ta yi ta tafi ɗin.
Zuwan nata ma dan bamu da yadda za mu yi ne tunda akwai rabon zaman a tsakaninsu..kinga ai yadda akayi ta shan fama amman duk ya tafi a banza,but inshaaAllah na yi miki alk’awari ba za ta yi dogon zango a cikin gidan nan ba.
Ina fatan kin fahimceni???”
Chapter 31 · 0% Book details