← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 152

Sashe 51

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ya fito, a yadda ya barta a haka ya sameta, sai dai ta d’an sassauta sautin kukan nata…
Ko bargon da ya sauk’a ya bar mata a iyaka guiwarta saboda saurin ganin ya bar cikin d’akin ba ta samu ikon ja ta rufe jikinta da shi ba.

Shiyasa ya samu dama ya yi tsaye a kanta ya ya shagala kwarai wajen kallota kawai.. yana kallon nata a ransa yace
“Allah mai halitta!
How can some one be this beautiful! and this perfect!!.
So awesome.
(Komai nata dai-dai kuma mai kyawu, abun mamaki..”)

Ta san yana kanta a tsaye, kuma yana k’are mata kallo, gashi ta kasa motsi, shiyasa kawai ta k’ara sautin kukan nata.

Shi kam yana chan, zuwa wannn lokacin idanunsa sun sauk’a akan d’an jinin da ya biyo ta gefen cinyoyinta d’an kad’an ba mai wani yawa ba!…(haɗe sannan gauraye da wani abu mai kauri, yawa kuma garai-garai)
Dama ko da ace bai ga hakan ba, ya riga ya sani..ya san a yadda ya sameta! Amman ganin da ya yi sai ya sake sanya shi cikin wani irin farin ciki, yana mai jin sa a saman gajimare yana yawo, ga kuma tsananin nutsuwa da nishad’in da ya samu, shiyasa kawai ya fara jinsa kamar wani
sabuwar halitta!.
Ya ma rasa wanne irin gift zai bawa Manubiya as token of appreciation (a matsayin ƙaramar kyautar godiya) dan tabbas bai isa ya ce zai bata gift dai dai da abunda ta basa ba….

Ba kad’an ba, ganinta a hakan ya sauya shi! Amman sai ya daure…

yana mai jin tausayi da begenta suna ratsashi,ahankali ya lumshe idanunsa waenda suka d’an fara chanja launi ya bud’e su, kafin ya k’arasa inda take ya d’urkusa ya shiga share mata hawayenta yana cewa
“ni kaina haushin kaina nakeji,kar ki damu anjima zan baki bulala ki zaneni!”yana gama fad’in haka ya d’auketa suka nufi bathroom d’in..

bai ajjiyeta a koina ba sai cikin ruwan d’umin da ya gama had’a mata.
..
Ita kanta batasan ta na da raki ba sai yau, amman kuma ba za ta kira hakan da raki ba dan wallahi ko macen soja ce ta ji kalar azabar da take kwasa to ta tabbata itama sai ta koka.
Da kyar ta tsaya ya yi
mata ruwa biyu, ya taya ta tai wankan tsarki, yai mata wankan sabulu, daga haka ya sake sakar mata warm water ya juya ya fita
domin ya samu ya chanja zanin gado.

Yaye mara kyan ya yi, ya shimfid’a sabo, tukunna ya d’auki mara kyan ya nufi toilet d’in da shi..yana sshiga ya saka a washing machine, bayan ya wanku an busar ya saka a closet domin ya d’an sha iska..

tukunna ya koma cikin bathroom d’in wajenta.

A kwance cikin ruwan ya sameta kamar d’azu ta lumshe idanunta,ita kanta tana jin dad’in yadda ruwan zafin yayi mata, tana jin yadda jikinta yake d’an sakewa ciwon yana raguwa….

kamar d’azu yanzun ma d’aukarta ya yi, bayan ya d’aura mata towel sai faman shagwab’a takeyi shi kam kamar ya maida ita ciki haka yake ji sai wani lallab’a ta yake famin yi kamar ya samu kwai..

A haka suka fito, sai da ya sanya mata babban hijabi ya kwantar da ita a kan gadon tukunna ya koma ciki domin yin nasa wankan bayan ya ce mata “ta yi sallah anan inda take babu,
damuwa.”

Sai da ta d’an zauna da kyar tukunna ta samu ta yi sallar, ta na idarwa ta kwanta
atake bacci mai masifar nauyi ya yi awon gaba da ita….

ko da ya fito ya ga tana baccin bai tasheta ba, Sallah shima yayi
daganan ya je ya soyo musu omelet, ya had’o da ruwan zafi, kayan shayi da dambun nama…
Sai da ya faranajjiyewa a ɗakin tukunna ya wuce sama d’akin shi ya shirya tsaf cikin wata dakakkiyar sky blue d’in shadda da farar hula!…
Ya yi kyau matuk’a, kyawunsa ya sake fitowa gashi har wani glowing yakeyi, ya fito ango abunsa ras…duk inda aka gansa dole a sake waigawa a kalla.

Tana cikin baccin ta ji ana shafa fuskarta, turo Baki ta yi
kad’an kafin ta d’an bud’e idanunta….kyakkaywar fuskarsa ce ta fara yi mata sallama, yana kallonta yana murmushi,
A hankali ta mayar ta rufe idanunta ta d’an kauda kai gefe.

Murmushi ya yi ya kama kunnensa kafin yace”sorry!”

Ganin ta k’i ta bud’e idanun nata ne ya sanya ya d’an rissina dai-dai saitin kunneta ya shiga rad’a mata wasu kalamai waenda suka sanya ta ta fara k’ok’arin tashi a gigice amman kuma ta gagara tashin….
ganin k’iri k’iri ta kasa tashin ne yasanya kawai ta fashe da kuka….
Cikin rashin jin dad’i yace “Wasa fa nake yi miki…so kike hawayenki su k’afe a yau ne??”
Ya fad’i hakan yana mai taimaka mata ta zauna kafin a
hankali ya sakata a jikinsa, ya shiga rarrashinta har sai da ya ga ta yi shiru tukunna ya mik’e zuwaga gaban dressing mirrow ya d’auko abincin.
Kamar jiya yau ma shi ya bata a baki yana ci yana bata tana ci yana gaya mata cewa”likita za ta zo ta yi mata allura, ta bata magani”

Tana gama cin abincin kuwa lokacin dai dai 8:00am ko gama saka kaya da shiryawa ma ba ta yi ba wayarsa ta hau k’ara, dan haka ya fita ya sauk’a cikin mintunan da ba su gaza biyu ba ya dawo d’akin ya kama hannunta suka fita wajen Dr d’in…….sosai ta ji dad’in allura da maganin ga wani bacci mai d’an karen dad’i da yake ta faman fusgar ta.

Akwai abubuwan tafiyar su da zai karb’a sannan ya kamata ya je ya ga su Mommy, dan
haka yace mata “ta basa 30 minutes inshaaAllah zai je ya dawo yanzu… “

Sai da ya rufe koina, ya tabbatar bata buk’atar komai
tukunna ya fita bayan yaga
bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita…..
shi kad’ai sai faman murmushi yake ta zubawa yanta saƙe saƙe a ransa…
….ya san dama zai iya yin komai akan Manubiya amman yanzu ya sake tabbatar da hakan! Mata rahama ne shakka babu…shi a
lokacin da bai fara soyayya ba
mamaki yake idan ya ga wasu mazan suna nan nan da matan su da kuma mutanen da idan suka fara zina ba sa iya dainawa sai waenda Allah ya kubutar…sai yanzu ya fahimci bayan zazzafan so da k’auna ashe wannan rahamar ce dalili….
Yana wannan tunanin ya tsaya ya karb’i sak’on nasu daga nan ya wuce gida.
…
Ba kowa shiruu parlourn, dama ba ya son hayaniya balle a rik’esa.
Zai samu lokacin su Yassira amman ba yau ba, dan a halin yanzu fuskar Manubiya kawai yake son gani!
Allah Allah yake ya koma gidan kawai!!!…..
Bayaga hakan kuma ba zai tab’a yarda ya ɓatawa kansa wannan moment ɗin (yanayin) da yake a ciki na asalin farin ciki na haƙiƙa ba, ta hanyar tunkurar su Yasira….
Maganar gaskiya,
wallahi jikinsa har ya fara karkarwa….ya san za su fafata da ita kam tabbas, idan ya je! Dan
shi kansa bai yi zaton jinsa a hakan, kurkusa ba, amman he can’t help it.

D’akin Mommy ya shiga, ga mamakinsa sai ya tarar ba ta nan, dan
haka ya d’auki waya ya kirata….har wannan lokacin suna d’akin Kausar, ta samu wani bacci mai dad’i ya kwasheta kenan
anan kan sofa, wayartata ta fara ƙara….

Baba larai ta kalla bayan ta ɗaukko wayar taa kalli screen d’in, kafin tace “Yashjub!”

Da sauri Baba larai ta matso tace”Ki d’auka. duk yadda na gaya miki ki yi, dan Allah ki yi
k’ok’ari ki danne zuciyarki…”

Sai da ta tsinke ya sake kira tukunna Mommy ta iya d’auka, dakyar, ahankali tace”Yashjub!”

Numfashi ya fesar kafin yace
“Na zo bakya nan”

“Ganinan zuwa”tace,
daga haka ta kashe wayar ta rik’e a hannunta tana huci.

Ba k’aramar lecture Baba larai ta yi mata ba, itada Yassira wadda aka samu da mugun mugun kyar karatun Baba larai ya shiga kunnenta ya samu mazauni a kanta, kafin ta mik’e ta nufi side d’in nata fuskarta a murtuke….sai da ta yi da gaske tukunna ta samu fuskar nan ta d’an sake, dan ba kad’an ba hankalinta ya ke a tashe, ji take kamar ta yi hauka!…..abubuwan sun yi mata yawa, jiya haka ta dinga zirya har asuba tana lek’e ko za da ga sauk’k’owar Ummi daga side d’in Daddy amma shiru babu Ummi babu alamarta, kuma har bacci ya d’auketa lokacin 8:49 ba ta ji ta sauk’o ba, shiyasa ta kuma shiga cikin tashin hankali tana mai jin kamar ta je ta barbard’a musu fetur ta kyasta ashana!
Tsabar rashin mutunci ko sallar asubah fa ba ta ga Daddyn ya fito yi ba…..

Ko da ta zo shiga side d’in nata ma, sai da ta yi da gaske tukunna ta samu ta tura k’ofar ta shiga dan wallahi sam ba ta k’aunar ganin fuskar Yashjub!.

A parlournta ta samesshi yana ta faman safa da marwa, dan ya k’agu ta zo su gaisa ya biya ya gaida Daddy ya wuce.

Sai da gabanta ya yanke ya fad’i sakamokon wani kalar fresh da ta ga ya yi.
Su na had’a idanu ya ɗan daidaita kansa, kafin ya taka zuwa inda take ya d’an rissina yana
kallon k’asa yace”Mommy Ina kwana!” ya fad’i hakan yana sosa k’eya.

Murmushi ta yi kafin tace”Da ikon Allah yau kunyata Yashjub yake ji. Ina ita surukar tawa?
ya ba ku zo tare ba??”.

Yanzun ma sosa k’eya yayi kafin yace”Am..tana bacci.
sai zuwa jibi InshaaAllah za mu zo tare” .

Dum!!!
Haka k’irjin Mommy ya buga, da kyar ta lalumo nutsuwa ta sakawa kanta
kafin ta yi yak’e cikin son fahimtar wani abun ta ce ”Ai dama da gajiya!”

Cike da son b’oye sirrinsu da kuma kar ya bawa kansa kunya Yash d’in yace”Ni kaina kam gajiyar bikin nan tambaya ta take yi, balle ita da ta ke mace”

Ajiyar zuciyar da Mommy ta sauk’e sai da Yashjub ya ji, dan haka ya d’an kalleta.

Da sauri tace”Inata fama da Kausar ma shiyasa ban yi muku ko breakfast ba, ku yi
hak’uri!”

Tashi d’aya Mommyn ta lura da yadda yanayin fuskarsa ta chanja daga jin an ambaci sunan Kausar, a ranta ta ce”Tabbas akwai aiki jaa a gabanmu”
Chapter 51 · 0% Book details