← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 152

Sashe 67

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To dai kamar yadda Yashjub ya fad’a mata ashe da gaske shi bai ma fara cin amarcinnasa ba sai yanzu dan ita kanta ta tabbatar a Nigeria appetizer ya yi (ɗanɗano ya yi)….Sai da suka shafe sati
d’aya da kwana uku ba ta lek’a waje ba, shima haka dan da kyar ma aka samu ya d’an fita ya je ya sissiyo musu abubuwan da za su buk’ata daga nan sai da suka yi sati d’aya da kwana uku tukunna suka d’an fara fita suka fara zageye island d’in…
Ita Manubiya har ga Allah so take yi ta zauna a gidan ta yi barci sosai ta huta, amman kuma ta san idan suka zauna a gidan ba barinta ta huta d’in zai yi ba, shiyasa kawai take yarda tana biyosa suna fita yawon ba dan tana jin dad’in yawon ba, gashi dai the view da duk wani abu game da Cyprus ɗin aljannar duniya ne amma ita sam ba ta enjoying tsabar gajiya…

A haka dai kafin su yi wata biyu ta samu ta d’an saba kuma ta karɓi mijinta a yadda yake, dan ta fahimci ba wai don ya takuramata bane hakanan halittarsa ta ke, ga kuma gudummawar da soyayyarta da k’aunarta suke badawa..

Shi kansa Yashjub ya na mamakin yadda Manubiya ta taso masa da wani tsumin dake a jikinsa wanda a da sam bai san da shi…dan a da kwata kwata ko kallon mata ba ya son yi ballantana su basa sha’awa..yana jin sha’awa ba wai kwata kwata ba ya jinta ba amman ko ta d’an taso masa to ba zai yi 10 minutes yana jin wannan feeling d’in ba dan tashi d’aya zai ji ya nemi feeling d’in ya rasa, shiyasa a wannan lokacin wani zubin har tunani yake yi akan’Anya kuwa lafiyar sa k’alau!?’.

Kafin 2 months itama ta ware ta zama y’ar gari ta shiga farantawa Mijinta rai yadda ya kamata, Wanda hakan ba k’aramin dad’i ya yi wa Yashjub ba, dan shi sai a wannan lokacin ne ma tukunna ya ke sake experiencing (yake sake jin) wasu ni’imomin da aure ya k’unsa…

Zaman lafiya kwanciyar hankali da asalin tattalin so da k’aunar juna shine ma’anar zaman Manubiya da Yashjub a Cyprus..wani zubin idan ya yi mata wani abun har kukan farin ciki takeyi ta yi sujjada ta yi ta godiya ga Allah S W A dan itakam in dai a fannin so da k’auna na tsakani da Allah ne to ba shakka za ta fito ta bugi k’irji tace “ta fi ko wacce mace sa’ar mijin aure…”

Hutun su kawai sukeyi gaba d’aya sun manta da matsalolin su, sun yi fari sun yi k’iba abunsu….suna waya da video call da su Jidda haka shima Yashjub ya na waya da Mommy kuma ba yabo ba fallasa suke gaisawa ita da Manubiya, itama Manubiyan da kanta takan kirata ta gaida ita ba yabo babu fallasa take amsawa.
Haka suna waya da chattin da su Ummi Yahanasu da Munirat sosai, su Yasira kuwa ko ‘hi’ babu a tsakanin su da Manubiya amma suna kula d’an uwansu.
Yashjub ɗin ya lura kuma ya sani, amma bai yi magana ba, itama Manu bata ce komai ba dan ko kiran sa sukayi basa cewa ya bata shima kuma baya bayarwa..Manubiya ba ta nuna masa text d’in da Ya’isha ta yi
mata ba 2 month ago kafin su taho amma shi ya gani..so yake kawai ya ga iyaka gudun ruwansu, Daddy kuma ya huce, daganan zai san abunyi.

Watansu biyu da sati biyu Daddy ya kira Manubiya..ta yi mamakin ganin kiran amma sai ta d’auka da mutuntawa ta gaidashi..
Da kulawa ya amsa ya tambaye ta ya Cyprus tace alhamdulilah daga haka yace”yaushe za su dawo?”
Diriricewa ta yi, ta rasa bakin magana da kyar dai tace” Ya Yash d’in bai gaya mata ba”
Jinjina Kai Daddy ya yi kafin yace”ok shikenan”
daga haka ya kashe wayar.

Sarai Yashjub ya ji komai, kuma ya fahimci me Daddyn yake nufi da yin haka dan haka ya d’au waya ya fita ya kira sa…
Bayan sun gama gaisawa Daddy yace
“A lokacin da Manubiya ta mari Yadira na ji haushi sosai, kuma kamar yadda ka yi zato tabbas jiranku kawai nake yi ku dawo in had’a ka kai da ita Manubiyan in yi muku warning, kuma in yi riga kafi saboda gaba, amman tunda har za ka iya yi mana k’aura saboda hakan InshaaAllah maganar ta wuce, kuma komai ya wuce, amman a kiyaye gaba…come home..da ni da y’an uwanka da Mommynka muna buk’atarka a kusa da mu, ba ka tashi tare da mu ba, bai kamata yanzu ma ka sake barinmu ba”

Shiruu Yashjub ya yi kamar zai faiyyacewa Daddy halin su Yasira ya kare Manubiyan amman kuma kawai sai ya bar maganar yace”ka yi hak’uri Daddy, dama nan da 4 days ma za mu wuce Uk mu yi musu sati biyu, daganan sai mu dawo inshaaAllah”.

Ahankali Daddy ya ce
“Allah ya kaimu”
daga haka ya kashe wayar ya dafe kansa…’he really can’t believe (ya kasa yarda da cewa wai ) Yashjub ya d’auke matarsa, sun yi nesa da su saboda ba ya so a nuna mata ta yi laifi!! kuma bayaso ma a ga laifin nata a kan komai….
tabbas da alama Yarinyar nan ta juya kwakwalwar Yash, kuma son da yake yi mata ba na wasa bane, tabbas zai iya rabuwa da kowa akanta dan gashi ya ga alama nan….
Dan haka zai yi iyaka bakin k’ok’arinsa wajen ganin ba ta raba sa da d’ansa ba, inshaaAllah daga yau ba zai sake ba shi dalilin da zai yi tunanin barinsu saboda ita ba…
Shikenan fa yanzu da bai ankare da wuri ba da sai dai Yash ya zo yi musu sallama, dan tsaf zai yi transferring komai nasa garin da yake so ya je ya ci gaba da business d’insa da rayuwarsa a chan su ya barsu a nan.
Tabbas ya yi da na sanin aurawa Yash Manubiya dan gashi tun ba a je koina ba tana janye Yash ɗin daga garesu!
amma tunda aikin gama ya riga ya gama ba komai, inshaaAllah ba zai sake bawa Yash dalilin da zai guje su saboda ita ba.
••••
Tsaraba sosai suka shiga jida a Cyprus dan sun kusa wucewa Uk inshaaAllah.

Sarai Manubiya ta fahimci dalilin Yash na tambayar ta akan batun period d’inta kusan kullum…
Ko last week har asibiti suka je yace a yi musu checkup d’in su malaria da komai amman ita sai da aka had’a mata har da scanning….
Da farko abun dariya yake bata, dan ita a ganinta ko wata uku basu cika ba amman ace har ya fara k’ulafucin ciki, sai dai kuma yadda ta ga yanayin sa tun jiya da ya ga ta fara period d’inta abun ya bata mamaki matuk’a ita har ya ɗan taɓata, dan tun jiya taga ya zama so silent, da kyar ma yake iya dariya sannan ko bacci bai yi ba a jiyan dan ko da ya tashi ya yi sallar dare ya ida kasa komawa ya yi har asuba…
Yanzu kuma da safe tana kitchen ya shigo ya ce mata “ya tafi jugging”
bayan da tare da ita suke fita kullum..kafin ma ta gama yi masa a dawo lafiya har ya sa kai ya fice daga kitchen d’in.
Ajiyar zuciya ta sauk’e ta juya ta ci gaba da aikin ta jiki duk ba kwari tana ta tunani…a haka ta kammala ta jere abincin a kan dining daga haka ta juya ta nufi d’akin su domin yin wanka.

Ta ji matuk’ar tsoron ganin sa da ta yi a d’akin zaune a kan gadon, dan batayi tunanin har ya dawo ba, ba ta ji shigowar sa ba sannan bai ce mata ya dawo ba, kuma idan sun fita jugging d’in sukan d’an jima kafin su dawo…

Ta na wannan tunanin ta ga ya sakar mata murmushi kafin ya mik’a mata hannu alamun ta zo garesa.

Ahankali ta d’an matsa kamar mai jin tsoro, ta zauna a kan cinyarsa…cikin cusa fuskarsa cikin wuyanta yace
“Morning wife!”

Ba ta amsashi ba sai da ta mik’a masa tata gaisuwar tukunna .
Sannan ta d’an kalle sa ta ce
“Kanada damuwa! mun ce ba za mu dinga b’oyewa juna komai ba.
Talk to me Dan Allah”.

Saida ya d’an shafa cikinta ya kalli cikin tukunna ya d’ago ya kalleta yace”Na ji har yanzu shiru ne!.
Baki tab’a shan wani magani mai k’arfi ba ko da na malaria ne? Ko mu je a duba ki sosai sosai..kin san yawanci y’an mata fa kunada matsalar da ku kanku baku sani ba. sai likita ya duba da ikon Allah sai kiga an dace…”

Shiruu ta yi ta sunkuyar da kanta k’asa alamun ta shiga damuwa, shiyasa tashi d’aya kamar zai yi kuka yace “Shiyasa fa kika ga na kasa yi miki maganar tun tuni…
Banason b’acin ranki, ni kuma har ga Allah a matse nake inji good news…”

Murmushi ta yi tace “ba b’acin rai bane, kawai dai nima kasa na fara tunani ne..”
Sai kuma ta d’an yi shiruu kafin ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna tace”Mu yi addu’a !mu yi ta addu’a!”

Daga haka ta yi shiruu ta fa’da duniyar tunani….itanma babban burinta a yanzu shine ta ga babyn ta ita da Yash, amma gashi shiru har yanzu, da farko tana gani kamar ya yi wuri amman itanma yanzu ya jefata a damuwa…mai zai faru idan ta kasance a cikin matan da basa haihuwa, ya kenan?
Ta ma san shikenan ta rasa soyayyar Yashjub ne!
Dan a yadda ta ga k’ulafucin son haihuwa a kwayar idanunsa to ba lalle ya iya zama da ita kad’ai ba tare da ƴaƴa ba sannan ba lalle ya ci gaba da sonta kamar yadda ya ke yi ba.
Yashjub ya riga ya saba mata da zazzafar soyayyar sa
Idan ya juya mata baya ba ta san ya zata yi ba.
Da sauri a cikin ranta tace
“Ya Allah ka sa zan haihu nima, Ya Allah ka bamu y’a y’a masu albarka.”
Chapter 67 · 0% Book details