Sashe 12
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daɗin daɗawa kuma ga maganar da Yasmeen ta gaya mata d’azun, shiyasa duk take a gigice ta rasa inda za ta tsoma kanta ta d’an ji sa’ida.
••••
Tun lokacin da Manubiya ta gama waya da Yash hankalinta yake a tashe, bata nuna masa bane dan bata so ta sake assassa masa abun gashi ta ga bashi da lafiya, amma ba k’aramin firgita ta yi ba da ta ji yace “ba accident (hatsari)bane wani ne ya so kashesa‘’.
Ganin ta a zaune tanata tunani ne ya sanya Jidda matsowa ta shiga tambayarta….ai kuwa ita kanta Jiddan ba k’aramin firgita ta yi daga jin zancen ba amman sai ta daure itama ta shiga kwantarwa da Manubiyan hankali, sannan ta d’aura da cewa’’kawai ta dage masa da addu’a Allah ya kare sa daga sharrin masharranta, dama mutum kamar Yashjub dole yanada mak’iya.’’
Suna zaune suna d’an tattaunawa Baba ya shigo, dan yau ya shiga busy shi da su Ya Musbah so suke su samu su gama shirye-shiryen tarbar su Daddy wanda za su yi a gobe idan Allah ya kaimu.
Sai da ya ci abinci ya d’an huta, tukunna ya kira Manubiya ya zaunar da ita….nutsatstsiyar nasiha mai ratsa jiki ya yi mata, wanda sai da ta kai Manubiya ga yin kuka.
Murmushi kawai ya yi ya dafa kanta yace ‘’Allah ya miki albarka da ke da y’an uwanki, Allah ya sa ki shiga gidan aurenki a sa’a.’’
Ahankali duk suka ce‘’Ameen.’’
Daganan Baba ya mik’e ya sake fita, dan ba su gama ba ya shigo.
Murna a wajen su Jidda abun ba’a cewa komai, dan yanzun kam maganar biki ta kankama tunda har suka ga Baba ya fara yi wa Manubiya nasiha.
Shiyasa suka yi ta murna suna cewa “Allah ya sanya alkhairi” kamar daga sama suka ji muryar inna ta ce ’’Ameen’’
cikin muryarta da suka jima suna begen jin.
Aikuwa duk d’insu rufar mata suka yi, saida ta sake maimaitawa suka tabbatar tukunna Muhsin ya fita da gudu ya je ya kira su Baba a masallaci inda suke ta shirye-shirye…..
A ranar murna wajen Manubiya da ahalinta ba’a magana, dan har kuka sai da Baba ya yi..kukan farinciki da ya ji muryar Inna a zahiri, haka suma su Manu suka dinga kuka suna godewa Ubangiji subahanahu wa ta ala.
Sun jima suna murna, suna godewa Ubangiji, har da Ya Nafi’u. kafin su Baban suka fita domin zuwa su sanar da su Kaka Mallan maganar kawo kud’i da saka ranar Manubiya wanda za’ayi a gobe idan Allah ya kaimu……
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 07*
Su Baba suna fita daga d’akin ba da jimawa ba, su Jidda har ma da Manubiyan duk sai suka kaure da hawaye, dan tashi d’aya suka sake fahimtar ‘nan fa da kwanaki goma Manubiya za ta tafi gidanta ta barsu.’
Da kyar ta samu ta share nata hawayen kafin ta samu ta shiga rarrashinsu, tukunna suma suka yi shiru, Muhsin ya yi bacci, ita
da Jidda kuma suka cigaba da tattaunawa…y’ar uwar Inna d’aya ce tak a duniya kuma Baba ya ce “ya riga ya gaya mata d’azu’’
dan haka sun san
inshaaAllah nan da kwana biyu za ta taho idan an ci sa’a
mugun Mijinta jatau ya barta kenan….Gwaggwo Furaira tana da son zumunci, amman sai ta yi rashin sa ar Miijin aure ‘Jatau sarkin yak’i’, a chan k’auyen su Inna take har yau,
Mijinta irin bokayen soron nan ne, ya kafeta a gidan, ko
kara idan ya ajjiye ba ta isa ta tsallake ta ba, dan tun lokacin da ya fahimci ta fara shiryen-shiryen guduwa sakamokon ganowa da ta yi ba ya haihuwa ga kuma mugayen halayen shi da su ka yi yawa, shikenan ya kafeta a gidan.
Tun daga ranar ko waya sai ya so tukunna za ta yi da Inna…..
Gwaggo Furairah sai Mama
ta gidan Ammi, su kad’ai ne waenda Manubiya za ta nuna ta ce za su yi mata uwa tunda
Inna tana kwance…
Dukda ta so ace Inna ta ga aurenta akan k’afafunta
amman bata isa jayayya da abunda Ubangiji ya riga ya tsara ba.
Ta san su Umma Kuluwa ba lalle su kulasu ba, amma dukda haka suma za’a gaiyyace su, watak’ilan in sunga dama su yarda Mazajensu ma su yarda idan aka zo d’aukarta su rakata d’akin Mijinta kamar yanda akeyi wa ko wacce ƴa mace….
Siyama kam sun san batada matsala, za ta tsaya mata a y’ar uwa, haka ma Aisha matar ya Nafi’u ..
Su kenan jama’ar Manubiya, bata da wani dandazon Jama a sai ko mak’ofta, dan haka suka yanke akan ko Gwaggwo Furairah ta zo tace a yi taro su kam ba za su yi ba, iyakacin
abunda suke buk’ata suke kuma adduar samu
shine a yi auren a gama lafiya, ta samu Matan da za su rakata d’akinta..
Dama kuma ita Manubiya tun ba yau ba bata da buk’atar hayaniya a biki, sam ba ta so.
Maganar kayan d’aki kuwa
Jidda tana sako zancen Manubiya ta ce ’’Jidda babu wani kayan d’aki da za’ayi, Idan ma ya ce a yi jere nikam zan fito mishi k’iri-k’iri ince ya yi hak’uri,
dan ba zan ma fara d’agawa su Baba hankali da wannan batu ba, an samu da taimakon Allah da na ya Nafi’u da ya Musbah muna ci muna sha to
hakan ma ya ishemu
Alhamdulillah.
Ke kanki kin san yanzu ana fara maganar jere
Baba zai fara tunani…
k’arshe na san bashi zai ci dan cewa zai yi sai ya yi, kuma na san k’arshen abun ba zai yi kyauba.’’
A take Jidda itama ta goya mata baya d’ari bisa d’ari akan hakan, dan haka suka yanke shawarar ana fara maganar jere ma za ta yi
kicin kicin ta ce ‘’bataso!’’.
Sun jima sosai da Jidda,
kafin daga k’arshe Jidda ta yi barci ta bar Manubiya tana ta tunani, sai da ta ga shigowar Baba tukunna ta samu ta yi barci bayan kowa a d’akin ya yi.
….
Washegari..
A jiyan, dare ya yi kafin suka gama tabbatarwa shiyasa sai a yau ɗin da safe su Jidda suka tura Muhsin ya je ya gayawa Mama ‘za a kawo kud’in auren Manu’.
Ba k’aramin dad’i Matar ta ji ba kuwa, dan haka bayan zuwan Muhsin da kamar mintuna biyar sai ga ta, duk da ta san Inna ba za ta iya bata amsa ba amma haka ta zauna ta shiga yi mata ‘’Allah ya sanya alkhairi’’
tana ta murna aikuwa ga mamakinta ta ji Inna ta ce mata’’Ameen’’ itama…
Ba k’aramin dad’i hakan shima ya sake yi wa Mama ba, sosai ta yi murna kamar za ta yi kuka dan farin ciki,
haka nan ta yi ta maimaita ‘’Alhamdulilla’’
su Manubiya suna ta murmushi, suna jin tsananin dad’i da annashuwa.
Mama ba ta jima da zuwa ba Sofia ta zo, suka fara aikin su, su kuma su Mama suka koma gefe itada su Manubiya, daga nan ta shiga tsokanar Manubiya wai ‘dama ashe tana da saurayinta amma shine bata tab’a ba ta labarinsa ba…..’
Bayan wasu ƴan lokuta, Sofia ta yi ta gama ta ce musu ‘sai zuwa anjima da magrib, za ta sake dawowa’
daga nan ta yi musu sallama ta tafi. ita
kanta tana mai mamakin ci gaban da ake ta samu na lafiyar Innar.
Da Mama da Siyama sai Aisha,
su hud’u ne har Jidda suka zauna har rana lokacin da aka kawo kud’in auren Manubiya daga b’angaren Yashjub.
Maama ta yi matuk’ar mamaki da ta ji sati biyu kacal aka saka
haka itama Aisha da kuma Siyama…Haka su ma su Baba Habu da Kaka Mallan wanda da da farko ya cewa Baba ‘’Ba zai je ba, ai an ja musu layi a tsakaninsu’’
amma tunda ya lek’a ya ga zunduma zunduman motoci a bakin masallacin a take hankalinsa ya tashi!
Haka nan ya je ga Baba Habu akan ya zo su je, har da zaginsa akan ya ce “shi fa ba zai je ba’’.
Cikin gaggawa ya dinga azalzalarsa yana ce masa ’’ai shine Babba, ya yi hak’uri, ya turawa Baba aniyar sa, ya je ko dan zumunci’’
Da fad’a da rarrashi haka nan ya jijjib’oshi, suka nufi masallacin yanata sauri
dan karsu makara…..
Ai kuwa jama’ar wajen sun ga ikon Allah a wajen Kaka Mallan.
Daddy da K’anninsa(Abhi) wanda ya iso daga uk jiya around 3:00am(wajajen ƙarfe ukun dare),
sai Yassir da wani babban Abokin Daddy ne suka zo suka kawo kud’in(naira miliyan biyu)
aka saka rana nan da sati biyu inshaaAllah…kaff cikinsu babu wanda Kaka Mallan bai bi ya karb’i numbersa ba, duk kalar disgin da Yassir ya yi masa da b’ata ran da yake ta yi sai da ya hak’ura ya kula shi ya bashi wrong number…dan ya tsani tsohon, ya tsani layin gaba d’aya,
shi tunda yake a rayuwarsa ma
bai tab’a tunanin akwai
tsukukun layi irin wannan ba, gashi karakakaf layin gida uku ne manya sai masallacin da yake da kyau shima amma gaba d’aya ragowar gidajen kamar kango a ransa ya ce “me Yashjub ya gani da ya zo nan??’’
ya yi wa kansa tambayar, ba tare da ya san wa zai ba shi amsa ba, Kafin ya d’an tab’e Baki a ransa ya ce ‘’koma dai yaya, shi ya sani, atleast zai k’ask’anta kafin ya mutu, dama nan ne ya fi dacewa da shi, shiyasa gashi ya zo nan d’in zai d’and’an k’ask’ancin daganan ya mutu’’
Ko gama tattaunawa ba a yi ba
Yassir ya mik’e ya fita daga cikin masallacin….
Kallonshi kawai Daddy da Abokinsa suka yi, kafin suka d’auke Kai aka ci gaba da tattaunawa.
Dakyar Baba ya yarda da buk’atar da Daddy ya zo da ita ta inda yake cewa’’Dan Allah kar su zo da komai, Yarinyar kawai ake so,
basa buk’atar kayan d’aki’’
Daganan suka tsayar ‘nan da kwanaki goma za su dawo a d’aura aure inshaaAllah’
bayan Baba ya nemi a d’aura a nan masallacin, sun amince.