← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 152

Sashe 79

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali Manubiya ta mik’e da kyar tace ‘’Mommy ki yi hak’uri nice ban yi masa bayani ba”
Sai kuma ta kalli Yashjub tace’’Ya Yash nice na ce su je zan iya…..”
Cikin katseta Mommy ta daka mata wata uwar tsawa, ta hanyar cewa “Ke dallah malama rufewa mutane Baki!”
Ba Manubiya ba hatta Yashjub sai da ya d’an firgita, ya d’aga kai yana kallon Mommy cike da mamaki al’ajabi da rashin jin dad’i.

Cikin b’acin rai da takaici Mommy ta d’aura da cewa
“bana son munafurci da iyayi da kankamba!,
A tunaninki idan kika ce masa ke ce kika ce mu tafi mu barki zai fasa dukan mu ne? Ko kina tunanin ke ce za ki gyara tsakaninmu ko kuma ki sanya ya k’i jin haushin mu?.
Har yaushe kika zo balle ki yi tunanin yin wannan shishshigin???”

Cikin rashin jin dad’i Ummi ta matso tace ‘’haba Mommy, ki yi tunani mai kyau mana, Manubiya fa surukarki ce kuma matar d’anki na farko, a ganinki hakan da kike yi ya dace?
Ai ba wai tana tunanin ita zata saka Yashjub ya yi muku wani abun bane, kawai ta so ta rufe maganar ne ta hanyar cewa ita ta ce ku tafi ku barta.’’

Cikin fushi Mommy ta juya ga Ummi sannan tace ’’Tabbas Ummi kwakwalwarki ba ta da rik’e abu!
Yara sun gaya miki nima na gaya miki amma har kin manta ko? To bari in sake tuna miki yanzu!
Daga yau har abada banaso ki sake yi mini shishshigi…
kamar yadda na cewa Manubiya bana son ta yi mini shishshigi to kazalika kema dan baku da bambanci da ke da ita.’’

Shiruu Ummi ta yi kamar ba za ta ce wani abun ba sai kuma kawai ta juya ta kalli Manubiya tace ‘’ki yi hak’uri, kiyi ta hak’uri, haka rayuwar auren yake duk hak’uri ne a ciki, Allah ya baki lafiya’’
daganan ta juya ta kalli Munirat tace ‘’wuce mu tafi.”
Suna zuwa daff da k’ofa za su fita, ƙasa-ƙasa Ya’isha tace “gara dai duk wanda ya san shi bare ne ya fita, dama hakan ne ya dace a yi tun farko ai.”
Ko kallon ta ba su yi ba haka suka saka kai suka fita.

Suna fita Mommy ta d’aura daga inda ta tsaya ta balbale Manubiya kamar ba surukar ta ba, wanda hakan ya sa hatta su Yasira sai da suka yi mamakin ta, sun san cewa Mommy ba ta son Manubiya, amma ba su yi tunanin za ta iya balbale ta a gaban Yashjub ta ci mata kamar haka ba, dama tun d’azu kafin su baro estate d’in Yashjub suka fahimci kamar akwai abunda ya fusatata sosai a tashi d’aya!! yanzu kuwa sun tabbatar, dan in da ace ranta ba a b’ace yake over ba to da bazata yi wannan b’aranb’atamar haka ba.

Zuwa yanzu Yashjub ya gama fahimtar tabbas Mommy fa ba ta son Manubiya, kawai dama pretending take yi tun farko, dan ko shi Yaro ne abubuwan da suke gudana a gaban idanunsa sun Isa su fahimtar da shi hakan…
Amma meyasa zata dinga pretending a gabansa, sannan me ya fusatata haka?
Dan tabbas ba iyaka maganar Manubiya bace ta harzuk’ata ta har ta kaita ga rufe ta da fad’a haka babu ji babu gani.
Gabansa ne ya yanke ya fad’i da ya tuna incidence d’in (abunda ya faru) jiya yadda Yasmeen ta ce Mommy ce ta turo ta, da kuma yadda tace Manubiya ba ta da ciki, gashi ta dage sai ta yi mata allura!…

Dan tashi d’aya kwakwalwarsa ta bashi anya ba Mommy ce ta turo ta ta zo ta yi wa Manubiya allurar da za ta zubar da cikin ba kuwa?..Dan shi kansa da farko ya yi tunanin rashin kwarewa ne ya sa Yasmeen d’in ta ce Manubiya ba ta da ciki amma da ya zauna ya yi tunani tun a jiyan sai ya fara wani tunanin na daban!
But a bayanin Doctor ya fahimci ita kanta Yasmeen d’in ba lalle ace ta fahimci akwai cikin ba ballanta har su yi yunk’urin zubarwa! Sannan tayaya?how? Mommy za ta bayar da goyon baya a kashe masa d’a?noo! Ba hakan bane ba gaskiya!! Dan babu mahaifiyar da za ta aikata haka ga d’anta, babu ita a duniya!……
Yqsh ya aiyyana hakan a ransa.

A b’angaren Manubiya kuwa, shiruu kawai ta yi ta k’i cewa komai ta sunkuyar da kanta…da farko hawaye take yi kafin daga baya ta daina, tabbas ta gama tabbatar da Mommy ma a bayan y’ay’anta take! duk ba sonta suke yi ba..
dama sai da ta yi tunanin’ta ya Mommy za ta so ta bayan Kausar niece d’inta ce, amman kuma yadda ta nuna sai kawai ta kawar da tunanin, but yanzu kam ta fahimci ashe shigo shigo ba zurfi ta yi mata…dan gashi yanzu idan banda tsantsar k’iyayyarta babu abunda take hangowa k’arara a tattare da Mommyn.

A ko da yaushe k’ok’ari take yi ta ga ta gyara tsakanin su amman ta lura sam waennan sun yi nisa ba sa jin kira… tunda har da mahaifiyarsu a gang d’in tabbas abun ba k’arami bane, sai dai ta d’ukufa gayawa Ubangiji.
Ba za ta tab’a yi wa Mommy rashin kunya ba, kuma bazata k’i ta ba tunda uwar mijinta ce amman fa amma fa idan akwai abunda ta san shi tabbatacce to shine ‘ba za ta yarda da cin fuska ba’
shiyasa yanzun ma sai kawai ta yi shiru, ta k’i ba ta hak’urin da ta yi niyya, kawai ta sunkuyar da kanta k’asa…...

Sai da Mommy ta yi mai Isar ta tukunna ta kalli Yashjub tace ‘’d’azun Ina ka je da ake ta kiran ka ba ka d’auka???”

Kamar ba zai ce komai ba,
sai kuma kawai ya lumshe idanuwa ya bud’e yace‘’d’azun Ina fita sai na tsaya waya, saboda a gani na gwara in tafi da ambulance da sojoji da k’arin y’an kwana-kwana…Ina tsaye Ina wayar na ga driver d’ina ya zo ya yi parking dama na aike sa ne akwai takardun da zai karb’o mini.
yana zuwa ya yi mini knocking glass, ni kuma na bud’e masa d’ayan k’ofan nace ya ajjiye takardun a wajen….a nan ne ya ji wayar da nake yi ya fahimci abunda ya ke faruwa dan haka ya tsayar na gama wayar ya jajantamin yace mu je tare…motar da ya zo da ita ta fi gudu kuma duk na b’ata lokaci wajen yin waya shiyasa na karb’i makullin nace masa ya maida wannan cikin asibiti ya yi parking, sai ya zo
mu tafi…
Ina gama magana sai na ga su Innaa sun fito, gashi arean nan ba a samun abun hawa, shiysa na cewa drivern nawa ya fara yin gaba ni kuma na tafi kaisu gida.”
Sai da ya d’an yi shiruu ya d’an kalli Manubiya kafin ya d’aura da cewa “muna zuwa muka tarar Baba ba shi da lafiya shine na mik’a su asibiti…”
Cikin tarar numfashinsa Mommy tace ‘’saboda ubanta bashi da lafiya shine ka gagara d’aukar wayar uwarka da ubanka??”

Da sauri yace “a’a Mommy, ba haka bane, garin kiraye kirayen wayar da na dinga yi ne saboda yadda na rikice inaga na saka wayar tawa a silent
sam ban ji kiran ku ko d’aya ba wallahi.”

Wani irin kallo Mommy take yi masa kafin chan kawai ta juya ta fice kamar wadda za ta tashi sama ba tare da ta sake cewa komai ba.
Hakama Yassira ta matso da ɗan guntun hawayen ta wai “ta kusan mutuwa saboda tsananin tashin hankali a ɗazu da ta yi tunanin wani abun ne ya same sa ne, ashe shi yana chan yana hidimar gabansa, ya barsu hankalinsu duk a tashe, kuma ya zo amman ko ya nuna damuwar sa akan d’aya daga cikin su. gaskiya abunda yake yi bai kamata ba sam!
Kuma a gaskiya ko dai ya gyara ko kuma su d’au mataki, dan wallahi tsaf sai su fice a harkarsa shima, saboda gaskiya abun nasa ya yi yawa.
ta san shine babba akanta amma dole ta gaya masa ‘he is wrong!’(bai yi dai-dai ba).”
Tana gama fad’in haka ta juya itama a fusace ta fice ..
haka suka juya one by one suka fita zuciya a kumbure.

Su ne suka yi rashin mutunci amma tun daga kan Mommy har izuwa kan Yadira babu wadda ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi, ji suke yi kamar su mutu dan tsabar bak’in ciki!! Takaici!! da tsanar Manubiya wadda ta rufe musu ido ta hanasu walwala, Mommy da Ya’isha har ma da Yasira ji suka yi inama ace bata farfad’o daga sumar da ta yi d’azu ba, kawai da ta wuce lahira…..

…Yarinya sai ka ce y’ar gwal?ace estate d’inka ya kama da wuta amma ka tura ɗan aike kai ka tafi hidimar iyayenta ba ka je ba, ina ma laifin ka saka drivern ya kaisu, sannan da ka gama still ba ka je estate din naka ba ka dawo wajenta saboda ka ji bata d’aukar waya!tabbas ba lalle ma ya san da mutuwar driver d’insa da batun y’an fashin ba, tunda har yanzu bai tsaya ya nutsu ya saurari kowa ba ballantana ya ji bayani……

Su Ya’isha suna fita, Manubiya ta sauk’e ajiyar zuciya ta juyo ta kamo hannunsa.
Tun kafin tace wani abun yace
‘’Ki yi hak’uri, dan Allah Baby ki yi hak’uri, komai zai yi daidai, inshaaAllah, kar ki sa damuwa a ranki”

Ahankali ta d’an yi k’asa da kanta, kafin tace’’ kar ka sa komai a ranka dan Allah, k’addara dama tana zuwarma bawa ta ko wacce irin siga..
InshaaAllah Ubangiji zai mayar maka da abunda ya fi estate d’inka.”
Sai kuma ta kallesa tace”InshaaAllah ma ba duka ne ya k’one ba, sannan Allah ya sa ba a rasa rai ba,ni na warke yanzu…ka je ka ga halin da bayin Allah suke ciki….”

Jinjina kai yayi, ya jata suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace
“ba gobara bane, Najeeb ya ce mini y’an fashi ne, su suka kunna wutar, amma yanzun zan je inshaaAllah, sai in ji komai…”

A hankali tace”Innalillahi wa inna ilaihirrajiun…”
Chapter 79 · 0% Book details