Sashe 118
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da su Abhi suka sake yin d’an k’us k’us d’insu tukunna Daddyn ya d’auki waya ya kira Ummi daganan ya kira manyan drivers d’in gidan da aka dad’e da su, yace “su zo!”
…Manubiya abar tausayice, duba da zargin zubar mata da ciki da suke yi, sannan Yarinyar ba ta da matsala ga kuma tarbiyya da hankali uwauba d’ansu yana sonta..he’s happy with her!.
Amma kuma Tabbas ya kamata a ja mata layi kar ta haura iyaka kar ta haura matsayinta, dan ba zai you su je garin tausayi su kunnawa wani haske su kuma su k’ona kansu ba…soyayyar Yashjub a gareta ta yi yawa!! Amma dukda hakan ba su damu idan ya so ta da yawan ba! kawai su mtsalarsu mahimmanci da kuma power da ya bata waenda su ke k’ok’arin danne su da k’imar su a idanun Yashjub ɗin.
Sannan ba a yiwa mace haka! Dan idan su ka zuba ido to a gaba za su samu babbar matsala.
Tunda akayi auren yake haka wanda inda ace gigin amarci ne to da tuni ya daina amma abun nasa k’ara gaba ma yake yi.
son da Yashjub ya ke yi mata ya yi yawa…ba sa jin haushinta saboda hakan hasalima su tausayi take basu na halinda take ciki ammafa fa hakan ba shi zai sanya su zuba ido Yashjub ya zama boyi boyi ba.
Sun san idan ya riga ya auri Kausar, ya saba zama da mata biyu to ko ya rabu da Kausar ɗin bayan ta haihu kamar yadda aka shirya ba lalle ya iya zama da mace d’aya ba…
Idan aka barwa Manubiya Yash ita kad’ai akwai gagarumar matsala….
Dan haka suka ga dacewar su jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya……
Yana gama waya da su Ummi ya sauk’e ajiyar zuciya ya yi shiruuu, yana mai jin kamar ya d’aura Hannu a ka! ya kurma uban ihu…wai yau shine da kansa zai aurawa Kausar Yashjub!
Tabbas shiyasa ba a son mutum ya tsananta tsana!saboda ba ka san inda rana za ta fad’i ba.
….
Sai da aka kusan yin fad’a da Daddy da Ummi da ta ji wai aure za a d’aurawa Kausar da Yashjub…so ta yi ta fita ta kira shi ta sanar da shi, amma Daddyn ya ce ta zauna Abhi kuma ya shiga bata Baki….ga drivers d’in gidan a zaune sun yi jigum suma kawunansu a k’asa,shiyasa Abhi ya dage ya lallab’ata ba dan ta so ba ita kuma ta hak’ura ta zaune ta na mai jin kamar zuciyarta za ta fito!!
babu yadda ta iya haka nan tana ji tana gani aka d’aura auren Kausar da Yashjub akan sadaki naira dubu d’ari, tq inda Abhi ya yiwa Yashjub wakili Daddy kuma ya yiwa Kausar.
Ba abunda ya fi d’aurewa Junior Kai kamar rikicewar da Yassir ya yi, Dan ba da shi ma aka yi d’aura auren ba korarsa su Abhi suka yi ganin yana shirin yi musu hauka, da kyar kuwa ya fita yana huci ya nufi side d’in Kausar, amma sama ko k’asa ba ta nan, kuma wayoyinta duk gasunan a zube a kan gado.
Ita kuwa Kausar b’uya ta yi a box room na floor ɗin, saboda shi…
tana kallonshi ya sauk’o a rikice ya nufi side d’in nata, sai da ya fito ya sauk’a chaan k’asa tukunna ta fito ta shige dan ba ta shirya fuskantar shi ba saboda Bata gama had’a wayon da za ta yi masa wannan karon ba.
Dukda tana zullumin son jin dalilin yanayin da ta gansa a ciki amma za ta bari ta ji zuwa gobe.
A b’angaren Mommy kuwa, ta fito kenan za ta tafi wajen Baba larai ta ji ya ake ciki ta ga Yassir ya sauk’o kamar ma yana kuka, shiyasa ta kasa hak’ura ta haye saman..ai
kuwa tun kafin ta k’arasa jikin k’ofar sosai ta fahimci d’aurin aurene ake yi….
Hamdala da sujjada ta yi, sai da ta ji an ida d’aurin auren tukunna ta juya ta nufi side d’in Kausar har tana tuntub’e.
A b’angaren su Daddy kuwa ba a tab’a d’aurin auren da babu wanda yake farinciki ba sai a yau! Kaff wajen babu wanda yake
farin ciki da d’aurin auren hatta drivers d’in da aka kira su ka yi
shaida ba su yi murna da wannan al’amarin ba, dan su kansu sun san Kausar ba ta dace da Yashjub ba, gashi bai dad’e da yin aure ba.
Junior ji yake kamar yayi kuka dan takaici, saboda gani yakeyi kamar hakan duk laifin sa ne
amman kuma shima bashida yadda zai yi ne, dan ba zai je garin taimakon Yashjub shi kuma ya lalata nashi relationship d’in da bai ma samu ya fara ba, tare da mutunci, martaba da kuma sunansa gaba ɗaya..
Su Daddy suna gama d’aurawa kuma sai suka fara da na sani..kamar irin ba a cikin haiyyacinsu suka d’aura d’innan ba.
Babu tsoron wadda ya fi rufe su a take a lokacin kamar na Hajiya mama!!
dan haka suka d’aura alhakin gaya mata a kan Ummi…a ganinsu tunda tana ji da ita
tabbas za ta san yadda za ta yi mata bayani ta fahimta ta kuma taushe ta ta hak’ura.
Ummi Tana gama jin bayanin su tace”to”kawai, daga haka ta juya ta fice ranta a mugun b’ace.
A b’angaren Yassir ma zuwa yanzu ya gama rikicewa, dan yana k’asa drivers d’in suka sauk’o ya tambayesu suka ce “eh an d’aura”
bai ma san mataki na gaba da ya kamata ace ya d’auka ba, shiyasa kawai ya zauna yayi shiruuuu dan kwakwalwarshi ta d’auke ta tsaya daga aiki.
Mommy tana shiga d’akin Kausar ta sameta a tsaye dan itama shigowar tata kenan.
Murmushi Mommyn ta yi, kafin ta k’arasa inda Kausar d’in take ba ta damu da yadda ta turo Baki ba dan ta san yanzunnan za su shirya…
Cikin tsananin farin ciki tace
“Ki yi mini alk’awari
goron albishir d’innan da zan baki yanzu shine za ki daina fushi da mu!!”
Gabanta ne ya yanke ya fad’i, a ranta ta shiga adduar “Allah ya sa hasashenta dai dai ne, Allah ya sa tarkonta ya kama kurciya”
A fili kuma sai ta kalli Mommyn tace”Inajinki”
Cupping fuskarta
Mommy tayi kafin tace
“Ki yi mini alk’awari tukunna!”.
Juya ido Kausar ta yi
kafin tace “okay fine!yawan farin cikina yawan daina fushi da ku”
Dariya Mommy ta yi sannan tace mata”Y’ata ta girma, ta zama matar aure
Matar Yashjub imam kura
yanzunnan Ubangiji ya yi ikonsa.”
Tun Mommy tana murmushi mai had’e da dariya har ta zo ta daina dan Kausar ta k’ame k’am!!!
Ta ma kasa yin ko motsi.
Sai da Mommyn ta d’an jijjigata tukunna hawayen farin ciki suka zubo mata,a hankali ta kama Hannunuwan
Mommy biyu da suke rik’e da kumatunta, idanunta na zubar da hawaye tace
“Mommy da gaske kike,
Dan Allah ki yi mini wasa da komai banda wannan”.
“Wallahi da gaske nake”
Mommy ta fada mata tana murmushi tana goge mata hawayen nata.
Fad’awa ta yi jikin Mommy kawai ta fashe da kuka…dai dai nan su Yassira suka shigo ita da su Yusra cikin farin ciki sukace
“Mommy da gaske ne abunda muka ji Ummi tana waya yanzu tana fad’a???”
Jinnjina musu Kai ta yi still tana rik’e da Kausar dan ta k’i ta cika ta har yanzu…
Aikuwa a take gaba d’ayansu suka taho suka had’asu suka rungume…
Farin ciki a ranar dai ba mahaluk’in da ya kai su Mommy.
Kausar bata ɗauki lokaci ba ta nemi yafiyar dukkansu, na ganin kamar sun daina sonta da ta yi, dan yau kam ta tabbatar da suna k’aunarta duba da yadda suke taya ta murna.
Cikin farin ciki suka wanzu a ɗakin kowaccensu Baki a washe Yasmeen ce kawai babu a wajen.
A ranar suka yi alk’awarin had’e kansu guri d’aya har Baaba Larai!
Sannan A samu su taimaki Kausar su tsaya mata ta yak’i Yashjub
su ga bayan Manubiya.
Cike da farin ciki Mommy take kallon y’an matan nata, batasan lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba….
Ahankali Baba larai ta kamo hannun Mommy tace
“Kar ki damu, na san hawayen me kikeyi inshaaAllah family d’inki ya kusan zaman complete.“
…..
Yassir so yake ya je wajen Kausar, amma ya san tana tare da su Mommy, dan tun d’azu da ya hawo da niyyar sake dubata ya ga su Yasira sun shiga bai ga sun fito ba.
shiysa ya hak’ura ya d’aga musu k’afa dan ya san yana shiga a haka akwai matsala, kuma ya riga ya gama yi mata alk’awarin ba zai fallasa plan d’insu a kowa ba, za su yi komai cikin sirrine.
Kishi da tashin hankali haɗe da bak’in ciki duk sun taru sun rufesa, ya san Kausar ba ta haramta a garesa ba, kuma ya san a yau idan ya ce a warware auren ba shi da matsala da ita sai dai Mommy, dan haka ya tsara akan
za su zauna shi da Kausar da Yashjub gobe inshaaAllah, a warware ba tare da su Momy sun ji ba ,tunda duk su ukun ba so suke yi ba.
Sai da ya kai ga wannan matsayar tukunna ya d’an ji sanyi a ransa..amma fa dukda haka kishi sai da ya sauk’ar masa da wani zazzafan zazzab’i..dan idan ya tuna cewa yau fa Kausar matar wani ce sai ya ji kamar ya cinnawa gidan wuta.
Shiyasa kawai ya wuce side d’insa bayan ya tura mata message yace”ta kirasa idan ta zama free.”
Yana shiga d’akinsa ya ware ac ya rage kayan jikinsa
ya kwanta akan tiles flat
daga shi sai boxer yanajin yadda kansa yake wani irin sarawa.
Assurance yake bawa kansa yana sakewa cewa”Yashjub ma ba zai yarda da wannan had’in ba! dan haka ba shi da matsala ta koina, InshaaAllah a gobe za a ware auren daganan duk abunda su Daddy za su yi wannan daga baya kenan! kuma ko sun yi fushi ya san za su huce.”
Yana waennan tunane tunanen
zazzab’in jikinsa ya nunku!….ya dad’e yana fama kafin ya samu ya d’an ragu, daga haka wani bacci mai nauyi ya yi gaba da shi………..