Sashe 82
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya Yasira ta sauk’e kafin tace”Mommy nima gaskiya abunda kika yi yau ban ji dad’in sa ba….”
Cikin tarar numfashinta Baba larai tace”Yasira yo
ai har da ku!”
Jinjina kai Yasira ta yi kafin tace”ni kam zuwa yanzu Baba larai duk yadda kika ce inshaaAllah hakan za ‘a yi,saboda hakan ne kawai mafita,gara in jure ta, in nuna ina sonta in ja ta a jiki na wata d’aya ko biyu, akan mu rayu da ita har abada, muna fama da ita tana janyo mana masifu kala kala, na tabbatar kashe Ya Yash da aka so yi a yau shima duk a cikin masifun da take tafe da su ne!.”
Cikin sauk’e ajiyar zuciya ta kamo hannun Baba larai ta ci gaba da cewa”dama ai ya san za mu je mu tayata gyaran gidan ko?” ba ta jira jin mai Baba laran za ta ce ba ta d’aura da cewa”zan yi wa Yasmeen magana ita da su Yusra. na yi miki alk’awarin inshaaAllah daga yau mun chanza zani, amma Ya’isha ba za ta bimu ba dan na san za ta iya b’ata mana komai…ki had’a duk wasu abubuwan da ya kamata inshaaAllah wannan karon ba za mu baki kunya ba, za ki sha mamaki…”
“Allah ya yi miki albarka Yasira, zuwa dare zan ganku ke da su Yasmeen d’in kafin ku tafi”
Jinjina kai Yasira ta yi kafin ta kalli Mommy tace mata”Daddy yana son ganinki…”
Daga haka ta juya ta fita ta rufo musu k’ofar….
Tana fita Baba larai ta saki murmushi dan tabbas ta hango jajircewa a idanun Yasira, ta san kuma su Yasmeen ma za su yi mata biyayya inshaaAllah wannan karon akwai nasara….cikin jikin Manubiya za su fara farma, a yadda Yash yake ji da cikin nan ta san cikin sauƙi za su samu matsala da shi da ita idan har suka nuna masa kamar Manubiyan ce ta zubar, amma tayaya za su nuna masa hakan??dole su nemo dalilin da zai yarda da shi……
Tana wannan tunanin ta ji Mommy tace”bari in je…”
Kallonta Baba larai ta yi kafin tace”Juyin duniya!Khadija, kar ki kuskura ki bari ya fahimci kin san wani abun”
Jinjina kai Mommy ta yi gabanta yana dukan uku-uku, ta juya za ta fita…cikin son kwantar mata da hankali Baba larai ta ruk’o hannunta tace”ki kwantar da hankalinki…”
Hawayen da suka b’allewa Mommy ne suka sanya ta kasa ci gaba da magana,a hankali ta isa gareta ta rungumota ta shiga rarrashinta..fashewa Mommy ta yi da kuka cikin kukan tace “dan Allah dan annabi larai kar ki sake cewa za ki tafi,a wannan worst situation d’in larai idan kika tafi kika barni Ina makomata??…”
Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e ta cikata tace”babu inda zan je amma Khadija kema sai kin chanja zani!kamar yadda su ka yi alk’awari dan Allah kema ki gyara…mu samu Yarinyar nan ta tafi daganan mu aura masa Kausar bayan shekara d’aya ko biyu idan ta haihu muka samu abunda muka so sai mu k’arasa shirin mu a samu a rufe chapter nan, wallahi na gaji, sai abu d’aya ake yi yau kusan shekara nawa amma ba riba!”
Ajiyar zuciya Mommy ta fesar kafin tace”Larai, ba zan iya yarda da Kausar akan lamarin Yashjub ba yanzu kam…saboda a da na d’auka soyayyar da take yi masa mai sauk’i ce ko kuma lust(sha’awa) ko wani abu makamancin hakan, shiyasa har na yi tunanin ‘idan ta auresa suka yi shekara d’aya ko biyu, ta samu abunda takeso, ta haihu ta d’an zauna da shi, ya fara fita a ranta to za ta iya yi mana abunda mukeso, dan na san tunda ba ya sonta to musguna mata zai ta yi…’
amma yanzu kam na fahimci masifaffiyar soyayya take yi masa, kuma duk runtsi za ta tsaya masa za ta tsaya a tare da shi ta so shi so ba na wasa ba ma kuma a ko wanne irin yanayi!!!
Abunda Yasmeen ta yi mini akan batun zubar da cikinnan ya sanya na fahimci ‘Yaran nan fa ba za a dad’e ba kowacce za ta fara fito da nata ra’ayin da abunda ta ke so itama tana jayayya da ni’
kuma indai har Yasmeen ‘y’ar cikina’ za ta iya yi mini hakan, to abu mai sauk’i ne ga Kausar dan ta bijere mini, shiyasa na gama yankewa akan
‘babu maganar Kausar da Yashjub’! Ba zan bari ta auresa ba!.
Za mu san yadda za mu yi dai, dan gaskiya ba zan taɓa yarda in iya trusting Kausar akan wannan Lamarin ba…..”
Shiruu Baba larai ta yi kafin tace”to amma kuma ta ya za mu samu wanchan abun kenan? Ko mun b’ata shekaru a banza kenan? Ki duba future d’in Yassir, ki sake tunani….”
Sai kuma ta yi shiruu da maganar ta d’an yi tunani kafin tace”to ko Manubiya za mu jira ta haihu, inyaso idan ta haifa sai mu rik’e…….”
Cikin katseta da d’an b’acin rai Mommy tace”haba larai!ke fa da kanki ki ka sanar da ni illar kasancewar Manubiya a tare da Yashjub, kuma gashi muna gani muraran!…bayaga haka ma ko dan masifar da wannan cikin da Uwarsa da Ubansa suka sakani a ciki wallahi dole sai ya fita! Ko ana ha maza ha mata……”
K’ausar tana hawaye, a haka ta k’arasa side d’in Mommy, ta shiga ta wuce parlourn ta nufi bedroom, har za ta tura k’ofar d’akin ta shige kawai sai ta ji Mommy tana cewa”babu maganar Kausar da Yashjub’!Ba zan bari ta auresa ba!.
Za mu san yadda za mu yi dai…..”
Wani irin duhu-duhu dishi-dishi Kausar ta fara gani da ji, ko ƙarshen maganar mommyn ma ba ta iya ta ji ba tsabar bala’i …ita da ta zo a kan ta cewa Mommyn ‘mai zai hana a yi tricking Yash (a shirya masa tarko), ta samu ciki, ta yadda dole sai ya aureta…’
amma shine take jin wannan batun daga bakin Mommy??
Dama ita ba ta yi shirin gaya mata tana da ciki ba, dan ta san ba za ta yarda a aurawa Yash ita da cikin Yassir a jikinta ba, shiyasa take so ta bata wannan idear ta yadda ko shi Yassir d’in bai Isa ya san cikin nasa bane kawai kowa a tafi a kan cikin Yash d’in ne,ta samu ta rufawa kanta asiri burinta ya cika.Sam ba ta yi tsammanin haka daga Bakin Mommy ba, wato ta barta ta gama lalacewa shine yanzu take kyamar ta had’a d’anta da ita kenan ko yaya?
tabbas blood is thick(jini ya fi ruwa)! Ita kuma ta tabbata ba ta da kowa kenan!!….
Wani Irin kuka ne ya taho mata, dan haka ta yi sauri ta juya gudun ma kar su jiyo ta, ta nufi k’ofar parlourn hannunta a kan bakinta tana mai k’okarin hana sautin kukan nata fitowa.
Kusan karo suka yi ita da Daddy wanda ya turo k’ofar parlourn ya shigo.
Shi ya wuce ya nufi d’akin ita kuma ta fice ta nufi d’akinta tana kuka kamar ranta zai fita.
A tsaye ya same su ita da Baba larai….sum sum haka Baba larai ta sa kai ta fice bayan ta yiwa Mommy wani kalar kallon da su kad’ai su ka san me take nufi.
Tana fita ya lumshe idanuwansa ya d’an bud’e kafin ya k’arasa kusa da ita yana mai kallon cikin idanuwanta yace”mallan lawal ya rasu”
Gefe da gefe ta kalla kamar irin tana tunani d’innan kafin tace”Daddy mai ya faru??? Kai fa ka ce a daina maganar nan kuma yau kai da bakinka ga shi ka kawo ta?”
K’ura mata ido ya yi, dama yana so ne ya ga reaction d’inta (yadda za ta yi), wai ko zai iya kamata da laifi amma sai ya ga babu alamun hakan a tartare da ita!
Ya san yadda Mommy ta kula da mahaifiyar Yahanasu, suka zauna lafiya!!! Shiyasa yake ganin kamar idan ya zargeta a kan al’amarin da ya faru a baya to bai yi mata adalci ba, wanda dalilin zargin ya samo asali tunda mallan lawal ya kirasa d’azu ya fara basa hak’uri yana cewa ‘yana son magana da shi’
to tun daga nan ya fahimci anya ba sharri aka k’ullawa Khadijansa a wanchan lokacin ba kuwa! Dan kansa ya d’aure matuk’a ta inda a baya yake da tabbacin mallan lawal d’in ya rasu tun shekaru wajen ashirin da bakwai baya amma yanzu gashi ya ji sa a raye ɗazu, dan ko a mafarki idan ya ji muryar mallan lawal sai ya gane, shiyasa tashi d’aya ya tabbatar akwai k’umbiya-k’umbiya a cikin al’amarin..
Khadija ba ta shiga ko mak’ofta sai tare da Mommy, kuma ko hayaniya ba ta tab’a yi da kowa ba, ita ba ma ta iya fad’an ba…..
duba da haukar da Mommy ta yi a lokacin da yace zai k’ara aure da kuma yadda ta shiryu lokaci guda ta rungumi amaryar(khadija) tashi d’aya dama tun a wanchan lokacin ya ke zarginta, kuma ya ke ganin kamar akwai abunda ta ke shiryawa, amma bai yi tunanin za ta iya yi mata wanchan sharrin ba!
Sai dai kuma in dai har sharrin ne aka yi mata da gaske to mommyn ce saboda Khadija ko y’an uwa ba ta da shi balle ace wani ne ya yi mata sharri sannan bata da Abokin faɗa!! Dan haka tabbas wannan aikin Mommy ne…
Sannan a cikin gidan ya yi waya da Mallan lawal, dan haka ya san wataƙila Baba larai ce za ta gaya mata, shine ta kashe sa kenan??gudun kar asirin ta ya tonu?Tabbas kuwa indai hakan ya tabbata to bai ma san wanne kalar hukunci zai yanke mata ba!
Matsalar guda d’aya shine yadda ta yi d’innan wanda ba dan shi da kansa gaba d’aya alamomi suna masa nunin kamar ita ce master mind a al’amarin ba, to ba dalilin da zai sanya ya zargeta.
A b’angaren Mommy kuwa in banda lugude babu abunda zuciyarta take yi!k’arfin hali ne kawai take, amma a mugun mugun hargitse take tun lokacin da ya shigo ta firgice…