Sashe 138
Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A b’angaren Yassir shima yanzu ya sake hawa ya koma gidan jiya..saboda da farko ya ji tsoro matuk’a, amma yanzu da ya d’inke da Abokinsa ya gaya masa komai ya samu goyon baya d’ari bisa d’ari daga wajen Abokin nasa sai zuciyarsa ta sake bushewa musamman ma da ya tabbatr video d’in a iyaka family yake yawo bai je ga hukuma ba! tashi d’aya tsoronsa ya kau!
Kuma ya ji Mommy tana cewa sharri aka yi masa, dan haka zai fake da sharrin aka yi masa ya dage har sai su Daddy sun yarda ya samu sun shirya.. daga nan zai yi mai kankat dan Abokin nasa yace”InshaaAllah zai tsaya masa zai taimaka masa su ga bayan Yashjub, kuma ba za su sake tura wani ya kashesa ba! saboda kar a sake samun matsalankamar lokutan farko! Next time kawai sakawa za su yi a d’auko musu shi su kashe sa da Hannunsu.
But first, ya samu ya fara wanke kansa ya shirya da su Daddy, inyaso daga nan sai su k’addamar da shirinsu saboda yanzu wani abun yana samun Yash shi za a zarga.”
A ranar da daddare Ya’isha tana tafiya daga gidan su Manu, itama Baraka ta je ta karb’o garin maganinta wanda za ta barbard’a ta haukatar da Inna, dan zuwa yanzu tace ‘ba za ma ta sakata jinya ba, haukatata za ta yi dan sai ta fi wulak’anta idan ta haukace akan jinya.’
Sam ba ta da mu da sharad’in bokan ba da yace mata”idan ta b’arbad’a abun Inna ba ta bi ta kai ba to itace za ta haukace”
Tashi d’aya tace masa “ta amince!”
Hakanan ta zube masa mak’udan kud’ad’e ta amso ta taho saboda ta san a inda za ta zuba ta yadda dole innar sai ta bi ta kai, ai abun ma ya zo mata da sauk’i tunda yace”kowa zai iya bi kawai dai ta tabbata itama Innar ta bi ta kai.Kuma awa ashirin da hud’u abun zai yi bai lalace ba saboda yana da k’arfi.”
Dan haka ta san babu ta inda za a samu matsala, kuma ta gama tsarawa ne akan a bakin k’ofar ban d’akinta za ta zuba, inda ta san ko cikin dare ko da safe ko da rana dole ta shiga ta yi uzuri ta yi alwallah!
ai Inna ta tafka babban kuskure tunda har ta bata damar shigar mata ɗaki anyhow sannan a duk lokacin da ta ga dama! Dan haka tunda har tana da access da bedroom ɗin innar to komai ta san zai zo mata da sauƙi….…
Hakanan, Baraka tana ta sak’e sak’e a ranta ta iso gida, jakarta kawai ta ajjiye, ta nufi cikin gidan…a nan ta samesu duk d’insu gaba d’aya har Baba ana hira, inna kuma tana zaune a kan darduma tana lazimi dan har ta yi shirin barci.
Tana shiga suka fara tambayarta “ya jikin maman Abbakar d’in”
Itq kuma tace musu “da sauk’i,”
daga nan ta fara rarraba ido…lucky for her ta ji Manubiya tace mata”ya yi barci, yana d’akin Inna, in kun zo tafiya sai in d’auko miki shi.”
Ita ba ma shi ɗin take nema ba, amma daga jin hakan ko gama rufe Baki ba ta bari Manubiya ta yi ba ta yi wuff ta mik’e ta afka d’akin tana mai cewa”ai
yanzu za mu tafi ma, bari in d’auko shi!”
Tana shiga ta tura k’ofar ta mayar ta rufe,sai da ta zuzzuba tukunna ta mayar cikin bra d’inta ta d’auki mai sunan Baban ta fito ta yi musu sallama ta tafi, yau ko jiran ya Musbah ma
Bata tsaya ta yi ba…shima kuwa ya yi zamansa, har sai da ya gama zancensa da Hadiza tukunna ya koma kuma da ya je ya balbaleta da masifa dan bai
san da zancen zuwanta dubo maman Abbakar da daddare ba sam ba ta tambayesa ba, sannan yace”idan Inna tana cikin d’akinta to za ta iya shiga amma in har Inna ba ta ciki kuma babu kowa a cikin d’akin to kar ta sake afka mata d’aki kamar yadda ta yi d’azu, tunda d’akin ba na sa’arta bane ba!”
Saboda shi har ga Allah haka kurum bai yarda da shigar tata da ta yi ba da yanayinta na yau ɗin gaba d’aya duk bai yarda da ita ba.
Ga mamakinsa har k’asa Baraka ta durk’usa tace”ya yi hak’uri ba zata k’ara ba!”
Ita kuwa a ranta cewa tayi “kar ka damu,zuwa gobe mai karekan ba za ta sake samun dama ba!daganan wallahi ko
kara idan na ajjiye baka isa ka shallaketa ba.!!”.
BULAMA ✍️
0903 441 3252
*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 43*
Ya Musbah yana tafiya su Inna ma suka fara k’ok’arin shiga domin suma su samu su kwanta barci, dan Baba shi kam ya jima da wucewa d’akinsa tun lokacin da suka gama yiwa Yash da Daddy gaisuwa, ya wuce ciki abunsa…
Hijab d’inta ta cire ta linke ta ajjiye a kan dardumar, tukunna ta d’auka bayan ta had’e su waje ɗaya ta yi folding d’insu, sannan ta tsaya kawai tana kallon Hannun kujera inda ta ajjiye hularta tun d’azu da Magrib lokacin da zata yi sallah amma da ikon Allah yanzu ba ta ganta a wajen ba.
Manubiya ta kalla ta kalli hular kanta wadda gwaggwo Suwaiba ta basu tsarabarta su biyu iri d’aya tace”Manu hularki ce a kanki ko?
Ni Ina tawa??”
Murmushi Manubiya ta yi tace”
Dama na sani!”
sai kuma ta d’aura da cewa”ai dama kinsan Siyama tace itama kalar take so..ba ta son kalar tata ita da Jidda!
bani da tantama itace ta d’auke takin a tunaninta tawa ce na ajjiye shine ta d’auke ta tafi da ita!”.
Shiru Inna ta yi kafin tace”Anya kuwa?
Kuma inda ace ita ta d’auka ai da na san za ta ajjiye tatan..
kuma ai kafin Magrib Siyama ta tafi,ni kuma sai da na zo yin sallar Magrib d’infa tukunna na cire!.”
Cikin tarar numfashinta gwaggo Suwaiba tace”To,watak’ilan mai sunan Baba ne ya d’auka ya saka a wani wajen.
yanzu dai mu je mu yi barci, idan Allah ya kaimu gobe da safe sai a duba!.
Idan ma ba a samu ba, sai in je kasuwa in siyo yadi kalarsa ai ba za a rasa ba, duk ku hud’un sai in had’a Hadiza ta kai tela ya d’inke a yi muku iri d’aya, kinga an huta ai ko?”
Dariya Manubiya ta yi kafin tace
“Allah ni fa Ina tunanin Siyama ce ta d’auke! Ta yi tunanin tawa ce, saboda fa tunda ta ga tamu(ni da Inna) tace ita za ta yi anko da Inna, kuma kalar ta fi so dan shine favorite colour d’inta, shiyasa ni kuma tun d’azun har ta tafi har bayan ma ta tafin ban yarda na cire ba!
Tsabar yadda na saba da hular a kaina”
tana dariya ta ci gaba da cewa
“wuyan Hijab d’ina ma fa ya yi mini kad’an amma haka nake d’aurawa a kan hular ina yin sallah tun d’azu”.
Ta fad’i hakan tana dariya…..
daga haka suka nufi d’aki gaba d’ayansu…ita dai Inna abun ya d’aure mata kai, saboda har bayan tafiyar Siyama fa hularta tana kanta…amma kawai sai ta tsaya akan watak’il mai sunan Baban ne ya d’auka ya jefa a wani wajen, dan haka ta bari akan gobe da safe idan Allah ya tashemu lafiya sai ta duba!!!!.
Manubiya da gwaggo Suwaiba ne kawai suka shiga suka kama ruwa suka yi alwallah, dan ita Inna da alwalarta, dardumarta da Hijab d’in kawai ta ajjiye ta kwanta saboda haka kurum ta ji ta wani iri ga kuma kasala!!!
da mugun kyar ma ta iya kaiwa kan gadon, tana kwanciya kuwa wani wahalallen barci marar dad’i ga takura ya yi awon gaba da ita….
Su kansu su Manu sun yi
mamakin baccin da Inna ta yi nan da nan gashi a karkace ma ta kwanta amma sai sukayi tunanin wataƙila ko gajiya ce, Manu ce ta d’aura mata Kai a kan pillow tana mamakin yadda take fitar da numfashi da kyar, daga haka ta rufa mata abun rufa ta d’an rage k’arfin ac dan a tunanin ta sanyin ne ba ta so…daga nan suka d’an tab’a hira ita da gwaggo Suwaiba suka yi addu’o’i suka bi gado suma.
Da asuba!!…kiran sallar farko ne ya farkar da Manubiya da Gwaggo Suwaiba.
Band’aki gwaggwo Suwaiba ta wuce, yayinda Manubiya ta d’an zauna a kan gadon ta yi shiruu har sai da ta wartsake sosai tukunna ta juya cike da mamakin Inna ta shiga tashinta, dan kullum idan suka farka a zaune a kan darduma suke tadda ita.
Sau uku ta kira sunanta tana mai d’an tab’a mata Hannu amma shiruu…cikin tashin hankali ta mik’e ta k’arasa ta kunna wutar d’akin ta koma gareta da sauri ta shiga k’are mata kallo tana kiran sunanta kafin ta zauna a daidai kanta a firgice ta d’an shafa fuskarta ta ajjiye Hannunta daidai saitin hancinta.
A firgice cikin tsananin masifaffen tashin hankali! firgice da tsoro ta tashi daga kusa da ita da mugun sauri ta d’an ja baya ta tsaya a kanta tana ci gaba da kallonta jikinta yana wani irin karkarwa!
Daidai nan gwaggwo Suwaiba ta fito daga band’akin…yanayin Manubiyan ne ya sanya ta yi saurin k’arasawa inda take ta ruk’o hannunta itama idanunta suna a kan Inna tace”me ya faru?”
Ta yi mata tambayar jikinta itanma yana karkarwa dan yanyin yadda Innar take a yashe da kuma yanayin Manubiya sun mugun firgigita.
Juyowa Manubiya ta yi ta kalleta dai dai nan hawaye suka samu damar b’alle mata cikin tashin hankali tana magana da kyar tace”ba ta numfashi, kuma jikinta ya yi sanyi”
Ta yi mata maganar tana mai nuna mata Innar da yatsa…
Da kyar Gwaggo Suwaiba ta samu ta yi namijin k’ok’ari wajen k’arasawa inda Innar take ta zaune a gefenta ta shiga dubata…..tashi d’aya ta fashe da wani irin rikitaccen kuka ta shiga ambaton “innalillahi wa inna ilaihirrajiun!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!!!”.
Luuu!!! haka Manubiya ta tafi ta zube a wajen sumammiya…….