← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 152

Sashe 125

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da farko ce mata kika yi ‘a’a’ amma da ta ci gaba da tsara ki Mommy saboda tsabar son kai da son zuciya tashi d’aya kika amince a yi mini duk wa’ennan abubuwan!
Duk dan kar in tona miki asiri, kuma kar in k’i amincewa da ke a matsayin mahaifiyata a lokacin da kika gama tsara plans d’inki kika gama duk abubuwan da kika shiryama yi, kika shirya karb’ata kika shirya gaya mini ni y’arki ce.”
Cikin kukan Yahansu ta ci gaba da cewa
“sam ba ki yi tunanin hakan da kika yi mini zai iya shiga tsakani na da aure ba!.”
ta k’arashe maganar tata cikin fashewa da kuka…..kafin ta ci gaba da cewa
“Ina tsaye a wajen Ina kuka har Baba larai ta fito daga d’akin naki ta ganni. na san ta san idan kika ganni a haka kika fahimci na ji komai to za ki karaya ne, kuma ta san akwai matsala, shiyasa a wannan lokacin ta toshe mini Baki ta ja ni d’akinta ta zaunar da ni….

Ita kanta na san a wanchan lokacin ta sha mamaki na, dan bata yi tunanin na yi wayo har haka ba saboda duk yadda ta so yi mini wayo ni kuma na k’i bata k’ofa, kuma ta fahimci na san komai na kuma gane komai, inaga shiyasa ta je ta yi tsafe tsafenta ba tare da ta sanar da ke cewa na ji komai ba.

Na san da ke da ita duk kun d’auka asirinku ne ya yi tasiri a kaina na daina shiga jama’a kamar yadda kuka tsara amma a asalin gaskiya Mommy tsanar ki! bak’in cikinki! da haushinki ne suka maidani na zama abunda na zama har kawo yanzu.”
..
Sai a wannan gaɓar tukunna Mommy ta iya tsayar da kukanta da kyar tace”Yahanasu dan Allah kar ki ce kin tsane ni! Komai da kika ga na yi wallahi duk na yi ne saboda ku!”

Cikin d’an d’aga murya Yahanasu tace”saboda ke dai Mommy! duk abunda kika yi saboda kanki kika yi!!!.
Mommy kina kallo fa tun Ina y’ar k’arama ko jama’a idan na gani kuka nake yi, hakanan na tsani komai na tsani kowa nima kuma Mutane suka tsane ni..
Kina ganin yadda aka dinga yawo da ni k’asashen waje domin a gano matsalata, na dinga shan wahala! daga k’arshe aka ce depression gareni lokacin ko shekaru sha biyu ban kai ba amma mommy ba ki yi motsin komai ba.
Sau nawa ana fasa d’aurin aurena!!kin san bani da kowa ba ni da komai amma Mommy haka kike murzawa idanunki toka ba kya zuwa ki dad’e da ni ki ji ainihin matsalata saboda kar a zargeki kar asirinki ya tonu.

A gaban idanunki su Yasira suke yi mini duk wani kalar cin kashi, amma sai dai ki zuba ido kawai idan anyi sa’a shine za ki ce musu su daina amma ba ki tab’a tsawatar musu ko kuma ki tsayamini ba.!
Ta ina hakan ya zama ba son kai ba ba??
ta ina hakan ya zamo duk a ta dalilin neman farin cikina ne????”
Yahanasu ta yi mata tambayar cikin d’aga murya.”
Cikin share hawaye ta sake cewa”kuma ko tsafin ma da kuke tunanin shine ya yi tasiri a kaina ba ki fa tab’a yunk’urin gyarawa ba dukda kuwa tarin duk waennan wahalwahalun da na sha a rayuwa, amma a haka kike tunanin idan kika ce mini ke mahaifiyata ce a gaba zan karb’eki in yafe miki saboda kina tunk’aho da kin yi mini asiri ko?”.
Ba ta jira Mommyn ta bata amsa ba tace”Never!!!”
Sannan ta d’aura da cewa”Mama Khadija itace mahaifiyata har gaban abada, shiyasa ma kika ga kawai na zuba miki idanu ban tab’a tunkarar ki da komai ba saboda ban d’auke ki uwa ba!.
kamar yadda kema ba ki damu da ni ba nima haka ban damu da ke ba…
na san a baya a lokacin da na ji maganganunku na shiga tashin hankali ga k’arancin shekaru ga kuma rashin wanda zan tattauna maganar da, to amma believe u me wallahi wallahi Mommy yanzu abun ba ya gabana. Alhamdulillah na daina damuwa da abun, Ubangijina ya yaye mini damuwar i’ve move on..”
Cikin sake matsowa daff da ita tana kallon yadda take kuka billhakki da gaskiya tace”Dan haka Ina mai sake gaya miki ‘ki janye maganar tsinuwa sannan ki kirawo Yashjub ya dawo gida cikin family d’insa, idan kuma ba haka ba, to tabbas Mommy za ki yi mamaki na saboda a yadda na ke jin haushi da takaicinki tona miki asiri shine mafi ƙarancin abunda zan iya yi a halin yanzu.”

Dai dai nan Baba Larai ta turo k’ofar ta shigo, a d’an hargitse!

Kallonsu ta yi kamar yadda suma suke kallonta, ta riga ta san Yahanasu ta gama fasa kwai! duba da yadda Mommy take kuka kamar ranta zai fita, amma ba ta wannan ta ke ba tukunna dan haka ta kalli Yahanasun tace”D’an bamu guri!”
Daga haka ta ja Hannun Mommy suka nufi bedroom d’inta.

Had’e rai Mommy ta yi, kamar ta turje ta k’i binta sai kuma kawai ta rabu da ita ta yi mata shiru, dan tsabar mugun mugun takaici da haushin Baba larai d’in ma ya sanyata ta kasa cewa komai.

Suna shiga Baba larai ta tura k’ofar, ba tare da ta damu da yanayin Mommyn ba tace”an yanka ta tashi fa!
babu aure tsakanin Kausar da Yashjub!..”
Ba ta jira Mommyn ta tambayeta k’arin bayani ba, ta d’aura da cewa”kin san ai kawar musu da lissafin duk wani abunda zai sanya a fasa auren nan muka yi dama, shiyasa kwata-kwata ba su yi tunanin ‘ba fa a d’aura aure da ciki‘ ba.
Na tabbata Kausar ma da kanta bata sani ba, dan ni ba, sai yanzu ne da na fito zan zo nan na ji suna maganar, Abhi da Daddy..wai har wani babban malami suka sake tambaya ya tabbatar musu da cewa ‘ba a aure da ciki!’
Ban ji bayanin nasu sosai ba, dan k’us-k’us suke yi a chan corridor na babban balcony kamar harda Hajiya Maama suke maganar ta waya,shiyas….”

Cikin katseta Mommy tace”Larai me yasa kika b’oye
mini batun Yahanasu???”

Cikin rashin jin dad’i Baba Larai tace”kash!!!
Ki bar wannan maganar za mu yi ta amma ba yanzu ba, yanzu mu ji da wannan, ba mu san wanne mataki su Daddy za su d’auka a gaba ba, dan haka ya kamata mu yi musu shigar sauri!”.

Cikin daka mata tsawa Mommy tace
“ni kuma wannan maganar nake so mu yi, dan haka ki amsa ni idan na ce miki me yasa kika b’oye min batun Yahanasu sannan me da me kika yi mata?. Har ma da ni ɗin kaina tabbas kin yi mini abu, dan haka ina son jin komai a yau a yanzu ba sai anjima ba, idan ba haka ba kuma wallahi za ki sha mamaki na!!”

Numfashi Baba larai ta fesar kafin tace
“shikenan, tunda kin dage sai kin ji!..

Duk abunda na lissafa miki nace shi za mu yi mata shi na yi…”

Cikin tarar numfashinta Mommy tace
“Sannan nima kika d’auke hankalina daga kanta ko?
saboda akwai abubuwan da kika saka ni na yi kika kuma bani na ci waenda duk sai yanzu kwakwalwata take fassaramin ma’anar su, sannnan tunda na yi har yau ban k’ara tunanin fad’awa Yahanasu gaskiya ba!
Dan haka ba na son k’arya da b’oye b’oye larai!! Inaso ki gaya mini gaskiya tun rai na bai gama b’aci da ke ba!!!”.

Ajiyar zuciya Baba larai ta sauk’e kafin tace
“Mommy gani na yi kina shirin tona mana asiri ni da ke, kina shirin kaimu prison…
saboda na san muddin Daddy ya san mun musanya Yara to
duk wani Abu da muka yi sai ya bnciko ya fito kowa ya gani a hankali a hankali k…”
Marin da Mommy ta d’auke ta da shi ne ya sanya ta yin shiru, ta zuba mata jajayen idanuwanta cike da asalin mamaki da al’ajabi.

Cikin fushi bak’in ciki da b’acin rai Mommy ta fara magana
“a duk tsawon tarayyata da ke ban tab’a ce miki ki je ki yi gaban kanki ki yi kutse cikin rayuwata ki yanke hukuncin da kika ga ya dace miki ba!
A tunani na shelter (wajen zama), abinci da gatan da na yi miki ya ishi ace kin yi hankalin yi mini biyayya sannan ki bi umarnina kuma ki girmama duk wani hukuncin da na yanke ba tare da kin yi mini shishshigi ba.!”

Cikin fushi sosai itama Baba larai d’in tace”Khadija ni kuma a tunanina na wuce wacce za ki ajjiye hakanan a cikin gidanki tana yi miki duk abunda kike so kawai kamar wata y’ar aikinki!!
A tunanina ni yayarki ce shiysa har na yi miki shishshigin da kike magana a kai na yanke hukuncin da na tabbatar it’s for your own best!(domin anfaninki ne)…
Amma tunda duk irin rufin asiri da abubuwan da na yi miki tsawon shekaru sama da talatin duk ba ki gani ba, yau ta kai har kin d’aga hannu kin Mareni shikenan!!!.
Ba komai, Allah ya had’a fuskokinmu da alkhairi..”
Daga haka ta juya ta nufi k’ofa taana tsammanin Mommy za ta tsaida ita, amma har ta fice daga d’akin Mommy ko tari ba ta yi ba.

Za ta nemo ta su daidaita su shirya amma sai bayan ta tafi yau ɗin, dan tabbas
Yau kam ba za ta tsayar da Larai ba wallahi, sai ta nuna mata abunda ta yi ba ta kyauta mata ba ta yadda gobe ba za ta k’ara ba…
Saboda Allah kalli yadda ta saka k’iyayyarta a cikin zuciyar Yahanasu! Duk ata dalilin makircinta, sannan gashi kwata kwata Yahanasun ma ba ta k’aunarta sab’anin yadda Baba larai d’in tace ‘Yahanasu ba za ta iya ko jayayya da ita ba!’
A tunaninta aikinsu ne yake ci shiyasa da ta ga Yahanasun shiru shiru ashe tsana da haushinta ne ya cika mata zuciya shiyasa ta ke yawan yin shiru ba ta kulasu….
Chapter 125 · 0% Book details