← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 152

Sashe 141

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mugun mamaki Yasirar ta bi ta da kallo har ta shige cikin bedroom d’inta ta banko k’ofar…
Tana shiga ta sak’ala key k’irjinta yana dukan uku uku, ta durk’ushe a nan bakin k’ofar…
kar dai maman manubiya ce ta rasu ba manubiya ba…Gidan babu wuta bata jona wayarta ba babu charji shiyasa dama bata samu ta yi waya ta ji batun wanne hali Manubiya ke ciki ba tun d’azu…inna lillahi wa inna ilaihirrajiun, kenan yanzu duk wani effort jajircewa da sacrifices d’inta sun tafi a banza kenan?
Kaii inaa ba zai yiu ba, inshaaAllah ma ba haka bane ba, inshaaAllah Manubiya da mahaifiyarta tata ne suka mutu tare…amma kuma inda Manubiya ta rasu ai da Yasira zata gaya mata…..
Wani Irin bugawa k’irjinta ya shiga yi, gashi zuwa yanzu dishi dishi take gani sosai sosai, ga wani irin juyawa da kanta yakeyi, dan haka ta mik’e da kyar ta k’arasa kan gadonta ta kwanta ta lumshe Idanuwanta tana jin kamar ta saka Hannu a cikin k’irjinta ta kwak’ulo zuciyarta ta jefar, tsabar azabar da ta ke yi mata………
Bata da wani zaɓin da ya wuce ta tirsasawa zuciyarta akan
‘Ta tsaya ta d’an jira zuwa anjima, in sha Allah zata ji labarin mutuwar Manubiyan itama’.
Saboda ko da wasa bazata taɓa iya Hasaso ko ta yi tunanin cewa ‘wai Manubiya ba zata mutu ba! Kenan Duk waniaiki da sadaukarwarta sun tafi a banza fa kenan, inaa.’

Tabbas Yasira ta tsorata, kuma ta shiga al’ajabi da lamarin Mommy, ko bayan shigar Mommyn d’aki har Yusra ta wuce d’aki ita Yasirar tana nan a yadda take ta ma kasa motsi, kafin da kyar ta nemi waje ta zauna tukunna ta zaro waya ta Kira Manu ta yi mata gaisuwa sannan ta ce mata “zasu zo inshaaAllah”
Daganan ta kashe wayar ta yi shiruuu…chan ta ɗago wayar tata ta danna kiran Ya’isha!….
Ta san Ya’isha tanada taurin kai amma zata gwada lallab’ata a samu ta hak’ura da aikin da Mommy ta turata yi kawai ta dawo, ba wai son Manubiya take yi ba, kawai ta ga Mommy ta wuce gona da iri ne, dan haka tun kafin ta kai kanta ga halaka ya kamata a dawo da ita saiti!
Wanne Irin bala’i ne har ka tashi mutum gari ya gari dan kawai ya je ya yo maka asiri ya dawo! Har mai ya yi zafi haka…….
Layin Ya’isha yana shiga ga mamakinta kawai sai ta jiyo k’arar wayartata a d’akin da Ya’ishan ta kwana, dan haka ta mik’e ta shige….
…
Tana shiga ta ga wayar Ya’ishan a ciki, har da charger da su AirPod d’inta da watch duk ba ta d’auki ko d’aya, ba sannan kayanta suma gasu nan ciff suke! Alamun ta d’iba ba, daga gani tun jiya ba ma ta tab’a ba…dan haka kawai ta juya ta fita ta je ta shiga buga d’akin Mommy…

Ta fi mintuna ashirin a wajen a tsaye! Har Yusra itama ta fito ta jona ta suka dinga buga ɗakin, tukunna aka samu Mommy ta bud’e…
yadda suka ganta dagaje-dagaje sannan idanunta duk kwantsa sai da abun ya basu tsoro, ya kuma basu mamaki, dan haka Yasira ta ji zuciyarta ta d’an yi sanyi (ta sauƙa daga fushin da ta hau) amma dukda haka sai cewa ta yi”Mommy ki gaya mini tsakaninki da Allah, Ina Ya’isha?
saboda na duba d’akinta Hatta wayarta ba ta d’auka ba!!”

Shiruu mommy ta yi, dan ita sai yanzun ne ma kwakwalwarta ta bata duk waennnan abubuwan…..da kyar ta nemo mafita, dan haka a hankali ta buɗe Bakinta tace musu
“da k’aramar wayata ta tafi, saboda hanya, kaya kuma ta d’auki dogayen rigguna biyu. Dan Allah Yasira ki bar ni in huta mana bakiga situation d’ina ba ne???
Ki huta kema ki zo ki je mini pharmacy ki siyo min maganin ciwon Ido, saboda wannan d’ayan har na daina gani da shi, sannan ki fita ki nemo min chargi ina buk’atar in yi waya da gaggawa….Yusra ke kuma ki d’aura girki…”
Tana gama fad’in haka ta juya ta rufo k’ofarta hankali a masifar tashe………
•••
Sai azahar tukunna Yash ya zo…zuwa wannan lokacin kowa ya fara jin tausayin gwaggo Suwaiba saboda sun fahimci zafin abun ne ya sanyata yin hakan! Ta inda kwata kwata ta k’i bari a nad’e inna a yi mata sutura…..ta zama kamar wata tab’abb’iya.

Manu tana zaune a parlourn ita da su Siyama da su anty Umma suna kuka su mama kuma sunata lallab’a gwaggo Suwaiba, Baba shima yana gefe shi da Ya Musbah in banda hawaye babu abunda suke yi, sun ma kasa tsawatar mata!
Suna a haka Muhsin ya shigo yacewa Manubiya “ga Ya Yash a waje yace ta je…”
Manu tana mik’ewa Gwaggo Suwaiba tace mata “tace masa tana son ganinsa ya shigo”
Sannan ta kalli su Baba tace “dan Allah tana buk’atar magana da Yash shi kad’ai…….”

Sai da suka gama kukan su shi da Manu ya lallab’a ta da kyar tukunna ta iya gaya masa sak’on gwaggo Suwaiba, ya d’an yi mamaki amma kawai sai ya bi bayan Manu, ta yi masa rakiya zuwa cikin parlourn.

Manubiya ta so zama amma itama Gwaggo Suwaiba ta sallameta, parlourn ya rage daga ita sai Yash sai Inna….

Sun jima sosai sun fi 1 hour dan
har mota Yash d’in ya fita ya shigo da ita kafin ya tafi ko sallama bai yi wa Manubiya ba!
Ta ji mamaki matuk’a, dan tun d’azu dama da ya zo ta Lura da yanayin da yake a ciki na tashin hankali firgici tsoro da kuma rud’ani!…tunda ya zo ɗin tana kallon idanunsa ta fahimci ya ci kuka ba na wasa ba, da farko ta yi tunanin rasuwar inna ce ta tab’asa haka amma yanzu yadda ya tafi kuma ya k’i d’aukar wayarta ya sanya ta fahimci tabbas wata matsalarce ta sake tasowa bayan waenda suke a ciki.

Bayan tafiyar Yashjub suna shiga suka tarar Gwaggo Suwaiba har ta shirya Inna an sakata a makara ma wanda hakan ya sanyasu sake rushewa da kuka, ko zama ba su yi ba Ya Musbah ya shigo yace “Baba yace ku ake jira.”

Da kyar aka b’amb’are Muhsin da Manubiya daga jikin gawar! Hakanan Ya Musbah shi da Ya Nafi’u suka d’auketa a cikin makarar aka je a ka yi mata sallah suka mik’ata gidanta na gaskiya…..

Ana tafiya kaita su Yahanasu sukazo dukkansu har Yasmeen Yadira da Hajiya Mama da su Daddy….
Hajiya mama ba su had’u da Mama ba, saboda da wuri suka tafi tare da su Daddy ita da su Yasmeen, Yahanasu ce ta zauna.
Ita kuma Mama a lokacin ta koma gida, sun d’an kimtsa tukunna suka taho ita da Ammi.
Yahanasu tana zaune a d’akin da Manubiya ta ajjiyeta kawai ta ga Mama ta shigo, wadda dama ita maman ta san tabbas yau kam za ta
had’u dasu, amma fa dukda haka sai da ta kusan fad’uwa a lokacin da sukayi ido biyu ita da Yahanasun,
Yahanasun kanta ta kusan suma, gashi lokacin babu kowa a d’akin sai ita kaɗai…
…
A hankali jiki ba lakka ta mik’e tsaye, bakinta yana wani irin karkarwa ta ce ”maa maa!”sai kuma ta tafi da gudu ta fad’a jikinta ta fashe da wani irin kuka…
Itama Maman kuka ta saka a nan wajen ta yarda tray d’in hannun nata ta rungumeta a cikin jikinta!

Ba abunda ya fi yiwa Yahanasu dad’i kamar yanzu da ta san ta san inda mama take! Dan A take a ranta ta aiyyana ‘shikenan za ta had’a Yash da mahaifiyarsa cikin sauk’i!’
nauyin da ya ke a kanta shekara da shekaru yanzu zai sauk’a.

Cikin sharar hawaye ta d’ago ta kalleta tace”Mama dama kin san su Manubiya? Ya aka yi kuka had’u?”
Ta yi mata tambayar waensu hawayen suna sake zubowa…..

Hannu ta saka ta share mata hawayen nata, kafin ta ja hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna…nan ta faiyyace mata duk wata alak’a da take tsakaninta da su Manubiya…
Tana kuka tana hawaye sannan tana dariya at the same time tace” da ma kece mama da nake yawan jin sunanki a bakin Manu?
Alhamdulillah!!
Mama na ji matuk’ar dad’in ganinki, bari Manu itama ta zo, na san zata ji dad’in jin wannan labari kwarai!”
Ta fad’i hakan cikin sake rungumeta.

Da sauri Mama tace mata “A’a Yaha, kar ki gaya mata komai!”

Cikin rashin fahimta Yahanasu tace”ko
me yasa Mama?”

A take wasu hawaye suka zubo mata cikin ruk’o hannun ta tace”Yahanasu a halin yanzu ba zan iya fuskantar Hajiya mama da sharrin tarin abun kunya da aka yi mini ba, sannan mahaifinku ya sanar mini muddin ya ganni ko da a kusa da ke ne to fa abunda zai aikata a gareni mummuna ne!!”

Cikin tarar numfashinta Yahanasu ta d’ago tace”Mama duk sharri ne ba shi ne ya fad’i waennan maganganunba! duk makircin su Momny ne!”

Da mamaki ya kalleta tace”su Mommy kuma?”

“Tabbas ita ta had’a Baki da mai makarantarmu a wanchan lokacin, sannan asalin abunda ya faru shima duk laifinta ne!
Kar ki hukunta Daddy ta hanyar cewa kar a gaya masa an ganki, dam na tabbatar shima neman naki yake yi yanzu haka.”

Cikin gyara zama da sake ruk’o hannunta ta d’aura da cewa”
Akwai abubuwa da yawa da nakeso in faiyyace miki, but first yanzu bari in kirawo su Daddy su zo Allah kad’ai ya san kalar murnar da za su yi idan suka ganki!”

Shiruu Mama ta yi, dan ba kad’an ba ta shiga shock da jin sunan Mommy a cikin lamarinta!!!
Mommy Mommy dai??anya kuwa?
Sai kuma ta kalli Yaha kamar mai nazari kafin cikin hanzari ta sa hannu ta karb’e wayar hannun Yahanasun ta kashe kiran….
Chapter 141 · 0% Book details