← Book details Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 152

Sashe 1

Manubiya Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bismillahirrahmanirrahim

*MANNUBIYA*
*Book 2*
*page 01*

Sai da aka fara kiraye kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an Yassir ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa.

Ba dan ya saka alarm d’in 7:30am ba to da ba zai ga fitar Yashjub d’in da ya shiryawa gani ba.

Alarm d’in yana fara k’ara, ya farka, dan bashi da wani nauyin bacci dama. Da sauri ya d’auki wayarsa ya kalla sannan ya kashe alarm d’in kafin ya ajjiye ta tukunna ya fad’a toilet…
Fitsari ya fara yi, tukunna yayi brush sannan ya fito ya k’arasa jikin windown d’akin ya tsaya.

Sai da ya yi kusan mintuna biyu a tsaye a wajen tukunna Yashjub ya fito..

Tabbas Yassir ya ji babu daɗi a lokacin da ya ga Yashjub ya kira driver ya bashi makullin motar ya ce “ya tuk’asa su je”, da alamun aiki ne a gabanshi birjik! Dan suna shiga cikin motar ya ga ya baza takardu da computer ya duk’ufa aiki a nan doguwar kujerar bayan, inda ya shiga ya zauna.

D’aga kafad’u Yassir ya yi ya d’an tab’e Baki a ransa ya ce ’’Atleast ka samu Abokin mutuwa’’
Sai da ya ga fitar su tukunna ya koma cikin d’akin ya d’auki airpod d’insa ya mak’ala a kunne ya kunna kid’a a wayarshi.
Wani d’an labule ya d’aga ata gefe guda chan kusurwar d’akin
kayan motsa jikinsa suka baiyyana,
tsaki yayi a ranshi ya ce
‘’Wajen motsa jiki sai kace d’akin b’era!
Wallahi na ƙagu a-yi-ayi a gama min ginin chan in tartara in koma gidana nima…
Gaba ɗaya a masifar takure nake a nan ɗin!’’.
Daga haka ya fara motsa jikin nasa…..

Ya d’an jima, dan a k’alla ya yi 30 minutes yana abu d’aya, tukunna ya fad’a toilet domin ya samu ya watsa ruwa
ko wacce b’ular gashi dake a jikinshi tana mai tsatstsafo da zufa.

A band’akin ma sai da ya kwashe sama da mintuna ashirin, tukunna ya fito ya shiga goge-goge da shafe-shafe da feshe-feshe, tukunna ya d’auki wasu had’ad’d’u kuma tsadaddun suite masu masifar kyau ya sanyawa jikinsa.

Tsaff ya shirya ya fito tas da shi, ya kuwa yi kyau, longsleeve d’insa ce kawai fara amma hatta takalminsa da belt da links duk komai bak’ak’e ne.
A gaban madubi ya tsaya yana taje sumarsa wacce takenan tsaf da ita sannan a cike taff bak’ak’irin, gaba ɗaya ilahirin kan nasa kuma babu ko da alamar sank’o ne….
ga wani had’ad’den gyaran fuska da ya sha wanda ya tafi dai-dai
da tsararren sajensa da kuma gashin Baki had’i da d’an guntun gemunshi….
Kallo ɗaya za a yi wa sumar tasa a fahimci ta asalin Bahaushe ce,
amman tsabar kud’i da gyaran da take sha ya sanya har wani shek’i sumar take yi, mai tsananin kyau da d’aukar hankali.

Kallon kansa ya yi a gaban madubi ya sake, tabbas ya san yana da kyau! Son kowa k’in wadda ta rasa….a yadda yake da kyan nan Wallahi mace ko da kud’inta sai da rabon ta,
amman wai dukda haka kalli yadda Kausar take gara shi itama wachchar shegiyar Munirat d’in sai wani kakkaucewa takeyi ta k’i ta bada had’in kai a yi a wuce gurin!Wallahi ba dan ya kwallafa rai a kanta ba da tuni ya watsar da lamarin ta….

Yana cikin wannan tunanin ya fara jiyo hayaniya a nan saman, bai gama fahimtar su waye ba ya jiyo muryar Yasmeen tana kuka tana cewa “Mommy!
Ya Yash ne sukayi accident shine doctor d’in ya kirani, wai
yanzun nan aka kai masa su.’’

Wani kalar murmushi Yassir ya saki daga jin zancen Yasmeen,
A take wani farin ciki marar misaltuwa ya lullub’e sa.
Sai da yayi da gaske tukunna dakyar ya samu ya iya kawar da farin cikin da ya baiyyana ƙarara akan kyakkyawar fuskarshi sannan ya fita a gigice….

Yana fitowa ya tarar da su gaba d’aya, kowacce tun a kallon farko ake iya fahimtar hankalinta a tashe ne har su Ummi…….
Tuntuni Daddy ya riga ya tafi office shi da Yasira, dan haka suka tura musu message kawai, daganan gaba d’ayansu suka d’unguma zuwa asibitin da Yasmeen ta gaya musu an kai yash ɗin, dan a yadda hankalinsu yake a tashe
babu wadda za ta yarda a tafi a barta.
Baba Larai ce kawai ta tsaya a cewar Mommy in wani ya dawo sai ita ta je.

Sai da suka kusan Isa asibitin ma tukunna su Yasmeen suka lura babu Kausar.
Kasancewar kowacce hankalinta ba a jikinta yake ba a wannan lokacin ya sanya basu neme ta ba.

A b’angaren Kausar d’in kuwa,
duk wannan ife-ifen da akayi aka gama sam ba ta sani ba, har suka fita
Jiya yadda ta ga rana haka ta ga dare, ko rintsawa bata yi ba. Shiyasa daff da asuba da taga ciwon Kai yana shirin halaka ta ta sha maganin bacci mai tsananin k’arfi.

Suna isa Asibitin direct su ka wuce cikin ward na emergency dai-dai lokacin Likitan ya fito kenan daga inda aka shiga da drivern domin bashi taimakon gaggawa.
Gaba d’ayansu rufar masa suka yi,
Yasmeen kuwa bata ma tsaya bi ta kansa ba ta fad’a cikin d’akin da ta ga ya fito.

Girgiza Kai likitan yayi fuska cike da alhini ya ce ’’sai dai fa haƙuri!
we couldn’t save him(ba mu yi nasarar ceto rayuwarsa ba)!’’

Diff numfashi kowa ya d’auke a wajen,
suka ma kasa cewa komai

Wani mahaukacin bugawa zuciyarta ta yi, jin Likitan yana ci gaba da cewa ‘’amma Yashjub is fine! Da ikon Allah
da taimakon seat belt
sannan kuma kasancewarshi a seat d’in baya…ya samu iyaka
gocewar k’ashi a hannunshi na hagu.
Amman motar da suka daka itama gaba d’aya mutanen ciki duk sun rasu!
Haka shima driver d’insa ya rasu sakamokon buguwar da yayi
da kuma glass d’in da ya chakesa a ciki, mun yi dukkan iyaka bakin ƙoƙarinmu amma Allah ya karɓi abunsa.”

A hankali Yassir, wanda ya fara ganin dishi-dishi, ya matsa kusa da Likitan ya dafa kafad’arshi tukunnan ya ce ‘’Doctor, Yashjub yana nan lafiya am man s h i ko??’’
Ya yi masa tambayar a rarrabe.

Jinjina Kai Likitan ya yi kafin ya d’aura da cewa “yana wanchan d’akin, a nan muka ajjiye shi domin ya samu ya huta, an gama gyara Hannun nasa da duk wasu abubuwan da suka kamata a yi masa.’’

‘’Alhamdulillah!”
gada d’ayansu suka furta, cikin tsananin jin dad’i banda Yassir wanda wata kalar zufa ta shiga tsatstsafo masa kafin a hankali wani hawaye ya biyo ta idonshi guda d’aya, da sauri ya sunkuyar da kansa k’asa ya sa Hannu ya goge ya fara murmushi mai kamar dariya kafin a fili ya ce ‘’Alhamdulillah!’’
sai kuma ya d’ago ya kalli Likitan tukunna ya ce ’’za mu iya ganin shi??’’

‘’Yes,sure!’’
Likitan ya sake bashi damar ganinsa a karo na biyu kafin ya kira wata nurse ya ce ‘’ta musu iso zuwa inda Yashjub ya ke’’.
Daganan ya juya ya koma wajen Yasmeen zuciyarsa taff
cike da mamakin yadda gaba d’ayansu suka nuna halin ko in kula game da rasuwar drivern Yashjub.

Yana shiga ya tarar da Yasmeen ta na waya, da alama da familyn drivern take waya.

Tana gamawa ta kallesa ta ce
‘’Sir! Wallahi na tsorata sosai, ashe ma ba abunda ya samu Ya Yash,
Alhamdulillah
bara in je in ganshi.’’

Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace “am sir….familyn deceased ɗin (iyalan marigayin) suna hanya, dan na ji yadda hankalinsu ya tashi a wayar na san daga yanzu zuwa ko wanne lokaci za mu iya ganinsu anan’’.
Daga haka ta wuce ta fita.

A d’akin da Yashjub ya ke suka tarar da Daddy da Yassira,
dan office d’insu ya fi kusa da asibitin shiyasa suka riga su zuwa. Suna shiga Yahanasu ta tafi da gudu ta fad’a jikin Yash ta fashe da wani Irin kuka.

Tun d’azu sai yanzu ya samu
murmushi ya d’an sub’uce masa, a hankali ya d’an bubbuga bayanta alamun rarrashi.

Cikin kuka ta d’ago ta shiga
duddubashi tana kallon Hannun a hankali tace ‘’Allah ya ci gaba da kare ka a duk inda kake’’

Murmushi ya yi, ya ce
‘’Ameen, Allah ya kare mu gaba d’aya’’
Daga haka ya d’aga Kai ya fara bin su da kallo d’aya bayan d’aya.
Duk matsowa suka yi suka yanyamesa suna yi mishi sannu.
Yayi mamakin rashin ganin Kausar amman kawai sai ya basar a d’ayan b’angare na zuciyarsa kuma yana mai sake tabbatar da zarginshi akanta.

Guri kowannensu ya samu ya zauna, aka shiga jimami kafin Daddy ya kalli Yahanasu ya ce ’’Likitocin sun fito daga wajen drivern??’’

Shiruu ta ɗan yi, sai daga baya tukunna ahankali ta girgiza Kai ta ce ’’ya rasu’’

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Yashjub da Daddy suka shiga maimaitawa.

Daga haka d’akin ya yi shiruuu.
Dan rasuwar drivern ta girgiza Yashjub ba kad’an ba.
Kasa zama ma suka yi shi da Daddy har sai da suka je suka ganshi, a lokacin har nurses d’in sun rufesshi an toshe kunnuwa da hanci…
Duk dauriya kalar ta Yash sai da ya yi hawaye, rai ba daɗi yayi masa addu’a tukunna suka koma d’akin da Yash d’in yake bayan sun ce “in iyalin nasa sun zo a yi musu magana.”

Ko da suka koma d’akin ma,
haka aka ci gaba da zaman jigum, kafin Yahanasu da Ummi suka ci gaba da jajanta al’amarin.

Gyaran murya Daddy yayi kafin
Ya ce
‘’Tsautsayi irin haka daman ya kan faru a irin wannan lokutan na shiga sabon fagen rayuwa’’

Duk nutsuwa suka yi suna sauraron shi yayinda shi kuma
ya ci gaba da cewa “Na so
dama yau in gaya muku,
amman tunda gamu duk anan
Alhamdulillah.

InshaaAllah
nan da sati biyu idan komai ya tafi dai-dai babu wata matsala to
Za’a d’aura auren Yashjub!

Hajiya Mama ma ta riga ta sani dan haka daga yanzu zuwa ko wanne lokaci in ta gayawa su Abhi za ku iya ganinsu, har da su
Imam.

Khadija ke da Saddik’a idan akwai walima da taron da kuke buk’ata za ku yi sai ku yi min magana in samu in sallameku da wuri.’’
Chapter 1 · 0% Book details