← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 157

Sashe 99

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan nan ta sallame Ahmed tare da ce masa yaje ya taho da brother hamzat su samesu acan sashen mahaifinsa inda zasuyi sallama.

Tashi yay ya fita ya barta tare da Adiaha dan already jikinsa ya bashi cewa da akwai wani maganan da hjya take so tay da Adiaha wanda bata son ta fadeshi agabansa ynzu..

Aikuwa yana ficewa kuwa ta zauna cikin lallami da taushin murya ta dinga bata hakuri akan rayuwar zaman aure tamkar wacce ta zauna ta gama harsasho dukkan wasu abubuwan dake faruwa da ita.

Hjya aranta tariga tasan danta sarai baiya bata isashen kulawa bare kuma yay mata Adalcin daya dace duba da sadaukarwan datay masa, haka ta dinga bawa Adiaha hkri akan zaman aure tace mata rayuwar auren dama ya gaji haka wata rana sai labari..

Hawaye mai ban tausayi Adiaha take sauke mata dashi sosai dan ta dade bata samu wanda ya taɓa nuna cewa ya fahimci yadda takeji aranta game da halin da rayuwarta yake ciki Agidan Ahmed ba..

Tay dakon wanda zai lallasheta ya bata hakuri amma bata samu ba saiyau da surkuwanta take bata wnn daman..

Tace mata tasan rayuwar ta anan itakadai babu wani nata atare da ita is not easy sabida babu wani mahaluki a duniya da zai yi zaman rashi tare da maraicin iyayensa aransa dana yan uwansa bacin yasan duka suna raye suna rayuwarsu awani waje saidai batare dashi ba..

Hjiya bata gajiya ba, ta kara karfafa mata gwiwa sosai tace mata komi zaizo ya wuce wata rana har iyayen nata ma dik zasu zo su yafe mata and she wll be fully happy and at peace...

cikin nasihar datake mata ta kawo mata misali da zancen yasrah, inda take mata misali da yadda aka haifeta ta girma a hannunsu batare da tasan nata mahaifyar ba hakama har mahaifin ta yazo shima ya rasu bata wani sanshi ba,ga dangin baban nata duk araye amma basa taba neman susanta ba.

She realised dat they have something in comon domin kuwa dukansu zucyarsa yana cikin halin maraici saidai gara ita nata suna raye what about the poor little girl da batama san dadin nata iyayen ba.

Nasihar da hjya tay mata sosai ya shige jikinta tay sanyi sosai ahaka har suka fito aka gaggaisa aka kammala duk wani sallaman da za'ayi acikin falon alhaj bello Ahmed da brother hamzat suka raka hjiya ta wuce lagos.

Yau drivern gidan ne yakai yasrah makarnta

She was late sabida delay din bankwana da suka tsayayi da mumyn ta, taji babu dadi da tay mata fada kadan agaban Ahmad amma still ranta ya wanku da yakasance agabansa tace mata duk sanda ya sake mata tsawa ko ya ajeta awani waje toh ta kira ta gaya mata zata aiko azo a dauketa agabansa.

Tana isowa schl tazo ta samu harma angama submiting din assigment din tazo ta samu yara da yawa sunata complains ba a amshi nasu ba sabida tsaurin malamin irin lecturers masu zafin kan nan ne, maryam ne take bata labarin yadda Fahad ya aiko kai tsaye aka miƙa nata assignment wa malamin snn aka karba da wurwri batare da wani korafi ba.

Awajen cin abincinsu nayau maryam ke bata labarin yadda Fahad ya kasance yana da power tare da iko ta izza mai karfi a makarantar domin kuwa yawancin malamai suna jin tsoron tabashi bare ajega kan dalibai..

Har Maryam ta kammala bata labarin rayuwar fahad a schl din yasrah bazata iya maimaita ko abu daya aciki ba dan bajinta ma takeyi ba cos mentally hanklinta ma baya kan hirar fahad.

Iya Abunda kawai ta iya fahimta acikin zancen shine iyayen Fahad masu kudin gaske ne kuma duk sun sangartashi, musmmn ma mahaifinsa alhaj shagari domin kuwa yana da bigger business and political influeneces snn kuma yana matukar kaunar dansa fahad shagari aransa barin ma da dan nasa ya kasance yanada matukar ilimi da iya sarrafa duk wata lamarin kwakwala wanda hakan shiyasa kwata kwata baya yadda wani mahaluki ya taba masa dansa komin matsayinsa da girmansa a fadin kasar.

Ta lura cewa abun fahad din nan duk yafara shigewa kan Maryam din yana juya mata brain itama dan harta fara daga kafadarta wa sauran dalibai mata dan adalilij feeling dayake dashi akan yasrah yasaka fahad din shine yake kulasu basune suke binsa kmr sauran ba.

Yau kwata kwata yasrah bata bari sun hadu dashi ba duk da tasan abunda yake tsammani kenan daga gareta taje ta gode masa dan ya fara samun hanyar ganin damanta kyabe bakinta tay cikin salon fahimtar yanayin shirinsa akanta, besides ba itace ta rokesa ya taimaka mata ba dan haka ta yanke aranta cewa bazata je nemansa a ko ina domin gode masa ba zata jirane har sai sun kara haduwa.

Duk matsawar marym akan da cewa zata rakata suje har ajinsu ta gode masa amma hakanan yasrah taki amincewa sam.

After a while aka tashe su tana fitowa daga ajinsu arond 4pm suka fito tasha mamaki data hango motar Ahmed a parke gaban department da alaman yazo da wuri

Tun Daga cikin car dinsa yanata satar duban gefe da gefe koda zai ganta tsaye da gayen nan dan haryau Abun bai kwanfa masa aransa ba, yana ganinta tare da maryam sai yay maitaining kansa yay sauri ya dena duban dayakeyi tareda maida kansa kan wayarsa yana famar daddanawa yay irin kamr baiya kallonsu daga can.

wani hade rai yasra tay daga nan sukayi sallama da maryam din ta isa bakin motar tay bisimillh sann ta bude ta shiga ciki tare da aje jakarta a seat din baya tunda ta shigo Ko kwakkwarn kallon juna basuyi ba ahaka ta gaishesa sama sama daga nan basuce ma junansu komi ba tafiyar kurmaye yakaisu har gidan jimada.

Ata fannin Adiaha kuwa tun bayan nasihar da hjiya Khadijatu tay mata shiknn abunda takeji aranta na tsananin kishi da zargin mijinta akan yar uwansa yafara gushe mata aranta tafara dawowa cikin hayyacinta

Tun 2.30 ta dawo gida sabida yau zubar jinin datay a shago ne snn baida wani yawa sosai

Tana dawowa bata wani huta ba ta shiga kitchen Iya bakin kkrnta tay yau wajen gyara ko ina acikjn gidanta snn tay musu abincin da zasuci har dare isashe...

Bayan dawowarsu da kamar minti talatin lkcin
Yasrah na dakinta ta fito daga wanka kenan tana shafa mai ajikinta ahankli daga kofa taji bakon murya na sallama abakin kofarta, daga nan ta bada izini, Adiahan ce ta shigo sanye da dogon riga na kanti,suna hade ido mmki yasaka yasrah ta mike tsaye daga zaune tana dan kallonta, fuska babu yabo babu fallasa Adiaha tace sister are u done?Yasrah dake kallonta ta gyada mata kai, tace "ki zo kici Abinci pls i knw u must be very hungry. Da Har kamr zatace no sai ga nan Ahmed ya leko.

Wani irin kallon rainin wayo taga yay ma Adiahan tun daga bakin kofa irin ransa baiso ganin ta anan din ba sai ta fice ta bishi baya suka wuce falon yasrah tabi bayansu da kallo.

Tun da ya zauna kan dinning din daddana wayarsa kawai yakeyi yanakan chatting da abokinsa banji dake can canada yana gaya masa cewa matarsa hidayat ta fara laulayin itama.

Cikin ransa acike da walwala amma fuskansa sam baya nuna hakan a fili.

Serving dinsa abincin Adiaha tay bai jira kowa ba yafara cin abincin har suka kusa cin minti goma anan yasrah bata fito ba nan da nan yafara jin ransa yana neman dagulewa,komeyasa ya damu da ita hakan oho ji yay har abincin na nemn gundurarsa yanata satar kallon kofarta dan Allah Allah yake yaga yasrahn ta fito.

Sai can daga baya sai gata nan ta fito jikinta na fidda wani irin sassanyar gamshin turaren humra data fetsashi ajikinta wanda daga fitowarta qamshin ya doki hancinsa yasaka shi lumshe idanunsa sosai,

Ahakan wai dan karta damesu da karfin qamshin turarenta data saba sawa yasaka ta murza iya humran ajikin ta, tahowa take anitse dan gefe can ta nema ta zauna tare da su kafin nan ta saka Abincin dan kadan acikin plate din dake gabanta nan tay bismillah tafara ci sama sama, abincin da duk basu iya ci sosai ba kenan, kowa na satar kallonta Kishi kadan kadan yana taba ran Adiaha ganin yadda yasrah tay taking time dinta ta gyara fuskarta yay kyau yana kyalli bayan nan da irin hadadden simple roaming gown dayake jikinta kalar ja da baki.

She is d real defination of is better to arrive late than to arrive ugly...

Komin ta acikin tattali da kasaita takeyinshi wanda kamewartan da ajintan akullum shine yake dada jan hankli tare da zucyar AHMED izuwa gareta batare da ta sani ba.

Wani Shiru ne ya ratsa wajen har suka kammala, buut Ahemd ya tashi ya barsu ya koma falo ya harde kafarsa daya akan daya a hakimce yana zaman kuwa ya kwala wa Adiaha kira as usual danta zo ta miƙa masa remote haka tabar kan abincin tazo ta miƙa masa ya karba baki bude yasrah take bin Adiaha ganin irin mulkin da ake mata batacewa komi.

Har saida tagama masa aikan snn ta dawo kan abincinta taci dan kadan snn ta mike zata fara tattara dishes din yasrah ta tashi cikin ladabi ta riga fara tayata batace komi ba takai matasu kitchen ta wanke matasu duka snn ta jera mata su a inda ya kamata dan jiya bakaramin tausayinta taji data gane cewa laulayin ke sakata irin wnn salon kazanta mai kunyatarwan ba..

Adiaha was happy and Amazed at the same time ganin yadda yasrah ta sauke kai tay mata aikin babu aufi ko raini daga nan ta wuce room dinta ita kuma Adiahar ta zauna a falon tare da Ahmed suna kallon chanell din daya saka musu na kwallo she is not really enjoying it amma bata son ta fada masa tsabar son datake masa aranta ta gwammaci ita ta cigaba da daurewa da choices dinsa.
Chapter 99 · 0% Book details