← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 157

Sashe 117

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aransa ahargitse cos yasan Bazai taba yuwa ace cikin farko ya zuba haka kawai ba, snn na biyu ma da baije ko ina ba ace mishi shima ya zuba, kai kai kai ders must be some sort of explanations from her dat he dersve to knw.

Yana isa gidan acikin daren yafara bincike He took evrything one by one snn ya bude phone dinta yayta bin chats har yazo kan na nurse din haka yabibbi chat dinsu da nurse din gabaki daya.

Wani irin bari bari hannun shi yakeyi kirjinshi na bugawa da karfin tsiya idanunshi sunyi jaaaa kirjinsa na fat fat tsabar hucin dayake har jijiyon kansa sun kumburo sun tattaso waje Hawaye ne ke sauka a idanunsa yanamai sauka akan screen din phone din atake yaji duniyar ta tsaya masa cak..

"So this is what she is been hiding from him?

Meanwhile itama Nurse din ita kanta lullube asalin gaskiyar maganan kawai takeyi da zancen abortion history dan tana jin matukar tsoron su kafayat da goddess amma ba gaskiya bane take gayawa Adiaha.

Gaskiyan shine Adiaha tana da karfin da ciki zai zauna ajikinta harta haihu iya yanda Allah ya bata cos she is fertile.

Wnn wani baiwa ne da Allah ya bata na musamn Wanda abunda yasaka kenan tayita zubda ciki alkcin datake yawon bin samari adacan, time din ko sau daya aka kwana sa ita sai kaga har ta dauka. She was used many times iyayenta sun sha wahala akan hakan wanda harsaida ta girma snn tayi wayo shiyasaa koda nurse tay mata wann rufa rufa din ta amince da wuri ta kuma yi imani dashi dan itakanta tasan yanayin rayuwar datayi adacan baya.

Gashi ayanzu zancen ba gaskiya bane amma shi ta amince dashi kuma Ahmed ma daya gani yanzu arubuce shi ya amince dashi.

he was devastated to knw dqt Her abortion history ashe shine yake causing dinshi asarar haihuwa,And yet she have the guts to hide it from him? ransa yaji yana baci "toh Meye dalilinta na boye masa?
"Amma badai kunya ko tsoron me zaice ba ko? "Yaga dai tun lokcin daya auro ta ya fara kwana da ita already tasan yasan da cewa tasan maza awaje amma bai taɓa mata gori Akan haka so why wudnt she tell him dat abortion history nata shine yake kawo mata bleeding? infact meyasa a matsayin sa na likita bazata gaya masa cewa tana bleeding ba taje ta nemo wata nurse acan sunayi a boye, wanda tasan iliminta na likitanci ma bai kai kwatan nashi ba despite yadda yake yawan tambayarta in akwai wata matsala tana fada mashi zai duba dakansa.

Aransa yace She have no excuse for all this kawai dagangan ne suke kashe masa y'ay'a.

Ransa yay matukar harzuka ko ina ajikinshi babu abunda yakeyi sai kyarma,ko ina acikin wayar tan saida Ya duba yaga ma harda pictures datake tura ma nurse na jini da kuma irin kudin datake kashewa awajen karban magani..

Bayan haka babu inda bai bincika awayar ba sann ya fara dudduba dakin nan kam baiga komi ba sai pads din datake amfani dasu.

Bayan nan dawowa asibitin yay baice ma kowa komi ya samu ana kan stabilising din jikin Adiaha sabidaa shock data shiga ciki sabida yawan zubar jini bai jira yaga ko tay rai ko batayi ba ya dauki yasrah ya dawo da ita gida duk ta dauka asibitin zai koma

Sassafe ta fito daga ita sai oversize nitynta zata kintsa gidan kenan sai taje asibiti duba adiaha nan tagansa a falo yana zaune awani irin yanayi kamar ma baiyi bacci ba.

Da sanyin murya ta gaishe shi ya amsa mata babu alaman fara'a atattare dashi..

Wucewa tay kitchen ta haɗa coffe tasha abunta
Tanakan sha sai gashi nan ya shigo.

Daga ido tay ta kallesa yace mata tay marmaza ta shirya zuwa schl.

Tace masa Asibiti zataje duba Adiaha amma yace sam saidai yasan taurin kanta kawai sai yace mata Adiaha is fiine idan ta tashi a schl zai kaita taganta.

Bata wani so ahakan aranta ba amma haka ta biye mashi taje ta shirya ta saka english wears high waist skirt da long sleeve shirt da karamin hijabi. Agurguje ya shirya shima ya fito sanye da black suit suka fito waje tare,yasrah bata saka komi aranta ba har suka shiga gaisuwa suka fito ganin bai gaya ma kowa kome game da Adiaha ba

She tot evrytng is fine with his wife kamar yadda yace din haka har yakaita schl ya ajeta bata fahimce komi ba.

Takwas da rabi na safe ya isa asibitin bai lekata ba snn bai tsaya jin ya aka kaya da nurse din ba.

Tunda ya samu tangible evidences na cewa ta hada kai da matarsa me suna abubuwa abayan idonsa dayake sa yake asarar haihuwa shikenan ya hadata husuma da hukuma da kuma asibitin datake aiki.

Yanzu haka an tattarata an kaita custody for questioning and interrogation.

Aikinsa ya faɗa yanata rubuce rubuce ransa na koña sosai wanda kallo daya kayi masa ayau zaka san ba adaidai yake ba.

Tun zamansa anan tunanin irin hukuncin da zai yanke akan matarsa yakeyi. Its pains him alot to knw dat He can't even divorce her, bazai iya sake ta ayanzu ba sabida bin umarnin iyayensa.

Amma tunda matarsa ce ai yasan ta inda zaibi ya hukuntata kuma so yake yaga yay mata rashin mutuncin da bazata taba mantawa dashi arayuwar ta ba dan kawai yaji ya huce aransa.

Adiaha dake durkushe a tsakiyar dakin tuni numfashinta ya dauke ta suma. Gashi Babu wanda ya zago tanan sabida private room ne inbashi ba only abokinshi doctor bankole is allowd.

Har 2.30 na rana bai leko ba, ana neman 3 sai ga kira daga police station da cewa za'a detaining nurse harsai Adiaha ta farfado tazo anyi case din da ita.

Nurse ta dawo abar tausayi ga tsaurarar da su doc bankole sukayi akan case din gashi asibitin datake aiki dasu har sun rantaba mata DC act na 1 month suspension.

Bayan sallahn asr suka hadu da Doc banky sukayi magana sama sama yake amsa shi, doc banky yay yayi akan suje ciki ya duba Adiaha yace masa sam shi bazaije ba babu kalar hakuri da bai bashi ba amma kamar da dutsi yake magana bada Ahmed ba.

Karshe ma kawai yace shi xaije ya dauko yasrah daga schl yana fadin hakan ya nufi motarsa, anan a tsaye ya barshi
Doc bankyn ya kada kansa kawai shima ya shiga ciki yaje ya samu Adiaha na cikin wani hali.

Taimaka mata yay snn ya kirawo elderly nurses guda biyu sukazo suka kimtsata aka mata tea mai kauri tasha snn ta dawo hayyacinta.

Kuka take kamar ranta zai fita sanin cewa ta tafka babban kuskure musmmn ma data matsa doc banky ya gaya mata cewa akan case dinsune da nurse ne, and then she lost the pregnancy, snn yahau yi mata faɗa sosai akan rashin gaya musu matsalar ta daba tayi ba.

Yadda yake ce mata ders nothing aciki inta fito fili ta gaya ma Ahmed cewa tana bleeding kodan ma abortion history dinta ne,

yace mata ai sunzama daya, snn aganinsa ai tasan da cewa Ahmed yana matukar son haihuwa so zai iya yay ignoring din wancan issure din nata na abortion ko dan ya ceto rayuwar abunda yake cikinta.

He blamed her for taking actions twice witou her husband consent..

Ya mammata fada tanata kuka sosai zuciyarta ya karye gabaki daya dan ko bai fada ma yau kam tasan tagama yawo ahannun Ahmed sai abunda Allah yay da ita kawai.

Tsabar tsorata dataji tayi She wish she can just run awaay.

Tun anan ta zuba gwiwowinta akasa tafara rokonsa arziki akan ya taimaka ya saka mata baki wajen rokon ahmed dan tasan dolene yau su kwashi yan kallo.
[7/19, 8:46 PM] SURAYYAHMS: Wajajen karfe hudu na yamma daidai Yasrah ta fito daga lectures kenan tana tsaye da fahad suna magana sai ga nn motar Ahmed ya taho cikin schl dinsu..

Yana ganinsu ya wani haɗe rai yanamai zuba musu wata muguwar kallo daga can,jin yafara buga mata horn yasaka tay sallama da fahad din a tsayetsaye suna tsaka da magana ta juya ta tafi, kaiwarta motarsa keda wuya ko jira baiyi ba suka bar schl premisses din, fahad ya jima awajen cikin jin takaicin Ahmed dan shikadaine yake kawo masa cikas a qudirinsa na zamowa very close da yasrah yanzu, he believe dat in yay winning trust din mace ya kwana da ita shikenan ya gama da ita, huci ya shiga furzarwa kafin nan ya juya shima yakoma cikin abokansa.

Tafiyar kurame sukayi sanda sukayi nisa snn taga yay parking agaban wani eatery ya mata take away, har sun fara tafiya ganin ba hanyar asibiti suka dosa ba yasrah ta dubeshi atakaice snn ta tambaye shi ko yay jikin Adiaha? Baice mata komi ba ya dauke kansa ya haɗe rai sai bata kara kulashi ba.

Hanyar gida taga yay dasu ta kyabe baki,nan mai gadi ya bude gate yay parking ya fita ya fara tafiya cikin sauri haryakai ciki snn ta bude itama ta fito ta biyosa abaya.

Ledar abincin tagani yaa aje mata akan table ta saka hannu ta dauƙa. Duk tay tsammanin zatazo taga Adiaha ta dawo gida amma sai shiru, room dinta ta wuce kafin tay komi saida ta shiga bathrum tay wanka sann ta fito ta neme abinci taci sabida yunwar data kwaso,saidai duk tana ci ne hanklinta na kan Adiaha tausayinta yana damunta thinkng dat she lost her baby once again must be very heartbreaking. Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke da tunanin irin halin da zata shiga ciki.

Bayan ta kammala cin abincin fitowa tay tafara dubawa koda zata ganta once again amma sai shiru. Kofar dakin shi ta dinga kallo ganin a rufe ta rasa yadda za'ayi ta kara tambayarsa karshe hakura tay kawai ta koma room dinta.

Bata wani jima da zama ba taji karar kofar alaman ficewarsa acikin sauri ta sako takalman ta tafito waje.

Hangensa tay acan ya nufi motarsa da waya a kunnensa yanaa magana da yarensu iya abunda ta tsinta shiine police station dayace zaije..

Yana sauri zai bude kofar motarsa saigata nan ta karaso cikin sauri.
Chapter 117 · 0% Book details