← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 157

Sashe 116

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana ta kallonsu Da mamakinta taga suna ta jan yasrah ajikinsu suna tarairayarta har magana mai ban dariya idan sukayi wanda bata ganeba suna taking time dinsu su mata bayanin me sukace din dan kawai susata acikin hirarsu.

They liked dat she is classy, educated, and from a very wealthy family gata kyakkwa.

Anty adizat tafara gaya musu tarihi tana cewa ai correct bayarbiyace ta haifo mahaifin yasrah, dat means kakan yasrah ta macen ma bayarbiya ce yar uwansu,she goes by the name hjya barakat shehu omawunmi,so aganinta definatly akwai jininsu na yarbawa ajikin ta yasrah, ita kam bata cewa komi.

Dagata dayan bangaren kuwa biyar daidai Ahmed ya dawo gidan ya samu ko ina shiru duk basa nan. Wayar Adiahan ne akan table sai ringing yakeyi nurse din can tanata kiranta ya leka ya ga sunan amma bai dauka ba ya basar.

Dakinsa ya nufa ya kulle ta ciki yay wanka ya kimtsa kansa cikin kananan kaya kafin nn abokinsa banky ya kirasa sukayi magana dan yau ne sukayi akan zai kaisa club yay whiling away time just to keep himself lively tunda yaga kamr Adiaha gudunshi ma takeyi.

Yana kammala wayar ya fice yaje ya same banky a hotel inda yake shanawa da yan mata.

Kwata kwata 30 min yay a hotel din yaga yadda yan mata suka yanyame shi kowace da salon ta, aransa yace bazai iya ba yay xcusing dinsu sai ya sabule kawai batare da yay wa banky sallama ba yana fita yajawo motarsa ya kamo hanyar gida.

Ahanya ya tsaya ya siya wasu abubuwan cime cimensa dan baiya bukatar fitowa yau kwata kwata. Ko sallahn ishai ma yau ji yake kamr a room dinsa kawai zaiy, so He plan to work till late night kafin nan ya kwanta.

Daga nan kuwa Sai duban time Adiaha take
wajajen 5:30 na yamma amma tsabar surutunsu anty adizat da kyar suka bar gidan mai jego.

Suna fitowa Anty nurat tace musu sam saidai suje dayan gidan dake gabansu suyi gaisuwar rasuwa cewarta ai maman mai gidan ce ta rasu.

Babu yadda suka iya hakanan suka shiga suka je suka samu antaru anata addua acikin gidan

Anan ma saida suka ci kusan 15 mints suna jira agama kafin nan suka samu shiga ciki lkcin duk hankalin Adiaha ya koma gida cos time din wankarta na karshe already har yay.

Da sauri sauri tajawo yasrah suka koma gida bayan sun kammala gaisuwar suna shiga ciki yasrah ta wuce room din ta tafara alwala domin gabatar da magrib.

A gurguje sosai Adiaha ta tube kayan jikinta tay tsindir cikin tsananin sauri tana Allah Allah kar lokaci ya wuce gashi har an shiga sallahn magrib abunda akace tanayi daf before magrib.

A gaggauce ta haɗa ruwan cikin bucket din karfe kirjinta daure da zani tana sauri sauri dan ta fice kafin Ahmed ya shigo dan batasan dazu ma ya dawo har ya sake fita ba kawai da bataga motarsa bane yasata jin ko bai dawo bane.

Wani irin kasala takeji ajikinta tana tafiya tana haki sabida sauri saurin datakeyi hakan yasaka ta dora ruwan asamn kanta dan tay sauri.

Tana isowa falo ta tsaya cak jin wayarta yafara ringing,acan akan dinning tabe tagansa, tahowa tay wajen ruwan nakanta tana sauri sauri ta leka taga mai gadinsu biodun ne sai ta share kirar,yana daukewa kuwa taga flash messge akan screen dinta na sakon da nurse ta bar mata,daukar wayar tay da hannu daya ta bude,cos she wanted to knw how far,sai taga babu komi aciki face cewa da tay tamata droping important message a whatsap dinta tana bukatar dubashi cikin gaggawa.

Bude datar watsap din tay batare da bata lokci ta duba sakon ta karanta tagani cewa akan tsohuwar tace in taga wann wankar suje yau da dare duk tsiya suje atare akan za'a a mata wani muhimmin aiki acan gani tayi sauran sakonnin are waiting basu shigo ba tukunna sai tabarsa abude ahaka da zimman kafin nan ta gama wankan ta dawo message din ya gama shigowa inyaso sai ta zauna a nitse ta karanta a wangale tabar chat din sabida azaban saurin datakeyi.

Bucket din ruwn dake kanta ta rike dam dam ta tunkaro kofa kamar kafarta zai harde tsaban sauri zata fita.

Tana taɓa kofar taji an bankoshi ta waje an shigo ciki mummunan tsorata tayi ta sake bucket din akasa tare da fadawa kasa ta kifu akan cikinta girifff ruwan yabi ya zuba gabaki daya ajikinta. Ji tay bata iya motsi cikinta ya riketa kam kam.Wani irin wahalallen ihu ta tsala arazane jin muryan Ahmed akanta yanamai cewa subahanallahi arikice kkorin dagata yakeyi sai yaga ruwan magani yana malala ga kwaryar ya tarwatse, gata nan half naked daga itasai daurin kirji, kansa a mugun daure yake kallonta cikin rashin fahimtar yanayinta ga maganij da wani irin wari marar dadi, jim kadan taji cikinta ya wani murda jikinta ya dau rawa rawa shikenan taji ko inata ya sake jinin ne mai azaban yawa yafara bibiyar kafafunta kamar an sake bakin famfo.

Lokaci guda ta dauke cak ta suma daga nan Bata kara sanin inda take ba kota bude idonta ba sai a washe gari data ganta akwance agadon asibiti babu kowa a dakin sai ita kadai...

Ahankli ta bude idon tanata kallon inda take saida ta tabbata cewa asibiti ne snn ta lumshe idonta sosai, tadau tsawon mintina talatin bataga wani ya lekota ba sai can da Dr banky ya taho tare da wata police woman in uniform wacce babu alaman rahma akan fuskarta.
[7/18, 9:12 AM] SURAYYAHMS: Koda taga Dr banky ya shigo mata da police woman Gabanta atake yahau dukan uku uku yanamai faduwa sosai.

Kallonsu takeyi har suka karaso ta bakin gadonta dukansu suna kallonga kusan atare suka mata yay jiki?..

tace Alhamdullh da sauki.

Satar kallon su tay ganin suna comunicating da ido, sai can snn Dr banky yay murmushi tare da sauke gyaran murya yace mata "eehmm our wife, juyowa tay suka hade ido yace ina dai ure feeling fine now?cike da rashin fahimta Tace "yes"..
bankole pls i..i na Ahmed yake? why is he not here with me,yaushe aka kawoni nan?kusan arikice tace ..i.. i dont understand.. banky yace hey hey calm down,relax Ahmed zaizo daga baya, pls cooperate, ki bamu hadin kai "we are trying to get to the root of the matter. Zaki iya bawa hukuma lokacin ki kuwa? ya nuna mata police din officially snn yace She have some important questions to ask u regarding the nurse.

Wani hadiyan yawu Adiaha tay tace i hope der is no problem?

Yace no babu komi tambaye ne kawai ai

Nan ya bawa police din waje ta matso tare da kara mata murmushi ganin ta tsorata sosai jikinta na dan rawa rawa daga bisani tafara mata tambayoyi akan nurse dinta.

Like how they met..
Alakarsu da kuma irin treatment din datake bata har da inda take kaita neman magani.

Sosai kan Adiaha yay zafi ya daure taji zufa na neman wanke ta sai rawa rawa muryanta yakeyi datake magana..

Meke faruwa ne? Meyasa ake tambayartaa akan nurse, is asif they want to confirm if the nurse was her culprit on sumting.

Sai can snn abun yay hiting brain dinta acikin azabar kaduwa da tsorata ahankli ta kalle kan cikinta jin gabanta na wani irin faduwa sosai.

Kirjinta na bugu har Allah Allah take doc bankole ya shigo ta tambaye shi ko cikinta na nan cos she can't handle the pain in aka ce mata ta rasa shi.

Bayan ficewar police din Zaman shiru tay na dan wani lokaci jin ta kasa samun nitsuwa yasaka ta fara dube dube.

daga can nesa ta hango files dinta aranta tay hamdala acikin gaggawa ta motsa tare da yunkuri wajen sauke kafafun ta kasa domin taje ta dauko
Files din ta karanta

Tafiya take tana layi sabida jiri jiri datakeji dayake neman kwasheta saukar wani abu ta dinga yarrrr yana sauka yana bibiyar kafafunta bata kulashi ba har saida ta dauki file din ta rike a hannunta.

Budewa tay hannunta na rawa tafara dubawa ahankli da kyar ta gane rubutun inda tagani an rubuta pregancy of 8 weeks terminated throu miscarriage.

Cause of the miscarriege was a scientific word da bata san ma'anarsa ba..

Wani Diskirin ta tsaya batako motsawa tay shiruuu cikin daukewar cak nq tunani da kuma gushewar hankli har bata
San sanda file din ya sulale a hannunta ya fada akasa ba, karar dayay ne da iya kasar ya dan tsorata lokaci guda hawaye suka wanke mata kan fuskarta.

Bari Bari kawai takeyi jin numfashinta na sama sama alokacin ita kadai tasan metakeji aranta musmmn data lura cewa cikin ne ya sake kwabewa..

Daga kafafunta dake mata nauyi tay da zimman zata koma gadon ta dan karta fadi akasa tana daga kafar taga jinine yake kan binta tun daga inda ta taso har nan a rikice take kallon jinin ta tattaba jikinta taji alaman har sanitary pad ma aka saka mata duk da haka jini nazuba.

Wani irin karayar zuciyq da sacewar gabobin jiki taji jin kafafunta sun kasa daukarta.

Hawaye kawai takeyi at that moment ta daga idanuwanta sama suna fidda ruwa sosai har cikin ranta Addua take and she was wishing she is dead right now kawai dan ta huta da wann irin baqinciki da matsala.

Durkushewa kasa tay tanamai rusa kuka jin duniyar yafara fita mata akanta mai gabaki daya.

Bangaren su Ahmed kuwa jiyan tare da yasrah suka kawota asibitin su biyu bai kira kowa daga gida ba sabida baison abaza maganan ayita gulmace gulmace.

Tun lokcin zubar jini Adiaha take kamar bazatay rai ba suna isowa asibiti ana gwadawa kuwa aka ce mishi cikinne ya zube daga nan Ahmed ya shiga wani mayuwacin hali marar misaltuwa dan kuka ne kawai baiyi agaban yasrahn ba but he was uncontrolbly and madly emotional.

hakanan yabarta asibitin ya koma gida agaggauce ya fara bincike dan sabida tunda yaganta da su weird iron buckets da calabash da garin magani yafara zargin wani abu game da ita..
Chapter 116 · 0% Book details