← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 157

Sashe 118

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace yaaa Ahmed wajen anty reema zakaje ne?..

Batare daya kalleta ba yace "a'a..

Shiru tay Tuna cewa Adiaha bata da kowa wanda hakan yadada sakawa tafara matsa masa, tace yaa toh kayi droping dina awajenta mana pls i wnt to see hw she is doing..

Wani irin kallo yay mata kamar zai hadiyeta fuskarsa a mugun harde Yace Bata nan zan bi ba ni police station zanje.

Tace but atleast u can drop me.

Yay shiru bai kulata ba

Ahankli tace yaa but Is not fair dat she is alone right now. Kuma ai kace karna fadawa kowa Ni gaskiya Inason na kasance tare da ita.

Lumshe idonshi yay jin maganan datakeyi na neman bata masa raii.

Ransa a bacen ya kalleta
"I said bata nan zanbi ba, snn bata asibiti. infact babu inda zaki je yamma yayi, wai kodan kawai kinason abu saina fasa yin abunda ke gaba na miki shi?

rau rau tay da ido Tace Ni fa bance maka inason wani abu ba, cewa kawai nayi kakaini wajen anty reema na duba jikinta kace tana lafiya amma banganta agida ba.

A tsawace ya juyo yace
To bazan kaiki ba and please Get out of my sight right now shegen surutun tsiya.

Ko motsi batay ba ta tsaya tana kallonsa cikin ido da daurarren fuska.

Tsaki yaja ya bude motarsa ya shiga har zai tafi ganin bata motsa ba yace "if u like dont move kijira anan harsai na dawo!..

Batace mai uffan ba ya kada kansa ya fita yana kallonta ta glass ayayin da ta koma cikin gidan acikin yanayin hanzari.

Ajiyar zuciya ya sauke thinking dat umarninshi kawai tabi ta koma ciki.

Hanyar police station ya nufa dan daga nan dr bankole ya kirashi cewa sun taho da Adiaha za'a karasa maganan acan agaban D.P.O.

Daga nan kuwa Mai gadi yana rufe gate abayanshi yasrah ta leko ta waje itama dauke da jaka da takalminta.

Ficewa tay agidan atake itama ta samu abun hawa nan tace mashi ya bi bayan motar Ahmed din har ixuwa inda zaije duk tunaninta ta bari acewa wajen Adiahan zaije.

Yay musu nisa amma haka tasaka aka dinga bibiyarsa har suka kai gaban police station.

Ahmed yana sauka ya fara amsa waya wanda ya bata daman isowa ta wajen ta rakube tana jinshi duk dama da yare yake magana batasanin meyake cewa few words daya fada da turanci yasaka ta gane cewa lallai case din ya shafi Adiaha.

Kanta sosai ya daure kirjinta ya dinga bugawa da tunanin abunda ya afku har akazo nan.

Yana kammala wayar kai tsaye ya shiga ciki, yana shiga ciki itama ta biyo bayansa confidently ganin shi har ya shiga office yasaka polisawa suka tsareta tace musu ai yayanta ne atare suka zo.

Rashin tsoron dake tattare da idanunta yasaka polisawa suka kyaleta itama ta isa.

A bakin kofar ta tsaya da tunanin yadda zatayi tafara shiga ciki tsayawa tay cikin tunanin meya kawosu anan sai can tafara jiyo sautikan muryoyinsu.

Aciki daga Wakilin asibitin da nurse take aiki sai Dr bankole da Adiaha da ita kanta nurse din.

Hankalin Adiaha bakaramin tashi yay ba musmmn da dr banky ya kawota nan tazo taga yanayin nurse duk ta birkice ta zama abun tausayi sabida yadda su Ahmed suka saka aka razanata.

Koda aka fara case din she decided to take all the blame on her self sabida dan ta wanke nurse din daga tuhumar da su Ahmed suke laying akanta.

Ahmed baice uffan ba yanajinta tana ta daura wa kanta laifin komi She said duk abunda ya faru game da kwabewar cikinta na farko dana biyun duk laifinta ne itace ta aikata kuskuren snn tay involving nurse din can aciki.

Bakaramin tausayi ta basu awajen ba hatta yasrah dake labe a kofa tanajiyosu sai dataji ruwan hawaye ya ciko idanunta face shi da baijin digon tausayin ta aranta saima karin tsananta dayaji yayi

Shiru yay yana Jiran asake su yaje gida tun da har tazo agaban hukuma tanacewa itace take son kashe masa y'ay'a danta kare mutuncin wata.

D.P.O yay musu warning ita da nurse din snn Ahmed yace shikenan nan aka tashi case din.

Tun anan yace ma Adiaha kar tasake ta dawo masa gidansa duk ta rasa me zatayi banda rawa da jikinta yakeyi shikadansa.

Ficewa a station din yasrah tay cikin sauri tun ma kafin su fito, abun hawa ta nema sharply acikin keke din ta karasa masa kwatance gidan nasu,dake bata wani san hanyar sosai ba tana isa gida suma suna isowa dan haka ta wuce cikin main house ta zauna a falo danma kar yagane ta bishi can.

Shikadai ya tuko motarsa Dr bankole ya dauko Adiaha din tana kukan ta shiga uku shikuma Dr banky yanata babbaka mata fada da masifa acikin motar akan Abunda tayi yanzu na amsa laifin komi dan kawai asake nurse din.

Yace mata dat is also wrong!! And he cant just believe dat taje gaban hukuma tayi admitting din duka laifi akan kanta bayan tasan Ahmed yana da haqqi akan abunda sukayi,yace mata dos dat means she value her friend's feelings more than her husbands feelings kenan?sosai banky yaji takaicinta dan A memakon tabari a yi musu hukuncin dede gwargwado ta inda zai rage yawan fushin Ahmed yanzu da tace laifinta ne duka and she did evrything willingly case ya zamo tsakainta da mijinta ne kadai.

Duk jikinta na rawa Sai kada kanta take tana kuka tana ce masa ba haka bane amma yaki jinta karshe ma yace mata babu ruwansa da ita shikam.

Ta dinga rokonsa akan yay ma Ahmed magana ya kulata zata masa bayani dan tsoro takeji matuka na yadda zata kaya tsakaninsu ayau.

Duk dama ta bashi haushi sosai amma yadda take kuka yasaka bai hana ya amince mata da hakan ba sabida tausayi datake bashi sosai.

Ahmed yana parking motar sa ya shiga cikin gidansa da tunanin yasrah tana ciki.

A falo su Adiaha suka zo suka samesa tana tafiya baya baya ahankli jikinta duk ya mutu tsabar tsoro har wani rawa rawa jikinta yakeyi tana tafiya kamar wacce bata da laka.

Agefe ta tsaya tana ɓari kar kar tana hawaye kanta na kallon kasa, har dr bankole ya samu waje kusa da ahmed din ya zauna batama sani ba.

Ji tayi ya fara masa magana da yarensu cikin sautin lallashi saidai batajin me suke cewa.

But by the way ahmed yake karkada kafafunsa a masife tasan bala'i da masifa kam ta riga ta jawo makanta yau.

Haka doc banky ya gama masa magana akan da yay hakuri ya bita ahankli sabida health conditon dinta ahmed baice masa uffan ba saidaima ya amsa da yanayin gatse.

Karshe ma daya ishe shi da magiya da basa hkri akanta cakka masa baqar magana ya farayi, direct yake ce masa ya bari inyay aure matarsa tayi masa hakan sai shi yay hakuri ya yafe mata amma bashi ba,snn kuma he dont care in rufa rufa tay ma nurse tunda dai ta amshe laifin duka ita kadai bazai hukunta kowa ba sai ita kadai.

Dr banky har ya tashi tafiya rokonsa yake akan yabita ahankli amma dukkan alamu sun nuna bajinshi yakeyi ba.

Yauko rakashi waje baiyi ba yay musu sallama yana daf fita ya kalle Adiahan dake rakube ata kofa da fuskar tausayi nan yace mata taje ta tsuguna ta bawa mijinta hakuri..duk fushinsa ai zai sauko!

Godiya tay masa snn ya fiice aka barta daga ita sai Ahmed din.

Wani irin shiru falon ya dauko fuskrsa a tamke kamr bai taba mata dariya arayuwarsa ba

Tsananta rawa jikinta yay ta Kasa iya cewa komi bare ta iya daga kafafunta izuwa inda yake. Matukar tsoron tunkararsa takeyi cos she dont knw what to say.

Jin ana kiran sallan magrib wani tsaki yaja snn ya miƙa yay waje fuuu ya wuce masallaci batare da ya kulata ba.

Kuka ta fashe da shi mai tsuma kafin nan ta wuce room dinta jikinta a sanyaye saidai tsabar damuwa ta kasa iya tabuka komi ga jiri jiri dayake yawo da ita har tana ganin duhu duhu sabida batasaka komi acikinta ba ga zuban jini

Ata dayan bangaren kuwa Ahmed yana shiga masjid yasrah ta saci jiki ta dawo cikin gidan abunta.

Direct ta nufi nata dakin dantayi alwala tay sallah tana Allah Allah ta fito ta samu adiaha musmmn data soma fahintar case din da ake ciki.

Bayan ta idar da sallahn kenan kiran kawarta maryam ya riketa.

Its was an important call daya shafi karatunsu dan hakan yasaka suka dau lokci lokacin data gama wayar har an kira sallahn isha'i, mikewa kawai tay ta dora, tana cikin sallahn takai raka'a kamar biyu tafarajin wani irin hayaniya mai daga hankli.

Fannin Ahmed din Tun fitrsa agidan zuciyarsa yake kuna yana tafarfasa sallan ma ba anitse yay su ba haka nan ya sallame ya dawo gidan cike da zafin rai kamar wanda ake ingixosa.

Direct ya shige room dinta ya samu Adiahar a zaune duk ta takure ta rabza wani uban tagumi

Wani fuuu ya shigo bata hankara ba taji ya fixgota waje..yana mai cewa
"How dare u enter my house? Ina wasa dake ne????.

A mugun razane ta miƙe zumbur take kallonsa jikinta na rawa kamr mazari nan da nan ta sulale kasa tafara kuka tana mai bashi hakuri.

"Ahmed pls i am sorry
"I made a mistake..
"its all my fault dan Allah kayi hakuri bazan kara ba.

Maimaitawa take kamr wanda ta zare tana rokon shi da dukan zuciyarta.

Zuciyarsa ya riga ya harzuka babu wani abunda ke brain dinsa sai tuna asarar haihuwar data jawo yayi, ahalin yanxu ma ko tausayinta bayaji aransa shiyasa Hakan datake fada ma haushi yake kara bashi yanajin kamr ya rufeta da duka ya huce takaicinsa.

He started insulting her as usual, zagin kare dangi, blue black, yana kiranta marar hankli,jaka wawiya,dabba, tanata kuka yace mata saidai ta bar mishi gidanshi tasan kuma inda zataje.

Ita kuwa tamkar wacce akayiwa maganin bita zaizai akanshi dan yana kan hankadata ne tana bibiyarsa kamar kariya tana kamoshi jikinta.

Tanamai kuma dada kaskantar da kanta bisa kasa tana kuka akan sawun kafufunsa tana kwanciya har kasa bisa kafarsan tanamai bashi hakuri.
Chapter 118 · 0% Book details