← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 157

Sashe 89

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yasrah na ganinta ta sunnar da kai don bata so ta fito ta sameta tare da shi a tsakar gidan ba dan ta lura kamr Adiaha tanada dan matsala da ita, idon Ahemd na kanta har ta karaso falon kanta a kasa itamq, tana isa yasrah ta dago kaivsuka hade ido lkcin Adiahan ta hade rai yanayin da daxu tagansu yana dawo mata aranta dada harde ranta tay batare da tasani ba
,nan yasra tay saurin dauke kai,snn ta ce "Ina kwana Anty"Adiaha ta kirkiri wani murmushin da bai kao wuya ba tace "Lfya lau, sister ko, Yasrah tace "eh"..bayan nan ta juya tadubi Ahmed din da wani irin yanayi snn ta fara gaishesa sama sama ya amsa ta, yasrah dai bata ce komai ba sai kofa da take kallo,..

Ganin Adiaha na tsaye batace komi ba Ahmd din ne yace Toh ki karaso ki karya mana? girgixa kai Adiahan tayi tace "A'a na sha tea tun daxu, yace "ohhhh, Ohk dats gud..ya dubeta sigar looking out for his baby, yace i hope bbu wata matsala dan i wll be going to the office now.

Tay shiru da tunanin me ma zatace masa kafin nn sai taga harya fidda kudi dubu dadaya haka a aljihunsa ya aje few mints agabanta,ta dago tana kallonshi,cewa yake koma menene matsalar taki just take this.." Da ido tabi kudin dan tasan he is just trying to fool her into the gaslight,wato gata mayyar kudi sai an ancuceta sai abata kudi duk ta lura yanayin dayake ciki musmmn in yay mata abu marar kyau saiyy kmr baisan metake ciki ba bayan yasani sarai.

Ahankli yasrah ta miƙe kofa ta nufa jin Ahmed baice komai ba,da gefen idonshi yake lura da tashintan yana ganin hkan yace "Ki jira ni agun mota, toh kawai tace ta fita, a sace yabita da kallo dan kallonta baiya isarsa dan dressing dinta datakeyi kullum in zata fita bakaramin kyau yake mata ba musmmn ma in tana tafiyarta slow and majestic cikin kasaita da tattali sai tay kmr wata arab celebrity,Adiaha da mood dinta ya canxa lkci daya ta sunkuyar da kai kar ya lura da yanayinta.

Yasra tana fita shima ya aje spoon dinsa atake batare da ya karasa cin abincin ba, da sauri Adiaha ta dago ta kalle shi ganin bai ko kulata ba yana kkrin mikewa tsaye Wani gulluton yawun takaici ta hadiye snn Tace "haba Hubby har ka gama cin abincin kenan?
Atakaice Yace ehmm can't u see im in a hurry, saifa na kaita schl inje office, ta tabe baki snn tace okay,sorry...ko kuma in kaita ne kawai tunda ni shop zanje kaga am not in a hurry saikai kar ka makara aiki".ba tare da ya kalleta ba yace "Ai ita ma ta iya driving din inda ina son taimako da mota zan siya mata, Adiaha ta dago ta masa wani irin kallon rashin fahinta, atake sai ya canja topic din kai tsaye, yace hmm, i'm suprised u asked thou na dauka ai baki damu da kowa bane saini.

Ta kara dago kai ta dubeshi "Why did u say dat?? Girarsa na sama a dage yace "Dats d truth."

Tace...Ahmed nifa matarka ce dole ne na damu dakai fiye da kowa, snn duk wani abunda ya shafeka nima ai ya shafeni..cikin datsar nunfashinta Yace hmm karya kenan kuma"..tace karya? Toh why wund u let me help ur sister haba dan Allah meye aciki dan nakaita schl din hubby?

Yace ohh, Thank you for reminding me, but point of corection pls, ke ki fara tambayar kanki why can't u help and be the matured one on ur own? Ko komi saina fada maki ne?..The first day my sister came to dis house u starve her, bata da lfya ko ajikinki, kikaje kinata baccin asararki ko sau daya baki zo kin dubata ba bare kisan ya take ciki....

cikin katseshi da fushi ayanayinta tace but U took her away kuma ai u knw my conditon. Snn ai kaika fara nuna cewa u don't need my help..

Yace ohhh, nine ma?toh Karki sake kice zakiyi amfani da cikin dake jikinki ki raina min hnkli ke kikasan abunda kika kulla aranki, ko saida tazo ne condition din naki zai tashi? Kafin tazo Anan gidan idan nace miki ki huta karkiyi aikin komi ko karki fita kasuwa bacemin kike lpyarki kalau u can handle it ba?..but all of a sudden u became sleepy and hard girl da sister tazo gidan nn, mtssss why i am even talking to u?..Shiru tay dataga ya fara daga mata murya, ransa bace yace..i didnt expect dis frm u...reema kin bani mamaki. Ke yanzu bakijin kunya intana gaishe ki? Pls What hve u eva done to her face kunyatar dakanki dakike kanyi agabanta..see Idan baki kama kanki ba, tazo tafara rainaki ni babu ruwa na kinaji na ko?..
Snn Wann ne karo na karshe da zamuyi wnn maganan dani dake.

Yana kaiwa nan ya miƙe snn ya kama hanya zai fice Adiaha dakejin kmr tafara mishi kuka ta riko hannunshi abazata tace
"To shikenan, kabarni nafara gyara kuskure na mana..let me take her to schl din kai sai kaje aikin.

Fuskansa ba a sake ba Ya fauce hannunshi, no i said, da Akwai kudin da xan bata ne shi yasa nace zan kaita dakaina.
"kudi? Adiaha taji kmr ta kwala ihu,wato har kudi itama yake bata kmr wata kishiyarta.

..murmushin karfin hali ta kirkira tace "Cmon hubby nima ai kanwata ce, cikin dabaran son sanin amount din tace, emm nawa ne xaka bata sai in bata kawai..

Batare da ya dubeta ba yace "pls Don't bother, ke ina kikaga kudin da zaki iya bata,suna da yawa kudin. mikewa yayi yana dada goge bakin sa da tissue yace "ni Na tafi, sai na dawo, take care of my bby for me" yana kai wa nan ya nufi kofa, bin sa da kallo tayi xuciyarta na tafarfasa, tana ganin fitansa ta mike da sauri har tana neman faduwa ta nufi ta window tana lekasu dan ta ga inda yasrahn xata xauna a motar tana bude labule kuwa dai dai lkcn da yake budewa yasrah ta front seat ta shiga, shi ma ya xaga ya shiga maxaunin driver, ta fashe da kuka da karfi wani mugun kishi yasrahn na karuwa acikin xuciyarta, anya xata iya ci gaba da yin abinda yake so din kuwa da tunanin hakan yasa ta rushe da kuka ta koma dakinta tana rerawa.

Har suka isa harabar makarantar Ahmed bai ce ma yasrah komai ba ita ma wayarta kawai take kallo abun ta, har saida yyi parking sannan ta dauki jakarta dake kafadarta xata fita yace "Ki na da hankali kuwa, "wa ya baki izinin fita?

komawa tayi da kanta jikin kujerar da take xaune ta lumshe ido tana mamakin audacity irin nashi dan yafara isarta da nuna iko, kallonta kawai yake, ita kam bata ma san yana yi ba, ya wani daure fuska yace

"Wann breakfast din da kikayi kina ganin shi zai rikeki?..meyasa kika bar kan abincin ki daxu, ba tare da ta kallesa ba cikin tuno da abunda matarsa tace masa itama tay rolling masa idanunta sigar cakka magana tace "Na sha tea".Adan tsawa ce yace "Hey look at me!"

Juyawa tayi afixge tana kallonsa tsege tsege, yace "Yaushe na fara wasa da ke xaki wani dinga dauke min kai ina magana "kinsha tea fa kika ce min?...when? Ko dan kinji matata tafada na kyaleta shine kema bari ki fada, did u think matsayinki daya ne da ita dahar zaki cemin kinsha tea?

Tagumi tayi tana kallonsa ko kifta wa bata yi dan har dariya taji ya bata ganin yanda ya firta maganan matsayi, aranta tace wawa kawai ko shi wayene oho, snn taja masa wata dogowar tsaki arantan batare da ya fahimce hakan ba.

Kamr wanda yake karantarta Ya kada kansa cikin takaici yace naga alama don kin ga ina kulaki shi yasa kike son ki raina ni koh? Toh zan kuwa baki mamki, Ita dai bata ce komai ba kuma bata fasa kallonsa ba.

Kayan jikinta ya kalla da yadda tayi rolling veil din abayarta a kai wajen kwllyar gold din ne ata gaba ya mata kyau bana kadan ba,yace wai karatu kike zuwa yi nan ko gasar fashion parade da xaki dinga irin wannan shegen shigar kina xuwa makaranta, kina da hankali kuwa ko bakisan kin girma ba?...

kallonsa take har lkcn kuma bata ce komai ba, kafin ya kara cewa wani Abu ta kalli agogon wrist dinta tace "Its almost time for lectures are u done? Da mamki Yace "whaat?tace Time for lectures i said, tana fadin haka ta dauki jakarta ta bude motar ta fice, bin ta yyi da kallo cike da mamakin ta, baisan lkcn da yyi murmushi yana shafa kansa ba cos bai taba haduwa da mace mai attitudes arayuwarsa ba, kamar wanda ya tuna wani abu ya bude motar shima ya fita ya kulle sannan ya bi bayanta.

tafiya take kamar mejin tausayin kasa tana rataye da jakarta mai tsada ko kai ka ganta sai ta mugun burge ka don a nutse take tafiyar ga wani irin sanyin kamiya dake fallasa kansa atattare da ita, kamar ance ta waiga kuwa taga yana biye da ita a baya ai bata san lkcn da ta tsaya cak ba gabanta na faduwa sosai, nan ya karaso ta gabanta ya tsaya yana facing dinta batare da ya sake fuskansa ba, sunkuyar da kai tayi, yana mata wani irin kallo yace " ina maki magana u walked out of me are u insane?" Kin cewa komai tayi, yay furxan iska tare da gyada kai yace "very Gud, nasan maganin irinku," Kudi ya ciro aljihunsa ya mika mata,ta karba kamr ansata dole murya can kasa tace "Thank you" bai amsa ba ya dada daure fuska, wani kati ya ciro shimq mika mata fuskarsa daure yace "yau Driver ne xai kira ki" ta karba katin tace "Toh.

Yadan tsaya kadan cos He expected her to apologise kamr yadda Adiaha take mishi komin karamin abu sai ta susuce tafara bashi hkri yaga wann batama san yanayi ba, hauka ma take son manna masa kmr.
Chapter 89 · 0% Book details