← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 157

Sashe 16

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauke ajiyar zuciya hjy khdijatu tace zainab u need to calm down pls. Zai iya yuwa kuskure ne
Kinga ai Babu wanda yafi karfin mistake ko?

Tace hakane mumy amma next time bazan yarda ba yakamata ta nayin abu kamr na mai hankli mana she is too clumsy.

Tace "Its okay kiyafe mata, kiyi hakuri, she is new to this place zatazo ta fahimci komi..kuna binta hankli kinji?

A ladabce sosai Tace yes mumy. Nan da nan tazo ta amshe tray din abincin ahanunta snn tace kibari ni zan kai mata abincin mumy.

Murmushi hjy khdijatu tay snn ta mika mata tray din tanamai saka mata albarka.

Kallonta ta dingayi harta fice a sashen ayayinda take murmushi...

Daga ta bangaren Adiaha lkcin ta fito daga wanka kenan jikinta daure da white towel saiga sallamar sister zainab a sashen nata.

Wani irin faduwa gabanta yay dataji muryanta kusan a firgice ta fito batare da ta saka komi ajikinta ba.

Adede tsakiyar falon suka ci karo mamaki ya datsar da ita dataga sister zainab dauke da tray a hannunta da wani irin kallon shan qamshi take binta dashi.

Muryanta harna rawa rawa tace sister zainab kece? Sannu da zuwa mmmm Ina fatan babu wata matsala , yaya hannun yaron ki i hope....?...

Cikin datsar numfashinta da masifa tace kimin shiru abeg, kinfiye son surutu, you hope what? Harkin fara zaton ya mutu ko?...Back to sender obanje..kece zaki mutu ba dana ba.

Muryanta a sanyaye tace
Am sorry sister ba haka nake nufi ba, i was just worried.

bata wani kulata ba tace Comn shut up abeg, karbi tray din nan mumy ne tace na kawo miki abinci.

Tun ma bata karba taja mata tsaki zata sake matashi akasa tay saurin tarowa tanamai cewa thnk u sister. Bari naci abincin na shirya zanzo na duba hannun yaro..im really sorry...nasan bansan zafin haihuwa ba
Kiyafemin sister.

Hakan data fada ya saka sister zainab ta danji tausayinta aranta sai batace mata uffan ba ta kama hanya zata fice kenan saiga hjy khadijatu ta shigo.

Da mamaki Tace haaa mumy harkinzo nan bana ce miki kina hutawa ba.

Murmushi hjy khadijatu tay mai fadi snn tace toh Angon nawa yaki ya kwanta akan gado yau yace abayan amarynsa zaiyi bacci shiyasa nace bari nazo dubaku tanan.

Adiaha tana jin muryan hjya sai tay maza ta aje abincin akan dinning ta wuce ciki da sauri ta fara shafa mai agurguje,yau sama sama ta shassfa powder a fuskarta bata wani yi kwalliya ba dan kusan kominta ya kusa karewa.

Banda wanda tazo dashi Haryanzu dai Ahmed bai ce mata komi akan kayan sawa ba bare kayan kwalliya.

Iya wanda akayi bikinta dasu shine kawai mata mata masu kyau,sai guda biyu bakin abaya da wani sleeping dress da grand ma ta bata acan yola take sawa, sai t sht dinta tun wanda ta gudu tabaro calabar dashi Banda wanda jiya aka basu pink lace da sukayi hidiman liyafa dashi.

Bayan ta kimtsa kanta saita rasa abinda zata saka ajikinta, karshe dai haka ta sako abayan ta fito dashi. She look prety sabida tana da natural beutynta wanda ko babu kwalliya dai bazaka ce mata mummunan mace ba.

Sallama a falon tay lokcin hajy khadijatu tana tsaye da shafiu abayanta sister zainab kuma ta zauna akan daya daga cikin kujerun dinning table sunata hira da hjy khadijatu akan yanayin tsarin gidan.

Ce ma hjy take bata taba tsammanin cewa Ahmed dinsu da taurin kansa zai amince ya zauna acikin family house ba duba da already yay nisa aginin nashi gidan awani sabuwar anguwa nadaban.

Tace mumy ayadda Ahmed ya tsara ginin gidansa kamar wata sarauniyace zata zauna aciki compare to this house ai kamar ma acikin takura yake.

Hjy khadijatu tanata murmushi tace zainab kenan, ai ba abun mamaki bane sai kiga Ahmed yafison zamansa anan gidan akan gidansa nakansa, badon komi ba saidan saboda yan uwansa dasuke nan.

Kinsan fa Yan uwantaka na da dadi sosai, Shiyasa bana son naga kuna raba kanku a matsayinku na yan uwan jini..kullum fatana shine zumuncinku ya daure har Abada dake da yan uwanki da kuma dangin mijinki, Cikin salo ta kalle Adiaha dake kan zuwa wajensu kanta akasa ta sunkuyar da kanta tana tafiya ahankli da alaman tanaso taji karshen hirarsun da sukeyi, cikin son taja hanklin sister zainab akanta tafara mata nasiha cikin salo sosai.

batare da ta zafafa maganan ba tace zainab Kece babbansu acikin mata ynzu, kamata yay kihada kanku dukan matan gidan nan..u have ur own husband, but this family is still urs. kisani Matayen dake gidan nan are all under ur brothers control,sukuma brothers dinki basuda kowa saike Idan har baki jasu ajiki kin koya musu hadinkai ba abun duk bazaiyi muku dadi nan gaba..

Cikin nitsuwa sosai Sister zainab tace haka ne mumy kin fadi gaskiya i wll do my best..

Tana fadin hakan Saiganan Adiaha ta karaso acikin ladabi tay musu sallama snn ta kara gaishesu tana shan mamakin yadda sister zainab tadan sake mata fuska.

Agogo ta kalla acan sama snn tace mata iyawo Dami Kixauna kici abinci manou its already Getting to noon.

Adiaha tace okay sister
Nan ta ja kujerar dake gabanta zauna ata dayan gefen tana ta sum sum wai dan Duk tana jin kunyar hjy khadijatu.

Zata bude abincin kenan taji sautin muryan hjy khadija cikin murmushi.

Tace toh."Bari naje na aje angona akan gado karya karyamin bayana nasan hala ynzu baccin nasa yay nisa. Tana maganan tana dada gyarashi sai dada kankameta yakeyi.

Sister zainab tafara musu dariya. Yeeey Mumy kiga wai har yana makale maki abaya this Ango bayason ya rabu da amryansa oo.

Dariya hjy khadijatu tayi sosai.

Cikin sanyin murya Adiaha tace mum ina fatan jikin nasa dai da sauki ynzu. Tasa fuskan tausayi, tace Its all my fault... ban lura ba am really sorry.

Hjya khadijatu tace
"Its okay, bakomi zai warware. Amma kina kulawa next time. Sigar wasa tace "bazn yarda kuna sakamin ango na kuka har da baccin dole ba. Duk wanda ya sake zai gamo dani agidan nan.

Tace in sha Allah bazai kara faruwa ba im sorry about that maaa.

Sister zainab tanajinsu batace musu komi ba.

Murmushi hjy tay snn ta fice a sashen tare da jikarta shafiun abayanta
Ta koma dashi main mansion ta shimfidashi akan gadonta ya cigaba da baccinta ita kuma takara shiga wanka.

Wani irin luxurious furnitures na gata yayan mijin nata suka mata inka ga sashenta tamkar Aljannar duniya haka suka maida mata.

A fannin Adiaha kuwa
Daga ita sai sister zainab
Aka barsu duk ta kasa sakewa saboda tsoronta datakeji aranta sosai

Adiaha tana jawo abincin gabanta tafaraci bayan tay kamr loma biyu kafin nan, sister zainab ta karbe spoon din tafara tabawa, sanda ta cinye kusan rabi kafin nan ta bata sauran ta cigaba da ci abunta suna dan satar kallon kuna Sai can sister zainab tace Hmmm Wai Abinci kenan wnn?hey Reema Did u really cook dis things as breakfast in ur fathers house? Ko anan ne kawai kikazo zaki raina mana wayo.

Adiaha tace no sister, mu yawanci coco yam da tuwo muke ci da safe with banga soup or dog meat stew..we do eat alot.

Sister zainab ta saka ihu mai kara ta mike tsaye tace "Haaaaaaaaaaa" God forbid, dog meat ke? Kina nufin kinci naman kare? Alade fa?..

Adiaha ta aje spoon arazane ganin irin ihun datayi, tace ahhh Sister zainab pls calm down now wann fa tunda can ne, yanzu na dawo musulumi bana cin kare da komi ma, even grand ma say is haram she say i cant even take wine.
Tace shan giyama haramun ne.

Cikin sauke ajiyar zuciya Sister zainab tace yess o u can't. And i beg u Dan Allah karki sake fadawa kowa cewa kintaba cin naman kare...Ahhh ahhhh reema zakisa mutane suna gudun abincinki harma sunajin kyamanki musammn ma da ayanzu kece zakina mana girki agidan nan.

Tace okay sister.
Dama Ina da wata tambaya danake so na miki

Sister zainab Tace what is it?

Tace sister, nace meyene yakamata ina dafawa agidan nan,pls what shud i be cooking?

Da wani irin tsiririn harara sister zainb tabita snn ta kyabe baki.

Lokacin da kika yarda zaki Aure Damilare alkcin bakisaan da cewa shi yoruba man bane?..kin auri yoruba man menene kike tsammani zakizo kina dafa ma familynsa did u think we wll eat ur dog meat?

Adiaha tace sister zainab pls now Taimaka min kawai fa zakiyi pls help me out now, idea zaki bani pls .

Tace hmmm kuma Nice zan gaya maki abunda zakina dafawa agidan mijinki Reema?...U sure say ure well?..nizan maki zaman auren?

Zatay magana cikin katseta tace bari nagaya maki labari, ni lokacin da aka kaini gidan mijina babu wanda yagayamin mezan dafa musu.

Nidakaina nayi tunani kuma bantaba samun wata matsala akan abinci da inlws dina ba
Wato saikece shafaffiya da mai kina neman wanda gaya maki ko?

Adiaha tay tagumi ganin harta mike tsaye tana harararta tace "ni zan koma wajen mumy go and sort it out urself oo, if u like browse,ask, but i dont care, gobe zaki mana abinci kuma akan lokci..dan kowa haka yakeyi agidan mijinshi.

Karki kara memeta abunda yau kikay mana fa,badan hajy ba da yau kashinki ya bushe a hannuna, be wann ooo!!

Tana fadin hakan ta kama hanyarta ta fita....

Tunda ta fice Adiaha tay zugum awajen bata motsa ba, tunani kawai takeyi na duk wani yoruba food data sani bai wuce tuwon Amala da ewedu soup ba.Kuma gashi bata wani iya yinshi sosai ba,musmmn ma miyan ewedu dan duk wani miyan yauqi sam bayayin yauqi a hannunta.

Tunani take koda ace zata iya tunawa da Abincin wasu kawayenta yoruba girla da sukayi university tare.

Daga bisani dai ta bude chat dinta dake sabon lambace da ita dakyar ma wasu kawayentan suka ganeta, nan tafara tambayarsu idea akan yorubq delicies amma bata wani samu gamsashen amsa awajensu ba. So she decided to cook jollof rice for lunch tunda dai kowa yanacinshi kuma ta iyashi sosai. Daga nan Bacci tay da niyyar inta farka akan lokci zata musu lunch kafin nan yaransu su dawo daga makaranta.
Chapter 16 · 0% Book details