← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 157

Sashe 65

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai da ta taje dab bakin kofa zata fita Taji muryan hajiya maimunatu daga can saman matakala tana ce mata "ke Yasra,

Gabanta ne ya fadi tana juyowa suka hade ido taganta sanye da kayanta tsaf itama,

hararta tay tace "kin kyauta zaki fice batare da sanni na ba ko?oya come back here, wai ina zakije ne, kuma ma cin abinci a waje ko bana sha fada miki banason hakan sabida babu kyau ba, shine kika wani dauki sandwich a hannu kamar wacce ta roko toh yayi miki kyau."

Shiru yasrah tayi sai da hjya ta gama maganan da takeyi tukunna ta kalleta da shgwaba akan fuskanta ta dubo tana k'arasowa cikin parlourn da tausashiyar muryanta mai sanyi tace "mumy ashe har kin farka nifa banma San kin tashi ba, a ladabce sosai tace "Ina kwana" ta sake maimaitawa bayanta karaso kusa da ita.

Da lpya ta amsa mata snn tace "ina zakije bayan nagaya maki flight dinmu is by 10:30am..har yaushe kika dawo daga yawon mukaje airpot..ina da meeting a Abuja yau da yamma bana fada miki ba?

Ta makale wuya tana bata cute face, mumy Dan nan din ma dazanje?
Kefa kikace su farida har sun isa can, dan Chocolate din ma da zan kara siya mana shine bazaki barni ba?

...fuskanta data shagwabar hajy takama lovingly ta ja .."kedai ba a rabaki da jaraba yasra,
Meye kuma cokalate? Kinsayi cokolates din nan fa gari guda,rabin jakanki duk sune,nagama duk sai yay muku yawa acan din,gaki da shegen son ciwon ciki, inma bai isheku ba l akwai a nigeria tunda ma Abuja zamu fara sauƙa ai saiki siya acan..yawo acikin turkey dai haryau bai isheki ba.

Kwanciya tay ajikinta cikin yanayin sakalci snn "mumy pls, nide na nan nake so, ai na nan dinma duk yafi na Abujan dadi ...tace ke duk abu dayane..ince dai baki mance komi naki anan ba ko?

Tace yes mumy, komi na tattara. Toh naji bari naje na duba nagani.. ta tashi zata wuce sama, yasra ta riko hannunta tanamai makale murya, snn tace "mumy inje din? Hjy tace Kai, yaaa subhanallhi,to shikenan bari driver yakaiki nasan in shine yanzun zaku dawo..
..Inkuma bashi kike so ba to babu inda zakije, bani ma key din motar.

Mika mata tayi, snn aka hadata da driver aka basu 30 minutes na shoping. Dan daga nan airpot zasu wuce su dawo nigeria.

Kafin nan jiya acikin dare kafayat ta fara aikata abunda yakaita garin lafiya wajen kawar mamanta anty rakiya..

She want to be rich by all means posble agidan jimada, along with her oder plans of dealing with Adiaha dan sosai ta kular da ita kwana biyun nan..

Tun zuwanta lafiya suke cikin jeji suna kwana ana secrifices na dabbobi domin ayi appeasing goddess sabida duk wani asirin da suka kulla game da mission dinsu yay tasiri.

Mahaifyarta hjy fatihat ce ta turota nan ita ta tsaya a Abuja dan kar ayi suspecting nasu idan wani abu yazo yana faruwa.

Washe gari sassafe Dauke da white hair towel Ahmed ya Fito daga bathrum yana goge black and silky smooth hair dinsa xtrmely gently daga ganinsa kaga shigen mutum mai mugun son jiki...

Bayan nn agaban mirror ya zauna ya shafe duk jikinsa da mai ya fesa body spray tukunna ya je closet ya saka kayansa sai da ya saka kayan snn ya dau wayarsa ya kunna inda yaga shigowar sakonni babu adadi.

Zama yay abakin gadonsa da mamakin ganin yawan sakon ciki harda na mahaifinsa.

Kkrin budewa yakeyi saiga kirar brother hamzat ya shigo..

Daukawa yay kai tsaye yarusana kai kasa cikin girmamawa kamar wanda yake gabansa yana kallonsa ya gaishesa, nan yake gaya masa cewa shima ya dawo Abujan jiya da dare amma Ga abunda yazo ya tarar ana bukatar ganinsa cikin gaggawa.

Ahmed yana sauƙe wayar a kunnenshi ya shafe kan fuskarsa da duka tafukan hannunsa jin wani irin kakkarfan baqon yanayin mai matukar saka farinciki ya mamayesa lokci guda.

He was snaped out of reality tareda kalman cewa He is going to be a father wanda hakan ne kawai yaketa famar memetuwa acikin kwakwalnsa yanajin kansa daban.

Bugawa zuciyarsa tahau yi da sauri da sauri yanajin wani irin kakkarfan sabuwar yanayin murna na cakuda masa ruwan cikinshi with lots of emotional rush with anxiety nashan mamakin jin wann news din sosai.

Bai taba tunanin haihuwa aransa ba sabida haryay aure baijin son auren aransa kawai yayi ne dan dole..,but being a father is indeed another achievement dat he cant ignore, shiyasa abun yazo masa daban yafarajin wani sabon obsession da hakan yana mamayesa, Hamdala yay jin duk jikinshi na rawa ya kasayin komi a nitse nan danan ya tashi ya hau shirin komawa Abujan idanunsa a rife.

Shiri yake kamar na wanda inya isa abujan dan nasa zai gani direct

Sama sama yaje ya sama suka gaisa da mum dinsa ya gaya mata abunda akeciki, tana son tabiyosa itama dan tazo ta duba jikin Adiahan amma hakanan ya hanata duba da yaune hajiya maimunanatu zasu dawo gaba daya,
Adan aggauce sukayi sallama ya nufi airpot yaje yay booking flight but due to weather conditions aketa shifting musu lokacin tashin jirgin. zaman da yay yana jiran lkcin ne ya jefashi cikin tunanin yadda zaije ya fara lallabata duba da yanayin da suka rabu cikin saɓani.

Duk dama yasan bai kyauta ba amma bai wan damu ko ya daga hanklinsa ba sabida yasani sarai zata yafeshi koda bai neme hakan daga gareta ba..

Besides bata da wani mafita sai shi dolene ma kawai tayi hakri da shi..

Ata fannin Adiaha kuwa tun asubahi ta farka jin karfin jikinta ya dan dawo
Wanka tayi ta hado harda alwala,sallan ma a sama sama takeyinshi duk tunanin inda Ahmed yake ya mamaye mata zuciya,

Izuwa yanzu Tay regrting haduwarta da urua harta gaji, bayan ta idar ko addua batayiba ta jawo wayarta tafara neman layinsa amma still bataji an bude anan ta shimfida akan dadduman tana ta hawaye sosai.

Acikin wann condition din har nurse din nan ta zagayo domin dubata ta sameta, akanta ta tsaya tana mamakin yadda ta cusa tunanin mijinta aranta tanamai kyabe baki.. agogon ta ta duba ganin karfe 6 na safiya ne kacal, daman ta kammala night duty ne zata tafi gida kafin yan safe su zo suma.

Tafi minti biyar tana kallon Adiaha batare da ta sani ba,gyaran muryan datayine ya dan dawo da ita hayyacinta,suna haɗe idanunsu waje guda Adiaha tay saurin goge hawayenta suka fara gaisawa..

Da fuskan tausayi nurse din ta zauna kusa da ita cikin mata fada akan yawan kukan datakeyi bayan likita yay mata gargadi akan ta dena daga hanklinta sabida kar hawan jini ya kamata

Adiaha tay shiru batace mata komi ba, cos all she care about is to have Ahmed back to her,bayan nan nurse tace mata ta share hawayenta inhar ta shirya tanada kudi a hannunta kawai tazo suje ynzun nan a nema mata mafita a magance mata matsalarta a inda tace mata zata kaita jiya, tace mata zasuje ne sudawo yanzun nan dan ba dadewa zasuyi ba.

Adiaha tana kokonto aranta amma hakanan nurse din nan ta cinye ta baki..tafara cusa mata ra'ayin ko hala dagsken yimata akeyi kmr yadda itama take zargin ana son rabata da mijinta.

Sosai ta lura kamr Adiaha irin matayen nan ne da suke cusa mutuwar son mijinsu aransu so kome za'a fada musu akansa bazata dauka ba.

Kowani maganan hankli nurse din ta kawo mata zakaga adiaha tana kkrin bashi kariya dan batasan aga aibunsa ko kadan .

Hakanan ta shirya tabi bayan nurse din a motarta suka dau hanya zuwa wani gida acikin anguwa.

Gidan na da mugun nisa dan tun ficewarsu 6.30 basuda isa gidan ba sai wajajen 8 saura na safiya.

A wani daki aka ajesu suna jiran layi tare da sauran mataye da suke neman temakon suma nn nurse din taje ta kawo ma Adiaha zazzfar ruwan tea mai madara da 2 slice of bread dan sabida kartana jin jiri jiri sosai.

Awajen Adiaha take jin differnnt stories na matsalolin mata da aka warware musu anan din.

Wasu shigen irin nata bbu zaman lpya tsakanin su da miji,wasu kuma masu mazaje masu neman mata ne, da cases din mother inlaws duk matayen dake zauna awajen sunata shewa cikin bada labarin yadda aikin matan yake tafiya dakyau wanda shiya karawa Adiaha wani irin karfin gwiwa acikin zuciyarta

After some minutes akazo aka kirata ciki ita da nurse albarkacin karamin cikin da akace musu tana dauke da dashi.

Suna shiga dakin Adiaha taga wata tsohuwar mace murdaddiya na zaune turus akan tabarman da akayishi da buhu da farantin kasa da kokon tsafi agabanta da wani irin tsohon kasko acan gefe yana ci da wani abu kamar hayaki.

Dandanin dariya matar batayi bare kuma ta amsa gaisuwarsu.

Suna zama nurse din tahau mata magana da murya kasa kasa, inda tace mata ta ciro wani abu ta zuba a kokon sabida matar taji karfin gwiwar duba mata lamarinta, nan da nan Adiaha ta zare dubu biyar daga purse dinta data riko,Allah yasaka duk tasaka an kawo matasu jiya da batasan ya zatayi ba..tana droping kudin acikin kwaryan tsohuwar
Matar ta dubesu nan danan ta kuma sake musu fuska atake ta fara amsa maganansu acikin fara'a.

Adiaha zatay bayani cikin tsareta matar tace mata tasan komi akanta.

Nan tafara tsakura mata yadda akayi ta rabu da iyayenta da duk tsinuwa da sukayi akanta,da walakncin datazo tasha a gidan miji a farkon zuwa,na ukun sai ta kawo mata maganan caccar bakinsu da kafaya, duk sama sama ta gaggaya mata ba dalla dalla ba.

Banda hadiyan yawu babu abinda Adiaha take jin matar tasan kusan komi akanta tsoron duk saiya kamata

Nan tay yan buge bugenta tay wasu camfe camfe snn ta dago da wani irin zaburarren kallo tana duban fuskr Adiaha.

Tayi kusan minti biyar tana mata wani irin kallon da baida fassara tanayi tana karkada kanta tare da kyabe bakinta.

Cikin Adiaha ya duri ruwa tafarajin kamr cikinta na tsurewa tsabar fargaban abunda zataji.

Ajiyar zuciya matar tay snn tace mata babu wani matsalar atsakaninta da mijinta, wai iyayen ta ne suke hanata zaman lapiya shiyasa Ahmed din yake behaving haka da ita.
Chapter 65 · 0% Book details