← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 157

Sashe 98

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa tay zata fice taje main house ganin goma saura ya dau hanyar yi kwata kwata batay taku yakai biyu ba taji wani irin iska mai karfi ya kwasheta ta tsaya cak cikin barin sanyi, tay tay bakinta ya budu tay ihu ko Addua amma ina dariya kawai takeji daga sama ana wasu kananan magana cikin amon dake fita a cikin dariyar..

Iya abunda ta tsinta acikin dariyar shine 14 days....iskan na daukewa cak tafadi kasa daga nan bata sake sanin inda take ba.

Past 12 Ahemd ya dawo ransa duk a dagule sai huci yake ga uban radadin daya kwaso na masifar da mum dinsa tay masa agaban yasrah dan baida tabbacin cewa bata jiyo su ba duk da yaga wai bacci takeyi..

Dolene ma yarinyar tana rainashi kuma duk su mummy ke neman jawo masa hakan, aransa yace he wont allow dat, inhar yasrah a karkashin sa zata zauna he wll find a way to discpline her by fire by force..

Da can har zai kwanta saiya tuna cewa baiga Adiaha acan main house ba.

Tsaki yaja snn ya diro daga kan gadonsa ya wuce direct dakinta ya bude kofarta, hangota yay asaman gadonta tana baccinta peacefully harta rungume pillow akan kirjinta..karasowa ciki yay ya zauna ata bakin gadon yanata kallonta, a mind dinsa yace she ave really changed kam, dan kyan nan datake dashi duk yana neman gushewa.

Dauke kansa yay akan fuskarta tare da mai dashi samn cikinta.

saman marartan ya shafa tare da yin kissing daidai wajen koda ma zaiji sanyi aransa cos dis baby is all he is proud of for now, snn harya zumudn cikin nan na makale acikin ransa, bargo yaja mata har saman kirjinta tare da rufe mata jikin nata gabaki daya snn ya kashe mata wuta ya koma room dinsa ya kwanta yanata tunanin babynsa, how will the baby look like, will it be a girl or a boy? He want his bby to look like him no mattr what tunanin daya dinga yi kenan yana murmushi da kyar baccin ma yazo ya daukesa...

Washe gari da asubahi Adiaha ta farka a mugun firgice tare da yin firo da pillown da bargon zuciyarta na tsananin bugawa da karfi.

Mamakin yadda ta kasance akan gadontan takeyi idanunta sun firfito waje da alaman firgita ganin wai harta saka nitynta da ta dade bata sakashi ba tana bacci,

but how comes? Who did all these for her..and why, dan iya abunda zata iya tunawa baifi girkin taliyar datakeyi a kitchen ba duk wani abinda ya wakana abayansa ta mance...
[7/10, 11:40 PM] SURAYYAHMS: A firgit ta sauka daga kan gadon duk dama a mind dinta tana Allah Allah karyau ma tayi zuban jini ahankli ta dinga takawa har ta isa bathrum ganin babu komi akasarta ta sauke ajiyar zuciya tay wanka tare da alwala ta taho ta gabatar da sallahn safiya.

Sama sama ta kimtsa kanta kafin nan ta fito cikin sauri sanye da doguwar hijabin datayi sallah tuna cewa hjy tace zata koma lagos din yau da sassafe. Sauri take Dan tasan duk yadda akayi by now Ahmed yana wajen and she don't want him to caution her na rashin zuwarta cikin family duba da jiya bazata ma iya tuna abunda ya faru da ita ba.

tana shiga cikin mansion kai tsaye ta wuce sashen hjya khadijatu lkcin ana neman bakwai saura na safiya tasan duk yadda akayi izuwa yanzu sun gama shiryawa tun daga bakin kofar dakin tafara jin sautin sheshhkar yasrah dake fitowa Ahankli cikin sauti mai dan saka kashe jiki...

Rage sautin takun datakeyi tay tafara tahowa a sadade tana karasowa daf bakin kofa ta tsaya jin maganganun da hajiya take gaya mata game da zaman duniya wanda sosai itama yaso ya taɓata dan haryau batasan meyasa taki sam taja yasrah ajikinta ba. Daga nan inda take tsaye tana jin yadda hjiya take dada nutsar da ita akan datay mata biyayya ta girmamata a matsayin ta na babba kuma matar yayanta, saidai duk da ruwan kishin datake hoarding acikin zuciyarta gameda yasrah hakan bai hanata jinjina ma irin kawaicin datakeyi akan lamarinta ba.

Haryau bata taɓa ji ko ganin inda yarinyar ta gaza wajen nitsuwa ba wanda tabbas nitsuwa da kamewartan shi yasaka haryau bata rainata ko ta fasa girmamata ba duk da kalar ire iren abunda takeyi mata na nuna ko in kula,da kuma kayan xubda mutunci da su anty Adizat suka dinga fada akanta kowani lkci suka samu dama.

Shiru tay bakin kofar kanta na kallon kasa wani fannina zucyarta na jin abubuwan da hjiya take faɗa wani kuma najimamin yadda take daukar zaman yasrahn agabanta bada zuciya daya ba.

Daga nan take ta kkrin fahimtar kalar borin da yasrah takeyi na cewa ita tafison ta koma wani waje da zama amma ba agabansu ba. Adiaha tay shiru, cos she felt sory nd embrassed da har hakan ya fara fita daga bakin yasrah,dan hakan tamkar wani hujjace akansu ita da mijinta dayake nuna cewa basu riketa da kyau kmr yadda hjiya take tsammani ba.

Ajiyar zuciyane mai nauyi ya kufce mata tana kkrin kncking kofar kenan sai ga Ahmed nan yanakan tahowa daga sashen mahaifinsa hannunsa rike da farin carbi...

Suna haɗe ido ta sauke nata kasa babu yabo babu fallasa tace "gud morning hubby"..kallo daya yay mata fuskan ba a sake sosai ba yace "hmm sai yanzu kika ga daman fitowa kenan, and ure doing what? Earves dropping...? Adiaha ta daga kanta da sauri cikin mamaki tace no no haba eaves drping kuma hubby naji kamr mumy tanata magana aciki ne bana son na katsesu yasaka na tsaya anan. A dan dakile Yace emmmm, amma ai kinajin me suke fada ta ciki toh meye bambacin hakan da shi laɓen danake fada?..

Tarasa me zatace Kanta akasa tace Sorry i don't mean dat..ni ba hakan nake niyya ba,Ahankli Yace kanki akeji snn ya wuce ya shiga ciki sanda ta sauke ajiyar zuciya snn tabiyo bayansa itama acikin sanyin jiki.

Hajiya khadijatu najin su ta yanke maganan datakey wa yasrah itama tay sauri ta goge nata hawayen snn ta miƙe tsaye da alaman zata basu waje.

Satar kallonta dukansu sukeyi kowa da irin kallon dayake mata harta iso daf da zata fice ta dan rusuna tace ina kwana yaa Ahmed..?mmki yaji dayaga ta gaishe sa, atake Wani irin girman kai yaji yazo masa har kai muryansa ciki ciki yace lafiya, hows ur nite? Batare da ta kalle sa ba tace Alhamdullh, daga nan dauke kai tay ta dubi Adiaha cikin sanyij murya tace ina kwana anty?a tausashe Adiaha ta amsa mata da lafiya dake tasan batama fiye kulata ba sai bata sake cewa komi ba tasakai ta fita ta barsu a dakin su biyu tare da hjiya.

Ahmed ne ya fara gaisheta acikin girmamawa kafin nan Adiaha ta daura daga nan. Her voice was really shaky duk ta hargitse sabida gani take kmr jiyan bata aikata daidai ba musmmn ma da bata kawo mata abincin dare na musammn ba.

Hajiya dake lura da ita batace komi ba dan daman neman chance takeyi da zata musu magana dukansu akan sabuwar rayuwa na zamowa parents da zasu tunkara musammn ma da yanzu bata tare dasu

cikin hikima ta fara musu nasiha mai ratsa jiki tare da tunasshe su akan da cewa susan sun girma..

Duk wani salo da ake bi wajen tunatar da namiji hakkin mace akansa saida tabi wajen tunashe da danta Ahmed sabida tana son yay ma Adiaha adalci arayuwarta, aranta haryau tanajin motsin sadaukarwan da yarinyar tayi arayuwanta domin ta zauna dashi and now dat she have no one face shi kusan dolene ya zamana ya jajirce Wajen bata kulawa na musammn dan karta rasa komi arayuwarta..

Koda hjya take nanata wa Ahmed tareda lissafa masa ababen daya kamata ya zamana yanayi as an incoming father duk hawaye saida ya taru acikin idanun Adiaha,ji take hjya nace wa hatta Abincin da zatana ci yana kulawa dashi sosai,barin ajega maganan duba lfyar jiki da kuma samar mata da kwanciyar hnkli, she wanted him to be gentle in words and actions with her at this time kodan sabida condition dinta data ciki tace masa ya kasance mai jimrewa da lauyin datakeyi na ciki tace masa yana taimaka mata wajen tsafta da yin wasu abubuwan agidan if he is able to do so har Allah yasaka tazo ta sauka lafiya haka ta dinga kafa masa misali da mahaifinsa alhaj bello jimada, duk dama they are not in good terms amma sosai ta yabe shi ata wann fannin, sounding proud of her man tace masa kusan ma atare sukayi laulayin cikinshi ita dashi, harma yafita shan wahala sumtimes baya bacci, and all his effort to help her and support her at difficult times is wat makes her journey to motherhood much more easiar toh bare kuma matarsa Adiaha da batada wani support din kowa nata saisu..

Kan Adiaha na can kasa tana jinta, She wish and wished dat Ahmad zaiji maganan mahaifiyar sa ya bata wann gatar Dan harga Allaah iya abunda take bukata daga garesa kenan wato tausayi da bada cikakken kulawa.

Baice komi ba har hjya khadijatu ta gama dashi ta koma kan Adiaha..

Ita din ma nasiha tay mata tsakani da Allah kamr yadda uwa zatay wa yar cikinta nasiha akan yadda ake kulawa dakai idan ana da ciki bayan ta bukace ta akan data dinga samun hutu da isashen abinci still tayi mata fada akan yadda ta dau hanyar sake jikinta domin karta bari ya lalace gabaki daya.

Duk dama kunya irinta bafulatana bazai barta ta fito gwari gwari ba amma tay iya bakin kkrinta wajen nuna mata Adiaha cewa tana da bukatar ta kara dagewa wajen kulawa da kanta a wann condition din dan acewarta idan mace tay wasa da haihuwar fari ahaka sauran haihuwar zasu ma zuwa mata da sabon salo snn komi nata zaina dada lalacewa ne musmmn ma dirin jikinta har yakaita izuwa gabar da bazata iya gyarashi ba. Duk jikin Adiaha yay sanyi dan acikin hikima hajya khadijatu ta kara tunashesu wasu darasi game da muhimmancin zaman tare a aure musmmn wajen taimakon jina da tausaya wa juna a lkcin bukata irin wann.
Chapter 98 · 0% Book details