← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 157

Sashe 48

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sassafe aka tashi a gidan anata shirin tafiyar brother kazim, kafayat tay kane kane itama wao saidai alaji bello ya amsata rabonta na kudi awajen brother kazim acewarta ai tasan dolene zai bawa hjya khadjitau wani abu itama dolene abata nata rabon.

Wann borin data dagowa
Alaji bello yasaka yau basu samu daman fitowa akan lokci ba..

Wajajen tara na safe yau kusan babu wanda ya fita wani waje face yaransu da aka kaisu makaranta, kowa ya hallara a sashen hajya khadijatu face Ahmed da haryanzu bai samu dawowa gidan ba.

Hijabi dogo hjy khadijatu ta saka cikin nitsuwa snn ta yi musu takaitaccen nasiha haryanxu bata nuna musu abinda yake cikin ranta ba.

Suna cikin maganan can sai ganan Ahmed ya shigo gidan shima yazo ya sameta bayan sun gaisa sukayi ma brother kazim addua snn suka rakosa har waje atare.

Hjya khadijatu tana can awaje tare da brother hamzat Ahmed yajasu yanamai nuna musu sabowar motarsa da yazo dashi. Dukansu suka hau masa murna snn ya koma ciki yabar su suna jiran fitowarsu daga sashen baban nasu.

Jim kadan Hjya Ta hada rai bata kallon kowa ta murtuka fuskanta sosai
Dan Basu wani jima ba sai gasu nan sun fito lkcin Ahmed na tare da Adiaha suna maganansu akasa kasa duk hanklin kafayat na kansu. Adiaha seems very happy kamr zata tashi sama sai murmushi takeyi hannunta sakale da nashi.

Kishi kamar zai kashe kafayat kirjinta sai kuna yake barinma taga yadda Adiahan ta makale shi sosai.

Saida kowa ya iso harabar gidan kafin nan Kowa hanklinsa ya koma kan dalleliyar motar da Ahmed ya shigo dashi
Lexusxv ce baka kirin ta wani kyalli daga ganinsa kasan sabowace dall.

Nan yay suprisng dinsu tare da fada musu cewa ya siya sabuwar mota snn dayan motarsa mai kyau din da bai cika hawa ba ya bawa matarsa Adiaha kyauta..

Adiaha ta fara murna har bata san da cewa ta rungumeshi agabansu ba dan batay tsammanin zai bata ba kawai nashin ya gaya mata, tafarajin kmr zatayi ihu awajen tsabar murna, brothers dinsa kuwa sai hyping dinsu sukeyi waje ya kaure da differnt types of emotions bakin kishi ya turnuke anty nurat tafara tari harsaida aka kawo mata ruwa tasha.

Anty adizat ta haɗa harda hawayen datakeyi na tafiyar mijinta ta zage tana fidda nata gulluton baqincikin daya tokare mata kirji ababu yadda suka iya hakanan suka jona jama'a sukayi ma Adiaha murnan samon babban motar dataci uwar tasu a tsada da kuma kyau duk dama ba sabuwa bace kal amma bata da maraba da sabo dan baifi sau akirga yay amfani da motar ba.

Masu baqin ciki sunayi masu nuna farincikinsu a fili duk sunayi..

Duk murnan da akeyi musu babu wanda ya lura da bacewar kafaya bat awajen...

Adua akayi gabaki daya as one happy family ko kallon juna iyayen nasu basuyi amma hakanan suka waske domin farin cikiin yaran nasu karya samu wata tangarda.

Rabuwarsu da brother kazim so emotional hku khdijatu ta share yar sassanyar hawayenta ahanlki daya rungumeta ajikinshi sosai tana mai tuna duk lokcin dayake karami in yana ciwo bayason tana rabuwa dashi, daya girma kuwa duk sanda ya samu wani abu mai kyau kona alheri arayuwansa saiyazo ya nuna mata.

Cikin aminci yay sallama da ahalinsa hjya khadijati ne ta fara komawa cikin gidan dan dama abunda take jirane kenan yafaru ta kama gabanta gobe itama.

Ahmd da brother hamzat da anty adizat ne suka rakashi har izuwa airpot alaji bello ya dinga waving dinsu har suka bace ma ganinsa sai nan kafin hankli ya dawo masa ya lura da cewa kafayat bata tare dashi.

A gurguje ya wuce cikin gidan shima dan yaje ya dubata dan yasan dai shigarta gidan bana lpya bane musmmn ma yadda ta matsu cewa sai a karba mata rabonta na kudi awajen brothr kazim dazu.

Ana watsewa awajen Anty nurat ta kwaso cikin sauri sauri hartana tuntube wajen zuwa sashen Adiaha aranta so take ta sha cikinta taji shin wani irin maganin mata take amfani dashi akan Ahmed haka daya bata hadadden motarsa a matrix jeep for that matter.....babu editing
[6/17, 9:31 PM] SURAYYAHMS: 38.

Isar Anty nurat kofar bangaren Adiaha kenan ta samu harta shige ciki ta kulle kofarta kirif cike da cizon yatsa ta tsaya a cike tanamai tsurawa kofar idanunta mai cike da wani irin feeling na tashin hankli ,tsabar hassada da saka wa kai damuwa jikinta har rawa yakeyi dakansa, tafi minti talatin tana buga kofar amma sai shiru ba a fito an bude mata ba, ranta ne yay mummunan dagulewa da sanin cewa Adiahan tana ciki tana jinta, sai can data gaji ta ja tsaki tabar wajen tana tafiya ahankli tanamai kallon motar da aka bawa Adiahan dan shine agaban bangarensun a parke kamar ba'a taba shigarsa ba..

Wani irin furzan iska tay bayan ta shaƙi tukukin baqin ciki dake kkrin cinye ranta akan wann cigaba da Adiaha ta sami a rayuwarta na samun babban motar dayafi na kowa kyau acikin matayen gida.

Tamkar wadda aka gaya mata sakon mutuwa haka take takawa izuwa sashenta duk ta cike kan kirjinta da maganganu masu tsananin zafi.

Aranta sai cewa take Lallai yarinyar nan makirace algunguma lamba daya, she is definately a green snake under green grass, wato duk gorin da muke mata tanaji taje ta saka shi ya siya mata mota...ohhh god. Komaa gwada mu takeyi a farko?
Faduwa gabanta ya dingayi data furta hakan aranta dan haryau basu san ya akayi ta samu hadaddun english wears shoes, bags, da abayas din datake sawa agidan ba bayan tace musu ahmed bai bata kudin lefenta ba tukuna.

Cikin wann lissafin akwakwalta tay shruging din kafadunta tanamai cewa Adiahar nan ma ba abar yarda bace dan kwana biyun nan gabaki daya lamarinta yafara kulle musu kai basu gane metake ciki ba sam.

Cud it be true dat kallon wawaye take musu? Ya fara kawo wnm tunanin aranta kenan then wani murya akanta yaja tsaki yanamai cewa hmmm nurat Abiodun kin fi karfinta Mtschewww Aikin banza inji dai ba sabo dal bace? Tace makanta "Am still untop nice gaba da ita duk dai tsiyarta bazata kamoni acct balance ba cos i run things in the market.

Haka tay ta maganganu a mind dinta tana bawa kanta dalilin cewa Adiaha is nothing harta karasa makaken falonta ta zauna akan cushion tareda rabza wani uban tagumi. Yau inama ace wata ƴa mace ta amma Adiaha? gaskiya Bazata iya kallon Adiaha tana dawowa daidai da level dinta a gidan ba, inhar hakan ya faru tayay za'a raba raini kenan?.. abun duniya duk yabi ya isheta shagonta zata fita amma duk saitaji komi ya fice mata aranta Allah Allah take su anty adizat su dawo daga airpot domin taji mata point of view din akan Adiaha.

Cikin lisafe lisafen ta harta fara tunanin ko zasu lallamota suji kalar maganin mata datake amfani dashi akan Ahmed koda suma zasu hau kan layi dansu kara canza motarsu su siya wanda yaci uban nata snn suyi mata dariya daga baya.

Adiaha tana room dinta tana waya da grand ma tsalle take tana murna harta kasa iya rufe bakinta tsabar zuba dan tunda ta dau wayar labarta mata lamarin motar kawai takeyi tana jin wani irin tsananin farinciki da murnan cewa Ahmed ya bata kyautar babban motarsa a DBX curvy jeep for that matter abunda ko a mafarkinta bata taba kawowa zata tuka irin wann babban motar ba saidai tagani awajen hadaddun matayen masu kudi.

Grandma din nata dakanta saida tasha matukar mamakin sauyawar Ahmed Akan jikarta Adiaha harta fara tunanin ko hala kuskuren fahimta tay masa tun farko. Hanklinta saiya fara dan kwanciya data ke jin positive vibes daga bakin jikarta Adiaha.

But still Adiaha seems way too much excited Abun sai ya daure mata kai dan gaba daya taga ta kasa nitsuwa, tamkar wanda duniya gabaki daya Ahmed ya damka mata haka take murna tanamai gwadashi kamr zata karar da dukkanin sanyayar kalaman yabo dana tsantsar soyayya akansa yau gabaki daya.

Saida suka kusa yanke wayar snn Grand ma hjy hajarat tafara mata nasiha tace mata...

"I am very happy and relief for u my grand doter, amma ki nitsu fa.
Apreaciate him, but Dont over worship a man just because he is durely paying up to his responsiblities ke matarsa ce, idan bai baki abun hannunsa ba mawa zai bayar dama?.. karki dauki hakan a matsayin wani privilige, its ur right amma karki nuna masa girman kai u shud thank him for saboda ba kowani namiji ne yake sanin hakkin matarsa akansa ba.

Mace tana gidan iyayenta namiji zaije ya daukota ya kawota inda babu kowa nata hakan ma kadai wani kalubale ne babba a rayuwar mata inda a wann gabar me mataye da yawa suke zamowa Ababen tausayi
Saboda rashin samun wann cikakken hakkinsu nasu na kulawa bayan rabasu da inuwar gidan iyayensu da akayi.

Adiaha tay shiru tana kan jinta batace mata uffan ba.

Tace "Su maza fa biyayya suke so ba rawan jiki ba, naga kamar duk abun yahau kanki kin susu ce kamr duniyan ya baki mai gabaki daya,..inaa gargadinki da ki kama kanki, snn komi zaki masa kiyi dan daidai ba wuce misali ba,randa kika nuna ma miji abun hannunsa ya dameki aranan ne zaki fara sanin me ake kira da iskanci da walakncin da namiji.

Adiaha tafara tura baki tanamai cije labbanta cilin jin gajiya da maganganun grand ma din nata dan duk maganan nan ba dadi suke mata aranta ba

Like how grand ma zata na fadan haka mtsww ita wann wa'azin bai mata wani ma'ana ba, memakon tace mata ta kara kaimi wajen tarairayar mijinta sai ta fara kawo mata zancen kama kai?ta yaya Ahmed zaisan tana mutuwar son sa inba tay worshiping dinsa ba. Ta ja tsaki aranta'..mtsww Dama wai laifi ne ka nuna farin cikin ka idan mijinka ya siya maka abinda bakayi zato ba.. tsaki takeja aranta sosai tanajin wani irin haushin grand ma kifi kifi tayi da idanun dan bama jin sauran zancen nata take yi ba dan gani take kamar ta tsufa batasan metake cewa ba.
Chapter 48 · 0% Book details