← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 157

Sashe 132

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin hanzari Aunty nafisa ta mike ta tareta ganin jiri ya kwaso ta tayo baya zata fadi,a rikice ta fada kanta kmr mai aljanu, sabon kuka ta fashe musu da shi tausayii ta basu da ta shiga girgiza ta ganin jikinta duk ya saki idonta lumshe yana hawaye.

sunanta hajy ta shiga kira cikin lallami tana cewa yasrah yasrah ki tashi kinji, babu wanda zai miki auren nan wasa sukeyi miki dama, ki tashi yanxu zanje in samu kannen baban naki da Adda ince suyi hakuri, kiyi hakuri ki tashi kinji auta na, babu mai sake saki kuka, ki tashi muje tare yasrah", yasrah kam ko motsi batayi sai dai har lkcn hawaye na tsiyaya daga idanunta.

bude kofan dakin akayi su ya sadik suka shigo jin hayaniyar da akeyi da ysrah, cirko cirko suka tsaya ganin kan hjy khadija a kife jikin yasrah dake birgima tana ta Kuka sosai dan duk sanda ta tuna wai Ahmed ne mijinta saitaji kamr ta rufe ido taga ta mutu, da kyar sadik ya iya yin karfin hali ya ja kafanshi ya karasa inda su suke, tsugunawa yayi dab da ita ya riko hannunta dayan hannun kuma yadaga hajiy dashi jikinta a muce, cikin sanyin murya yace "mumy control urself, wai duk akan maganan auren ne har yanzu yasrah bata hakura ba?

kasa bashi amsa tayi sai hawayen dake ta zuba daga idonta, juyawa yayi ya dubi sauran yan uwansa dake wajen da har lkcn sun kasa motsi suna nan inda suke sai tausayin yasrah da suma suka fara har yace ma farida je ki kira mummy tana babban falo, gyada kanta tay ya juya yaci gaba da murza hannun yasrah yana dan jijjigata ganin numfashinta ya dauke gabaki daya.

Ba'a fi minti biyar ba da fitan farida ba saiga hjy maimuna ta shigo dakin arikice tana tambayan yasrahn tana ina, ganinta kwance jikin hjy khadija kamr bata motsi yasa ta kasa magana itama, sosai jikinta yayi sanyi dan tasan duk yadda akayi kan maganan auren nan da taji ne ya dameta..

Bata sake cewa komai ba sai da ta sunkuya ta dauketa cak sannan tacewa sadik ya dauko key su wuce a tafi asibiti"

Jim kadan bada jimawa ba ya dawo, sadik din ne ya tuka su suna zuwa asibiti cikin gaggawa aka karbeta akayi emergency da ita wajen doctor aka fara dubata sabida minor nervous break down data samu atake.

Hanklin kowa saida ya tashi ganin Yasrah Bata farfado ba har saida yamma ya rufa liss.

Hakan ya jawo ba a taho da ita Abuja ayau din ba harsai washe gari.

Tun jiyan data farka take ta tunanin yadda zatay ta saka a tsinke wann auren
By fire by force, Duk rarrashi duk lallamin su na duniyan nan taki ji, itadai koda ma wani za'a kawo amma ba Ahmad ba.

Takaici sosai takeji aranta dataga babu wani wanda yake nunawa dagaske zai temaka mata a tsince auren saidai kawai ata bata hakuri ana ce mata qaddarar ta kenan.

She bacame really really angry and frustrated musammn da hajiya maimunatu datake mata matsayin uwa agareta..

Taki ma sam suyi magana da ita sai kuka kawai take mata sai bori taki taci abinci har karfin jikinta ya kare gabaki daya zazzabi ya rufeta.

Ahakan washe gari ranar liyafarsu aka taho da ita Abujan duk batajin dadin jikinta aka hau shiryata, bahaushe yace sarkin yawa yafi sarkin karfi dake bamai bin bayanta haka harsaida sukaci galaba akanta ta hkra akayi bidirin kyafaffen liyafa mai ji da lafiya nagani na faɗa wanda yazaga ko'ina, ya samu halattar dumbin mutane masu girma, inda akayi shagalin liyafar acikin wata sanyayyar salo mai cike da natsuwa da ban sha'awa matuka sabida matukar dacewar da sukayi da juna acikin weding dresses dinsu.

Shiga biyu aka musu bayan na liyafar.

Haka akazo aka mata kwaliyya ta fito da Red and golden yoruba asoke mai dan iskan kyau da tsada aka bazama wuyarta da hannunta expensive red colour beads bakaramin kyau yasrah tayi saidai aranta ji take kamar zata mutu alokcin.

Duk wani abun nishadi da akeyi harga Allah konamata gangan jikinta yakeyi tamkar wuta hatta Adiaha saida ta bata tsananin takaici ganin yadda take suporting auren mijinta 100% dan alika mata shi shiyasa ko magana ma bata yadda ya hadasu ba.

Ata fannin su fahad kuwa har dan zazzabin nan saida yay jin wai anma yasrah aure tunma kafin burinsa ya cika akanta, yau din tamkar wata ranace ta baqinciki arayuwarsa wanda bazai taɓa mancewa dashi arayuwarsan ba dan hanklinsa bai dawo jikinsa ba harsaida maryam ta dawo daga wajen bidirin biki take sanar dashi cewa auren dole ne akayi ma yasrah yasrah bata son auren.

friends dinsa atake suka fara zugashi akan cewa zai iya cimma burinsa ta hanyar amfani da hakan ma. Nan da nan suka fara shirya wani salo.

Bayan angama hidiman liyafa kowa ya watse haka nan akayi shiri na gagarumin family prayers ma amarya da ango.

Ita dashi suka shigo acikin wata kyafaffen matching tribal outfit na yoruba shiyasaka kalar blue stylish abgaba da hularsu dake karkace na yorubawa itama tay masifar kyau acikin nata cultural attire din aka mata rufi da mayafi yaloyalo.

Kowa ya hallara aka taso su atsakiya inda suka yi tsugune acikin salon nuna girmawa da biyayya wa manyan gida.

Adiaha was super astonished to see that duk family sun amshe yasrah wholeherterdy, badon komi ba saidan itama tana da jininsu na yarbawa, Su anty moju da anty ramoutu and co evryone was so happy with the whole wedding arrangement kowa yana mai alfahari da su anata gwada kyaun yasrah.

Fadin irin ababen darajawa da karramawa da akayi ma familyn yasrahn bazai iya girkuwa ba.

Koda aka fara hakan Adiaha sosai taji abun aranta, saidai batada yadda ta iya face ta kyale hawayenta daya makale ya zuba sabida saiyau ne take ganin asalin wauta da gazawar datayi a matsayinta na ƴa mace da bata bari itama an karba mata darajanta da martabanta agidan kamr yadda akayi ma yasrah ba.Tay cizon yatsa aboye ayaudin babu laifi, yaune ta fara asalin fahimtar wasu daga cikin irin maganganun da kakarta take gaya mata akan sauki da kuma gaggawar data nuna awajen saida ma Ahmed da famlynsa kimarta a araha.

Tana kallo anan hatta fuskr yasrah da za'a bude agani a fili su hjy basu yarda ba,har saida aka zuba kudi mai sunan kudi..

Deep down She felt so soryy for herself amma tasan wann duk ihune bayan hari musmmn da ayanzu takejin she cudnt even give ahemd the joy and happiness of having a peaceful family and a child, aranta saitake ganin kamar aurensa da yasran ma yafiye mata kwanciyar hankli,yanzu dai yadda zata danne kishinta ne kawai yake kan baffling inta aranta musammn dataga hanklin kowa ya koma kan yasran.

Ana gama addua Ahmed da abokansa suka fara jigilar maida baki gida wasu kuma airpot.

Shikansa saiyau yakeji aransa kamr yay aure sabida yadda abokansa da well wishers suke gwada auren nasa agari.

Kafayat has been calling and calling bai daga ba dan a social media taga komi gashi acan har anfara mata aiki ankaita can cikin wani tsohon gidan tsafi na temple a bayan duwatsu manyan guda bakwai ance bazata fito ba sainan da bayan kwana bakwai bayan sun kammala hada mata magani..she felt like dying tun awajen.

Dan bata girgiza a auren Adiaha kamr yadda ta girgiza da aurensa da yasrah ba sabida abun yazo matane a mugun bazata.

Da yamma Maryam taci kwaras tazo gidan biki itama tare da fahad suka tsaya daga bakin gate suna ta magana bisaga plan dinsu da suka shirya akan dauke yasrah.

lokacin yasrahn na kwance adakin hjy khadija ita kadai anmata kwalliya ta saka wata doguwar riga coffe brown colour na atamfa fuskarta a lullume tanata kuka ahankli.

Kowa yazo domin yay mata nasiha da magana da fada da masifa suke rabuwa har kowa yagaji aka kyaleta.

Adiaha ce data fahimce irin matsanancin tsanar da Yasrah tay ma auren ta debo abinci ta kawo mata har dakin danta rarrasheta. .

Haka yasrah ta bushe ido ta zazzageta ta gaggasa mata maganan banza itama..

Tace "Anty reema ban taba sanin baki kaunata ba saiyau, U alsi allow them to marry ur evil husband to me? Allah zai saka min akan abunda kuka min, nide bazan taba yafemiki ba kema.

Aikinsan bai dace dani ba,nide bazan aure namijii irinsa ba nide walhy na fi karfin nakasance matarsa amma dan tsabar mugunta za'a hada kai dake har alika min shi a matsayin miji nime zan muku dashi..wawa ma wanda baisan darajar matarsa ta gida ba?

Tay ta maganganu tace ma Adiaha kawai so take tazo musu dan haihuwa amma bawai dan sun damu da abunda takeji na tsanar Ahmed aranta ba.

Duk yadda Adiaha taso su fahimce juna haka yasrah taki ta dinga gasa mata bakaken magana tareda ce mata batason mijinta.

Jikin Adiaha a sanyaye tabar dakin ta koma sashenta tanata mamakin yadda yasrah ta mugun tsanar Ahmed aranta haka.

Bayan ficewar ta bada dadewa ba sai ga maryam din ta shigo

Lallashinta ta dingayi kamr dagaske,yasrah tana mai gaya mata damuwarta da zuciya daya dan sosai abun ya sosa mata ranta, can kafin nan ta ce mata zata taimake ta inhar dagaske take batason auren, ta zo su gudu subar kasar tare da Fahad, as her friends they will surely help her.

Convincing dinta tay da cewa taimakonta kawai zasuyi dan a warware auren akan lokaci ta cigaba da karatuntan datakeso anan.

She also told her dat fahad is more than ready to help her out as a friend inyaso suna guduwa hanklin kowa zai tashi sai aynke hukuncin raba auren kawai.

Haka yasrah ta amince bawai dan tay zurfin tunani kawai dai alokcin she is mentally unstable and tensed, so kawai take taga ta yaface auren nan karfi da yaji aranta.

Kayanta ta sauya ta saka wani wanda baza'a gane ta dashi ba, ta window ta fita waje, can suka hadu abakin gate da maryam harta shiga motar Ahmd suka bar anguwar luckky enough babu wanda yagansu.
Chapter 132 · 0% Book details