← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 157

Sashe 18

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banji yace just let it go, i knw u liked her, but She is gone now. Kasani tun lokacin da tayi deciding cewa zata aure dady a lokcin kafayat ta zamo strnger awajenka, bansan meyasa kake neman bayani abakinta bafa, she is not a friend the moment she decide to maryy ur father just forget about her. Idan ka share shegiya hakan zaifi mata zafi ita dakanta zata nemeka tafara maka bayani i trust ooo i knw u can do this damilare..just ignore the hell out of her.

Ahankli Ahmed ya lumshe idanunsa yay tsam yanamai assimilating din maganan banji acikin kwakwalrsa yana mai jerasu hade da basu fassara na daban.

Saida yagama duk wani calculations din da zaiyi kafin nan ya bude lumsashun idanunsan ahankli cikin kyabe baki yanami sakin wata miskillyar murmushi yace "understoood.
Shege Ashe kaima kanka na kawo wuta. Inaga abunda zan mata kenan.

Tafawa sukayi tare da fashewa da dariya suka dauko drinks dinsu suka sha, basu wani jima ba suka canja topic suka dawo hirar kwallo.

After a while banji yanata tsammanin cewa Ahmed zai tashi yace masa zai koma gidansu tunda dai yanzu yasan yana da amarya amma sai shiru baiga ya tashi ba snn baiji yay maganan komawa gida koda awaya ba.

Infact his phone was off tunda yazo gidan.

Har Wajajen 12 na dare suna kallon chineese movie lokacin banji harya gaji da jiransa ya mirgina yay bacci akan kujeran falonsa,sai can wajen karfe daya na dare snn ya kashe musu wuta shima ya kwanta anan din shima yay bacci hnklinsa kwance bai tashi farkawa ba sai can da Asubah da aka kira sallahn fajr.
[6/7, 8:43 PM] SURAYYAHMS: _Jimada house_

Da yamma lis lokacin duk yayun Ahmed sun wuce sashunansu da matansu Adiaha ce kawai a tsakiyar gidan hnklinta duk yanata bakin gate wai koda zataga dawowar nata mijin daga wajen aiki ta tarbeshi.

Tay ta lura da yadda sauran matan gidan suke bada cikakken kulawa da soyayya mai tsafta ga mazajensu da yadda yayun Ahmed din ke tarairyar matarsu sosai kamar sarauniyoyi.

Hakan yasaka tsuminta ya tashi tafara tunanin ko Ahmed will soon turn out to care for her this much.

Aganinta inhar haka yan gidansu suke da nuna kulawa ga matarsu to hala itama dolene akwai lokcin da zata zo ta more irin wnn salon soyayya da kulawar awajen mijinta dan sosai rayuwarsun yake bata sha'awa sosai.

Ayanzu tsakaninta da mijinta Ahmed is rough and distant amma bata cire rai akan cewa komi zai iya dawowa daidai atskaninsu anan gaba ba. She is not planning to give up on him dan gani take kmr tay sadaukarwa mai yawa akansa, she has come dis far bai dace ace ta juya makanta baya tun ayanzu ba, ko grand ma saida ta gaya mata cewa zaman aure yar hakuri ce saida hakurin ake cin riban zaman gidan aure. And she believ that hakurinta datakeyi dashi aynzu bazai taba tashi a banza ba.

hakanan tayita jiran dawowarshi a gidan hartakoma ciki ta mannu da jikin window kmr yar marainiya tana ta leken waje nanma harta gaji ta hakura taje tayi barci..

washe gari da sassafe ta farka sabida tsoron masifar sister zainab data kwana dashi acikin ranta tana dirowa akan gadonta ta shiga batrum ta dauro alwala nan tay sallah agurguje, tsabar sauri sallama kawai tay ta tashi bayan ta idar ta shiga bathrum ta watsa ruwa sharp sharp tazo ta saka abayanta na jiya snn ta fito main kitchen din sassafe kowa yana bacci itace kadai a waje ta fara dafa musu breakfast da wanda yaran su zasuje makaranta dashi.

Abincin da tay musu jiya a lunch da dinner taga suk sunci batare da wani complain ba dake tuwon semo kawai tay da miyan ganye da yaji kifi.

Yau kuma Spaghteii jollof tay da pper chicken sann tay tea mai zallan lipton da madara, ta zuba harda cokolate ma yara.

Around 7:15am na safen Adiaha har ta kammala breakfast dinta nayau.

Hakanan ta jerasu snn ta taho da tray har bakin kofar sashunansu kowa ta danna bell ta miƙa masa Abincinsa.

A sashen Anty adizat babban danta ne ya fito mai suna shehu yaron ya dan girma zaikai 16yrs yana kkrin shiga ss3 shi photocopyn babansa ne, har halinsu ma iri dayane dan tamkar yadda baban shi yake da hali mai kyau haka shima yake wajen sanin darajar mutane,
obafemi shine na biyunsu dan 14yrs shikuma dan shiru shirune baison magana, sai kuma Sulu dayake 11yrs ya kammala primary kenan zai fara jss 1 shikuma uwarsa ya biyo zak zak shiyasa sosai ta sakaltashi.

Yaran anty nurat kuwa duk mata ne sunason Adiaha sosai. Yau koda tazo sashensu kawo abinci da gudu sukazo suka tarbeta suna murna sunga sabuwar antynsu, sunan su madina da karima, Madina itace babba yar 13yrs sai karima 10 yrs.

Adiaha taji dadin yadda yaran suka tarbeta da murnansu duk dama zasuje schll amma saida sukazo kitchen din suka dan tayata hira suna sakata dariya sann suka ce mata abincinta yana musu dadi.

yau kwata kwata batayi gamo da zagi ko wani cin fuska ba dake harta kammala rabo bata ci karo da su anty adizat da nurat ba.

She was happy yau ranta bai baci sosai ba.

Hjy khadijatu ta farka yau tana zazzabi dan haka sister zainab bata wani kulata ba sai ma wani sabon haushin ta datake kanji aranta. Ko magana tay acikin ladabi sai ta hantare ta tabita da habaici mai zafi.

Sosai Adiaha ta fahimce cewa har yanzu sister zainab gani take kamar itace ta dawo musu silar komi dake faruwa tsakanin iyayensu.

Xafin zazzabin da hajy khadijtu takeyi yasaka duk ta sauke fushin hakan akanta.

Kowa acikin matan gidan yazo dubata amma Haka ita ta hakura na dole ta koma sashen ta tazauna itakadai sabida yadda sister zainab take ambatar ta da badluck bad energy kememe tay ta hanata zama a kusa da hjya khadijatu.

Ata bangarensu Ahmed kuwa tun da safen da suka farka suka fara musu da abokinshi Banji akan Adiaha amma baice masa komi kwakkwara gameda hakan ba ya shareshi.

Banji yanata lura da shi yaga ma Ko abinci baici ba,wanka kawai yay ya bude wadrob din banjin ya dauko wani casual wear mai kyau ya saka ajikinshi ya kammala shirin sa na zuwa office tsaf.

Abubuwa sunata damun zucyar Banji daketa kallonshi can dayaji kamr bazai iyayin shuru ba sai yace Ahmed, Bangane ba yau bazaka leka gidanka bane? Batare da kulawa sosai ba Yace nop office zanje...ina da tarin aiki agabana mezanje nayi agida kuma?...

Banji yace Damilare kana tunawa da cewa kayi aure fa kuma aure ba abun wasa bane abunda kake ma yarinyar nan fa is not fair. Kasan she wll wait for u toh ko kiranta kayi mana.

A gajiye da jin maganan Yace Banji naji aizan kirata, bari naje office din tukuna inna zauna i wll call her. Ahaka ya share maganan har suka fita kowa yaje wajen aikinsa..

Koda ya isa office dinshi aikin dake gabansa kawai ya kama bai nemetan ba.

Haka kawai yakejin kmr Adiaha ta sane masa akansa, aransa inbanda danasanin aurenta babu abunda yakeyi, dan yasan dabai aureta ba da hala familynsa bazai wargaje kamr na yanzu ba,zuciyar imaninsa ne kadai bazai barshi ya fito fili yagaya mata cewa baya sonta ba duba da wahala da kuma yawan sadaukarwan datayi domin ta aureshi.

Yarasa ya zaiyi ya dena jin haushinta aransa no matter how much he try saiyaji itadin ce kawai take bashi takaici.

Yasan ba duka bane laifinta amma itace babban silar dayasaka mahaifyarsa take cikin kunci da damuwa sai yaji duk bazai iya bata wani hakkin aure ba, aransa haushinta yakeji dan bazai iya farantawa wance tay sanadiyar faruwar kunci da damuwa acikin zuciyar mahaifyarsa ba.

Acikin tsohuwar family house din bello jimada kuwa bazaka taba yin tsammanin cewa da akwai mutum aciki ba

Wajen yay shiru sosai dan bayan ficewar kafayat Alhaj bello ne kawai aka bari acikin gidan daga shi sai dan guntun tunaninsa akan familynsa.

Yay kallo yayi baccin duk abincin dake cikin gidan ya cinye anma baiji hanklinsa ya kwanta ba bare kuma ya samu nitsuwa, duk ya rasa abunda yake damunshi aransa ga danbanzan kewar matarsa khadijatu dayake tafasashi taciki.

Yayita tsammanin wani daga cikin yayansa zai zago yazo ya bashi hkri ya lallasheshi musmmn ma babban dansa kazim dayake sunfi shakuwa amma sai shiru ko kiransa awaya babu wanda yay...

Gashi dama Sune suke daukar duk wani nauyin financial needs dinsa dik sai yaji hanklinsa ya mugun tashi dan idan sukace shine zai nemo kudi yay rayuwarsa shikadai shikansa yasan bazaiyi lasting ba sabida jikinshi yafarayin nauyi sosai.

Duk fushi da baqinciki ya cika masa zucya har Tambayar kansa yakeyi shin laifine dan ya kara Aure? A Da can dai yanata daukar khadijatu a matsayin wata mutuniyar kirki ce to gashi yau tazo ta rabashi da yayansa duka he is now left alone nd rejected.

Tunaninsa duk ya rikice akan hjy khadijatu,Abun sosai yafara damun zuciyarsa, ta yaya za'ayi ace yaransa kaf sun zabe khadijatu sun zubardashi batare da jin tausayinsa ba,was he really a bad father to them?bayan yasan ayau inya saki khadijatu alakarta da su ya kare kenan har abada Amma shikuma fa jininshi ne ajikinsu babu yadda suka iya dashi.

Tunda ya zauna a falonsa babu abunda yake tafarfasa masa ransa kamr kishin yadda khadijatu ta kwace masa matsayinsa awajen yayansa da kuma bakin cikin yayansa da suka gujeshi suke tare da ita.

Tsabar damuwa yauko maganin hawan jininshi baisha ba, Gashi ya cinye komi na abinci dake gidan yunwa na cin jikinshi bana wasa ba.

Sai can yay deciding ya kira sistersa ramatou

Tana daukar wayan suka gaisa babu bata lokaci yace "temi im soo hungry i need food babu wanda zai bani abinci U need to bring food for me yanzu yanzu.

Da mamaki a muryanta tace" brother bello meya faru kake jin yunwa haka ita kafayat din fa?i

Tsaki mai tsayi yaja tare da balbaleta da masifa wanda yasaka taji duk ta rude tana katse wayar tay gudu taje ta same anty mojushola .

Anty moju akwai matsala
Chapter 18 · 0% Book details