← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 157

Sashe 62

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake kofar yay a mugun razane dan shidaukawa ma yay ko mutuwa tayi

Jikinshi na rawa ya shigo dakin ya tattabata jin suma tay yasakashi sauke ajiyan zuciya..

Lambobin matayen gidan ya kira har ya gaji babu wacce ta dauka acikinsu, ga kafayat bata nan brother hamzat ma ya tafi porthocourt wajen business yau da safe.

A rikice ya fito izuwa sashen anty adizat ya dinga buga mata kofa har sanda ta bude.

Da masifa ta tareshi akan damunta dayakeyi

Bayan ta gama masife shi nan Yace mata ga fa halin da ya tarda Adiaha aciki tana nemn taimako

Kallon sama da kasa tay masa snn tace masa yaje yafadawa nurat tana zuwa snn taja kunnenshi akan karya sake kirar wayarta bare kuma ya buga mata kofa.

Hkri ya bata snn ya wuce sashen anty nurat itama the same thing yasha masifa bana wasa ba.
Koda ya gaya mata halin da Adiaha take ciki
Ita kam Bata wani boye masa ba tace bazata zo ba dan ba zamanta takeyi agidan ba. Ai tana da mota sai motar tata yay figa ya kaita asibiti tunda mijinta baya gida.

Nan ma warning tay masa akan karya kara damunta snn ta koreshi

Yarasa abunda zaiyi haka nan yazo ya tattareta gata ba kadan ba dake tana da jiki, da kyar ya fito da ita waje snn ya dauki key na motar ta akan table ya tuƙata ya kaita asibiti aka bata gado.

Nan da nan aka saka mata ruwa snn aka fara kkrin stabilizing blood pressure dinta sabida condition dinta na mai dauke da juna biyu..

Abiodun ne ya tsaya mata trout the nite sai can da Asubahi data farka snn suka gaisa yace mata zai koma bakin aikinsa kar wani abu yaje faru agidan baisani ba.

Godiya tay masa jikinta babu dandanin karfi ga azaban yunwa datakeji kamar zataci babu..

Wann halin data shiga cikin ne yasaka ta ta dinga tunanin rayuwarta banda hawaye masu ban tausayi babu abunda takeyi ita kadai...

Duk ta rasa wani irin jarabbiyar so takeyiwa Ahmed haka dahar son yake kin barinta tayi tunani mekyau akan rayuwarta? She want to be mad and upset with him amma duk sai taji ta kasa,.

Just Now dat she is awake bata tunanin kowa sai shi, batason taga fuskan kowa a kusa da ita yanzu face shi..

Despite what he did to her shi kawai zuciyrta yake ambata,idanuwanta kuma suke matukar muradin ganinsa adede wann lokcin..why havent he come? Take tambayar kanta rinannun idanuwanta ta zubasu sunamai kallon ta bakin kofa.

Fargaba takeji aranta wai Kodai harynzu bai huce bane dahar zai bari mai gadi ya kawota asibiti snn ya kwana yana kulawa da ita.

She was feeling really weak and remorseful and confused about ko tay fushi dashi ne ko kartayi?

Aranta tace Maybe she was wrong to shout at him dat way..

Maybe is a her fault data bari kanwarta ta zageshi bata kwabeta ba..

Kanta dake mata wani irin ciwo mai tsanani ta dafe tare da fashewa da wani irin kuka danji take kamar inta rasa Ahmed dinta hauka kawai zatayi..

..dan dana sanin haduwarta da Urua takeyi aranta kmar me,cos dukan wayann abubuwan da suka faru da ita jiya da bazasu faru ba..inta rasa Ahmed dinta a ina kenan zata saka ranta.."

kuka take hartana jan shesshka sai can kafin nan wata nurse tazo dubata ta same ta ahaka ta dinga lalllashinta dake yar garinsune har sun dan gane juna.

Bata tsaya jin damuwarta ba amma sosai ta lallameta tace mata tana bukatar cin abinci snn likita yana son ganawa da ita bayan haka.

Godiya Adiaha tay mata Snn ta kira lambar Mai gadinsun ta landline na gidansu ta gaya masa ababen datake bukata tace ya kawo mata snn ya gayawa father inlaw inta cewa anbata gado a asibiti.

Baiyi kasa a gwuwa ba kuwa yaje ya fara aikata dukkan abunda ta faɗa masa. Alaji bello da nauyin jikinshi haka ya fito yana neman su anty Adizat sai samu yay wai duk sunje aiki.

Masifa ya dingayi a tsakar gidan yana zage zage musmmn ma da Biodun yace masa ai tun jiyan ma ya sanar dasu halin da ake ciki.

Masu aikinsu suna zuwa yasaka akayi ma Adiaha lafiyayyen ppr soup na kaza, aka dafa mata abinci aka hado mata da komi da komi na tea da duk abubuwan datake bukata suka taho asibitin tare dashi..

Tun kwanciyarta anan hawaye take zubarwa tana kirar layin Ahmed amma haryanzu switched off ake gaya mata.

Dagata bangarensa kuwa tun isarsa lagos jiya da daddare yake nanike da mahaifyarsa fuskarsa normal tamkar wani abu bai faru a gida ba dan inyana tare da mum dinsa baiyason yana ganinta tana cikin wani yanayin damuwa ko tashin hankli.

A victoria island suke zama dan haka har Daki na musammn yake dashi a hadadden gidan nata

Da safen daya farka bao fito waje da wuri ba sabida gajiyan da jiya ya kwaso atattre dashi, sai wajajen 10.30am sann ya shirya kansa cikin wasu casuals ya taho wajenta ya gaishe ta suka zauna suka karya atare nan take ce masa baki biyu yau zasuyi expecting shiyasa takeson ya kasance atare da ita dan ya tayata yin wasu abubuwa na sabuwar office dinta ita zataji d shirye shiryen tarban baki.

Tace mishi duka yayan Adda maimunatu su biyun ne zasu taho nigeira yau, wato babban yarta Nafisa da kuma dan autan ta sadik.

Nafisan duk ta girme su duka dan zatay kusan sa'a da brother hamzat tana da yarta kwalli daya wanda ake kira da suna farida ..a Can kasar U.K take da aure.

Sadik kuma zaizo ne daga turkey, Adda maimuna da yasrah kuma zasu taho daga baya.

Tun zamansu anan hira kawai suke yanata bata dariya baimasan me duniya take ciki a acan Abuja ba.

Duk wani abinci da za'a shirya na tarbansu hajya ta kayayyada wa masu mata aiki.

Sai can da suka samu nitsuwa snn ta kira brother hamzat dan taji ya meeting dinsa na jiyan ya kare dan ya kirata jiya da daddare sunsha hira.

Shigar kirarta wayarsa ne yay daidai da lokcin da alhaj bello yake ta kkrin neman layinsa awaya don ya sanar da shi condition din da yazo ya tarda Adiaha aciki snn ya gaya masa abunda matayensu sukayi wanda sam bai masa dadi aransa ba.

Busy ya dingaji da alaman yana waya ata daya bangaren. Yaja tsaki ya kira brother kazim yana daukawa yafara masifeshi.

Sai cewa yake kazim Call ur brothers now now now, kace ma damilare matarsa tana asibiti ya kirani yanzu, what kind of reclessness is dis?..

Hanklin bro kazim ya tashi yace" meyasa sameta"..tsabar masifa da kyar ma yay masa bayani aka hadasu awayr suka gaisa shima yadan kwantar mata da hankli yace mata karta damu yanzu zai nemo mata mijinta haryasaka taji dan dama dama.

Bayan ya katse wayar shima nan ya shiga neman layukan Ahmed din saiji yake ana ce masa switched off.

Alaji bello kuwa tinda yazo yaga yanayin jikin Adiaha sai yaji duk ta bashi tausayi sabida aman datakeyi yasa bata da karfin jiki tana abu sum sum kamr ruwa ya kwasota ga uban tunanin Ahmed data cusawa ranta bana wasa ba.

Tunda ya zauna a dakin mita kawai yakeyi yana dada kirar layin Ahmed

"This boy is soo careless
Ina zaije yabar matarsa in dis condition wazai kula mashi da ita..?mtsww...sai ya dube Adiahan da fuskar tausayi sosai, cikin lallabata yace sorry my dear u will be fine, eat ur food okay?...im here for u my dear, get better soon _e pele_ . Haka ya dinga lallashinta tamkr shiya haifeta harta samu ta saka wani abu mai nauyi acikinta tadan fara jin dama dama.

"Duk abunda kike son ci just tell me yanzu zansaka akawo miki kinji? Gyada masa kai tay cikin ladabi da sanyin murya tace yes daddy" after sum minutes sai ya kalleta da fuskan damuwa sosai yace toh menene zaki ci Talk to me my doter i dont like the way ure looking. Acikin damuwa yake mata maganan sosai.

Intace ta koshi sai yay ta mata masifa yana ce mata bazata warke akan lkci ba inbataci abinci ba a Irin salon dai stratergy na iyayen nan ahaka harya ja ra'ayinta ta gaya masa cewa tana son taci tuwon pouded yam da stew da dried fish.

Hakanan yasaka biodun ya aika gida akaje aka fara shirya matashi acikin gaggawa.

Sai lallaminta yake yana kwantar mata da hankli dan sosai yakejin tausayin Adiaha har acikin ransa tun lkcin dayaji cewa ta rabu da kowa nata akan dansa.

Later later likita ya kirata zuwa office dinsa father inlw din nata ne ya biyota yana tsaye daga bakin kofar yanajin su ta ciki..

Nan likita yay mata bayani akan cewa tana dauke da juna biyu na wata daya da kwana shida, snn yay mata faɗa sosai akan tana kwantar da hanklinta sabida akwai barazanar hawan jini agareta wanda acewarsa zai iya zubar mata da cikin snn ta rage yawace yawace ta samu isashen hutu ta dena aikin gida sosai har yay suggesting mata cewa ta samu mai tayata aiki for now.

Duk alaji bello yanajin abunda likita yakecewa jikinshi har rawa yake tsabar murna ya kasa zama sai yaji murnan samun jikan ya lullubesa sosai dan rabonsa dayaji kanshi acikin farinciki irin hakan har ya mance.

Tana fitowa daga wajen likitan ya tarbeta da murna da fara'a, duk damuwarta sai da ya kawar mata gabaki daya dankuwa bakaramin zumudi alaji bello ya shiga nuna mata ba, tasha addu'oi kamar me, hakanan ya dinga showering dinta da kalamai masu tsananin saka kwanciyar hankli da sakata jin dadi. He stated treating her like a queen baison wani abu ya dameta. Komi tace tana so sai taga yasaka ana mata shi da barin jiki.

Har ma'aikatan asibitin suna mata murna suna ce mata she is soo lucky to have a father like him dan kowa anan ya dauka mahaifinta ne na asali..

Hawaye kawai ta dingayi aboye tanayi tana murmushi tsabar farincikin daya ke sakata aciki dan har waka ya rera mata yasata dariya sosai hartana shidewa.
Chapter 62 · 0% Book details