← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 157

Sashe 8

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Masifan dake ciccin ta arai ta fara amayarwa Tace kabani mamaki bello..butulu..in banda kaskanci da walaknci da neman zubda mutunci sai karasa yar da zaka auro ka kawo wa yayanka sai budurwan dan uwansu?

Kaji kunya wallh nayi nadamar hada hanya da gidanka, Allah ya isa wa khadija sam baka dace da ita ba, butulu, ka saurareni, dan kotu shine zai rabani dakai.

Tana fadin hakan ta juya tabar wajen ta koma ta jikin mota inda hajy kahdijatu take banda kuka babu abunda takeyi aciki dan batason ganin hayaniyarsun nan ko kadan.

Alhaj bello duk saiya rude aransa baisan me zai fara gayawa hjy khadijatu ba anan kuma Dake kafayat ta birkice masa saidai ya je ya karbo mata uwarta a hnnun polisawa Nan da nan yaji kanshi ya dau zafi

Fuskarsa a sigar lallami Ya kalli babban dansa kazim, yafara cewa kazim nine na haifeka fa amma kana kallo anmin irin wann abun har gidana? I knw u have contacts, why wont u call them and ask them to release kafaya mother for god sake.

Akan hakan dayace wani zazzafar argument ya kaure tsakaninsa da brother kazim din sabida ce masa dayayi Bazai kira kowa ba,.

Yace "Baba ina tausayinka yake lokcin da suke ci wa damilare mutunci har suka kaishi police? A tunaninka zan zubar da mutuncin dan uwana akan wasu banzan yen mata ne?
Ni ai ba kai bane ina da darajata snn bazan taba kaskantar da family akan kowa ba.

Maganan sosai yy ma alhaj bello zafi har yana diri.

Sister zainab kuwa ta dinga ihu tana zagin kafayat din kamar zata kasheta tana cemata baqar ashana ƙona gari, tace kafayat kinga irin bakin jiniinki ko? Ure a mistress of doom and sadness, duk inda kika shiga sai kinci amana sann sai anyi bakinciki akanki, ure a bad omen, tacigaba da cursing dinta.

Agefe kuma brother hamzat ne yakeyi da su anty mojushola da anty ramoutou.

Su anty adizat kuwa tuni suka ja gefe wajen hajy khadijatu suka tsaya daga can suke kallon draman

Zagin da brother hamzat yay musu akan bikin nan awasa wasa saida yay musu mugun zafi fiye da komi sabida shi asalin gaskiyar ya fito ya gaya musu na cewa selfish interest dinsu ne yake kkrin tarwatsu musu zaman lpya da kwncyar hankli acikin familynsu

_Yana hawaye yana cewa Shame on u for allowing this to our family_

_Anty ramotu, aunty mojushola, itiju lori rẹ fun gbigba eyi si ẹbi wa_

Ya rufe ido kamr baisan su ba ya zagesu tsaf yace musu dattijan banza, abun sosai yay musu zafi sabida har hawaye yakeyi dayake gaggaya musu bakar maganan yana tir da su yace sune suka haddasa musu faruwar komi.

Da kyar da fitina Alhaj bello yay bori irinta maza snn ya lafar da kurar yacewa kowa yay masa shiru baison jin surutun waninsu a tsakar gidan.

Kowa ya hakra yyi shiru harda manya manyan gidan amma haka Kafayat ta bushe idonta ta cigaba da zage zage kmr mahaukaciyar asali.

Rashin yin shirun nata yasaka sister zainab itama taki tay shiru tace
Kafayat baki ga komi ba wallh hauka zaki yi agidan nan since ure Witch, ode, so This is revenge for u right? _Kafayat, eyi jẹ igbẹsan fun ọ ni ẹtọ?_

Kafayat ta buga kirjinta cikin masifa da hargagi tace sister zainab nafi karfin na baki amsar wnn saidan nayi da ubanki and yes i am ur step mum ki mutu..

Tun bata karasa ba brother kazim ya daka mata wata tsawa saida ta razana snn yace shut up u little brat.

Baya baya taja tanamai hararsa tace ehnn ehnn brother kazim or whaat eva _o jẹ haram tabi o jẹ ilufin?_ marryny ur father izit haram or a sin so why are u even shutting me up?

Duk surutun na da ake Ahmed bai saka baki ba sai adede wnn gaban daya dago jajayen idanunshi ya dube ta cikin ido, snn yace kafayat Dont u dare talk back at my brother, ki bala'in kama kanki anan wajen kona tattakaki yaya na ba sa'arki bane.

Nan ta matso kusa irin bari ta kular dashi din nan tace yayanka ne amma ba yayana ba and,as a matter of fact im equal to ur mother now oo. _"we kii ṣe awọn tọkọtaya nibi"_ "we are not mate"

Kafin nan ta kammala harda kalman ta rufe baki Ahmed ya harzuka ya watsa mata wani irin gigiyacciyar marin da yakaita har kasa rigijib ya sake saka kafarsa ya kwasheta yay ball da ita can gefe harsaida ta tsorata tay suman bazata......
[6/3, 11:59 PM] SURAYYAHMS: Yanayin yadda Ahmed yay ball da ita a zuciye tayi tumbul ta fadi kasa rigijib tayi suman kai tsaye yasaka dukansu saida suka mugun razana dan kowa ya dauka ko mutuwa kafayat din tayi..

A cikin shock duka suka tsaya suna kallonsa da bakinsu a bude..

Brother kazim ne yay saurin janshi gefensa sabida yadda jikinshi yake kyarma da tsananin fushi. Still aransa ji yake kamar ya kara tattaka kafayat din ta mutu dan haryanzu bawai hucewa yay ba.

matayen kaf sun tsaya a tsandare tareda dafe Kirjinsu cikin razana da mamakinsa kowa na cewa."Innalillahi wa inna ilaihi raijiun,.wnn fa bugu daya kenan ya gigita idan yafi haka kuma ya kenan?

kusan a rude Anty ramatou take zagaye tanacewa haaahhhhhh Damilare, Damiiii,what have u done now? Kasan kana da karfi haka kamar doki zakana dukan mace? Did u want to kill her or what? _Dami, oya werey? matar ubanka ka tattaka haka, Are u sure ure not crazy_

Fuskarsa a mugun daure Ko amsata baiyi ba...

Ana cikin tashin hanklin nan anata kkrin tattaba pulse din kafayat Basu hankara ba kawai sai sukaji saukar ruwan sanyi shaaaaa akansu tun daga kan kafayat din harsu anty ramaouto dake kanta sister zainab ta jikasu da ruwa shataf..

wani irin Ihu suka saka mata tashin hankli akan tashin hankli kowa ta mike tsaye a sandare ruwa na zuba ajikinsu tsurrrr, amugun gigice kafayat dinma ta miƙe tana ihun firgita sai hammm ta sake yankar jiki ta kara sumewa tsabar tsorata da masifarsu datayi.

Zafin rai zainab din take dashi dan yadda kasan shedan haka zuciyarta yake inya dafe har basa son zuwa kusa da ita idan ranta na bace..

A koda yaushe inta tuna cewa kafayat bata da kamun kai kuma tana da dan iskan zazzagagen baki marar rike sirri sai ta karajin zuciyarta yana tafarfasa. Tasan sun shiga uku, dan yanzu kam sai yadda Allah yay kawai da duk wani sirin familynsu dazata je ta bazashi abakin mutanen waje.

Tana da irin bala'i da darun nan ne yarbawa.
Tana diri ko ina ajikinta na binta yana dirin shima

a wargaje taje ta kara debo ruwan ana riketa amma haka taki sam sanda ta kara kwarawa akan kafayat din, kafayat ta ja wani numfashi kamr zata shide ta bude ido tana kallon sister zainab bibbiyu cikin layi.

Faduwar anty mojushola akasa tana birgima da sunan Ahmed dana sister zainab shi yasaka alhj bello ya kasa yin motsi sabida rirrikota da yay ajikinshi. Yana sane da cewa Acikin yayansa kaf babu wanda yakai Zainab da Ahmed taurin kai,rashin tsoro da tsinannen rashin ji.

Sister zainab tace ke kafayat dan ubanki baki ga komi ba, u must wake up to dis reality ooo,ba ubana kika aura ba? Aikeda bacci agidan nan har abada this is just a welcome to hell party to you kafayat, ure very much welcome, zaki san cewa hauka na yafi naki, "wallh ina dede dake...ta wurga mata bucket din ajikinta da mugun karfi ya bugata snn ta kama hanyarta tay waje da gudu tanata zage zage

gidanta ta nufa cikin sauri tunma kafin babansu yace zai capkota.

Daga can gefe kuwa Sosai Hajiy maimunatu ta ririirike hannun hjy khadijatu datake kkrin saukowa acikin tashin hankli tana cewa babu inda zakije khadija kibarshi ya karata da yaransa sukadai ma sun isheshi.

Ayanayin damuwa Tace Adda kina kallon Ahmed ya mari matar ubansa ki sakeni Wann ba tarbiyr dana bashi bane..akan me zai mareta? Yanzu akanta sai ya rabu da ubansa kenan? Wann ma ai wani salon cutarwan ne, ta rabani da mijina tanason ta raba mijina da danshi Ahmed kenan?

Hjy maimunatu tace
"Toh saime? Kedai Kizauna anan kawai bana son wata maganan banza khadijatu, zuwa zakiyi ki rama mata marin kome?cikin kyabe baki tace hmmmm Ai bello baiga komi bama tukuna. Yaran nan bawai akanki kadai ke suke fada da shi ba,sunayi ne wakansu suma.

Habawa khadja, wann ai wasu yayiwa abun kunyar, ya tozartasu, kiduba fa cikin yaransa nan duk babu yaro karami acikinsu, kazim is in his mid 40s,Ahmed dake last born dinsa ma is 32 meyake nufi da zai kawo musu irin wann kalar dabbancin agida? Inama ace yar mutunci ya auro yar masu arziki da ayadda suke da ilimi da hanklin nan wallh bazasu hanashi zaman aurensa ba.

Amma ace wann yar iskan yarinya, kowafa ya san meyakawota gidan nan naku,dolene auren nan yay musu zafi. Sun san Bason ubansu take ba, and drama irinta daukar fansa datake son bugawa acikinsu will not be good for them,and she is still in love with Ahmed,aynzu da suka hade kansu waje guda sunata kkrin suga sun daga familynsu yay kyau yay daraja a idon mutane wallh bazasu kyaleta ba.

Gaskiya bello ya cuce su daya Auro musu wann tababbiyae yarinyar dan tabbas zata iya zame musu wata tsaiko ga cigabansu anan gaba..

Hajiy khadija tay shiru cikin tagumi,tanaji tana gani Hakanan yar uwarta ta hanata fitowa wajen firr ta dinga mata surutu acikin motar..

Ata fannin kafayat kuwa ko motsi batayi dan Atake su anty ramotun suka taru akanta suna famr tattabata duk su anty adizat suma suka iso ana mata fifita koda zata farfado. Gefe sukayi da ita can nesa da inda ake rikicin suka jinginta da bango koda zata samu nitsuwar ta dawo hayyacinta acikin gaggawa.

Banda bari babu abunda alhaj bello yakeyi dan baitaba ganin rikici da tashin hankli irinna yau a tsakanin yayansa ba.

Ransa a hargitse ya taho fuuuu zai shakure wuyar Ahmed din har yana huci brother hamzat ne ya shige tsakaninsu.

Tsawa ya daka masa yy kamr baiji shi ba.
Chapter 8 · 0% Book details