← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 157

Sashe 111

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna kan ci Adiaha tafara engaging yasra acikin hira,she was telling her about her wish
Na dazu Tana cewa tay Adduan Allah yasaka ta haihu lafiya da kuma yasrah ta cigaba da zamowa topper a class dinsu har agama.

yasrah tay murmushi mai fadi tace nagode anty reema Allah ya amshi wish din nan naki dukan su sukayi murmushi

..shirune ya dan ratsa wajen snn Adiaha tace "so what about you? Wht did u wish for urself..
Uhmmmm lemme gues to be a good lawyer right?

Dariya yasrah tay ayayin da take aje spoon din har sanda ta nitsu snn ta kalle Adiaha tace yes i wabt to be a good lawyer amma my wish is not about me..

Adiaha tace really?
Then who,ohh is it abt dat handsome guy..?

Murmushi yasrah tay tace cmon stop it anty
He is just a friend nothing else.

Adiaha tay smirking tana duba kofa dan kar ahmed ya jiyosu, murya kasa kasa tace Okay tell me wasnt ur wish about him Ai inma bakison gayamin ne zan ganoki am a woman i knw all dis yeye tricks..

Yasrah tafara dariya sosai wanda shi ya jawo hanklinsa ya fito daidai bakin kofarsa yanata lekensu daga nan he doenst even knw when suka fara shiri har haka dan baisan duk abunda ya faru da Adiaha lokcin da baya kulata ba last few month datay bari.

sauke kanta kasa ahankli tay snn ta dago tana kallon Adiahar snn tace its not abt him, is about you anty.

Daukewar cak Adiaha tay da mamaki a muryanta tace ur wish is about me? Ahankli yasrah ta gyada kai...murmushi tay ta riko hannunta snn tace to ki fada mun mana i want to knw.

Dagowa yasrah tay suka hade ido tace are u sure kar na fada miki kiji haushi? Tace just try me..

Yasrah dake kallonta calmly tace "I just wish u cud get alot of things that u lost, Like ur smiless,ur baby, ur friends,ur siblings and relatives,ur parents And evrything u ever wanted.

Bcos i cant even imagine living witout them, amma ke gashi kina rayuwarki anan batare da kowa naki ba, anty reema ure really braver than u think cos is not easy to live witou ur family or friends i hope one day zaki neme su.

Jikin Adiaha atake yay sanyi ta lumshe idanunta
Sosai cikin sauke ajiyar zuciya mai nauyi jin maganan yasrahn ya saukar mata da wani irin radadin kewarsu aranta na daban.

Shurun datay nadan lokcin jimami cikin lumshe ido yasaka yasrah ta tsorata tace anty i hope i dint say anthing bad, i knw dis might be personal for u pls am sorry in bai kamata na fada miki hakan ba. It just dat wani lokaci i just really wish u cud to have ur parents support cos kinsan i am just a temporary company ba lallai na zame maki abunda kike so nan gaba ba.

Da sauri Adiaha ta bude idonta da sukay jaaa atake ta kalleta tanamai girgiza mata kai lkcin hawayenata suka soma sauka mata zurrrrr tafara murmushi acikin hawayen snn tace "Noo noo my dear ure not a temporary comppany to me,kidena damun kanki besides whats so personal about my life kowa fa yasani, my life is like an open book, ive got to Thank u for seeing my deepest pain even tru my eyes, kinga tun da nake babu wanda ya taba min wann adduar saike..babu wanda ya taba kulawa sosai da yadda nakeji araina da bana tare da kowa nawa.

muryanta na rawa tace u knw, sumtimes i do wish can see just my mother, or father, like, even in my dreams, amma its neva happens to me..ko garin mu ban taba mafarkinsa ba..so u see im very grateful to u for evrything Tanakan maganan hawayenta masu sanyi na sauka akan hannun yasrah data kama sosai sosai yasrah takejin tausayin ta ,idanun yasran ma yay jaaaa sosai, cos she was sumhow touched by Adiahas painful words wanda kanaaji kasan daurewa kawai takeyi.

Yanata kallonsu daga wajen bai iya cewa komi ba face harsaida suka tashi awajen suka fara kai kayan abincin kitchen

Jingina bayansa da bango yay yanamai sauke ajiyar zuciya idanunshi a lumshe sai can daya budesu.

Sabulewa yay ya fita masallaci zuciyarsa cikke da tunanin yanayin Adiaha. Saiyau da yasrah ta furta snn shima yay tunanin hakan aransa shima, cos gosh..she tried.. is not easy to leave alone witout friend and family.

Yay tunani mai nisa akan haka wanda ya saka masa tausayinta aransa bana kadan ba...

Washe gari ya yasra tay sallama wa Adiaha ya kaita har lagos hutu zatayi 3 weeks kafin ta dawo 200lv, saidai wnn karon ko kwana baiyi a lagos din ba ya dawo Abuja abunshi Adiaha nata shan mamakin ganinsa daya dawo akan lokci.

Dake abunda bai saba ba duk yarasa yadda zaiy ya fara mata magana akan parent dinta altho ita bata taɓa nuna masa tana kewarsu sosai aranta har haka ba.

Deciding yay yakaita hutu garinsun kawai koda ma ace bazasu amshe ta ba atleast taje ta gansu su ma su ganta cos dat will help her alot....

Bayan tafiyar yasrah da kamar 5 days Ahmed ya kawo mata news din cewa zasuyi tafiya zasuje trip na shakatawa.

Adiaha was super happy
Tahau shiri tana deban abubuwan datake bukata..

After ishai sukaje main house sukayi sallama da alhaj bello Kafayat na labe ajikin bango tana son taji ina ne zasuje amma Ahmed yaki sam ya bayyana inda zasuje Alhaj bello yay musu fatan alheri.

Bayan nan Yabi gaya ma yayanshi kafin suka dawo room dinsu shine ya riga ta bacci sai can data farka zata aje masa phone dinsa akan bed side taga hotonan yasrah daya dauka awayrsa witout her consent.

Haka ta danne hakan aranta tay shiru itama ta juya ta kwanta tay bacci

washe gari sassafe suka shirya har saida lokcin tashin jirginsu yay kafin nan Adiaha tasan cewa calabar zasuje.

Since then tafarajin hanklinta na tashi tabi ta rasa nitsuwarta duka..

She cnt believe she is going back to where she flee from, wani irin tsoro da fargaba na cinta ata cukin ranta ata wani bangaren kuma bakaramin zumudin ganin iyayenta takeyi ba.

Da wuri suka isa, babban hotel din da Ahmed yay booking musu ata can wajen gari yake dan karamin five star hotel ne dayaji kayan More rayuwa.

Atmosphe na wajen is very peaceful ga sanyi ga ruwa ga duwatsu masu kyan gani..

Daga cikin room din da ya kama musu she can view water falls from der wanda suke tsattsafo mata da wani sabuwar kwanciyar hankli da nitsuwa wanda ta dade bataji irinsa arayuwarta ba.

Wani sabuwar rayuwa suka fara shimfidawa wanda sukayi Kusan sati mai kyau acikin hotel din Ahmed yanata kkri wajen ganin yafara jin sonta aransa amma ina, son yaki zuwa, sam sam, daga ya fara tuna all the moment da sukeyin sharing sai kuma yafara jin dama bai aureta ba.

Hakanan ya yita dannewa aranshi yana fita da ita tana zagawa tana cin abin da ranta yake so, wani bin ya zauna tare da ita a pool side wani bin suje picnic tayita bashi labarin garinsu kala kala yana murmurshi.

These 1 weeks is almost the best days of her marrigae life so far cos ahmed yay kkri wajen ganin ya samo kusanci da ita duk dama ya kasa iya samo feelings din hakan acikin zcyarsa.

Time din da sukazo calabar din is almst perfect sabida the end of calabar festivals ne zak zak lokacin dayazo nemanta wancn karon wanda yadinga dawo musu da memories na yadda alakar su ta aure yafara kulluwa, saidai kowa da irin Abunda yakeji aransa,da wasa da wasa in 2 weeks time aurenta da Ahmed zai cika shekara guda despites d hurts and the struggles..

Tay ta son ta leƙa wajen festival din tare dashi amma sam yaki sabida baisan me zasuje su tarar awajen ba itakuma tana bala'in son taje tay feeling kanta at home the feeling is almost unberearable for her yace mata wai saidai tana kallon komi a tv, da kyar ta iya daurewa har suka kammala cin duniyarsu anan na sati guda suka huta sosai batare da sun fita gari ba. Ana saura kwana biyar su dawo Ahmed ya fara fita da ita da daddare haka suna dan zuwa last last event na programe din asace tana kalla tanajin dadi..

Ahmed is with her right where it all started a zuciyarta She wished they can start afresh as best friends and lovers for real kamar yadda take mafarkin rayuwarsu ta kasance cikin son juna da shakuwa..

Kwana uku da suka jera suna zuwa wajen babu abinda take tunawa sai rayuwarsu, shikuwa a fannin sa babu abunda yakeji face kaico da nadama, duk sanda yazo yaga tana murmushi tanajin tsananin farin ciki da jin dadin ganin kabilarta da rayuwarta na nan data bari dominsu sai yaji aransa kamar bai kyauta wa rayuwarta ba.

Ita anata zuciyar tana ta tunanin su fara afreshh shikuma dan dana sani kawai yakeyi daya rabata da komi ma rayuwarta na kwanciyar hankli da kuma annashuwa...

Cikin kwanakinsu na karshen Kullum suka fito cikin taron mutane saita boye kamaninta da hijab ko nikaf Ko tsayuwa basa yin shi a inda kowa zai yi suspecting itace

haka zatayi ta hawaye idan ta hango wanda ta sani ko taga yan uwanta daga nesa cikin masu hidima.

She is alwys in state of melancholy jikinta yakanyi sanyi sosai wanda yake dada saka Ahmed yake dadajin karayar zuciya da lamarin auren nasu aransa gabaki daya.

Saidai qaddara ya riga fata he cant run awy from dis anymore.

Yayita tunanin Abunda zai kai ma iyayenta da kuma yadda zai basu su amsa,duba da koda sau dayane arayuwarsa bai taɓa ganin ko daya daga cikinsu ba baima san ya kamanninsu yake ba.

Yasan duk yadda akayi by now sun tsane shi daya rabasu da yarsu kuma ba lallaime su amshe kyautar kudi ko wani abu daga gareshi ba, But for the sake of tausayin lamarin Adiahan daya faraji aransa yasa ka ya fara bincikan ta inda hakan zai yu.

Yay zaman garin dan haka yasan tsirarrun mutanen da zasu iya taimaka masa..
Chapter 111 · 0% Book details