← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 157

Sashe 80

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda hjy ta umarce ta mike tsaye izuwa gaban alhaj bello jimada duk sai kallonta sukeyi yuuuu babu mai kiftawa face Ahmed da idanunsa ke kan wayarsa yanata chating da abokinsa Banji as usual kansa ya kulle ya rasa yadda zai fara kulawa sa yasrah dakansa musmmn ma da matarsa Adiaha take da ciki bayason yana stressing dinta da wani
Aikin kulawa da kowa yanzu..

Saida har Yasrahn ta tsuguna ta fara gaishesa na musammn snn Adiaha ta iso kofar falon,
kasa isowa ciki tay ta tsaya cak daga bakin kofar falon ganin irin natural likeness da alhj bello ya fara nunawa akan yarinyar cos she was very prty and calm sai ya farajin inda har ya mace khadijatu ta haifa masa a farko this girl will definately be his child sabida kamaninsun dayake gani a idanunsu karara.

As jovial as he is shine kadai ya iya saka yasrah yin murmushi da jokes dinsa shida brother hamzat, sai tsokanarta suke sunata tambayarta akan meyasa ta zabi law duk dama she seem quiet and calm, da can sabida kunya taso tay musu shiru, amma dake karatun law din is her passion, ahankli cikin hirar take basu amsa dats full of vision and confidence duk sai sukaji ta bala'in burgesu sosai.

Duk sai taji mamki aranta dataga hanklin family mmbers din gabaki daya yakoma kanta,they all seems to like her boldness da ganin cewa ta waye sosai har ta iya sanon metake so arayuwanta duk dama ita karamar yarinyace.

Badon wani gulma ko dan munafurci ba the likeness da su anty adizat suka fara nuna mata is sumhow true and genuine sabida harga Allah ta burgesu sosai msmn yadda wayewa ya gama ratsa ta sosai babu kuma girman kai mai yawa atattare da ita.

Murmushi Hjy maimunatu ta dingayi ganin yadda yasrahn ta samu karbuwa acikin familyn jimadan sosai harma fiye da yadda tay zato cos the way irin kowa yake tsoma bakin ana hirar law anata cewa za'ayi supporting dinta wajen cimma burinta na zamowa lawyer domin ta dabbaka justice acikin al'umma is so beautiful.

Daga Adiaha har kafayat kallon yasrah sukeyi da dukkan imaninsu dan basai an gaya maka ba kasan she lack nothing na kyau, da gata tare da kumwa waye na ga ilimi da wann kasaitaccen yanayin na kamammun mata yan kwalisa wanda ko da a matsayin yar gidan sarki ko shugaban kasa aka jerata zata zauna daram dan hutu tare da nitsuwa sosai yake ratsata.

Agefe alhaj bello ya umarceta ta zauna kusa dashi ta inda Ahmed yake zaune tana zama Qamshin turarenta ya fara bugashi sai yaji ya kasa cigaba da abunda yakeyin gabaki daya sai ya fara juya wayar dake hannunsa ahankli, dago kai da Ahmed din yay suka hade ido da yasrahn ganin irin piecing looks dayay mata atakaice yasaka kafayat dake lura da su sosai tayi saurin barin wajen tana huci dan haka kawai taji ta mugun tsanar yarinyar duk yadda bata daukar Adiaha wata abar amma bataji tsananin tsanar Adiaha ya kumtseta a ciki kamar na yarinyar nan ba,irin tsanar to see sumone dat is better than u in all aspect din nan takeji dadin karawa dataga yadda ake bi da ita kamr yar kwai kowa na haba haba da ita harda su anty adizat duk dama su sunayi da biyune dan aganinsu wata hanya ne sabuwa tazo dazasu rinka cusawa adiaha baqin ciki akan yarinyar.

Jiki a sanyaye Adiahar ta karaso ciki kirjinta sosai yake bugawa ganin an zuba mata ido dan ita kanta batasan cewa muryanta na rawa rawa ayayin da ta fara gaishe da iyayen nasu ba.

Hjy khadijatu ce ta amsa mata da fara' a sosai tana ta tambayarta lapyarta tare da kara mata karfin gwiwa akan tana kulawa dakanta sosai har Allah yasa ta sauka lpya itama.

Bayan gaisuwa iya Kallo daya kawai hjy maimuna tay mata atakaice dan itakam batako tsayawa wajen tambayarta ya jikin ba tay shiru dan ita haryau bawai yarda takeyi da matan kabilu ba.

Batama son ta cigaba da
Sakewa Adiaha fuska bare nan gaba tazo tafara azbtar mata yarta dazata zauna ahannunta.

Sama sama Hjya kahdijtu ta gaya mata cewa ganan yasrah sun kawo musu.

Adiaha kuwa Duk sai taji ta kasa iya daga ido ta kalle yasrahn, itama ysrah tay shiru abunta batace mata uffan ba duk dama anan akayi introducing din kowa aka gaya mata sunayensu amma basu cewa junansu uffan da Adiaha ba da kyar dukansu suke kkrin murmursawa juna

Bayan dan wani lokci hjy maimunatu ta fice waje tare da su Ahmed da brother hamzat domin shigowa ciki da tsarabar data kawo musu.

Nan ma Duk su anty nurat sukayi wajen sabida gulma dan kuwa bakaramin kayan duniya ta saka abayan booth dinsu aka kawo musu ba a matsayin tsarabar da yasrah ta taho musu dashi ba, sai tsokanan Adiaha sukeyi acikin habaici ayayin da aka fara kawo kayayakin ciki,
As usual goranta mata suke duba da yadda aka kawo ta gidan ko kayan sawa batazo dashi ba bare tsaraba sudai so suke sufara cusa mata irin feeling din jin kamar yasrahn kishiyarta ce ta asali dama kuma neman hanya suke da zasu fara rama iskancin datake musu agidan kwana biyun.

Lkcin yasrahn ce kawai a falo tana zaune tana kalon tv ita kadai tana dan karewa gidan kallo a hankli duk ba laifi suna da kyale kyalen arzikinsu daidai masha Allah bazaka raina musu ba.

Alhaj bello ya bukaci tattaunaawa da matarsa privately shiyasa suka wuce private room dinsa acan inda kafayat ta gindaya masa yake zama shikadai..

Tunda suka shiga dakin take a tsorace dashi dan bata son suyi wani abar kunya duk ahanklce take dashi, yau duk naciyarsa Sam taki ya taɓata bare su dawo da maganan tasu musu ko cece kuce duk wani complains dinsa akan barin gidan datay tabarsa tajishi sarai amma sabida tsoron kartace zata tuno masa daren ranan dayay mata na karfii yasaka ya zamo baida wano karfin gwiwa ko baki sosai wajen tursasata akan data zauna dashi,duba da yadda ya dinga cewa itace tay masa sihiri ta rabasa da yayansa da kuma matarsa kafayat.

And he just cant take back his words now duk dama he wish dat bai fada mata ba koma yayane da yanzu tana tare dashi,..

After long conversation din da sukayi ta lura da cewa bazai taba sake ta ba, kawai saita wayance masa ta nemi damar yin zamanta a lagos din officially daga wajensa danta kyalesa da matar sa shikuma yace sam saidai in zatana kulawa dashi kota yayane tana daukar kiransa awaya snn ta hanyar taimaka masa da kudi tunda ayanzu baya samun isashen kudin kashewa.

Ya gaya mata yanzu wanda y'ay'ansan ma suke bashi baya isarsa sosai sabida yawan demands din kafayat wanda baya son ya furta mata su a fili. Duk takaicin shi yabi ya isheta cos she have no idea irin kalar sihirin da akayi akansaz duk ta kan dauka harda halinsu na budurwan zuciya irin na maza.

He practically beged her for his fundings duk dama da akwai girman kai da nuna iko da ya iyayi ma ta dan aganinsa ai ita din ma matarsa ce abunda ta mallaka tamkr nashi ne kuma itace ta saka shi acikin matsalr dayake ciki da rayuwarsa ayanzu aransa He is still accusing her of rabashi da zaman lfya agidansa.

Duk dama hakan daya nema wajenta ya mata ciwo aranta amma ta gwammanci ta rika bashi ko nawa ne domin ta samu kwanciyar hankli ta kuma kare kimarta tasan dole akwai ranar da zaizo ya fahimce cewa duk abun da yakeyi din nan ba daidai bane.

Ahaka suka tsaya ta amince cewa zatana tallafa masa akai akai da kudi da wani sabuwar acct na daban tunda dai damuwarsa duk dai kudi ne ba ita ba, while aransa yasan ba hakan bane kawai babu yadda ya iya da rayuwarsa ne...

Bayan nan basu wani jima agidan ba suka fito
Ahmed din kawai suka kirawo agefe suka masa nasiha tareda dada jan masa kunne akan zaman yasrah ahannunsa.

Bayan sun fito waje hajy khadijatu ta jawo yasrah jikinta suka tsaya agefe tana mata nasiha ahankli
akanda ta zauna da kowa lafiya agidan snn ta bawa Adiaha girmanta ta dauketa kamar yar uwa sabanin irin abunda hjya maimunatun take yawan gaya mata cewa Ahmed ne kawai dan uwanta ba Adiaha ba.

Hjiy maimunatu kuwa taki sam ta kyale Ahmed duk saita tuna masa cewa yasrah marainiya ce inhar ya sake aka cutar da ita bazaiji dadi a hannunsu ba .

Duk adiaha ta shiga rudani da tunanin ko zasu kirata itama su damka mata yasrah a hannunta amma sai taga wa Ahmed kawai suka jadaddawa amanarta snn tare da shi sukaje da ita kawai suka rakasu.

Dubu dari biyu hjiya maimunatun ta bawa matayen gidan akan su raba a tsakaninsu banda tulin tsaraba da akawo musu kowacce ta samu jakar gift mai cike da perfumes luxury watches da atmfofi guda biyu aciki hatta brother kazim da baya kasar shima hardashi an kawo masa tsarabarsa.

Kafayat ce kawai ba'a san da ita ba dan haka ko takanta basu bi ba.

Tun ficewarsu agidan su anty adizat suketa shewa suna masu cakalar Adiaha da tsokana dan har sashenta suka kara binta da zancen kyaun yasrah suna using styles suna mata habaice habaice da gorin talaucin da ta zo gidan dashi tare da maganganun banza duk tanata shanyewa.

Atake suka saka ma yasrah suna na Pet names kala kala most importantly suna ce mata yar amanan Dami
Da kyar suka kyale Adiaha tasha iska ganin ta turmuke fuska kamr wanda zata fashe musu da kuka, sun mata dariya sosai ransu yay dadi.

A Falonta ta zauna cikin yanayin tagumi tanakan jiran ganin dawowarsu daga rakiyar duk dai tana son taga ko shima ahmd Din bazai hadata da yarinyar bane kmr yadda taga iyayensa sunyi.

Bataji dadi ba sam da ba a hanunta aka damka amanan yasrah direct ba wanda yana daya daga cikin abunda ya jawo su anty nurat sukasamu gangaran mata dariya.

hakan yana nufin har yau dai bata da wani daraja ko martaba sosai kenan a idanun nasu a matsayinta na matar dansu Ahmed.
Chapter 80 · 0% Book details