← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 157

Sashe 133

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk suka taru a motar sunata bata baki, sai suka nuna mata kamr suna matukar jin tausayinta musmmn ma shi fahad din da har hawaye taga yanayi, batasan plan dinsa aransa shine yaje yay badalarsa da ita ba. Daga nan kuma Bayan an samusu ai dolene abashi ita na dole daganan kuma zai yi duk abunda yaga dama da ita.

Daga can gidan jimada kuwa ba atashi neman yasrah ba har saida lokcin kaita dakin mijinta yay.

Godiyan Allah ma dayake sabuwar gidansa za'a soma kaita dan acan aka mata jere sakamakon nan din bazai dauke tulin kayanta da aka mata ba saidai duk su Adiaha basu san da wann tsarin ba dake anan dinma an cire mata daki an zuba mata kayan alatu aciki akan idan ta kammala schl sai ya tattarasu duka yakaisu sabuwar gidan dukansu biyu.

Wasa wasa aka fara neman yasrah a dakin ba a' sameta ba wanda hakan Yaso ya tadawa hjy maimunatu hanklinta sosai.

Nemanta sukeyi acikin sirri dake ma basa son kowa yasan me ake ciki gashi har motocin daukar amaryn ya iso.

Su yasrah kuwa sauri sukai suka isa airport suka fara booking flight da zai wuce da su America acikin gaggawa.

Lokcinn bata da wani buri face taga tay abunda zai kawo ace anraba wann auren dan gani take kamar su hjya basajin tausayinta kuma basusan waye ma Ahmed din nan ba.

Process din tafiyarsun ne ya dau musu lokaci sosai sabida babu wani passport dinta anan da sauran tarkacenta So fahad is busy calling his father's contact ta inda za'a musu komi akan lokaci.

Dagata can gidan jimada kuwa saida Hanklin kowa ya kusan tashi garin neman yasrah. Sun kira maryam bila adadin bata dauka ba.

Tun 4 suka bar gidan Har kusan Bayan magrb kafin hjy ta saka akakaisu har gidansu maryam din da taimakon iyayenta aka samu gaskiyar abakinta dan itace karshen gani tare da ita.

Yay sadik yaje airpot cikin gaggawa aka fara neman yasrah awajen, daf lokcin har sun kammala komi zasu tafi sai aka kira fahad aka sanar dashi cewa an ganosu, atake ya mata wayo yace yana zuwa snn ya zame ya gudu ya barta a airpot din dan kar ace shine yakeson ya gudu da ita,tsaye tay tanata jiransa har su yay sadik din sukozo suka sameta suka taho da ita gida.

Bayan isha'i aka taho da ita wajen su hjya, yau Bakaramin masifa tasha awajen hajya maimuna ba domin kuwa ranta ya matukar baci sosai dataji cewa guduwa take sonyi bayan andaura mata auren danta tozarta su da mutuncinsu da matsayinsu da komi.

Ran yasrah ya sosu sosai tanata kuka mai cike da gushewar hankli har tace musu ai dan basune suka haifeta ba shiyasa sukaga Ahmed ne ya dace da ita amatsayin mijin aure.

Tacewa hjya maimuna dama amfani da ita kawai takeyi amma bata kaunarta aranta.

Maganan sosai yay ma hjya maimuna ciwo har hawan jininta ya so ya kadata aka kaita asibiti a ruwa ruwa.

Sai a sann yasrah ta dan dawo cikin hayyacinta ganin abunda ta jawo nan da nan tafara nadaman abunda ta gayawa ma hjy maimunatu a wann rana.

Jikin Ahmed sosai yay sanyi ganin irin tsanar da yasrah tay ma aurensa hade da girman kai da kuma takaicin jin cewa tay rejecting dinsa with all her heart hartana ikirarin gara ta mutu data kasance matarsa.

He plan on dealing with her dan yadda takejin ta tsanesa shikuma alokcin yaji aransa dolene tay zaman aure dashi.

Duk abunda akeyin nan saidai yabada hakuri amma baitaɓa yunkurin jin cewa a since auren ba

Tunda yasrah tay musu izgili da gori akan mutuwar iyayenta shikenan Duk su hajy suka yi fushi da ita suka dauke mata wuta cak suka dena mata magana dukansu biyu aranar.

Ta shiga damuwa Tarasa meke mata dadi aranta dataga duk sun mata hakan, ita kenan koyaushe a kuka, duk su anty nafisa da yaya sasik ne suka dinga mata fada sosai suna nutsar da ita wanda hakan sosai ya so ya ragwabar mata da zuciyarta gabaki daya tafara tunanin amsar auren kodan amana da girmamawa dake tsakaninsu da iyayen nata dukansu biyu.

Duk dama bataso ace akan Ahmed ne zatay wann tulin sadaukarwa mai girman ba dan bata taɓajin sha'awar kasancewa matarsa aranta ba.

Kowa yazo saiyay Allah wadar da abunda datayi nason kunyatar da hajya maimunatu.

Daga bisani dan dole ta amshe auren kawai aranta, washe gari sassafe bayan hjya ta dan samu sauki ta taho tazo ta tsuguna agabansu ta basu hakuri tace musu ta amince.

Duk da maganganu masu ratsa zuciya da suka yi ta mata da safen nan bashine yasaka ta hakura aranta ba, kawai ta amince ne a matsayin biyayya da sadaukawar agaresu dan tasan batada wani gata duk duniya saisu din.

Albarka suka saka mata aka shiryata aka kaita gidanta na can aka musu nasiha acan saidai har iyanzu bata kara sake fuska da iyayen nata ba, da yamma lis ranar karshe wato ranar sunday aka dawo da ita gidan jimada.

Nan ma aka musu nasiha dukansu uku a falon alhaj bello aka kuma umarcesu akan da su zauna da junansu lafiiya.

Sosai Adiaha taji dadin yadda wann karon aka karramata aka yabe irin hakurinta snn aka damka mata amanan yasrahn ahannu..

Hajya maimunata ta bata kyautar kudi mai yawa tace ta kara akan business dinta na shago snn duk sanda take da wani damuwa ta kirata kai tsaye zata cika matashi

Hakama Ahmed aka basa amanan yasrahn aka ja masa kunne sosai.

Alhamdullhi at long last komi ya kaammala cikin mutunci, wajajen karfe tara na dare aka kai yasrah bangaren su Ahmed dakinta nanan gidan shi ne irin na Adiaha dake gefen sa ta hannun dama shima ankyafe mata shi single room ne irinna adiaha zak zak.

Hatta falonsu saida aka sauya masa sabbin kayan alatu komi na gidan ya zamo sabo kar kar.

Tunda adiaha take arayuwarta bata taɓa gani ko jin irin qamshin turaren wutan da gidan sun yakeyi ayau da dare ba. Evrything seems so serene..aranta ta raya cewa dolene ahmed yana nuna zumudinsa cos dis atmospher really smell love and nothing else.

10.30 na dare yasrah na kwance akan sabuwar gadonta na gidan anan cikin sabuwar room dinta ita kadai tana hawaye masu zafi Adiaha tazo ta fito da ita suka same ahmed din a falo yana zaune.

Danne zuciyarta kawai takeyi amma sam sam bata cikin hayyacnta

Koda suka hade ido dashi taga yanata kallon ta da wani irin salo ji tayi kamar ta kashe sa.

Nasiha yay musu daidai gwargwado snn ya dan gaggaya musu yadda zasu zauna a gidan. Har da kwanakin kwanan su duk bai yi jinkira wajen raba musu ba.

It was agreed dat zaina yin two two days adakin kowacce bayan ya samu cikakken 2 weeks da amaryarsa yarsa. As expected Adiha ce kawai ta amsa masa yasrah tun da ta sauke kanta kasa batace mai uffan ba harsaida ya gama yay shiru.

Bayan nan ya sallame su ta tashi ta wuce room dinta ta kulle kofar da key taciki abunta.

Kafin yaje yay sallama da iyayensa yazo ya samu harta kulle kanta aciki karshe karkada kansa kawai yay ya koma room dinsa.

Ko bacci baiy samu daman yi ba tuna yadda yasra take nunamai tsana sosai abun ya dameshi aransa dan wata ƴa mace bata taɓa nuna masa kalar wann tsanar ba..

He wonder what she see in him dats so distateful harta tsanesa haka kamr mutuwarta.

Kyabe bakinsa yay cikin rashin jin dadi aransa yanaji babu wanda ya isa ya tsince auren nan komin tsiya komin rintsi kuwa yasan wata rana dolene ta shigo hannunsa.

Karfe Daya saura ya buɗe idonshi da matsanancin tunaninta aransa, ganin Adiaha bata nan yasan tana can dakinta hala, tashi yayi ya dafa kanshi tare da sauke ajiyar xuciya sanin cewa ita bata da matsala koma yayane zai iya ya shawo kanta ya kuma san ta hakura, yanzu babban matsalar sa yasrah ne, mikewa yyi ya fada toilet ya sakarwa kanshi shower mai dumi yayi wanka yayi alwala sai da ya fito ya canja kaya zuwa normal sleeping wears, karfe 1:30 na dare ya gani lokacin ya tuna yasrah bataci komi ba,dan tsaki yaja tunawa da yayi wai tanakan bori akan auran nasu har yanxu.

dolensa kenan yadawo gidan da zai riqa fita yana nemawa mata abinci awaje,dn tsaki yaja dan itama yanxu wata liability ce agaresa, fitowa yayi yabita hanyan dakin da aka ajiye yasrahn,a kan gado ya sameta kwance tana bacci ta kudundune waje daya a cikin bargo tay lamo da kanta akan pillow tamkr wacce take cikin matsanancin bakin ciki da damuwa

Karasawa yayi bakin gadon yasa hannu zai yaye bargon yaga sexy figurenta tana bacci dat seems peacefully adan takure, gyaran gashin da aka yi mata ya rufe rabin fuskanta ya mata wani irin masifar kyau, dan tabe baki yyi ya bugi gefen gadon da nufin tada ta amma ko motsi bata yi ba, zame bargon yyi lkci daya ta mike xaune da sauri ta shiga komawa baya baya ganinsa datayi, karamin tsaki yyi yace "wato bazaki ci abinci ba ko?"
Chapter 133 · 0% Book details