← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 157

Sashe 15

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adiaha ta juya embrassingly zata bar wajen cikin sauri,sai ta tsareta tace hey iyawo comeback here ki zoki budemin abincin naga mene kika kawomin tukuna i no wan go see wetin my eye no fit carry budemin inma kinsaka min magani saiya fara kasheki.

Adiaha ta dawo ta dauko tray din abincin sama ta bude snn ta miƙa mata

shunhsuna abincin tay tare da cuna hancinta sama sama tanamai cewa hnn wani irin wari wari nakeji,What kind of awful smell is dis?

Adiaha tace nima fa bansani ba.

Ahhh give me dis food lemme check it nn ta karbe abincin ta tattaba
sai ta dawo mata dashi tace ahhh Warin ba daga cikin abincin bane fa.

Adiaha ta sauke ajiyar zuciya.

Saida tay jimmmm snn ta dubeta tace haaaaa maybe is ur armpit.

Ran Adiaha yy mummunan harzuka ta kasa iya dannewa tace excuse me anty nurat, wht do u mean by is my armpit? why are u insulting me now..

Ganin ran Adiaha ya baci yasaka ta sauko tay kmr a wasa kawai ta fada, Tace ni ba zaginki nake yi ba ooo, just go an take ur bath aahhhh u stink like an onion..idan akazo gidann aka ganki haka akace ke matar damilare ne Allah bamai yarda cos ure left and he is right ata wajen tsafta kije kiyi wanka mono.

Tsabar bacin rai adiaha batasan lokcin da taja mata tsaki ta kama hanya ranta a bace ta bar wajen ba.

Agaggauce ta koma wajen kitchen din tana tsayawa wasu hawayen bazata suka fara zubowa daga cikin idanunta kmr ruwa.

Ta jima ahaka tana hawaye kafin nan ta rarrashe kanta ta sake daukar dayan plate din sai dar dar takeyi dan batasan wani kalar zagin zataje ta karba awajen sister zainab ko hjy khadijatu ba.

It seems like the women in this household are cruel basu da kirki ko kadan komi masifane awajensu ga iya maganan banza abakinsu kmr ruwa.

Sashen hjy khadija ta nufa asace dan kar suci karo da sister zainab din awajen dan har tsoronta takeji aranta.

Tana isa sashen ta samu babu kowa aciki, tay ta sallama nan ma shiru, da alaman hjy khadijtu bata gidan ta fice tare da yar uwanta, nan ta aje tray din abincin akan dinning table snn ta fito da wuri taje ta dauko last tray na abincin zata kaiwa Sister zainab.

Tafiya take kirjinta na bugawa haka ta iso kofar cikin main falon dashi....
[6/6, 8:06 PM] SURAYYAHMS: Lokcin Sister zainab tana zaune akan doguwar kujera yaron ta shafiu yana wasa akasan kan tiles da toys dinsa dake barbaje akasa.

Nan Adiaha tay sallama cikin sanyin murya bata ko amsa ta ba, tana shiga tahau binta da wani irin banzan kallo.

Dauke idonta tay dan tasan dolene ta sha masifa awajen sister zainab dan tun zuwanta gidan iya abunda ke shiga tsakaninsu kenan.

Ko kammala ayyana hakan aranta batayi ba taji anja mata wata tsaki mai tsayi "Mtschewwww" kai amma lalaci baiji dadi arayuwarsa ba.Breakfast 10ckl in dis house?haaaa, harde ranta ta dadayi cikin kyabe baki tace "Repeat dis mistake tomrw and see idan ban gayawa damilare ya sake ki ya tura ki kauyenku ba. _oya werey ?_ U cant come and kill us abeg.

Adiaha batace uffan ba ta aje try din abincin agabanta ta dagokai kenan da niyyar zata mata magana kafin su hankara agarin wasa shafiu ya jawo mug din tea din ya zubar akan hannunshi, Wani irin razananen ihu ya danna mai karan bala'i.

Dukansu abirkice suka tashi suna kallon shi, sister zainab tay saurin dagoshi ta rike hannun tana dubawa cikin gaggawa, Allah yaso tea din baida zafi sosai amma still hannun yaron yay jaaa Sai ihu yaron yake kmr ransa aka zare

A birkice Adiaha taje ta kawo ruwan sanyi mai kankara duk tausayin yaron ya kamata tana kawowa sister zainab ta karba ta watsa matashi akan fuskarta. Tsawa ta daka mata mai cike da hatsala, a cikin masifa tana cewa get out of my sight, Its ur fault, its ur fault,kin konamin hannu yarona da ruwan zafi Haaaaa.. Ure soo wicked reema menene yaro na yay miki da zaki konashi?..how evil are u?
Muguwa ta zungureta da karfi.. duk farincikin da yake gidan nan kin karar yanxu kuma dana kikeso ki kashemin?

Adiaha dake kkrin mata bayani kawai saita fashe da kuka sosai dan batasan ma mezata fara cewa ba.

Masifa sister zainab ta dinga mata kamr zata hadiyeta harji take kamr zaneta akeyi ajikinta
..tana kiranta muguwa azzaluma mayya.

Acikin lokaci kadan tay mata kwalala ta tara mata mutane su anty adizat da anty nurat nan da nan suka zo wajen tafara mayar musu da maganan tace musu adiaha ta kona mata yaronta da ruwan zafi.

Haka suka taru akanta anty nurat har da mata gorin haihuwa tunma bata kwana da mijin ba

They nagged her down till she cannot longer take it ,tanata kuka ta fita waje da mugun gudu tay hanyar sashenta tana kuka kamr ranta zai fita.

Lokcin dede shigowar hjy khadjatu gidan kenan bata ko sauka a motarta ba ta kalli Wucewar Adiahan da gudu ayayin da ta wuce sashen ta cikin kuka, hanklinta sam bai kwanta ba ta sauka tabi bayanta har cikin sashen.

Akan gado ta sameta tanata kuka kamr zata cire ranta. Harta tsaya akanta batasani ba saida ta dafata snn ta firgita ta juyo.

Da suka hade ido Tausayin yarinyar gabaki daya sai ya kamata ganin yadda fushi da rudani ya cikke mata kwayar idanuwanta, tafara goge hawayenta ahankli tana kkrin tsugunawa kasa zatayi gaisuwa jikinta harna rawa rawa, cikin sauke ajiyan zuciya hjya khadijatu ta rikota jikinta cikin yanayin lallami da rarrashi tanamai cewa meke faruwa dake reema and why are u crying my dear? Dake da waye haka.

Wani sabon kukan ne ya kufcewa Adiaha tafara gaya mata iya abunda ya faru tunda safe da akace mata tay abincin har izuwa yanzu.

Iya zagin da su anty Adizat suka mammata shine kawai bata gaya mata ba Amma duk abunda ya faru tsakaninta da sister zainab saida ta fada mata.

Tace "kiyi hakuri"
Ba haka halin zainab yake ba, but she is alwys like dat a farko farko idan bata fahince ki ba, In Kinyi hakuri da ita zakizo ki fi kowa morartta.

Gyada mata kai kawai tay badan ta yarda da Abunda tace din ba.

Ta tambayeta taci abinci?a kunyace sosai Tace a'a bataci ba tanajin yunwa sosai.

Cikin nuna tausayawa Tace okay Kizauna anan am coming.Tana fadin hakan ta fice.

Adiaha tacigaba da kuka ahankli maganganun su yanata dawowa mata cikin kwakwlata dakyar ta daure ta tashi ta shiga wanka kodama zata dena tuna yadda suka dinga ce mata kazamiya.

Haj khadijatu tana shiga main mansion din ta same su sunyi cirko cirko da shafi'u ahannu sai kuka yaron yake kamar ransa aka cire hanklin sister zainab ya mugun tashi tanata lallashinsa amma yakiyin shiru.

"Haaaa this girl is wicked ooo Bazan taba yarda ba fa,bari damilare ya dawo gidan nan yau. I wll make sure i report her to him inyaso tay masa bayanin dalilin dayasaka take son ta kashemin dana i wli not agree to this witch craft injustice oo.

Su anty nurat kuwa sai dada xugata sukeyi

Hajy khadijatu tanayin sallama awajen kowa yay shiru ya nitsu nan suka fara gaisheta ta amsasu babu yabo babu fallasa, kowa yana jiran yaji tay magana sai bata ce musu komi ba bare ta tambayesu meya faru ba

saka hannu tay ta amshe shafiun a hannun sister zainab tadan rungumeshi tana jijjigashi nan da nan sai yadanyi shiru.

"Kije ki kawomin first aid box zainab.

Ta kalli kasa taga duk datti inda tea din ya zuba ba'ako shareshi ba tace nuratu can u clean dis up? A ladabce tace yes maaa. Nan ma Anty adizat tabita suka bar wajen atare daga can ta sudade ta koma side dinta abunta.

Itama anty nurat din sharp sharp tazo da mopper ta goge wajen daganan itama ta gudu sashenta abunta.

Babu bata lokaci sister zainb taje ta dauko first aid box ta kawo nan hjy khadijatu ta goge hannun yaron ta tsaftace shi snn ta bude box din ta dauki pain relieve oitnment ta shafa masa hannun ta rufe wajen dan kar yaron yasha ko yay wasa dashi.

Bayan ta kammala Ta dubi sister zainab cikin sanyin murya tace ke kuma zainab tsabar masifa saikika barshi yanata kuka haka bazaki nema masa pain relieve ba, wai bakisan zazzabi zai iya shigarsa ahaka bane kome?

Zatay magana cikin tsareta tace je ki kawo min zanin goyo yanzu inadai yaci abinci?

A ladabce tace yes mummy Na dafa mana noodles da egg a kitchen dinki bayan kin fita

Tace okay.

Nan taje ta kawo mata hadadden zanin goyonsu blue big shawl mai kyau
Haj khadijatu ta karba ta goyashi damas abayanta nan tafara jijijjgashi tana masa waka ahankli sai gashi ya fara gyangaydin bacci.

Murmushhi sister zainab takeyi jin hanklinta ya dan kwanta sa yaronta ya dena kuka.

Hjy khadijatu ta haura sama sashenta tare da shafiu abayanta jim kadan ta dawo dauke da tray din abincin da Adiaha ta aje mata ta sauko tare dashi.

Sister zainab tana ganinta tundaga stairs ta mike tsaye aranta tana tunanin ko hala Adiaha ta saka mata wani abunda bai gamsheta bane aciki

Tun bata iso kasa ba tafara tambayarta tana cewa.

"Mumy what is it?
Abincin ne baiyi miki dadi bako?...

Bata amsata ba harsaida ta sauko lokacin sister zainb ta gama yin ready zuwa masifa wa Adiaha dan acike fam da ita take
Haryanzu bata huce ba.

Hjy khadijatu tace karki damu Abincin baiyi komi ba zainab, bazan ci bane shiyasa zan bawa reema
Taci tunda ita tanajin yunwa kuma bata samu abincin ba.

Sister zainab Tace ohh
Mumy shine kene kuma zaki kai mata abinci.?

Tace To wazai kai mata inba nidin ba bayan ke kina fushi ta kona ma yaronki hannu.

Cikin daure fuska Sister zainb tace yarinyar ai muguwace,ta konawa yaro na hannu ko hakuri bata bani ba, she just left here crying like a baby kamr itace ma aka konawa hannu bata da tausayi ko kadan she is just wicked tunda har zata iya sama karamin yaro ruwan zafi ahannu
Chapter 15 · 0% Book details