← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 157

Sashe 9

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In a Respectfully sacarstic tone yace "i am sorry Baba, but u cant touch Damilare. kadai fara controlling matarka tukuna. yakamata tasan da cewa ita ba kowa bace awajenmu.

A tsawace Alhj bello yace dukanku kuna hauka ne? Am i not ur father, u cant disrespect me like dis..

Aure nayi!!! Kafayat na Aura,what is wrong with dat?Me zaku iyayi akai ehhh? Auren nawa Haramun ne?meyasa zaku zo kuna raina ni har haka..are u guys mad?
...yau idan baku daraja ni ba hakanan yaranku zasu zo suma rainaku. Mene matsalar ku dani? Auren danayi haramun ne ku amsani mana ?see oo baku bina bashin wani bayani akan abunda nayi duk wani abun da nace zanyi shizanyi, evrything about this marriage ra'ayi na ne sabida ku ba iyayena bane da zan muku bayani nine na haifeku bakune kuka haifeni ba, all ur lifes ina muku adalci amma ni ashe bazaku iyamin uzuri dan naga yarinyar nan tayimin na aureta ba?

Ahmed didnt marry, so i did..Kazim what is wrong with ur head,kaine yau kake daure musu gindi sunamin hauka? Ni na baku goyon baya akan auren Damilare, amma nawa yazo har damilare yana daukar hannu agabana yana marin matar dana aura kuna goya masa baya...Ashe dukanku baku da imani bakuda mutunci yan iska ne ku?To wallh ku sani, aurena da kafayat is already done and babu wanda ya isa acikinku ya canza hakan, yau ko ku amince ko karku amince ruwanku, kafayat is my wife and u most respect her.

Brother kazim yace With All due respect sir, baba ure soo shameless idan wai kafayat ce kake kira matarka agabanmu.

Wani irin Ihu yay masa acikin yanayin mamamki yace "Ahhhhh"kazim me? "Shameless ke?, haaaaaaaa,"Kazimmmm, 'ka budi bakinka yau kace banida kunya? _oya werey?just bcos ure 45...u think i cant slap u? "haaaaaa Penu re._ "Is The audacity For me..

Brother hamzat yace
Baba babu amfanin ihun da kake mana anan. You knw what u did to us is not fair, zancen Adalci ma bata taso ba, kaje kayi aurenka aboye, mu bamu hanaka aure ba, amma kasani acikinmu babu wanda zaiyi supporting dinka tunda auren dakayi zai jawo mana tozarci da kaskanci acikin family.

Ransa a matukar bace Yace waye na tozarta acikinku? iya sanina tunda na haifeku nake muku adalci,dukan matsayin da kuke ji da shi ayanzu adalilin adalci na ne,infact u owe me alot of respect.

Ahmed dabai taɓa amsa masa magana acikin tsananin fushi ba a zuciye yace is true we owe u alot baba, ka bamu ci da sha da sutura snn ka ilimantar damu.

Shiyasa yau kaga daman ka zaɓe ni, da nida mahafiyata a matsayin target din da zaka fanshi price din Adalcin da kake mana arayuwarmun ko?.

Idan mu bama maka adalci kmr yadda kace what about my mother? Metayi maka?She have done nothing wrong to u amma me kayi? Ka kaskantar da ita, ka tozarta ta. Kaje auri yarinyar data raineta tamkar yar cikinta behind her back kaci amananta, and its seem like u dont even care about how she feels, in yar cikinka akayi wa hakan zakaji dadi aranka ne?..i use to think ure a responsible father but i dint knw dat ure dis senseles and heartless.

Da wani irin mari mai cike da kufula ya daukeshi da shi, dukansu idanuwansu yay jaaa ya tara ruwa suka tsaya kallon junansu suna huci kallo daya zakama alhaj bello kasan cewa he is already in pain and depresssed da bhvrs din yaransa nayau akansa

Shiru ne ya dauke awajen kmr wanda akay mutuwa snn ya kalle Ahmed din muryansa harna bari bari yace "Stay out of this damilare,daga yau karna karajin wann maganan abakinka, _oya werey?_ ni sa'arka ne? "Am i ur mate?,i have heard enough of this nonsense ka tsaya a matsayinka, Abunda yake tsakanina da mahaifyarka ayanzu ba damuwarka bace damuwarmu ne..

Ahmed ya girgiza kansa snn ya dago idanunshi da suke zubda hawaye ahankli ya kalleshi cikin tsananin bacin rai, yace damuwata ce mana, and I swear i wont let u hurt her again. A zuciye ya fada mashi hakan.

Ya sake daga hannu zai mareshi hajiy khadjitun ne ta tareshi dukansu basu san ma daga inata bullo ba.

Tunda taga an mare danta ta kasa hakura harsaida ta fito daga cikin motar.

Tace Ahmed, "is enough, ya isa haka.

Ahmed ya kauda kanshi gefe duk jikinshi na rawa yanamai share hawayen shi dake mugun kashewa kowa jikinshi awajen dan wani irin bacin raine ke dawainiya dashi.

Hjy khadijatu ta kalli brother kazim daya harde fuskansa tamkar bai taba dariya ba tace
"Kazim, ya kamata ka bude gidan nan ku shiga daga ciki haka,maganan nan taku ya isa haka
..kowa yay hakuri u can talk it down amicably.

Brother hamzat yace mumy, babu wani abunda zamu ce mishi. He made his point and is clear.

Tace "a'a, duk rashin kwantar da hankli ne yasa akayi magana cikin rashin fahimta sn shine ya jawo hakan pls do this for my sake..

Brother kazim baice komi ya dau wayarsa ya kira masu kula musu da gidan aka bude masa security lock nan tane kofofin shiga gidan duka suka budu.

Tsakanin hajy khadijatu da mijinta ko kallo daya bai gifta a tsakaninsu ba.

Su anty moju ne suka dan karaso kusa da dan guntun gulmansu ehen kagani?tooh fah ga remote control din yayanka tazo, all this unruly behaviour of ur children wann mata itace take koyamusu.

Hajya maimunatu dake cikin fushi taji kamr ta sauko kasa daga cikin motar amma sai taki ta motsa dan dama saida tace ma hjy khadijan karta sauko.

Anty ramotou dake kallon kasan idon hajy khadijan tace brother bello kar ka shiga gidan nan ooo ka tsaya anan harsai yaranka sun tsuguna kasa yanzu sun baka hakuri kaida matarka kafayat..

Ahmed shud apologise to kafayat personally, ka kalleta acan fa haryanzu bata dawo hayyacinta ba.

Baice musu komi ba wani doguwar Tsaki yaja snn ya juya yaje ya dauko kafayat din dake nishi kadan kadan cikin nuna mata kulawa sosai ya jawota har suka iso gabansun atare suka tsaye tanadan layi tana kwanciya jikinshi cikin salon makirci tana narke mishi sosai.

Su brother kazim su kara harde ransu basuce masa uffan ba.

Hjy khadijatu taji kamar wuta ake konawa akan gangan jikinta.

Ya dube hjya khadijatu babu kunya yace iya dami tunda magananki kawai sukeji agidan nan saiki ce musu subata hakuri idan ba haka ba bazamu shiga gidan nan ba.

Hjy khadijatu da bakin ciki ya isheta Batasan sanda tay musu wani irin busashen dariya mai cusa bakin ciki ba..

Cike da danne kishi da salon dauriya irinna kasaitattun mata tare da shan mamakin rashin kunya irinta da namiji tace Alhj bello kenan gida ai Gidanka ne ba nawa ba. Inkaga dama har duniya ta nade ka zauna anan kai da yaran ka kuyitayi karku motsa har mahdi ya bayyana, ko a tunaninka nazo nan ne sabida kai? Hahah ayyuriri toh Sabida dana Ahmed nazo dan kar akashe min shi kuga kasawarku a duniyan nan, Snn sabida mutuncin dake tsakani da su kazim shiyasa na sauko nazo nan dan nace musu su shiga cikin gida sudena haushin kare tare dakai tunda kai bakasan mutuncinsu ba.

Mamakinta yakesha aranta sai yaji gwiwarsa tay sanyi sosai ganin yadda ta bushe ido take masa magana batare da ta nuna kishinta a fili ko irin kukan nan bata yi agabansa musmmn ma da kafayat ta manne mashi tana narkewa ajikinshi agabansu duka.

Yace "Saiki zo ki koyamin min yadda ake sanin mutunci Mutum tunda ke kinadashi..ure not ashame of them kina ganin abunda suke min ke wata irin uwace iya dami?.

Da kyar ma ta amsa shi ciki ciki Tace ni banda lokacinka. ai Mutunci jinshi ajiki akeyi..kuma inamai tabbatar maka lokcin da zaka ji ajikinka cewa bakada mutuncin ma zaizo.

Yace "How dare u talk to me like dat in my own house khadijat? Dama saida na fada kece kike kowa yarana raini agidan nan, Toh wallh ki fada musu kafayat is my wife, duk wanda bazaiyi respecting hakan ba bana bukatarsa a inda nake yaje duk inda zaije.

Tace kana da baki gasu nan saika fada musu dakanka, Alhamdullhi.
Dama am leaving mezan yi anan din? Mtssss

Ta juya zata koma mota kenan Ahmed ya juya shima zai bita,brother kazim ya riko hannunta yace mumy ure not going any where ooo Shidin da yake son ayi respecting matarshin ai yana da gida yakaita chan suyi duk abunda zasuyi.

Ya hada rai ya kalle baban nasa cikin ido snn yace baba kayi hakuri fa amma bazaka zauna mana da wata yarinya agidan nn ba.

Anty mojushola tace what? Kazim are u sending ur father out of this big house?

Ko kallonta baiyi ba yace "yes. I am !!!

Anty ramouto tace haaaaaaaaa kazimu.
Yaushe ne kayi masa sabuwar gidan nan har kafara masa gori akai

Yace anty ramoutou karma ki juya maganan ya dawo wani iri Baba shine ya bada condition,

yace wanda yasan bazai respecting matarsa ba yaje duk inda zaije. And dis house belong to all of us, dan haka duk wanda yaga zai iya respecting baba da so call wife dinshi yabisu gidansa suzauna acan, duk wani wanda yake suppoting auren san ma yabishi..

Wann family house dinmu ne so only the family will stay here.

Nan aka ware wanda yake supporting dinsu da wanda basa suporting dinsu.

Lokaci guda kowa ya watse ya dawo gefen brother kazim aka bar alhaj bello tsaye shida kafayat da su anty mojushola su hudu.

Brother hamzat yace Alhamdullh since we r done here sai kowa ya koma gidansa babu kyau tashin hankli...we have enough for today.

Tsananin mamaki ya hana Alhaj bello yin wata magana awajen imagining yane wai dansa na cikinsa yay masa korar kare acikin gidansun yau

jikinshi duk yay sanyi musmmn ma dayaga cewa dagske kazim din yakeyi, korarsa agidan yay dashi da matarsa kafaya.

Kafayat tana ta kallonshi cikin rudani tana son taga yace wani abu sai taga baice komi ba

hjy khadijatu sam bataji dadin hakan ba amma haka suka dinga rokonta agabansu sunamasu cusa musu bakinciki..
Chapter 9 · 0% Book details