← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 157

Sashe 76

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayuwa acike take da jarabawa iri iri in yau mai dadi ce gobe sabanin sa ne. Dukan abunda ya faru abaya ya zame mana darasin rayuwa.
Kai namiji ne AHMD yaci ace duk hankli ya shige ka yanzu, duk dama Duk dai laifin mu ne dayasaka zumuncin yay'an mu baiyi zurfi kmr namu ba amma kusani wasu kakkarfan dalilaine suke sawa wasu abubuwan suzo da ban..in wata rana bama duniyar dolene kune zaku rike sunan ahalinmu.

Ya zame mana abun alfahari kuma ya zame muku abun alfahri ta har abada amma hakan bazai yu ba sai kun amshe girmankubsnn kun nuna mana mu iyayenku cewa kunajin kishinmu.

Wasu abubuwan ma baiya gane metake nufi amma haka nan tay ta musu nasiha kafin sai can ta sallamesa ya tafi.

Yaso ya koma Abuja as soon as posble amma yana son ya kammala komi anan kafin ya tafi dan baison yaje ya sake dawowa da wuri cos recently din nan ana yawan nemasa awajen aikinsa he knws yana bukatar bada hanklinsa acan.

Dagata bangarensu Adiaha kuwa sam bata jin daidai aranta hadi da wahalar laulayin cikin fari dayake matukar damun ta sai tunda akayi bidirin hidiman nan tafara jin tarasa nitsuwarta sosai dan kuwa bakaramin cusa mata haushi su anty nurat da adizat sukayi ba.

Dan tun dawowarsu saga katsina da sukazo musu da tsarabar hidima na musammn sukayo zuga sukazo har sashenta dan su cusa mata baqin ciki da wayo dan dama acike da ita suke kusan kullum.

Anty nurat make sure ta dauko dukkkan clips din Ahmed da yasrah musanm part din dayay trending a IG lokcin daya kamo ta jikinshi suna kallon kwayar idanun juna.. she make sure to read the coments for her loudly da karfi inda taji yadda dumbin mutane sukata gushing akan chemistry dinsu.

Already social media suna daukar ko cewa event na aurensu ne.

Wow this couple are🔥🔥🔥,❤️❤️meant for each other..fairy and her prince .coment kala kala wasu har suna imaging babies dinsu irin dai over hyping na social media din nan.

Tun Adiaha bata so abun ya dameta aranta ba su anty nurat sanda suka kara gishiri da maggi da yaji wa Abun gabaki daya saitaji ta rasa nitsuwarta.

Suka ce mata Ahmed was oll over the girl shine ma yake nanike mata saboda gata young gata kyakkwa,wayayya girman capert wanda arziki ya gama ratsata. Har faking mata situation din sukeyi and as usual cikin raha da wasa mai soka takaici suke cusawa zuciyarta damuwa da baqin ciki mai tsanani suna nuna mata cewa finally Ahmed has met his class ba irinta gajarable ba.

Kowa sai cewa suke sun dace, anty nurat sai dariyar mugunta take mata inta cannko mata wani romantic coment a IG...tunda anty adizat tace Ai dama yarinyar kalar Ahmed kenan yar fara doguwa wayayya ba yar azo muci arziki ba Adiaha tasan da biyu suke mata hakan sai ta fara musu kora da hali.

Saidai all the damage has been done dan shi kishi wani halitta ne ajikin mata, duk sai taji ta rude ta rikice tana son lallai mijinta ya bar duk abunda yakeyi kawai ya dawo..

Hade da lauyin she was feeling uncontrollby insecure shiyasa idan ya kirata sai tay ta masa wasu tambayoyi shikuma abu kadan ne intayi yake bata masa ransa.

Kwana biyu situation din dake shiga tsakaninsu kenan har yazo ya dena bata fuska sosai daga ya kira saiya tambaye lapyar babynsa baiya jan hira da ita sai katse wayar dan shikansa baison tambayar datake masa akan hotonsu da ysran nan.

Bayan hidima sati guda cur sukayi dukansu anan katsina din by then duk sun kammala wata tattaunawa da maganar da zasuyi akan future na yasrah da batun auren Sadik da za'ayi shi acan Abuja..

Shirin komawa lagos tare da hjy khadijatun yasra takeyi dan daga wajenta ne Ahmed zaina zuwa daukarta in lokcin makrnta yayi.

Tsakaninsu iyayen sun riga sun gama tattauna komi shiyasa hjy maiminatu bata missing oppurtunity nayi ma Ahmed duk wata nasiha akan rike zuminci da kare mutuncin kannensu.

Kullum sai ta bashi amanar yasrah wanda kasan kamar yar kwai haka sukeji da ita.

Ranan da zai wuce abuja around 10 am ya shirya ya fito yasaka kananan kaya yay matukar kyau lokcin yasrah na kwance a palon kasa tana kallon tv abunta, bata zata ba taji sallama lokcin dogon gashinta na bude..

Tanajin faduwar gaba da hanzari tamike daga kan kujerar saidai kamin ta tashi ta rufe kanta har ya shigo ciki idonshi ne ya faɗa akanta ido hudu sukayi ta sauke kanta ya lumshesu kamar mai jin bacci tare da galla mata wani harara.

juyawa tayi da sauri zata bar falon taci karo da yaya sadik nan ya tareta cikin sauke ajiyar zucya yace "orange peel whatsup,ke sai kiyi ta sauri kamr ana korinki inata nemanki tin dazu ina kika shiga ne"?.

a takaice tace mishi "ina nan mana ina kallo yaya na kaine dai kawai baka ganni ba"..kafin ya amsa sai taci gaba da tafiya yafara binta har suka kai cikin dakinsu hajiya.

Jim kadan saiga Ahmed din shima ya taho,a bakin kofar dakin ya tarar da sadik har ya kammala mata magana ya juya zai fito nan sukai magana sama sama ya wuce snn shikuma ya bude dakin shima ya shiga ciki, a gaban madubi ya tarar da yasrah tana taje doguwar sumanta, yay sauri ya harde fuskansa ganin bakowa aciki sai ita, cikin dakewa yace "ki dena zamawa mutane a gida kai a bude kina kira musu aljanu ke kenan kullum sai an ganki kai babu dan kwali akanki tsabar rashin sanin ciwon kai?..

idanunta ta juya masa a mugun masiface atake yaji ransa ta kule ai ko juya idanun da tayi yasashi yafixgota har ta kusa fadawa kan jikinshi tukunna tayi maintaining balance dinta ta tsaya tana huci, duk da haka tana jiyo numfashinshi a fuskanta,..ke wai ni saarki ne ni kika harara haka?yana tambayanta fuskarsa daure, yaune karo na farko da tsoro ya sa ta kasa ansashi.

Kiciniyar kwace kanta ta farayi daga rikon da yayi mata idonta taf da ruwan hawaye, dada janyota yayi jikinshi ta fada kan kirjinshi abazata,shiru tayi a jikinshi tana jiyo tsabar bugun zuciyanshi dayakuma razanata.

Shikansa baisan meyakeji alokcin ba dan bai taba experincing irin wnn shocking din dayake ji ajikin kowa ba sai anata jikin inta langwabe sai kuma yaji kmr yanajin tausayinta aransa.

Sun kai kusan minti biyu a haka babu wanda ya motsa daga karshe ta samu ta kwace kanta ajikinsa ta gudu ta shige toilet ta rufe kofar tare da fashewa da kuka ahankli cos she have neva felt like this before im her life,.sai ji take kamar tama tsanesa.

binta yayi da ido ya kai tsawon minti uku yana tsaye daga baya ya juya yyi kwafa ya fice daga dakin mai gabaki daya.

Hayaniyane ya jawo hanklinsa yayo kofar babban palonsun da wurwuri a nan ya tarar da su dukansu tun daga kan hjiya maimunatu da ita kanta mahaifiyarsa hjiya khadija kowa ya fito rakiya wa su anty nafisa da farida da wanda sukzo daukarsu, bayan sun gama gaisawa ya jonasu sukayi musu sallama har suka tafi su hjya sukayi musu fatan komawa gidajensu lafiya bayan hada musu guzuri dayawa da sukayi.

Daga nan kusan dukansu sukayi bankwana nan Ahmed da sadik suka wuce airpot tare da hjiya maimunatu dan itama Abujan zataje aka bar yasrah da hjy khadijatu akan cewa satin suma su zasu wuce lagos bayan sun kammala kimtsawa.

Basu jima da isa Abujan ba hjy maimunatu ta wuce sabuwar office dinta cos she is a woman full of diginity bata wasa da duk wani nauyin al'umma da ake daurawa akanta...

Duk da busy schedules din sadik amma bai hanasa biyo Ahmed har cikin jimada mansion ba duk dama da suka xo ata wajen mahaifinsa suka fi jimawa suna gaisawa dashi.

Alhaji bello duk ya jeme damuwa ya nuna sosai a idanunshi, cos of how lonely and depressed he is living alone a gidan babu kowa, gashi tun da kafayat ta tafi bata amsa wayarsa saitaga dama and he is now feeling ashamed akan abunda yay ma khadijatu the oder night..

Yana son ya kirata koda yaji muryanta sau daya amma tsoron kafayat da na yan uwansa su anty mojushola duk ya hanasa. Alredy akan cikin dake jikin Adiaha ma sunce dan jikar Hjy khadijatu ne yake murna sosai, Baison su cigaba da ce masa yana lashe kafarta ne dan yaga yar uwarta tana da kudi da matsayi.

Sama sama Ahmed ya hada Adiaha da sadik suka gaisa dan sam baiji dadin ganinta ba, cos already cikin ya fara sakata kazanta da yawan lazinesss saita dawo bata son kulawa dakanta tayi kwalliya kullum kmr na da, daga ta kwanta mashak akn kujera da kaya daya shikenan batason canjawa.

Ranar da ya dawo din tun ficewarsu da sadik agidan bata kara ganinsa ba sai dare. Baida wani option haka ya zage ya bata hakkinta na auren sosai acikin dare cos yasan tana bukatar hakan ta more daren sosai.

Bai kuma fasa bata cikakken kulawar dayake bata albarkacin wann cikin nashi dake jikinta ba duk wani aikin wahala baya son tanayi saidai Abunka da wanda ya saba duk sau tanajin kanta kamar a daure.

Wani bin suyi faɗa har suzo su shirya duk dai har akaci wani sati guda agefe yake kkrin yay setting mata business dinta dan yaga duk tafi matsowa da shi.

Friday 5.30am

Cikin wata nitsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan sanyi dayay yake tahowa ahnkli cikin dakinta hannun sa dauke da wata lallausar Sallaya bai tsaya kwankwasa kofar dakinba kai tsaye ya bude ya shigo,da kallo daya yabi kan gadon kusan a yadda ya barta haka ya dawo ya sameta kwance cikin bargo ta lullube jikinta daga kafa har kai tana kan tikan bacci harda minshari.

Day by day she is bcoming soo lazy.

kansa ya girgiza sannan ya dauke hanklinsa daga kanta sai daya fara shimfida abin sallar sannan ya karaso gareta yana mai dofanuwa abakin gadon daf da ita.

Ajiyar xucya ya sauke,Bacin wani kasalallen kallon daya karema jikinta Gefen fiskarta ya shafa da tafin hannun sa mai tsananin laushi sann ya tadata tay alwala.
Chapter 76 · 0% Book details