← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 157

Sashe 71

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya share ya juyota gaban ta yaja drwer sabon syringe taga ya
jawo zai fara hadawa

wani irin bugawa zuciyan ta yayi hannun ta har na karkacewa wajen jawo cup din shayin agigice zata kai bakin ta, nan ya tashi ya dube ta tare da hade rai yace Ah a,Ai na dauka allurn kika zaba
Bata amsa shi ba ta kafe cup din akanta tsuru tsuru tana shan shayi dama ya riga ya fara hucewa so ba gargada ta shanyeshi. Satar kallonta yake Ya tabe baki yace kai i just cant waste my syringe tunda kika sa na bude bari namiki kaawai..

A sulale ta sauke shayin daga bakin ta zata fashe masa da kuka...tuni ya sa yatsu ya mata shhhh quietttt. Yace Baki so ne? Ta gyada kai innoncntly ba don san ranta ba yace amsa ni zaki nayi ..tace kace idan nasha tea ba xakamin Allura..did u enjoy hurting ppl?

Rudely Yace mata yes ki dauki sandwicth dinnan kici idan bahaka ba gaskiya zan yi miki Alluran tunda harna bude. .he sound serious da yake maganan don haka take jin tsoro sosai..

Lokaci guda ta daure ta cije ta shiga cin abincin agaban sa kamar ba ita ba yana lura har wani zufa ke fetsowa agoshin ta...

Yana tsaye har tagama cii tayi kyam da cikinta har da karamin gyatsa
Ya zuba mata ido duk Jira yake ta nitsu tahau gode masa ita kuwa jitake da akan data goden ne gara kawai tayi faking jin fitsari, nan ta shige bathrum tabarsa awajen atsaye, Tsaban dadewar datayi har ya gaji ya bar mata dakin bata fito ba.

******

Tunda daga wann lokcin jikinta ya warware sosai
Amma bata kara barin sunhadu da Ahmed ba sabida bugun zuciyar dake damunta sosai inya kalleta duk ta dauka danshi mugune kawai shiyasa jikinta hala yake rejecting din presence dinsa da alaman bugun
zuciya. Dan izuwa yanzu ko sunansa aka kira sai taji gabanta ya fadi.

Ana washe gari hidima ta jona farida suka fara shiryawa dan anriga da kawo artist din da zata musu kwalliya da komi.

Da sassafe masu shiryasun sukazo domin tsantsara musu kwalliyar da zasuje event din dashi

Mai make up ta kalli yasrah tana murmushi ganin natural beautyn ta dat is striking barinma da babu ko digon spot akan fuskrta.

politely tace 'maamm pls pls wani irin make up kike so ayi miki?

Babu yabo babu fallasa
tace kar amin mai yawa nude kawai nake so wanda baiya nunawa sosai, pls ko foundation bana so a samin just do my brows then liners,nd gloss i just want everything to be nude nd natural,..thank u

Gyada kai artist din tayi tace mata"okay Na gane"

Gashin girarta ta kalla taga acike suke, ta fara gwadawa wao ko za a danyi caving ya bada slim shape, Kai tsaye yasrah tace no A'a batason haka.

Artist din batace komi suka haura can ciki wanka tay ta fara suna zaune suna jiranta lokacin har ankawo musu dukkanin abubuwan da suke bukata domin shiryata lokcin farida har anfara mata a data dayan dakin

agaban sink ta tsaya tare da matse tooth paste ajikin brush ruwa ta kunna snn tahau goge white set of teeth dinta a hnkli har tagama ta kuskura bakinta ta bude goat milk body scrub and gel ta gogga a fuskarta da jikinta after like 10 min tayi bayan yasha tasa duster tay wipping nakan fuskar sannan tabishi da wani haɗaden face mask din turmeric dilka paste which its so yummy gashi ye'llowish in colour kalar ya balain daukar fatar jikinta sosai shima saida yaci 10 min a jikinta snn ta wanke shi snnn ta hada ruwa mai dan dumi tayi wanka ta wanke kointa tafito soo freshh tay fess sosai.

Tana fitowa ta kimtsa jikinta snn aka fara mata kwalliya,wajajen karfe goma daidai suka gama kwalliyar yaci akalla 1hr 20 mins ba acika mata dayawa ba kamar yadda tace amma fa baramin kyau tayi ba dan tamkar wata princess hakanan tafito.Artist din ne tayata saka mata jewries dinta a wuya komi nata brand dayane har da agogonshi sai golden earing da matching bracelet din sarkanta mai kyau dede hannunta. Duk dama an gyara mata gashinta kamar na sarauniya amma batayi gigin jin zata barshi abude ba, turban scarf red color mai dauke da wasu redish crystals aka daura mata akai yy kamar flower cap ga front hair inta da ya fito ya kwanta lub lub yabi sajenta sai ya kara mata wata muguwar kyau mai dauke numfashi sosai.

wani kayataccen murmushi artist din sukata sakarwa dan ba karamin kyau yasrah tayi musu ba. takalminta mai kyau marching colour na kayanta sabuwar sandal heels ne golden colour mai tsini ta saka a kafafunta .

A hankali take takawa kan step akai har ta fito izuwa babbaan falonsu na waje.

Lumshe ido sosai hjy khadjitu tayi snn tace tubarkalllah, Masha Allah dan data ganta duk ta sake baki kamar bata gane ta ba, Tana isowa gareta tana murmushi tace "Autar mama kinyi kyau fa" da murmushinta mai kyau tace "nagode mommy, toh ina su anty nafisa da farida? Nasan dai hajiya ta ta wuce tuntuni daman tace ai bazata jirani ba bakinta sunacan..

Hjy khadijtu tay murmushi tace mata duk sun wuce sadik ne yaje ya ajesu, yasrah tafara jin kamr zatay kuka cikin lallami tace Karki damu my doter, kema yanzun zaki bisu. Nima daga baya zanzo ina jiran wasu ne bana son kuma ki takura acikinmu.

Batace komi ba ta dawo kusa da ita ta zauna alokacin ita kuma wayarta yafara ringing ta dauka tana magana da bakinta na Abuja da zasuzo..

Ta kammala wayar kenan sai ga Ahmed yana saukowa acikin gaggawa jikinsho sanye da wata sky blue getner mai laushi dinki babban riga yay kyau looking real matured sosai kamr bashi ba,hjy khadijatu ta kallesa sai tace Alhamdullhi tazo ta
Gidan sauki ma yasrah ga nan yayanki zai wuce saiku fita atare.

Da sauri ta daga kai tanamai duban ta gefensa duk ta dauka yaya sadik ne yy appearing frm nowher suna haɗe ido da Ahmed ta tsaya cak ganin shima kallonta yakeyi acikin sarkafewan idanu yarasa abunda yake haifar masa da shocking a dukkan ilahirin jikinshi indan ya kalleta.

Bugun zuciyarta daya komayi agaggauce yasaka tayi sauri ta dauke nata idon batace uffan ba ta saukeshi can kasa jin koinanta ma rawa rawa taciki.

Haka kawai taji kamr tace ta fasa tafiya wajen hidiman inhar da shi za'aje.

Yana isowa cikin falon Qamshin turarensa ya gauraye wajen da qamshinsa yana lura da gefen idonsa yadda tabi ta bata rai tabi ta toshe hancinta stylishly da da veil dinta kamr ba son shakar qamshin takeyi ba.

Tana ji sukay magana da hjy khadijatu. Har suka kammala batace masa uffan ba shima baice mata ba yasaka kai ya fita.

Tashi tay da sauri ta koma ciki tareda cewa hjy khadijatu zatay fitsari.

Ahmed Yafi minti 10 a mota yana jiran ganin fitowarta amma sai shiru sanda ya fara danna horn daga waje snn hjy khadija taje har kofar dakin ta buga mata kafin nn ta hakura ta fito Kanta akasa bata bari sun hada ido ba ta bude kofar, hjy na lura da yanaynta ta basar, tace maza Kiyi sauri kije yasrah yana jiranki karki bata masa lokci.

Muryanta a sanyaye Tace toh mummy saikin zo.
Daga nan ta fara tafiya ahankli kamr bazatayi ba cikin nitsuwa hartakai harabar waje.

Tun fitowarta yake satar kallonta daga cikin glass din motarsa, lumsashun idanunsa da suka cike da ruwan takaici sune suka sauka akanta ayayin datake tafiyarta cikin wani irin jan aji mai tafe da nitsuwa da kamiya.

Lullumshe idanunsa yakeyi abzata yafara jin kamr wani iska mai sanyi yana hurashi from nowher ayayin da yakure kyakkwan surar jikinta da haadadden fuskrta da narkakkun idanunsa da kwalliyar da aka mata dats sooooo breathtaking,yadda suman ta yay coils ya kwanta agaba yay luf luf ya dada shagalar da shi, kusan narkewa yakeyi ahankli akan seat din motarsa batare da ya sani ba.

Tana isowa ta gaban motar ta tsaya daga nesa kikam dan batasan wani mota yake ciki ba.

Horn ya danna tare da mata alama da wutar dake gaban motar snn ta taho, nan ma ta tsaya agaban kofar, shiya gaji ya bude lock tayi saurin bude gidan baya zata zauna yabita da wani irin kallo. Ya hade rai yace "ni driverki ne da zaki zauna abaya ina gaba?..ta lumshe ido kafin ta hanklta har ya sauko dakansa yazo ya bude mata gaban motar tareda turata ciki harsanda ta zauna snn ya rufe motar suka kama hanya.

Acikin wata Babban jeep na landcruiser maiji da lpya ya dauƙesu izuwa inda hidiman hajiya yake gudana. Banda sautin wakar oumo sangare babu abunda ke tashi, dan Tafiyar kurame sukayi har suka isa wajen event din dan tsakaninsu saidai satar kallon juna.

Wajen ya bala'in cikawa da jama'arsu dan haka aka dauki lokci wajen shirya musu wajen parking da security checks .

Tana Allah Allah ta sauka ta shiga ciki Shikuma a lokcin ne wayarsa ta hau ringing ya dauka yafara amsawa Batare da yy unlocking kofar ba.

Basu wani dade da isa harabar hotel din ba sai gasu hjy khadijatu da bakinta na Abuja sun iso haka nan duk aka dakatar da kowa domin basu hanyar shiga ciki.

Lokacin ne Ahmed ya kammala wayar dayakeyi daga asibitin har sai bayan hayaniya ya dan lafa snn ya bude lock din motar yasra ta bude ta sauka kasa tanajan tsaki acikin wuyarta da takaicin yadda ya ajeta ciki for no reason.

Adan dole kawai take binshi abaya abaya sabida iyanzu shine kawai ta sani gashi batason wani hayaniya duba da yadda kowa ya zuba musu ido kamr sune kadai mutanen da sukayi kyau awajen.
Chapter 71 · 0% Book details