← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 157

Sashe 101

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Samu datay cewa babu kowa acikin gidan sai ita yasata dada jin karfin gwiwar aiwatar da abun da take son aiwatarwa.

Kwana tafarayi tanamai cigaba da dabbaka tsafinta domin kuwa inhar wann na farkon yay aiki shikenan Adiaha da haihuwa kuma sai har bayan ta fice a gidan Ahmed..

Tunda ta dawo bata fice ko ina ba tana cikin main mansion din tana baza gwaramarta aciki da wani irin farin kaya take kasancewa dare da rana amma babu wanda ya san da hakan duba da duk matayen gidan ba zuwa kusa da ita sukeyi ba..

After 3 more days wanda ya kasance yaune su Ahmed suke cika 6 days agarin ibadan tareda mahaifinsu alhaj bello..

A bangaren Adiaha kuwa tasha mamaki matuka daya kasance tun ranar da kafayat din ta dawo gidan shikenan kuma kominta ya dawo normal domin kuwa yau kwananta uku kenan batay bleeding ko wani ciwon mara ba.

Ana washe gari su Ahmad zasu dawo Da tsananin farincikin hakan ta farka ta shiga shirye shiryen tarbansa tuna irin alkwarun dayayi mata tasan kuma baya saba alkwari, duk suna gidan dan ko yasrah ma bataje schll dinsu yau ba sabida ciwon ciki na period daya dan kwantar da ita agida time to time haka Adiaha tana lekowa tana dubata.

wani bin intaga wahalar da yasrah take sha Aranta tana son taga takaita asibiti just to be nice for once amma zumudin jiran ganin Ahmed bazai kyaleta ta fita ko ina ba.

Haka yasrah tayita murkususunta a dakinta har ta gaji tay bacci, Har sai can da yamma kafin nan komi ya lafa mata wanka tay da ruwan dumi snn taji dan dama dama tana fitowa ta samu wayarta yanata ringing daukawarta keda wuya taga maryama ne

Zama tay kafin nan ta amsa wayar suka gaisa.

Maryam tace mata tazo cikin anguwarsun ne anata birthday partyn faisal daya daga cikin big boys acikin abokan fahad shine zata wuce tace bari ta zo dubata da jiki.

Babu wani jaaa yasrah tay mata kwatancen kofar gidan kafin ta gama shirya kanta kuwa saigata nan harta iso.

Wajajen 6 saura na yamma saiga maryam din, Koda tay sallama a kofar palon Adiaha ce ta amsa mata suka gaisa snn ta gaya mata cewa yasrahn tazo nema.

Iso tay mata izuwa ciki tana ta kalle kallen uban hidiman da Adiaha tay na tarban mijinta nan tay mata jagora harta shiga room din yasrah ta sameta a zauna bakin gado ita kadai tana daddana wayarta a hannu.

Sosai yasrah taji dadin ganinta, hirar schl suka fara kadan kafin nan ta fara bata labarin birthday din and all the fun..

Abun ya bata mamaki dataji ance fahad baije wajen birthday din ba...

Shashantar da hirar yasrah tay suka cigaba da kawo tadin karatunsu dake gaba wanda hakan ne yasaka maryam tay saurin cewa zata wuce gida dan tagama lura da cewa yasrah ba yar son wann harkan holewar bace ita kanta tana yawan jinjina ma irin kasaitarta.

Duk yadda yasrah taki ta rakata amma haka tafi fir tace mata lallai saidai tabita ta waje kodan tay xcising kafafunta.

doguwar Riga da wando ne na turkish material marar nauyi ajikin yasrah sai tay rolling da veil dinsa sun fito kenan suka ci karo da Adiaha tana zaune har tagama cancarewa da Ado..

Yasrah ta kalleta tace
"Anty bazan raka kawata zata tafi.

Da fara'a Adiaha tace mata no problems, sann tace ma maryam din sun gode da ziyara.

Daga nan suka fice ta bisu da kallo..

Har kusan bakin titi Maryam ta dingajan ta sunata hirarsu na shirme har aka fara kirar sallahn magrib basu dena surutu ba.

Adiaha na zaune a falonta taji an danna door bell har wani firgita tay tsabar zumudin tarban mijinta dake dawainiya da ita,
Wani lumshe ido tay snn ta miƙe agugurje ta isa baqin kofar da tunanin cewa Ahmed dinta ne ya dawo dan yace mata suna hanya tun dazu wanda tasan inhar jirgi zasubi baifi suyi awa guda ba but har yanzu da hakurinta yafara gazawa.

Da zumudinta ta isa bakin kofar tanamai sauke wasu kayatacun murmushi tana budewa suka haɗe ido da wani mutum nadaban wanda atake murmushin fuskarta ya dauke cak....
[7/12, 7:55 PM] SURAYYAHMS: Tsayuwar cak Adiaha tay a bakin kofar batare da ta motsa ko tace wani abu ba ganin bata taɓa ganin wann halittar arayuwarta ba,kyakkwa ne dogo fari mai kyan jiki na bugawa jarida daga ganinsa tasan dan gidan masu shine sabida yadda hutu ya gama ratsashi ta ko ta ina.

murmushin sa mai matukar sanyi tare da tafiyarwa yake sakar mata yay mata sallama, cikin sanyin muryansa mai tafe da aji, ta amsa cikin gyara tsayuwarta daga bakin door din snn tace"How can i help u pls"?

Muryansa mai sanyi ya miƙa hannu yana sosa gefen kunnensa kadan snn cewa My name is fahad,..kallon shi take still yace "fahad shagari. pls Nan ne gidan su yasrah hussain?Adiaha tay smirks tare da maida masa gentle gesture din snn tace masa yes!! "Daga ina? ..

Yace daga schll..

Wayarsa mai tsada idonta yafada kai ayayin da ya rike yanamai cewa nakirata bata daukar wayanta kuma da akwai muhimmnin sakon danake son na bata hannu da hannu.

Adiaha tace ohhh..
Cikin mind dinta already tafara concluding cewa hala saurayin yasrahn ne na schl, which makes her curious cos daman tana son hakan ya kasance ace yasraha tana da saurayi dan finally tasan cewa mijinta is saved.

Tace mishi Toh shigo ciki mana.

Fahad yana murmushi yace noo thanks basai na shiga ciki ba,yamma yay already intana nan ace mata ta fito pls ina son naganta. Cikin katse shi tace no pblm, pls ka shigo ciki kawai mana are u not her friend?wai baka san bata da lafiya ba ko?

Yace "nasani." But dis is very important shiyasa nake son ta karba da hannunta,if not bcos she is not picking my calls i wont be here ma, yana maganan da wani file a hannunsa.

Tace to shikenan anma zanso ka shigo din kawai sai inyaso kaganta aciki, with the way she is insisting sai ya amsa mata da toh dan baisan meyasa ta dage sai ya shigo cikin ba.

Tana tafe yana binta a baya, kallo daya yay ma falon duka snn ya dauke idonsa. Cike da rawan kai taja shi har bakin kofar dakin yasrahn tana murmushi Tace mishi.
"I am her aunt.

Ya tsaya anan yace "nice!!So where is she?

Kofar ta nuna mishi nan
Mamaki ya fara rufeshi
Sounding normal Tace Ka shiga ciki zaka ganta aciki.

Atake Fahad yace nooo maam, im sorry i can't.

Tace oh why not meyasa arent u her speacial friend?

Yace i am but..did she Allow ppl into her room? Bare ma koma yaya ne ni bazan shiga ciki ba, aikan ya miƙa mata acikin envolepe yace ga aikan kawai ki miƙa mata ni zan koma daga nan tunda ke aunt dinta ne..

Yana mika mata ta basar tare da cewa No way..ai nice nace maka ka shiga ko?Just take it to her urself pls, zaiy maganq cikin katse sa tace cmon this is my house inda akwai wani matsala da zan gaya maka. Abundai bai kwanta ma Fahad aransa ba amma haka tay ta insisting wai saidai ya shiga ciki.

Karshe dai da kyar ya amince snn ta bude masa kofar ya shiga ya zauna akan couch yay shiru ganin babu kowa nan tace masa ya jirata tana zuwa in a short while.

Fitar ta keda wuya yafara duba agogonsa da yanayin matsuwa akan fuskansa cos he is not comfortable being in yasrah's bedroom dan duk iskancin shi haka kawai yaji abun bai kwanta masa ba.

Can Dayaji abun bai masa ba kawai yay deciding ya fito ya fice abunshi, ya miƙe tsaye kenan zai fice sai ga kofar ya budu ahankli yasran ne ta shigo suna hade ido ta tsorata taja da baya mamakin ganin fahad a tsakar dakinta ya daskarar da ita tay ta kallonsa batace mishi uffan ba.

Kai tsaye ya karaso ta wajenta kafin ya budi baki yay mata magana cikin katse shi da mmki a muryanta tace "fahad? And How comes ure in my room who let u in?

A rude tay maganan ganin yanzun nan ta wuce Adiaha a falo har suka yi magana amma bata gaya mata komi game da hakan ba.

Ajiyar zuciya ya sauke cikin yanayin fargaba snn yace "i met ur aunt..cike da mamaki tace my aunt? Yace yes and... just forget it.!!! anywys, na kiraki baki dagawa kuma its urgent shiyasa nazo har gidanku...

Adan rude yasrah tace snn Aunt din nawa ce tace maka ka shigo har nan cikin dakina? Wtf!!!

Yace yeah yeah and she is the one dat insisted not me,..sai bai karasa gayan sauran labarin ba kawai yace Anyways aikan ki kawai na kawo miki, im in a hurry, pls make sure u go trou it dats inhar kina son kiyi passing wnn course din with top grades kmr yadda kike cewa.

Yana fada ya mika mata envelope din wanda text book ne aciki da wasu refernce na law daya dauko daga libry na babban court a Abuja.

Ta fannin Adiaha kuwa kafin nan data tura fahad cikin dakin yasrah dawo wa tay falonta ta zauna tanamai cigaba da jiran mijinta hnklinta kwance, anan tana zama baifi da minti 5 ba sai ga nan
Yasrahn ta shigo.

Normally ta tarbeta tace sister har kin raka kawarkin kenan?

Yasrah tace mata eh anty
Daga nan room dinta ta wuce direct Adiaha tanata kallonta harta wuce room dintan bata ce mata komi gameda zuwan fahad ba.

Tasan yanzu Ahmed zai iya shigowa so Aranta so kawai take taga tay igniting wani magana na saurayi akan yasrah dan ta gama gane pure intention din Ahmed akan yarinyar sabida yadda taga yake yawan over reacting akanta musmmn ma a makarnta

Kwana biyun da yay tafiya ibadan sosai ta zo ta fahimce cewa kamr yasrahn sosai tafi ta muhimmaci agaresa.

Tasan inyazo yaga Fahad is eida yay fushi yay ma yasrah fada agabanta ko kuma yay mata bayanin alakarsu acikin sauki kowa ya gane matsayin sa agidan dan haryau ji take ajikinta kamr yasrah tana samun kulawa da hanklin Ahmd fiye da ita.
Chapter 101 · 0% Book details