← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 157

Sashe 134

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin haushin tambayar taji batace mai uffan ba, Kai ta gyada ba tare da ta kallesa ba ta harde ranta sosai, yace " no answers?hmm Gud, kinsan dai babba agidan nan baya girki, is eida u eat from me or you fend for urself, matata dai bazatana miki komi yanzu ba sabida kema matace agidan, Jin bata ce komai ba yasaka ya duka kusa da ita har tana iya jiyo numfashin sa da kamshin turarensa da ya cikata, cikin kaushin murya yace "kin fahimta?" Kai ta gyada masa tana kkrin mayar da hawayen idonta, ya juya ya fice daga dakin taja tsaki mai kauri....
[7/25, 9:15 AM] SURAYYAHMS: Koda ya fice mata a dakin saida yay kusan dakikanin sekanni biyar awajen bai iya bude lumsashun idanunsa daya runtse su da karfi ba,Washe gari da safe Sanye da farar jallabiya plain original na saudi wanda babu ko design ajiki ya fito da shike ba komawa bacci yakeyi bayan ya idar da sallah ba sai chan wajen 7am ya mike gaba daya. He has planed his ways well wa duka gaba dayan su yasan yadda yake shirin tafiyar da su agidan.

Sosai yasaka rai wajen shawo hanklin yasrah musmmn ma dayaga tana cikin yanayi na tsananin fushi dasu baki daya. Saidai bai wani damu sosai ba aganin sa ai mata duk abu dayane, halittu ne masu tsananin rauni musmmn inya duba lamarin yadda haryau soyayyarsa ne yake controling rayuwar kafayat da kuma Adiaha, gani yake kmr itama zatazo ta gaji da borin ta dena fushi dashi indan wai akan zaman aure dashine.

Don haka baiyi yun kurin soma shiga dakin Adiaha ba ya kamo hanyar dakin yasrahn da sanin cewa ita yarinyace dole ne kawai ya dan kame mata fuska donkar ya sake mata tazo ta rainashi agidan sosai.

Yana turo kofar hancin sa yayi bugu da sassanyr qamshi mai tada hankali saidai Gani yay Tana kwance Ga hijabin ta anan gefe alaman tayi sallah ne ta koma.

Gefen gadon data ke Kwancen ya zauna ya mugun shagala wajen kallon very pretty face dinta tana bacci a tsanake Sai yanzu ya lura da yadda fuskarta ya haura dan kuwa kadan ya rage kumburin idonta ya rufe masa ganin ta gaba daya....

Ahankli Ya tabe baki ya sake karamar smirk tare da tapping din gefen gado sau biyu bata tashi ba ya sa hannu ya yaye comforter nan ta mike adan razane tare da bude kasalallun idanun ta akanshi wanda suke cike da tsanarsa ayanzu..

Wani irin Bugu kirjin ta yayi da suka hade ido taga ya kureta da wani irin piecing looks kamr tsohon maye, yace ai sai ki tashi safiya yayi...kin ma cin abincin naki na juya kuwa? Tayi saurin dauke kai ranta a harde batace mai komi ba.

Ji take dan bata masa hauka bane akan auren shi yasa yake neman ya kure mata hanklinta yake shigo mata daki anyhow.

Shiru yay yana kallonta Jin tayi banza da shi ya daga kafadunsa sama yace ok tashi zakiyi kiyi abunda ya dace dake ba bacci ba, this is ur first day, and U have alots to do cos my wife won't do anything for you kema kin sani al'adarsu ce amaryace mai girki a ranar farko kema kinga Daga yanzu U will cook for me, lclean and take care of the house and
Anything else, as my wife...ai sun gaya maki ko?

Wani irin shaukin kuka ne ya taso mata amma sai tayi shiru batayi ba don tasan tana amsawa kukan zai kufce mata kuma harga Allah ta soma jin tsananin haushin maganan dayake mata a yanzu..

Itadai bazata iya dena jin takaicin jin cewa wai shine ya aureta ba don kuwa ko a mafarki bata tabajin sha'awar auren namijin da baisan darajar matarsa irinsa. She have double standard for her life, saidai aynzu ji take kamar duk wani mafarkin ta ya rushe akanshi.

Gashi A zahiri tsoron auren ma ya mugun shiga ranta yana birkita mata tunani dan baatay tsamanin zuwansa ba kwata kwata, hannu ya kawo zai jawota ,ta buge hannun ta kara tantame ranta tana hararsa.
Yadan daure fuska yace
"Ke ni wai sa'anki ne da zakina bugeni?

Cikin katse shi da sigar fushi sosai ayanayinta tace can you pls let me be, cos ure really suffocating me.

Ya hada rai Yace suffocate? what do u mean by dat?

Tace Toh me kakeyi anan dahar zakazo kana mun wasu maganganu Nifa ba matar kace. Dan wallhy inma ji kake ka aureni kasaka aranka cewa dani da budurwa duk dayace agidan nan dan har abada ni yasrah bazan kasance matar namiji irinka ba.

Juyawa yay yanata kallonta ganin wai hawaye sun fara zubo mata acikin idanunta.

Yace What is wrong with u, meyasa kike cewa haka? Ai abunda zai faru ya riga ya faru Kina jayayyar da qaddarar da Allah ya zaɓa maki ne?

Tace "Allah ne ma ya zaɓa min ko? Eh aje haka na amince, da kuma dan girman iyayena amma kasani wallh baka da wata hakkin zamowa miji agareni har Abada muddin ina gidan nan sabida bana sonka bana kaunar kasancewa matar ka.

Magana zaiyi ta runtse ido tace if u really dont want me to disrespect u just get out.

Yadda ta karashe idonta a rufe kuma cikin tsawa yasaka shi mikewa tsaye babu shiri yanata kallonta seeing how serious she looks jikinta harna rawa rawa tana ta hawaye sosai.

Kinada hankli kuwa wai bakisan kin wuce wann stage din bane ayanzu? Ure no longer a child, ure my wife now, u better get dat cos duk yadda kikayi hakane zai cigaba da kasancewa a tsakanin mu.

Tace fita ai nace kayi..
Bana son ganinka na tsaneka...duk kaine ka jawomin, aida cewa zakayi baka son auren kaima, amma meyasa kayi shiru kana ganin aka likamin kai?

Yadda maganan nata ya daka tsalle ya cakkeshi aransa yake kan shan mamaki cos no girl has ever told him dat an liƙa masa ita.

Matsowa kusa da ita yay zai taɓa ta tamike tsaye cikin tsananin kyarman jiki da kuma fushi..

Magana yake mata amma ba kulashi takeyi ba,gani tay baida niyarr fice mata a dakin ta juya zata fita kenan ya wani irin fixgota tana juyawa kuwa ta kifa masa wata hatsallen mari akan fuskarsa abazata.

I said im not ur wife..ka fice min a dakina ina gaya maka. Just let me be.

Kallonta yay muryansa karsashe yace yasrah kika daga hannunki kika mare ni?..

Tsaki mai kauri taja tay banza dashi, yanajin yadda take huci tana fidda kananan magana tanamai cewa ta tsanesa.

Zamewa yay ya bar mata dakin bai kara dawowa ba itama bata fito waje ba.

Yauma A dakinta ta wuni har bayan ishai banda Adiaha datake kawo mata ziyara time to time wanda itama ba kulata takeyi ba.

tara nayi na dare ta nemi waje ta kwanta abunta sai a sann ya kara zagowa dubata, hangota yay tana bacci hankalinta kwance cikin bargo, ya tsaya daga nn bakin kofar yana kallonta da mamakin yadda ta sauya gabaki daya, bai taba sanin wasu matan suna da zafin zuciya har haka ba, can yyi wata karamar murmushi ya gyada kansa alamar zaki gane kurenki snn ya karaso cikin sabuwar bathroom dintan.

wanka yayi anan din ya fito daure da towel a kugunsa yanadan goge gashin kansa da karamar towel,bude sabuwar wardrobe dinsun yyi ya ciro sabon sleepn robe dinsa fari ya saka ajikinshi, wayarsa dake gaban madubi ya shiga kara ya karasa gaban madubin yana kallon screen din wayar ganin kirar mahaifiyar sa ce

karan da wayar dayakey din ne ya farkar da yasrah ta bude fuskarta a hankali tana kallonsa, yana tsaye gaban madubin yana amsa wayar har ya katse snn ya kashe wayar gaba daya.

Nan ta maida kanta cikin bargo da sauri tana mai jan tsaki,she tot after the slap bazai kara kulata ba marar zuciya gashi har ya wani dawo, bargo babba ya dauko cikin wardrobe din ya shimfida a kasa dan baison su karayin wata rigima da ita ayau akan wajen kwanciya.

snn ya karasata daya side din da take kwance ya dauki pillow ya ajiye kan bargon snn ya kashe musu wutan dakin ya kunna bedside lamp.

Sai a sann ta dan bude ido yaga yaje fridge ya dawo da ruwa ya kuma xaunawa gefen gadon ya dafe kansa kmr mai raya wani abu aransa.

Sai tsaki takeja aranta wanda tasan ba lallaine ace baijinta ba, saidai dake ta cikin bargo take bata damu ba, don wutan dakin na da duhu, juyawa taga yyi yana kallonta, nn da nn gabanta yyi mugun faduwa ta rumtse ido da sauri tay lamo ita kadai, ya dade yana kallonta daga karshe ta ga ya mike ya sauka kasa inda ya aje bargon ya kwanta kan bargon da ya shimfida nn kasan, sai a snn hnklinta ya kwanta.

Wani shiru ne ya ratsa room din, tana nn kwance har kusan karfe daya na dare bacci ya ki zuwa mata ta mike zaune a hankali tanata tunanin rayuwarta da duk irin haushin da takeji data kasance matar Ahmed.

Ita gani take kamar babu wani agidan wanda ya san asalin boyayyar halinshi dayake ma matarsa Adiaha har ynzu.

she canr forget all his hurtful and embrassing word, she just cant erase the numerous domestic violence, duk wani wahalar da Adiaha tasha a hannunshi da wanda take kan sha aynzu gani tay dan ya sameta a banza ne cikin sauki shiyasa baisan darajar mata ba itakam bazataa taba amincewa ayi hakan da ita ba.
.
gani tay ya juya ma gadon baya,hanyar waje ta kalla xuciyarta na raya mata cewa ta gudu a gidan koma ta sauya daki izuwa nata na dacan.

mikewa tayi a hankali ta cire bargon jikinta da hijab ta sakko kan gadon ta isa gun kofa din ta bude taji shi a rufe, ta bude baki da mmki to meye na wani rufe kofa.

Ahankli ta lalubi wayarta ta samu,dauka daya tayi ta danna sai ga haske, kofa din ta nufa da wayarta hannunta tana haskawa ta ga ashe key din na wajen.

budewa tayi snn ta jawo kofar a hankali, duk wnn abinda take batasan yana na kallonta ba, tana murda kofar taji an wani daka mata tsawa "keee"
Chapter 134 · 0% Book details