← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 157

Sashe 43

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan aka samo wata yar karama anty ramoutu tay bayanin inda za'a kaisu dan wajen yana da nisa sosai shiyasa ma suka dauki shatar motar gabaki daya,wani hanya suka dosa a can ta cikin garin lafiya adan wani karamin kauye mai nisan tafiya sosai wanda mafi yawancin mutanen wajen kabilune suka taru suka yada zango.

Tsabar tafiyar da sukayi harsaida yafarajin kamar sayar dashi zasuje yi tun karfe bakwai basu kai destination dinsu ba sai wajajen azhr, nan ma suka hau neman abinci sukaci snn aka kama musu layin ganin malamin da sukazo wajensa.

Manyan mutane sai shige da fice sukeyi a zauren gidan, anty moju tace masa ai malamin kankat ne duk wani shedanincin mutum bazai iya ja dashi ba.

Hakanan suka zauna sunata jira kafin nan layi yaxo kansu ga wayoyin su kaf babu service....
[6/14, 9:11 PM] SURAYYAHMS: Ata fannin Adiaha kuwa har sai bayan fitar Ahmed snn ta kimtsa gidan tay tsaf irin yadda taga sister zainab tayi, ko ina ta lailaye shi sann tay hadadden breakfast makanta taci tanajin wani irin nitsuwa da kwanciyar hankli bayan nan ne tay wanka taci kwalliya sann ta zabi wata hadaddiyar abaya daga cikin sabbin kayanta ta saka dake maroon colour ne komin ta to march tayi.

List din abubuwan da bata dashi wanda sister zainab ta sata rubutawa ajiyan shi ta dauka ta jefa acikin jakarta snn ta kama hanya ta fita da tunanin inda zata fara zuwa.

Cikin sa'a kuwa harsai da ta bar gidan kafin nan Anty adizat tazo dakanta dubata, samu tay wajen a kulle cikin jin tsananin haushi ta koma sashen anty nurat suka ci gaba da kulla makircinsu da tunanin cewa sune zasu cinye kudin da Aka bawa Adiaha na siyan kayan sawa.

Bank direct Adiaha taje tayi seting pin ta amshe credit card dinta snn ta zuba 150k ma kakarta a acct kyauta, dan kadan ta kara akan wanda Ahmed ya bata da safe sauran kuma ta zubasu duka a sabon acct dinta.

Tasha wahala sosai kafin nan ta gana fahimtar cikin ƙasuwanin Abuja inda tay dukkan wani siyayyr tata datake bukata,wajajen karfe biyu na rana ta dawo gidan da kaya lodi lodi lokcin daf anty nurat tana shigowa gidan kenan bayan ta dauko yaranta daga makarnta. Tun saukarta a adedeta take kare ma kayan jikinta kallo har ixuwa kan takalmin data saka banda ma ire iren abubuwan dataga ta sissiyo, wani bakin kishine ya rufe mata ido hartana gani duhu duhu agabanta wanda shi yasaka ko kyale yaranta batayi sun sauko kasa domin taya adiaha kwashe kayanta izuwa cikin gidanba.

Mai gadinsu ne yake tayata yana kaimata har bakin kofar bangarensu yana ajiye mata. Manyan manyan shoping bags ta shigo dashi na abinci da kayan kawata gidanta da irin abubuwan da bata dashi da wanda zata karasu domin su isheta itama.

Can dai anty nurat din ta daure ta sauko, yaranta kaf suka hau gaishe da Adiaha da fararta sosai ta amsasu tare da basu tsarabar oranges da ta kakkawo kowa ta amsa tana murna sosai. Sama sama anty nurat ta amsa mata gaisuwarta dan tsabar leken kayan data shigo dasu din datakeyi duk hanklinta ya tashi tana son tasan menene acikin manyan ledojin nan da Adiaha ta shigo dasu bayan sunyi da anty adizat akan cewa sune zasu rudeta sucinye kudin. Ajikin motar ta ta tsaya cikin tunani mai zurfi zuciyanta na mata wani irin zafi.

Adiaha tana sallaman mai adedeta tazo ta wuceta batare da tace mata uffan ba tay nata bangaren dukansu sukabi bayanta da kallo

Da gefen ido Ta kalli yaranta tace musu suje ciki tana zuwa, yaran suna kama hanya itama ta bar wajen jiki na bari kar kar tanufi sashen anty adizat tafara buga mata kofa karfi, arikice anty adizat ta fito tana cewa lpya? Hannunta ta riko sukayi waje dan kowani tsayawa tay mata kyakkwan bayani batayi ba ta sakota agaba akan tazo taje ta gani da idonta, acewarta Da alaman Adiaha har taje kasuwa ta kashe kudinta duka..anty adizat duk bata wani Yadda ba sabida ta riga ta san kalan rashin wayon Adiaha.

Adiaha tana shiga ciki ta barbaja kayan a falo snn ta wuce ciki da niyyar watsa ruwa domin tay alwala tay sallah snn tazo ta nemi abinci.

Sosai ta gaji dan hatta miscalls din kakarta ma ba daukawa tay ba tsabar tana Allah Allah ta dawo gida. Tana shiga bathrum ta fara jin kara ata waje kamar ana buga mata kofarta, hakan ne yasakata yin gaggawa ta kammala wankan ta fito a hanzarce. Ta zo ta samesu abakin kofarta sunkime duk sun hada rai suna kumbura fuska kamar zasu fashe ganin ta da towel din ne yasa sukadan rusuna fuskarsu.

"Ashe wanka kike munata buga kofa bakiji ba."..

Babu yabo babu fallasa tace eh anty nurat
..fatan lapiya?

Anty nurat ta harareta cikin tune din jin haushi tace Allow us in mana sai kace wasu barayi zaki tsare mu awaje ba tambaya .

Matsa musu a kofar tay batare da tace komi ba suka shigo ciki suka tsatsaya kowacce tana karewa wajen tanadi da idanunta. Ganin komi tsaf tsaf..

Adiaha tace "Zanje na dan kimtsa ina zuwa"..

Suka gyada mata kai duk suna Allah Allah ta shiga ciki dan suyi gulma tana kuwa bada baya kuwa suka hau tattaba kayan dake zube a tsakiyar falon suna dubawa daya bayan daya.

Gulma suka farayi da yarensu kamar wanda aka aikosu kowacce tana fadan albarkacin bakinta.

Adiaha kuwa bata fito ba har saida tay sallah ta shirya tsaf ta sako wani sabon kayan english wear amma mermaid gown ne purple colour mai shape sosai snn ta fito tana zuba gamshi mai azaban dadi wanda daga ji kasan turare mai tsada ne.

Koda suka kalleta duk saida suka kasa iya haɗiye kishinsu bata wani kulasu ba suka zauna pretending to do nothing, tafara gaishe su acikin nitsuwa.

Anty adizat tafara kawo mata maganan kudin kayan, anty nurat ma ta tsoma baki suka dinga zuba mata karairaye suna nuna mata irin zasu yi rebranding dinta da kaya masu kyau kyau har saita fi kowaccensu haduwa. Duk bayanin su
Tay shiru tanaji dan maganganun sister zainab bakaramin shiga brain dinta yay ba musmamn ma dataga alaman da biyu suke mata maganan duk suna nuna mata cewa irin sun raina ma ajinta ita local ce batasan kan kwalliya da gaye ba saisu.

Itama sake baki tay ta zuba musu karyan tace musu ai kudin bai shiga hannunta ba tukuna, iya na cefane kawai ya bata shiyasa ma taje kasuwa ta siyo abubuwan da bata da shi. Batako ji nauyin su ba ta bubude musu kaya suka gagga abunda ta siyo a kasuwa tsabar gulma sune suka tayata shirya wasu food stuff din a kitchen dinta da sauran ababen da ta siyo takai room dinta wanda basu samu daman shiga har ciki ba.

Sunsha mamakinta kwarai dasukaga irin original kayan amfanin gida data sissiya, cos she look daft kalar marasa wayo sai dai kuwa sosai ta iya harkan siyayyan harma fiye dasu she is bold like a typical calabar girl with alot of businesss spirit kamr wata inyamura ,Duk da ta burge su aransu amma ba hakan bane ya hanasu mata habaici tare da gasa mata bakaken maganganu masu zafi acikin raha da wasa.

Cewar anty adizat duk wann iya cinikayyar nata a gidan miji zara kare a matsayin matar kullle sai abunda aka bata kmr almajira har miji zaai zo ya gaji da bani bani, snn babu alaman samun aiki babu wata sana'a hatta tsohuwar wayarta saida tay mata habaici akai, duk ta fada mata hakan in a mocking gesture

Anty nurat kuma tay mata habaici tana cewa ai duk wankan da zatayi agidan jimada bazata taba zamowa daidai dasu ba sabida su in sunyi wanka basa shiga adedeta sahu saidai su tuka motocinsu na kansu. Adiaha duk bata san da cewa cigabanta ne yake kuntata masu aransu suke kusheta ba ta dauka duk raini da habaici ne daga garesu wanda suka saba yaɓa mata wanda bazai taɓa karewa awajensu ba.

Ranta sai yadan sosu kadan tafarajin haushin su aranta itama dan tun ficewarsu a sashen take tuna zancensu a brain dinta ji kawai take yakamata ta fara gogaggaya dasu dan sugane kuransu akanta sosai.

Wayarta ta dauka ta kira sisterr zainab suka gaisa cikin raha, tasan sister zainba yar qa'ida ce ta tsani mace mai depending akan idea din wasu, dan haka bata fito fili ta tambayeta ba a cikin salo ta nemi shawararta akan telolin da suka dace takai musu dinkin kayanta dan itama so take tafara wankan leshuna da atampopi dan su anty nurat sugane cewa basukadai ne sukasan yadda ake kwalliya a duniya ba.

Sister zainab ta tura mata IG page din good tailors harda lambobin wayarsu, snn ta haɗata da asalin tailor nata wanda ko anty nurat din ma tayi tayi ahada ta shi sister zainab taki sam.

Da ta hada Adiahar dashi saida taja mata kunne sosai, duk dama bata fayyace mata shiwaye bane, shima haka, kawai ce masa tayi tunda ita zata bar zama a Abuja ga nan sabuwar customer nan ta kawo masa yay make sure yana mata dinki masu kyau kamar yadda yake mata itama.

Adiaha taji dadi bana kadan ba tay ma sister zainab godiya bayan nan tafara harhada sabbin kayan datake so ta dinka din a leda da niyyar gobe inta fita sai takai masa da kanta har Adress din daya bata.

Wajajen bayan asr bayan ta kammala gyara gidan ta ta ciro sabon bedshet mai kyau data siyo ta lailaye kan gadon mijinta dashi snn ta feshe gidan gabaki daya da room freshners masu gamshin dadi da ta siyo koina ya dau zuba kamshin dadi.

Bayan nan zama tay a falonta tana hutawa sai anan ne ta kira kakarta hjya hajarat suka fara gaisawa cikin kewa duk ta damu tana son sanin irin zaman datakeyi tare da mijinta dan haryau hanklinta bai kwanta akan auren nasu ba.

Murmushi Adiaha takeyi cikin zakuwa da zumudi tahau bata labarin duk yadda takejin dadin zama tare da Ahmed dinta a yanzu,..

Komi da ya siya mata saida ta fadawa kakarta
Chapter 43 · 0% Book details