← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 157

Sashe 40

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cike da bushe idanunta tace yess oo, iyawo dami Ure wicked , Anan kika min munafurci kika saka damilare yaje ya daki sulu agabana kamr zai kashe shi, snn ya hada ma mijina karya akaina.

Haaaa Reema kin bani mamaki oo, bazan boye maki ba inajin haushi naki..duk dariya da muke miki agidan nan baki gani kin rufa mana asiri ba kinje kin gayama dami karya cewa ni ina kiranki housegirl, and nurat tana zaginki...toh inde munafurci zakiyi mana agidan nan zaki sha wuya oo, saikin dawo kamar kafaya kowa zaizo ya tsaneki ki shiga uku.

Ure just tooo lucky i am not heartless like you, ni adizat Inada imani a zuciya na, shiyasa nake son ma na taimake ki in tayaki zaban kayan sawa
Masu chau chau Or dont u want to be a goood fashionista like nurat?

Cikeda sanyin fuska Adiaha tace am sorry anty adizat, nifa bance masa komi ba fa i swear..

Da harara tabita tana cewa "Ahhhh pls shut up basai kin min wani bayani ba oo, just answer me bakison ki dawo kinasaka kaya masu kyau kamar nurat ne?

Adiaha tace inaso anty...amma ai Ahmed ya.. cikin katseta its Okay
Ki manta da zancen Dami shina namiji yasan kan kayan mata a ina ne? Let me tell u bayan kafaya ma damilare baiyi wata budurwa ba...see why am telling u dis is sabida nasan zai baki kudi ki saya kaya anjima, idan ya baki ki, saiki kawomin kudin duka duka,nine zan je na siyo maki latest kaya masu chai chau irin laces din nan na can lagos gangariya irinna nurat.

Tana cikin zuba mata karya cikin salon yaudara can sai ga karar bude babban gate dinsu motar sister zainab ne ya shigo ciki yau batazo da yaronta ba. zuba kawai anty adizat takeyi ido a rufe munafurci ya gama yin gaba da tunaninta har bata lura da shigowar motar sister zainab gidan ba.

Ita kuwa Tun shigowarta ciki ta soma jin zancen da anty adizat takey ma Adiaha na batun kudin kaya Sai tay kamar bataji ba harta karaso ciki.

Anty Adizat tana hangota ta yanke maganan cak tay shiru ta tsime kamr batacewa komi awajen.

Sister zainab tana isowa da murmushi akan fuska Tace anty adizat whatsup, kilode na? Menene kike gayawa "Reema the saviour.."
..tafada tana dariya.

Adiaha ta dan rusuna kai ta gaisheta ta amsa mata da fara' a sosai

"How are u my darling reema, I hope Damilare is around?

A ladabce Adiaha Tace no sister baya nan yanzun nan ya fita, Cikin katsesu tun kafin adiaha tay barambarama Anty adizat Tace tazo rakoshi kenan ai shine naganta anan kinsan Amarya da ango love one tin tin.

Cikin kyabe baki Anty zaynab tace Abi oo yarinya kici zamaninki kema, aikowama yaci zamanin sa..ask anty adizat kiji a lokacin nata amarcin har kuka takeyi idan brother kazim zai fita aiki,hahahaha haha anywys i dont blame her my brother dey give her woto woto in d nite why she no go follow him cry inzai tafi.

Anty adizat tace "Ure really shameless zainab Ahhh..im not dat type abeg. Ni namiji baya gaba na. Duk wai tana fada ne danjan aji da kuma dankar Adiaha ta rainata.

Sister zainab ta fashe da dariyar mugunta Ta dafa kafadunta cikin neman tsokana "ahh adizat kikace baki damu da namiiji ba?Aurenki bai kusa karewa agidan nan lkcin da Brother yace zai fara aiki da companynsa a U.S ba? Duk makwabta nan saida sukasan cewa ke harija ce.

Harara mai zafi Anty adizat ta watsa mata zainab pls kidena wann magana haka ya isa mana..

Ure just ashame baki son kowa yaji, but reema is part of us now..ko na fada ko ban fada ba, wata rana zata zo ta sani cewa bura na brother kazim wnn, shine yake kafaki acikin gidan nan 100% sauran feelings din kuma kudinshi ne.

Ran Anty adizat a hargitse da kunya da takaici tace zainab wht is dis now pls stop it, bana son wann maganan banza fa.

Dariya ta karayi mata ganin ta kufula sosai tace "To kidena cikamana baki mana, anyway magana ya kare, reema darling zo muje wajen mumy pls.

Harzata jawo hannunta su wuce anty adizat tay saurin tsaresu tana cewa a'aa, reema bamu gama maganan mu bafa.

Sister ta dube su duka kamr wacce bata saan komi ba tace wani magana ne kunayi haka?

cikin katseta da masifa anty Adizat tace Babu ruwanki acikin maganan nan zainab, and Reema pls dont tell anybody oo wann tsakani na dake ne. "E get why..

Sister zainab tace inyeee oshey head of women associations of jimada house. Toh ki dai aje maganan naki agefe kijira ta zamuje tare da reema tukuna inta dawo saiki cigaba.

A kufule anty adizat tace
"Dont forget ooo.
Kina dawowa kizo ki nemi ni..is for ur own good oo.

Aladance Adiaha tace yess anty.

Daganan Janta ciki sister zainab tay sukaje har wajen hjy khadijatu suka gaisheta anan takejin yadda sister zainab take gayawa hjya cewa na da kwana uku zasuyi tafiya zasuje London tare da mijinta zasuyi wata uku acan, snn idan sun dawo kuma zasu tare acan garin su mijin acikin oyo state bazasu dawo Abuja nan kusa ba harsaidai angansu kawai.

Jikin hajy duk yay sanyi jin zasu rabu da zainab amma hakanan ta daure tay mata fatan alheri snn tace mata toh ba matsala Allah ya kaimu lokci.

Daga nan suka fice ita da Adiaha sukaje bangaren baban nasu suka samo yanata shan shayi babu wani abincin kirkin dayaci banda neman lambar kafayat babu abunda yakeyi tunda yazauna a falonsa.

Duk ya rasa inda ta shiga ga zaman kadaice na damunsa sosai yana son yaganta kusa dashi kodama bazasu zauna cikin aminci ba. He is sad and lonely at the same time ya rasa abunda ke masa dadi.

Sallamarsu sister zainab din ne ya katsesa nan ya zuba musu ido har dukan su suka taho suka rusuna suka gaishesa acikin girmamawa ya saka musu albarka snn sister zainab tay masa bayani yadda tay wa hjy khadijatu.

Amsata kawai yay amma duk bayajin dadi aransa musmmn ma yadda suke fifita hjy khadijatu sama dashi yanzu dan ya lura ko gaisuwa ne saisunje sun gaisheta kafin nan suke zuwa wajensa, snn inba acikin mutane ba basa sake fuskarsuda shi haryanzu. Duk da aynzu basa shiga tashin hankli saidai hanklinsa ba akwance take ba ba.

Duk tsakaninsa da yaransa daya ruguje yafi damunsa, da can sune abokan shawara da kuma hiransa amma yanzu babu mai sake masa fuska kowa sama sama yake kulasa daga gaisuwa, saidan kuma ya aika akirasu dan ayi wata magana amma duk sun ajeshi acikin kwandon shara.

Bayan ficewarsu sister zainab awajenshi nan frustration din kafayat hade da na yaransan yasakashi agaba yarasa samun sukuni sai yay wanka ya fice agidan ya nufi gidan yan uwansa su anty mojushola inda yasan zai iya kai musu duk wata damuwarsa snn su sauraresa.

Sashen Adiaha suka shigo sister zainab ta nemi waje ta zauna Kafin nan Adiaha ta shiga kitchen din ta dafa mata jollof din spagheti da sardines ta hado mata tea mai kauri.

Kafin kace wani abu harta kammala ta kawo mata, a falon suka zauna tare sun kunna tv kowa nacin nashi,nan ne tafara tsokanarta akan kayan dataga ta saka ajikinta.

Tace hmm sai yanzu kin gaji da gorin da ake miki kinje kin saya kaya mai chau abi, i tot ure foolish bazaki tabayi wayo ba ai, Dats very good for u oo, im impressed with ir dressing today, gashi kin iya siyan kaya mai kyau kyau, dan wayann mata agidan nan sai sun kasheki wata rana da bakin gulmansu inbaki saka kaya kina burga.

Adiaha tay gyaran murya tana murmushi mai sanyi tace its all thanks to my husband sister. Shine ya siyamin kayan jiya.

Sister zainab ta dago kai tana murmushi tace ohhh really? Inye hhhhh ai Na dauka ai kin ji jikine da gori shine kikaje kika saya kayan sawa na dole, Anyways congrats dear.

Cike da jin dadin reaction dinta Adiiaha tace thank u sister.

Cikin katseta tace ehen menene anty adizat take fada maki dazu?Dami ya baki kudine?..dazu ina jinta tana miki gulma wai wanne kayane take cewa zata siya maki, ahhhh dont believe her oo, tana da karya, zata cuceki batasan kan kaya ba oo duk nurat ne mai siya musu sabida tana da business a lagos na kaya. Karki bawa adizat kudinki oo.

Cikin sauke ajiyar zuciya Adiaha ta gaya mata duk abunda sukayi.

Sister zainab tahau girgiza kai da alaman tausayawa tace reema ure just too foolish..wato ke baki san idan mutum yanajin kishinki ba? Daga wani kauye ne kika fito ne? Ke ba mace ba ne? bazaki budi baki ki mata magana sosai tajiki ba.

Meyasa baki gaya mata cewa kema kin iya siyen kayan sawa ba. Aidama kince mata mijinki ya siya maki kayanki, tell her dat u dont need her help now and in the future.

Kinganni ina zuwa anan gidan tare dasu duk nasan halinsu oo, ki raba kanki dasu reema.

concentrate on urself oo
Da suna sonki da sun baki kaya a lokcin da baki da shi, amma basu rufa maki asiri ba sai yanzu da sukaga kema kin fara zamowa irinsu? Ki sharesu, suna jin kishine..inhar zakiji shawara na bazaki fada acikin trap dinsu ba. Cutar ki kawai zasuyi.

Adiaha tay shiru cikin tagumi har sister zainab ta kammala yimata surutu cikin wayar mata dakai akansu anty adizat alokci guda..

Bata wani boye mata komi ba duk dan haryau tana jin sonta aranta musammn ma data ceto rayuwar danta daga mutuwa sai batajin zata iya cutar da ita ko ta bari wasu su cutar da ita..

Zuwan sister zainab sosai yay ma adiaha amfani dan kuwa ta koya mata wayon zaman da su anty adizat daki daki cikin salon da zata fahimta.
Chapter 40 · 0% Book details