← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 157

Sashe 53

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tace au bakason hirar yar uwankan kenan ko?
yy murmushi yace "wata rana ma hala nime zan na baki hirarta since you wont be having too much time for us..dariya tay kadan snn ta sauke ajiyan zuciya batace komi ba sai can tace dik inda uwa take yaran ta sune makale acikin xuciyarta kodani ko babu ni wata rana zaku rayu tare dukanku awaje guda har abada in Allah ya so

Yace hakane amma i wont let dat slide kafata kfarki a lagos...

Dariya tay tace dama nasan zaka ce hakan ai,
Amma karka damu ba kayi aure ba? All this obessesion with mumy zaizo ya ragu, yace a'a nidai, babu wata macen da takaiminke har abada mamy na,Aure changes nothing mmy, cos ure still the priceless queen in every coner and space of my heart. Dariya tay tanamai masa kallon sha
shasha, while duk aransa dagaske yake fada dan haryau dai shi dan abi yarima asha kiɗa ne baijin son wata mace acan cikin kololuwar ransa kamar mamansa.

Sun jima suna hira kafin nan sukayi sallama ya koma bangarensa yaje ya tarda jarabar Adiaha na jiransa dan tun da ya dawo shikenan kuma aka lular dashi wata duniyar na daban yaudai duk dan a burgesa ake bashi jiki yanaci back to back..
[6/17, 10:34 PM] SURAYYAHMS: Turkey 6.30 pm

P cap dinsa fara mai zanen tambarin arewa ta gaba wanda ya kusan rufe kyakkyawan halittar sa mai dauke numfashin duk abunda yayi tozali da shi Jikin sa a gine take da kwarjini da hutu ba fari tas bane amma arabian milk mai dauke da madaidaicim lips wanda ya soma yin pitchy-pink,..shima suman kansa tamkar na jariri yake baka wuluk dashi har tana neman kwanciya dakan ta yayi masa saje luf luf a fuskan sa wacce ta sha gyara tubarkallah.

Sanye da designers shirt fara kat da bakar wando na companyn whitehorse los angeles

Shiru yayi bayan ya rage volume din karatun qur'ani dayake ji yana dube dube dai dai setin kwanar shiga makaken mansion din su.

Kaiwa nan ya buga horn ba tare da bata kokaci ba aka bude ya lume cikin wata hamshakiyar gida data ji komai da komai na duniya Kai tsaye Wajen Jerin cars ya ajiye nasa sannan ya zaga baya ya dauko wata karamar gift bag guda biyu ya sa kai zuwa cikin gida

Bayan minti biyar mai aiki ta biyo sa da karamar trolley dinsa.

Ko da ya shiga gidan bai wuce ko ena ba sai shashin sa Tsaf ya kimtsa kansa ya sauya zuwa white armless mai kyau ya dan jeme suman kansa ya kame shi kadan abaya kamr na yan kwallo Sannan ya kuma feshe kansa gaba daya da mild perfume mai sanyin kamshi ya fito..

Zaune hajiya maimunatu take rike da kofin shayi tana kallon News channel ana kan haskaa lamarin shariar siyasan tsohon shugaban kasan America wato donald trump duk hanklinta na wajen gabaki daya.

Kallon ya tsayayi Wani faffadan murmushi ne ta kufce masa bazata kamr kullum Don a duniya duk lokacin daya ganta haka hankalinta akwance farinciki ne kawai yake mamaye zuciyar sa na musamman, Bata hankara ba taji saukan bakin sa a gefen kuncin ta.

Adan farge ta jiyo Da murmushi ta damko hannusa sa suna haɗe ido tace Sadik?

Rungumarta tay yana mai cewa mummy

Shafa kansa tay cikin jin
Dadi sosai tace Alhmdullhi Ka dawo kenan! Yanzu nagama zancen ka araina dan albarka Welcome home my pride. Tafada tana mikewa tsaye cikin tsananin farin ciki tana taba fuskansa dayake kama danata zak zak dan yafoi kamani da fulanin fiye da yaren babansa.

Dauke da Faffadan Murmushi kan fuskan ta tace ya hanya toh?
Tell me all about the meeting naji ance kayi bala'in kokari wajen represnting dina.

Dariya ya fashe da shi sanda white teeth dinsa suka bayyana sannan ya zaunar da ita nan ya kwantar da kansa kafafun ta ya cigaba da yin dariyr sa hankali kwance...

Hannu ta sa tana dan shafa kansa tana murmushi sosai tasan duk farin cikin ganin ta ke damunsa..duk ya kasa magana sabida yay kewar ta aransa sosai.

A nitse ta sunkuya saitin kansa ta kure sa da ido "awwwn? Yau kuma ka dawo mumy boy ne 'wannan wani irin sakalci ne hakan?

Yace...'Ohh sakalci ma zakice ko mumy?cikin muryan shagwaba ya fada Shima yana facing din ta..Tace "to idan ba sakarci ba kato da kai old enough ka bani jika ynzu kana sakani aranka sosai krm dan 4yrs idan nazo na mutu muku fa

Yace...shhhhh mummy
Bana son jin haka.

Tace To me ye ne? Tell me ko gajiya ne?,ta fada tana duban sa.

ko ya kula shikam
Dada lume kansa yayi kan cinyar ta idon sa alumshe a hankali yace
Yace i missed mumy"
Kar ki taba rabuwa da ni kinji?Wallhy bazan iya rayuwata ba in babu ke ba..ina ga Zan..

sai ya kasa karshewa muryan sa ya soma rawa'
Shiru ne ya ratsa wajen yayin da ta cigaba da sassaita sa tana shafa suman kansa a hankali ba tare da tace uffan ba
Itama daurewa tayi sosai din tasan meya ke nufi dan shikadaine yasan health condition dinta na (ciwon zuciya)heart disease.

Sam Baya so ya sake dandana zafin rashi a rayuwar sa kmr yadda ya rasa babansa.

Tace Auta na ka tashi min nikam zaka karya min tsofafin kafafuwa ta ba fa makai na ajiye ba
Wann na Jikoki na ne..tayi maganan cikin wasa don ta kawar da yanayin su a lokacin

Kamr an tsakure shi ya mike zumbut Yace too in ba jikan fa.

Dan zungurin sa tayi tace
Watanni nawa ne yay saura Har Allah Allah nake mu koma nigeria kaima acan ne zamuyi shagalin naka biki Abuja

shiru yayi baice komai ba dan matar da zai aurar ma basu wani gama sabawa da juna ba amma har anyi fixing musu rananr aure,

wata kyakkwan yarinya ce yar gidan wani babban nigerian politician kuma business patner na hjy maimunatu ne dake zama Abujan wanda sune sukayi ruwa da tsaki wajen tsayawarta a kan kujerar data samu aynzu. Auren hadi zata masa but already yay accepting hakan with no objection saboda azaban son dayake mata.

Da sauri ya sa hannunsa cikin nata ya rike. Tace Good ..muje ka ci abinci don tun tuni nake jiran ka

Yace No ammy .na koshi

Tace Meyasa? Kai
Bana son sakalci fa, kaji min iyeyi tashi muje inga guri..Zaman diris yayi agabanta ya make kafadun sa "Im not going untill u promise me one thing. Tace ikon Allah sadik Ehen go ahead ena jin ka juyawa yayi gwuwar sa na kasa kusa da ita yace mummy zan yi duk wani abunda kike so a duniyan nan just promise me dat zakina kulawa da health dinki ko bana nan kusa dake

Serious face din daya sa ne ya so ya bata dariya tace "i promise"Oya tashi muje saikafa ci abincin nan, Allah shi zai bar wanda ya ga dama kar ka damu kaji?

Bai saKe cewa komai ba ya bi bayan ta Suka nufi dininng Cikin so da kulawa ta sa shi ya cinye abincin sa tas bisa kan tsari kafin suka dawo palour suna taba hirar su

Suna zama basu wani jima ba mumy ina yasrah take ne bangan ta ba tunda na shigo

Tace Uhm kawar ta jasmine ne tazo ne shyasa bazaka ganta ba,

Ya hade rai yace Ok suna dakinta kenan?

Tace No .kafin tay bayani cikin katseta yace What

Tace Sun fita nace maka ..na dauka ai ka gansu don basu wani jima da ficewar bama

Ya takune fiskansa 'haba mummy amma kinsan na hana ta wannan yawon tsiyar ko to meyasa kika barta ta fita?

Tace Ahh kaji min dan nan,yo ita kenan kullum daki sai kace sabuwar amarya? Da sannu na nace taje tasha iska Kaga ni bana son draman ku nan kar kuma ka taba min ran yarinya na kaji.. lallabata nakeyi nima.

Ya kalleta mum kinsan yanayin nigeria is not friendly at all, toh yaushe har yasrah zataje tai adopting da halayyarsu na can bazafa taje can tana fita da yamma da abokanta ba.

Cikin katse shi tace toh inama zataga abokan yawo bayan nayi mata miji acan..

Mum kinki kifada min waye ne mijin yasrahn, i hope ba wani dan gidan business partner dinki bane, kema dakanki ai kinsan illan haka ga ya mace.

Dariyar manya tay tace lallai yaro yaro ne..
Sadik a tunaninka saina bada auren yasra ma wani bare bayan ganan na gida baici ya koshi ba.

Just trust me nasan mena keyi karka damu sanin kanka ne bazan cutar da rayuwar kowa acikinku ba..amma yasra kam nayi mata miji ko bana duniya zanso ka cikamin wnn burin nawa.

Shiru yayi baice uffan ba don ji yake kamr yayi iska
Ya tsamo ta daga duk inda taje yanzu dan baison yawonta da dare barinma dayasan anan turkey dinma bawai tsira tay daga hannun samari ba.

Har kusan 7.30pm
Suna zaune da ita a falon
Nan ya tashi ya tallafa mata zuwa sashin ta ya kammala mata komai da komai kamar yadda kullum ya saba. Sannan ya mata sai da safe ya sauko falo abunsa.
"
Can abun bai masa ba ya tashi ya nufi massallaci daganan ya yi tsayuwar sa a farfajiyan gidan yana jiran yar kanwar tasa ta shigo

Armed driver dinta ne ya tuko ta ciki tun daga can kofa tayi Suman tsaye tana kare masa kallo daga nesa yayin da suke shigowa Suman Kanshi sai sheki yake hannun sa dauke da tasaddaen classy phone dinsa yana latsawa hankli kwance

Dagowa yayi jin Kamr ana kallon sa Charaf suka hade ido da ita da mugun gudu tazo ta faɗa ajikinshi ta kankamesa sosai shima ya rikota kamar bashine ya gama kufuluwa da ficewar nata ba.

Fuska ba yabo ba fallasa
Yace My little orange peel? Tana murmushi sosai tace "im soo hapy ure back yaya na nakaina

rikota yay yana cewa wai yaushe na bar nan n dakika kara girma hakan
a kunyace ta rufe ta idonta a sanyaye tace
"Dont start yaya.

Yace toh..ya gida ?fatana kina lpya right?..

Ta girgiza kanta alaman a'a hannunshi taja suka zauna akan chair tace yaya, i have millions of things to tell u.
Chapter 53 · 0% Book details