← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 157

Sashe 147

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sama da kashi 50 na rayuwar namiji tana ga harkokinsa ne na waje, yayin da sama da kashi 50 na rayuwar mace tana ga harkokinta ne na cikin gida, ko da kuwa ma’aikaciya ce. A nan, ‘Yar uwata, kina buqatar dan zaburowa da cicciba matsayinki. Saboda ki san yadda mijinki yake rayuwa a harkokinsa na waje. Ba fa ina nufin ki yi binciken sirrorinsa ko neme-nemen matansa ba, No! Wato nufina ki san sana’arsa ko kasuwancinsa, ko aikinsa da wasu harkokinsa da ba zai damu ki sani ba. Ki yi qoqari ki san ababe da dama game wadannan. Idan kika sani, sai ki zama abokiyar hirarsa a kai. Ki sa shi jin cewa, kin yi wa harkarsa sanin da dolensa ya buqaci shawararki ko ya yi hira da ke a kai. Da zarar kin samu wannan matsayi, to, kin gama mallake mijinki, amma fa da sharadin kina inganta ciki da shimfidar can, yes!

Snn tace
Yar uwata, soyayyar nan da kike gani wacce ke ba kya gajiya da ita a zubin halittar dabi’arki, wallahi gundurar namiji take yi.

Maza da yawa sun sha yi wa matansu tsaki, ko gwasale, wasu ma har banka wa matan ashar yayin da suka kira su da tsakar rana don su nuna ko su furta mu su kalaman qauna. Saboda a lokacin, ba abin da ke gaban mazan ke nan ba.

Haka abin yake a wani zubin idan miji ya dawo gida. Wai ba ki lura cewa in mijinki ya ga abokansa ya fi sakin jiki da su a hira a kanki ba? Ai ba wai don yana fifita su a kanki ba ne, a’a sam, sai domin kawai hirar da abokan za su yi masa ke ba za ki yi kwatankwacinta ba. To don me ke ma ba za ki koyi hirar ba ‘yar uwata?

Wasu mata sukan ji cewa, ba su da wata hira da za su yi da mazajensu wacce ta wuce qorafin abin da babu a gida da qorafin rashin lafiyar wani ahalin gida da hirar iyayenta da ‘yan uwanta da qawayenta. Ba ruwanta da halin da mijinta yake ciki bare ta yi hira da shi a kai. Irin wannan hali ke sa maza fita waje hira da wasu abokai, wasu ma har su dade a can, daga nan har su hadu da wasu matan da za su qwace miki miji kina ji kina gani. Irin wannan hali ke sa maza fita harkar mata a cikin gida, ko tasa talbijin da kallo ko waya da chatting.

_Surayyahms tace_
‘Yar uwata, rashin koyon ilimin rayuwar harkokin mijinki na waje, da rashin nuna kwadaituwa a kai, gazawa ce babba daga bangarenki. Don Allah ki gyara!.

Yasrah tay shiru sosai ta zuba idanuwanta akan screen dinta tanata karantawa daki daki tare da kallon maganganun nasu dataji suna ratsata sosai...kusan yau din ma gabaki daya nazarin maganganun nan tay kamun ta gaji tay bacci.

Bayan kwana biyu laulayin Adiaha ya fara tsanantawa sosai ta dawo bata iya wasu abubuwan kawai taƙura kanta takeyi da azaba wajen ganin salonta na iya bautawa soyayya da kuma zakewa wajen daɓbaka lamarin mijinta da baisan tanayi ba ya bata wani sabuwar matsayi.

Saidai wnn karon wayar da kakarta take dan mata yanadan taimaka mata dake yanzu ta dawo nigeria sukanyi waya kusan kullum kafin Ahmed ya dawo ahankli har kakan nata ta fahimce abunda take ciki.

Koda laulayin yafara mata yawa sosai kuma taga mijinsu Ahmed babu ruwansa hanklinsa ma ayanzu naga kan samun yasrah ne sai taji aranta kamr tafara gajiya da kkri saidai kuma naciya da dumbin yarda datay makanta na cewa wann salon nata ne kadai zai iya bata sabuwar daraja da matsayi wanda yasaka bata iya nazari mai zurfi akai kwata kwata.

Kullum kakarta takan so ta ja hanklinta amma ina bata fahintar metake cewa.

Acikin satin nan Koda yasrah ta kammala shanye dukkn wasu zakwalan kalamai da hikiman dake cikin dumbin lectures din marubuciya surayyahms ahakli Adiaha ta soma ganin sauyi mai rikitarwa atattare da ita.

Sai taga kmr dukkn wasu abubuwan nuna so da kyaytawa datake ma Ahmed din sam baya bawa yasrahn sha'awa.

Taga komi zatay da nata salon na daban mai mugun daukar hankli take fitarwa.

Wani irin tsantsar kasaita da kuma kamuwar kai da wani irin sanyayyar halayyar shawagaba da Yasran take fitowa dasu sarari bakaramin gigita Ahmed din nasu yakeyi ba.

Dake yanzu tana dan fama da laulayi har mijin nasu ya gano sai tuni yasrahn tafara saka mata hannu a wasu abubuwan aikin gida datake daukawa akanta duk dama haryau aranta sam batason barin mata tanayinsu harsai taga abun yafi karfinta ko inshi Ahmed din ya bata rai ya hana.

Adiaha ta kasa samun nitsuwa ta kuma daburce musammn dataga yasrahn ma ta fara fidda nata salon acikin hkiima da kuma wayewa kwarai dagske.

Sosai salon yasrah ya fara caza mata kai duba da yadda mijin nasu yake over reacting in total opposite da yadda tasanshi all her life.

She had no idea na cewa Halin yaran nan is very important sai dai ba koyaushe taga yasrahn takeyi ba gudun raini kada ace baiwar Allah nan bata da wayo.

wani lokacin haka zataga yasrah tazama masa very firece and classy, wani lokacin very smart bata nuna wautarta a fili

Snn brave bata yawan nuna tana tsoronsa, koda wani abun tashin hankali da riikici ya faru sai taga yasrahn ta jure tayi haquri ta furta kalman tawakkali.

sai wani salo datagani daya dameta shine inda kwana biyun yasrah take taking charge when it comes to decision making even wajen al’amarin neman iliminta bata yin masa wasa.

sai an dade sai taga tana masa yar shagwabar nan yace watau duk haduwar yarinyar nanntana da rauni da take buqatar kulawa ta.

Haka tana kallonsu yasrah zatayo masa laifi kiri kiri snn ta tuma ta fashe masa da kuka sai yayi lallashinta jikinshi na rawa yana kwantar da wuya, badon komi ba saidan sabida taki mayar da kanta kamar wata sokuwa ko kamr namiji da ke jira azo suyi dambe ko yana fada tana fada tana daga murya kamar qato dan uwan sa.

Ko gabansu anty adizat haka in anfito a tsakar gidan ana gaisawa sosai adiaha tasoma lura da yadda yasrah take murza kambunta akan mijinsu Ahmed.

Bazata zataga tayi yar tsallenta na dagangan cikin salon kama aji da shagwaba ta manne masa, kota maqaleshi tace sai ya mata wani romantic silly abu kafin nan ya wuce office, haka nan kunya zata kama shi ya kasa sauketa kasa, ko ya kasa magana, snn sai tay abun shagwabr sai ta wuce abunta ta barsa da jin nauyi da kunyarsu.

Duk wani aikin rainin wayo dayasaba saka Adiaha tanayi masa kamr baiwarsa itakam batay masa ta cikin sauki batare da ta ladabtar dashi ba.

Kai hatta dauko remote ko su tsallake waje haka duk nunawa da qyar take iyawa a gaban sa, takan nuna ne bata iya daukan abubuwa masu nauyi ba.

Tunda Yasrah ta fara fidda wayann kasaitatun salon shikenan kuma zuciyar Adiaha ya fara shiga wani muguwar mayuwacun hali na tsananin tsoro da fargaba.

Dan kuwa kamr kiftawa da bismillah ta rasa gane inane take shin a duniya take ko a lahira, shin ko mafarki take ko a gaske, domin gani takeyi kamar batama san waye Ahmd ba kwata kwata.

She still cant belive dat dukkan wani salonta na so da biyayya da kokarinta na nuna masa tsantar maitanso marar ganin aibu da kuma dumbin sadaukarwarta agareshi amma wai a tashi daya akan wata ƴa mace Ahmed dinta ya zamo tamkar sabuwar mutumin da bata taɓa saninshi a duniyarta ba.

Tana fama cikin laulayi amma Agaban idanunta take kallon yadda salo da kuma Dabiaun yasrhn ya sauya mata Ahmed ya dawo wani mutumin da batasanshi ba kwata kwata.

Dukkan wani Abunda tay tsammanin bai iya ba, kuma bazai taɓayi ma wata mace ba, ko baima san dashi ba, da wanda ya san dashi din ma cikin kwanakin nan saida taganshi ido da ido yanaywa yasrah harma da qari.

Wann tarin rikitaccen anxietyn tare da dumbin mamakin Ahmed da kuma rugujewa tare da rushewar tunani dataci karo dasu a kwalwarta yasaka taji atake komi ya cirke mata, kullum acikin question kwakrlta takeyi tanamai tambayar kanta

*what really went wrong da nata irin salon?*

Dan kuwa ta so Ahmed matukar so.

Ta kuma nuna masa soyayyarta matukar nunawa.

Ta sadaukar masa da kanta harda kimarta na ƴa mace.

Ta dorasa sama da Iyayenta,da Ahalinta, da kabilarta da kuma Addininta snn ta biyoshi har inda yake.

So What can be more greater than this?

Wasnt this enough for her to get him kamr yadda yasra ta sameshi cikin sauki kuma acikin kankanin lokaci ta gigitashi yadawo baya iya gane komi sai salonta.

Meyasa ita nata salon bai janyo matashi har haka ba? Meyasa sai wanda take ja masa aji take bi dashi da wuya yake nuna zaucewarsa akanta..meyasa yasrah ce take da dumbin ƙima da daraja a idanunsa ba ita ba? Meyasa yasra ce matar sa ta tarairaya ita kuma marainiyar wayon sa uwar jakunansa maicin ko wani irin kashin sa?

Wayannn dumbin tambayoyi da kuma damuwar ta zubawa ranta haryafara taɓa mata zuciyarta kullum saitay tunani akai tanamai kara tuhumar kanta dasu.

Bayan sati uku lokcin cikin ana daf da za'a karkare case din Alhaj bello jikinta ya tsananta ganan kafayat ma tanata kkrnta agafe wajen ganin ta buga wasarta akansu saidai ayanzu hanklin Adiahar ya kaso kashi uku ne sabida damuwar da salon yasrah ya cusa mata. Batama iya kulawa dakanta sosai tsabar yadda ta maida hnklinta akan yasra tanamai lura dasu, dan kuwa yanzu ne kishin mijinta yafara asalin gigita yanamai taɓa mata zuciya da kwakwalr musm ma wajen ganin sauyawar da Ahmed din yay akan yasrhn ya fara wuce karfin nazarinta da tunaninta.

Tun tana amfani da boyayyr salon makirci na son rabasu wajen samun shakuwa ko wata alakar aure har abun ya fara nunawa a dabiarta na karara.

Yasrah kuma dagangan take biye mata sabida tagama lura sa cewa is not alwys easy mace kmr Adiaha datake mutuwar son mijinta ta bawa mijin nata goyon baya dari bisa dari batare da na ciki na ciki ba.
Chapter 147 · 0% Book details