← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 157

Sashe 28

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A rikice hjy ta kamo hanyar waje saidai tsinkewar da sister zainab tay ta danna ihu yasaka duk ta birkice itama dan kuwa yaron nan shine mata kwalli daya dan tun haihuwarta na fari aka cire mata mahaifa sabida wani hatsarin datayi tun tana amarya.

Tun da taga danta ahaka tafara samun sudden panic attacks da tunanin ko mutuwa zaiyi ya barta ta shiga uku da rayuwar da babu haihuwa aciki, Lokaci guda ta rasa hanklinta wani irin ihu da Birgima tafarayi akasa tana kiran Allah ya cece ta yasaka yaronta yay rai badon halinta ba

Hajy khadijatu dake sauri sauri zatayi waje da shi bata iya motsawa ba sabida tsoron ganin halin da zainb din ta shiga ciki a lokaci guda na birkicewa da tsorata da jimami mai tsanani.

Acikin bacci kafayat ta tsinkayo ihun da zainab din takeyi sanda ta farka ta kwashe da wani irin mahaukacyar dariya kafin nan ta fara tashin alaji bello bacci tafara pretending kanta na ciwo sai yamutsa masa fuska takeyi tanajan tsaki, fuskarta a kumbure kmr batasan meke faruwa ba tace masa tanajin kara karan hayaniya ata waje snn karan zai hanata bacci dan haka yaje ya duba mata waye ne yake musu ihu acikin gida da sassafe yasakashi yay shiru dan tanason tay baccin safe..

Ta dinga masa masifa kamr danta haka har ya sauka daga kan gadon

Da gigin bacci a idanunshi amma hakannan ya hakura ya diro harsaida ya watsake snn ya tsinkayo muryan yarsa zainb tana wani irin kururuwa tana ihu cikin kuka..

My child..my child..pls wake up my child, na shiga uku..i dont want to go childlesss..

Lokaci guda yan uwanta kaf suka cike wajen suka mamayesu kowa jikinshi yahau rawa rawa ganin yadda shafiun ya wani sandare ga jini na yoyo a hanci ga kumfa ata baki.

Alhaj bello na fitowa shima yaji ya razana da ganin yanayin yaro amma dake kafayat ta biyosa abaya nan sai ta fara masa zugi acikin habaici tanamai ce masa gangancin zainab din ne ya jawo komi.

Su anty adizat duk sun rirrike sister zainab shikuma sai ya fara zagin ta yanamai mata masifa da cewa taurin kanta ne ya jawo mata gashi zata yi rashin danta kwaya daya.

Maganganunsa dana matarsan yana yi wa su hjy khadijatu da sauran yayunta zafi amma haka sukayi shiru sunamai rarrashinta dan karta cusa damuwa sosai aranta najin cewa itace ta jawo halinda danta yake ciki kmr yadda babanta da kafayat suke ta memetawa

Ahmed ne ya karbe yaron acikin gaggawa ya kwantar dashi dake shi likita ne tuni ya fara dubashi acikin gaggawa kafin dakyar yaron yake numfashi, idanunsa sunyi wani rammmmm kamar wanda zai wula lahira cikinshi na famar kumbura yanamasa ciwo bana wasa ba.

The boy is in serious pain sai murkususu yake aban atausaya mashi

Ahmed yay iyayinshi dan ya sama masa relieve sai can snn yace sukaishi asibiti kawai sabida ya gano cewa case din poison ne kuma zai iyayi ma brain din yaron illa nan da minti 7 idan har ba'a samu taimakon gaggawa ba.

Abun shaƙar numfashi ya jona masa akan hanci dan yana taimakonsa wajen maintaing counsiouness dinsa.

Tunda Ahmed ya fayyace musu komi sister zainab tafara yankar jiki tana fadi kasa tana suma ana zuba mata ruwa da fifita,

Ahmed ya fita a sashen agurguje yaje bangaren sa ya dauko wayarsa dake daki domin ya kira nearest hospital store wanda zasu kawo masa taimakon gaggawa na oxygen da detoxifier wanda zai tsare illar poison din daga shiga kwakwakr yaron tun kafin su isa asibiti akan lokci sabida muddin suka fita da shi ahaka batare da wani kwakkwaran support ba hala ba lallaine yay rai ba.

farkawan sister zainab na karshe sai a idanun mijinta,duk aka rasa waye ya kirashi, dan arikice sosai ya fantsalo, yana zuwa yana kallon yanayin dansa sai ya dada firgita ya fado kasa tumus cikin yanayin ragwabewa dan kuwa ya shaku da yaronsa bana wasa ba shima.

Emotional attachment dayake da shi akan dansa yasaka ya birkice yafara zage zage yana daura ma sister zainab laifi yafarayi kmr zai sharara mata mari agaban iyayenta.

Cikin borin masifa Ya dinga ce mata dama ai saida yace mata kartazo gida tay mishi taurin kai tazo toh gashi nan yaronsa zaiy biya bashin taurin kanta.

Su kafayat kuwa anan ne aka samu shiga ta fara zuga alaji bello yanamai bin bayan mijin sister zainab din.

Nan suka dinga zagin ta na cewa tazo wargaza auren mahaifinta gashi har zata rasa danta akan aikin banza.

Sai kuka takeyi kamr ranta zai fita alkcin ma bata cikin hayyacinta tsabar razanan dake dawainiya da ita. She just dont want to loose her only child..

She was soo confused as to ya akayi yaronta ya gamu da poison har haka, a ina? Meyaci?
Dan Tasan iya ruwa kawai tabashi yasha da safen nan ko abinci basuci ba bare tace Ko Adiaha ce ko kuma kafayat suka saka ma danta magani acikin abinci.

Mijin nata har yay rantsuwa cewa inhar dansa ya mutu zai rabu da ita na har abada.

Hjy khadijatu ne take ta kkrin calming din situation din amma ina duk wajen ya rikice kowa na fadin albarkacin bakinsa ayayinda ake jiran Ahmed ya dawo cikin gaggawa.

Ata fannin Adiaha kuwa Tun Ahmed yana dubashi ta rusa da gudu tajeta can kitchen ta dauko fresh neetle leave da betroot ta yi squashing dinsa a blender da ginger ta markadasu atare sann ta matsa ruwan ganyen rosemary da lemon tsami aciki.

Bayan ta haɗa ta debo oil din black seed mai yawa ta zuba akai dake ba mai yawa bane acikin dan kankanin lokaci ta dawo dashi.

Zuwa tay ta samu waje ya rikice yaron yanata luii luii da idanunshi kamar wanda zai ja numfashin sa na karshe.

Suna cikin hayaniyan basu hankara ba Har Adiaha ta dawo da ruwan maganin data kwamusa..

Hannunta na rawa ta dago yaron tare da yin addua azuciyarta dan ya danne mata kokonton datakeyi na tsoron kar maganin nan yaki yay amfani ace ta kashe musu ɗansu mai gabaki daya.

But she just have to take the risk to save life sabida she is very sure dat duk wani herbs din data hada aciki yana detoxifyn poison ajikin mutum inbai fitar bama dolene zai rage karfinsa.

Sharp sharp ta dago yaron tare da fincike abun taya numfashin dake fuskarsa acikin hanzari tafara bashi ruwan maganin abaki harsanda tafara bashi kafin nan suka farga.

Nan Kowa ya fara tambayarta metake bashi?sister zainab a tsorace tazo zata kwace ta kwabar saiga Ahmed ya iso cikin gaggawa.

Yace pls calm down We need to take him out now motar emergency yakusa karasowa da magani.

Kafin ya kammala bayani Adiaha harta yima yaron duren karfi da maganin duka abakinsa ya shanye da kyar. Maganin na ratsashi kuwa yay yunkuri snn ya fetso ma wani irin aman jini ajiki wanda ya razana kowa, nan duka suka yahaura mata da surutu kamr zasu cinyeta tay tsuru tsuru kamar yar kaza tana hawaye.

Ahmed ya rasa mema zaice musu ganin yadda kowa ya haura mata da guntun masifarsa su anty adizat kamar zasu cinyeta dan tsabar rainin wayo..

U better had not kill my child oo...duka iyayen yaron suka fara maida frustration dinsu akanta ana rirrikesu kamr zasu bugeta tsabar jaraban masifa.

Lokcin zuciyar kafayat kamar zai fashe tsabar dariya da murna cos she is enjoying evry bit of the drama aranta sosai.

Hankli tashe Hjy khadijatu tajawo Adiahar gefe take ta tambayarta ko menene wann din ta kawo ta bawa yaron yasha ya fetso da aman jini, bayani ta dinga musu amma sunki fahimtarta acikin nitsuwa kowa dai yana sace mata gwiwa suna mata fada akan daukar hukunci datay acikin gaggawa batare da neman izinin kowa ba.

Duk sukace idan yaro ya mutu toh tasani cewa itace ta kashe shi..

Ahmed baice komi ba ya dauke yaron akafadunsa ya fice dashi waje daidai lockin motar ambulance ya iso harabar gidan.

Kafayat sai dariyar mugunta take musu kasa kasa ganin yadda hanklin kowa ya tashi a sanadiyarta.

Da Ahmed da mijin sister zainb din ne kawai suka shiga tare da yaro sauran kuma suka biyosu abaya.

Su Ahmed suna shiga da yaron cikin motar emergency aka fara tukasu izuwa asibiti tun bai fara masa komi ba yaron yafara murkususu cikin azaba can sai ya kakarin amai.

Within some minutes yaron ya fara watso aman sosai yana fitar da ruwan jini da sauran ruwan maganin da Adiaha ta bashi yasha

Banda bambambi da mita da kamkamba babu abinda mijin sister zainab yakeyi yanamai tsinewa Adiaha yana ce mata mayya snn sai ya kulleta idan har danshi ya mutu.

Ahmed duk sai yaji ransa ya sosu sosai sabida rainin wayon nasu yafara isarsa. Shiyasa ya haɗe ransa yay masa shiru ko bayanin meke faruwa bai masa ba

Amai yaron ya dingayi abun tausayi har suka isa asibitin, Ahmed ya daukesa cikin gaggawa lkcin yaron ya farfado sosai yanata kukan rikicinsu na yara dake baifi 4yrs ba ahankli yana kankamesa yana uncle uncle my stomach ahaka yakaishi cikin emergency da gaggawa yafara dubashi.

Tsabar tsoro da fargaba yasaka Adiaha bata ko biyosu asibitin ba, ana watsewa agidan kafayat ta dinga mata dariya har abun yaso ya dameta aranta dan bata fahimce manufarta ba.

tun da suka bar gidan ta rasa sukuni aranta sai jeka ka dawo takeyi da Adduar Allah yasa kar yaron nan ya mutu ta shiga uku dan tasan duk laifin wa ita kawai za'a dora, yanzu hala kuma tsakaninta da sister zainab kuma tsana da gabace zata kullu na har Abada.

Kafayat da mijinta tare jikokinsa ne ata cikin main house sai dada tunzirashi takeyi tanamai zugashi akan batun abunda yake faruwa duk ta daga masa hankli jinin shi saiya haura sama sosai zazzabi ya rufesa atake.

Adiaha ta rasa nayi duk ta razana kawai sai tafara tattara dan sauran kayanta a jaka tafara kwana da shirin duk wani abunda zai biyo baya.

Tunda ta kammala hada komi nata ajaka ta sulale kasa tazauna jikinta a sanyaye ata bakin gadonta tare da jingina kanta akai tanamai runtse idanununta cikin jin wani irin ƙuna da radadin zuci.
Chapter 28 · 0% Book details