← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 157

Sashe 5

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dagata can hajy maimunatu ta rikito kasa daga kan gadonta hankli a mugun tashe tanamai cewa subhanallhi lapyarki kuwa khadija, khadija, meyasameki?
Wani abune ya faru kike kuka...ina Ahmed,Khadija meke faruwa ne Ke dan Allah kiyi min bayani waime hakane fisabillahi?

Tambayar datake mata ma kara mata azaman kukan yakeyi gashi irin kuka mai tsumayin nan takeyi mai daga hankli sosai ahankli cikin kukan take cewa "Adda na shiga uku, Bello yaci Amanata Adda. Nayi nadamar auren Alhaj bello bantaba kawowa cewa akwai lokcin da namji kamar alhaj bello zai walakantani har haka ba. Da bacin rai take maganan tana kuka kmr ranta zai fita.

Hanklin hjy maimunatu in yay dubu duk ya tashi..

Muryanta haryana diri Tace Bello yaci amananki fa kikace khadijatu? Huci ta saki dan Tun ma kan taji sauran bayanin taji ranta yayi mummunan hautsina ya baci .

zaman katsinan ya shige jininta sosai ashar kawai ta kora rai abace tace "Dan kutuman ubansa yau kuma meye ya miki? ina fatan ba daga wancan mutaccen hannunshi yay ya sake marinki da shi ba?

Da kyar cikin kuka tace Adda ba haka bane, wann lamarin yafi karfin mari,wann cin amana ne da tsantsar kaskanci da walakanci, nidai wallh ina cikin tashin hankli adda ya zanyi da raina? Innalillhi wa inna ilaihi rajiun Adda Na shiga uku.

cikin damuwa da tashin hankli hjya maimunatu tace "nifa na tsani wann kalman tashin hanklin kinsan bani da hakuri ki gayamin kawai ko kema ranki ya baci yanzun nan

Ta kara fashewa da kuka mai tsuma snn tace " 'ADDA aure Alhj bello yayi.

Hajya maimunatu ta dafe kirji tare da sakin Wani doguwar Salati snn Tace "Aure?da wa kenan, kutuma Wai kina nufin Alhj Bello ne yay auren ko danki Ahmed? kunne na baiji da kyau ba sake memetamin, kikace mene?..

Hjya khadijatu tace eh Adda Aure yay, nifa ba kara auren nashi ne ya dameni ba..dan tsabar ya tozartani ya walakantani yarinyar nan fa yaje kawomin a matsayin kishiyata..haba Adda wallah wann Kaskancin yayi yawa, bayan na raineta kuma budurwar dana?nashaku da ita snn Duk wanda ya gama sanin sirrin gidan ka ai ya gama dakai.

Cikin zazzafan huci mai tattare da rudewar tunani hnklinta a mugun atashe tace wacce yarinyace nifa na rude.

Muryan hjy khadija harna shakewa da kyar cikin sheshhekar kuka mai zafi snn tace "Adda budurwan Ahmed din nan dai ya aura fa...tace kina nufin yar iskan yarinyar nan kafayat?

Tace eh ita fa yarinyar nan da muka raineta agabanmu tamkar mu muka haifeta wai ita yaje ya kawomin amatsayin kishiyata.

Hjy maimunatu ta dafe kirjinta dataji yay harbawa sau goma cikin sakin ihun mai tattare da mamaki, bakin ta har na rawa tace kan facalin bala'i?kuka kawai kika tsaya musu Shine baki konasu dukansu ba? "Dan ubansu Suna ina yanzu?

Kuka hjy khadija ta kara fashewa da shi sosai tafara fayyace mata kan labarin..

A tsandare hajy maimunatu ta koma ta zauna jin har wani zufa zufa yafara karyo mata duk da ac dake dulmuye da dakinta.

Har hjy khadijatu ta kammala mata bayanin kuka kawai take mata tana cewa zata kashe auren kawai ta dawo gida dan bazata iya zama acikin wann cin mutunci da kaskancin ba

Karkada kai Hjy maimunatu ta shigayi cikin zafin zuciya da tsananin kunan rai snnn tace tab di jam..
"Eh..lallai..dan Adam butulu..mutumin nan baisan da waya keja ba. Har manice za'a nunawa bura ubanci da tashanci??kutuman ubancan..bello yake ko wa? toh ko yalo ne shi saina koyamasa hankli, dan bai isa ya walakanta ki ina raye ba karyanshi dan ubanshi.

Saida ta dau lokaci tana masifa tanamai cewa dama ai nasan za'a rina wai biri yaci ya koshi a gonan ayaba. Tun da can nasan baza'a taba auna abun arziki da yarbawan nan ba. Yan iska kawai munafukai makirai.

Dama can matarsa suka kawo kike raina masu dan rainin wayo yan rainin hankli kawai duk sun san me sukashirya miki na mugunta.

Har saida tay bambamin ta huce snn ta hau lallamin yar uwanta Tace khadija kiyi shiru ki share hawayenki kinji, ki shirya kawai ki jira gani nan yanzu zan shirya nazo Abujan kaf sainaci ubansu wallh. Shikuma mijin naki zai gamu dani,dani hjy maimunata yakeja,zanga mahalukin da zai tsaya masa a babban kotu dan wallh saiya sakeki koda mutuwa zaiyi.

Tana gama fadin hakan tana huci ta sauke wayar a kunnenta jikinta sai rawa yake da tsananin bacin rai dan saida takusan minti biyar a tsaye tana zazzafar huci kafin nan ta shiga wajen wanka.

Tana fitowa bayan ta kammala sallahn asubah ta kira agent tace ayi cancelling flight dinta na komawa turkey ayau snn a turo mata da driver yazo yakaita abuja acikin gaggawa.

Ata fannnin su Ahmed kuwa asuba nayi suka farka a barci shida brother hamzat suka gudanar da ibadunsu, bayn nan a gurguje ya tashi zai saka takalmin sa kenan da niyyar zai je ya duba jikin mahaifyar sa cikin gaggawa yana bude kofar bai hankara ba sai ji yay yaci karo da mutum didim agabansa da alaman shima yana shirin bude kofarne shima zai shigo ciki...

Kirjinshi ne yay saurin bugawa yana daga kai suka hade ido da brother kazim, baisan sanda ya fado jikinshi tare da rungumesa yana kiran sunansa ayanayin jin farinciki da mamakin ganinsa adede wann lkcin ba.

Brother hamzat ne ya fito ya samesu ahaka sun makalkale juna..

Baki bude cikin tsananin mamakin ganinsa yace "Ahhh "Brother kazim?..

Ahnkli ya ciro Ahmed din ajikinshi yanadan musu murmushi snn brother hamzat dinma ya taho cikin murnan ganinsa suka dan rungume junansu sosai.

Ahmed yana murmushi ya rusuna har kasa yafara gaishe shi yanamai cewa..."Ure welcome back _Arakunrin kaabọ_..what a surprise.

Brother hamzat yace
Karde tun jiya cikin dare ka taso.

Ajiyar zcyya ya sauke fuska ba yabo ba fallasa yace hmmmm dimeji, Kabar wann maganan tukuna, nan ya kalle Ahmed cikin nitsuwa snn yace _Bawo ni mama ṣe n ṣe bayi?_

Ahmad yace
"She is stable Alhamdullhi, dama
Yanzu ne muke shirin zuwa dubata.

Agurguje Yace Alhamdullahi lets go then.

Ko zama baiy ba haka suka juya dukansu uku suka nufi dakin da aka kwantar da hajy khdijatu.

Ata fannun hajya maimunatu kuwa Tun kafin ta kammala kimtse kimtsen da zatay har umarnin data bayar ya kammalu.

Nan ta fito tana tafiyar ta na isashiyar mace wacce dukiya ya gama ratsata.

Wani irin dankarerren black ceibo lace ne ajikinta mai tsada da yasha design da golden stones daga samansa har kasa sai sheqi kayan yake ajikinta dake ita farar macece mai cikar haiba sai ta haska sosai ta fito tana takawarta akan wani irin half cover heel na gucci da jakarsa yanayinta da aji sosai kamar shekarunta bai wani ja sosai ba.

gwalagwalnta na gold na kece raini sune wal wal a kan wuya da hannunta ta yafa mayafinta golden colour shima mai dankaran kyau da tsada tabi ta toshe idanunta da dark shades yau tamkar an mata mutuwa haka nan ta fito sarari ranta a mugun hargitse.

Tunda suka kama hanya zuwa garin Abuja bata yi wata magana da kowa ba sai waya kawai datakeyi da wasu private agent da kuma manyan lawyoyinta a Abuja.

Ranta a harde matuka Tace helo Don, bana son aikin wasa shiyasa kaga ma ban zabi na bi jirgi yau ba nakebin mota, i want all the nessecry information regarding my target right now, tun Kafin in isa Abujan nake son sanin komi da komi akan yarinyar nan ita da mahaifyarta kar da kubar koda tari kanajina?

Babban Agent dinta Don yace "Angama hajiya kibani nan da minti Arbai'in zaki ga komi ya kammalu.

Bayan nan ta sauke wayar tay shiru aranta tana cewa bazata kara barin tarihi ya memeta kansa akan khadija kamr yadda yafaru akan yar uwansu aminatu ba.

Alkawari tay tace babu wata kishiyar kabila da zata kara cutar mata da yar uwa dan wann karon kam sai inda karfinta ya kare..

Kusan tafiyar kurame su Ahmed sukayi ayayin da suka doso hanya izuwa dakin hajya khadijatu datake kwance .

Duk inda suka ratsa sai kaga anata satan kallon su sabida yanayin kamaninsu na yan uwan jini dayake nunawa.

Abu dayane kawai a fili dake Ahmed din ne kawai fari acikinsu duk sun fishi duhu. Amma brother kazim is bold and tall duk yafisu tsayi da jiki sosai.

He look fit and build up duk dama shekarunsa sunkai 45. A nitse yake kominshi dan kodaga yanayin tafiyarsa ma kawai basai an gaya maka cewa shine babba acikinsu ba.

Sallama sukayi a bakin room din bata amsa ba, Ahmed yana dan bude kofar kadan suka hangota sanye da hijab dinta acan kan gadonta akwance fuskarta na kallon jikin bango hawaye masu sanyi sun gama wanke saman fuskartan jikinta na rawa sabida sheshhkar datakeyi ahankli.

Kallonta dukansu suka tsayayi kowa da irin facial reaction dinsa na jin tausayinta, lura da cewa bata ma ji motsin shigowarsu wajen ba, Irin kukan zucin nan takeyi wanda yake fitowa silently marar kara sai yawan hawaye masu radadi dake saukowa daga cikin idanunta tana tarewa suna dada tuluwa.

Atake jikinsu yay sanyi duk suka kasa cewa komi sunata kallonta kmr basu taba ganinta arayuwarsu ba.

Atake Ahmed ya share ruwan hawayensa da suka taru acikin idanunsa acikin dan kankanin lokci, dacan harzai wuce wajenta Ahnkli Brother kazim ya y sauri ya rigashi isa.

Harsuka tsaya akanta suna kallonta bata farga ba saida brother kazim din yace."Mummy?..

A firgit ta juyo saicin karo datayi da idanunwansu dasuka gama rinewa akanta. Take taji wani irin kunya da suka ganta ahaka, nan da nan Ta share hawayenta cikin sauri sauri snn ta gyara zamanta cike da mamaki tanamai cewa "kazim? Is dat you Har yaushe ka zo nan? Ta kalle brother hamzat tace "kaima kana nan da sassafen nan ? Ta dubi Ahmed cikin dauriya da son kawar da yanayinta tace kaikuma why are u not with ur wife?..

Basu ce mata komi ba suka tsaya kallonta da fuskan tausayi duk fuskarta yy fayau jikinta yadau zafi.

Rusunawa kasa sukai atare dukansu suka fara gaisheta cikin girmamwa
Sosai..Bayan nan brother kazim ya zauna daf da ita snn ya fara tambayarta jikinta cikin nuna kulawarsa sosai.
Chapter 5 · 0% Book details