← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 157

Sashe 113

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aikuwa wayarta ta dauka ta kira musu youth tace ga barayi agidanta suzo marmaza su kashe su.

Kuka Adiaha take tana neman gafararsu ahmed yana janta tana mika musu hannu...

What is paining her father immensely is the way da har yanzu take Admitting agabansu na cewa bazata iya rayuwa babu mijinta ba.

Duk da baiy son magana but He cursed her once again, da ita da dan cikin nata duk ya tsine musu wanda yasaka Ahmed ya sake mata hannu snn ya fara mata borin shima..

He was like he can't do this anymore fitinan yay masa yawa. koda ya fara ce mata su tafi dan bazai iya tsayawa ana cursing jininsa tun baizo duniya ba adiaha ta turje taki sam shikuwa ranshi ya fara baci da halin iyayen nata sosai, can da ya harxuka yace mata toh saidai kawai su rabu anan agaban iyayen nata dan baiga amfanin auren sun ahaka ba,yace zai saketa kowa ya kama gabansa inta haihu zaizo ya dauke Abunda ta haifa...

Har ya juya zai tafi kenan a zuciye Adiaha ta rikeshi
Gam gam Cikin idanun shi take kalla mai cike da kalmomi na nadama dayawa dake yawo aciki, nan take taji komi nata ya dauke cakk jin wai har Ahmed yafurta cewa su rabu ta zauna da iyayen ta ta bashi babyn sa inta haihu.

But what about the feelings and the love she have for him?

Ahmed daga can cikin zuciyarsa ya fara convincing dinta akan cewa hakan daya yanke musu na rabuwar shine daidai. He can't be dis selfish and heartless if her parent are suffering dis much sabida wnn auren nasu.

Adiaha tafara girgiza mai kai a mugun rikice tana kuka jin kamar ba da ita yake maganan ba.

Sosai ta tsorata ganin From his heart yake neman rabuwa da ita...

Yay mata bayanin duniyan nan amma ba jinshi takeyi ba. Cikin bayanin har ma he admit dat he doesnt love her dat much da zata bashi rayuwarta duka haka aganinsa der is soo much to lose is not even worth it.

He feels really tired shi basonta yakeyi ba har yanzu, snn she is losing alot of peace in her life bcos of him abun sosai ya dameshi. Kawai yaga gara su rabun anan ta huta ma ranta atleast koda ma iyayenta zasu yafe mata tay rayuwa mai cike da kwanciyar hankli batare da shi ba.

Hakanan iyayenta suka tsaya sunata jiran suga kalar hukuncin da yarsu zata yanke game da batun Ahmed na rabuwa but at the end she ended up choosing her husband agabansun ta tsuguna tafara rukonshi tanamai cewa bazata taba iya rayuwa babu shi ba..

She said she doesnt care if he love her anymore or not, she just want to be with him forever, kuma bazata iya rainon abinda yake cikinta sabida dan su rabu da juna ba.

Maman Adiaha ta saka hannu aka cikin jimami mai tsanani tanata kallon yarta tana rolling akasa tana riirrike kafafunsa tanamai rokonsa tana kukan fitar rai akan kar ya saketa wai bazata iya rayuwa babu shi ba.

Kan Ahmed yay wani irin zafi dan harta fara bashi tsoro ynzu, idanunsa take suka cika da ruwan hawaye sosai. He wish akwai abunda zai mata ta kalli abunda yake gane mata.

Cikin kwanakin nan He tried his best to feel sumting for her amma ina and she is losing so much bcos of him.

Atake Kawai ya rufe idonshi yace mata gaskiya shi kam bazai iya cigaba da auren nan ba, tay hkri kawai, sabida akwai cutarwa mai yawa aciki tanata rokonshi tana ta rokonshi ganin dagaske yake zai saketa
Nan danan ta miƙe tsaye tareda juyawa kan iyayen nata tafara sauke musu buhun rashin mutunci da masifa, kuka take cikin bori tanace musu sune suka tsorata Ahmed da mugun bakinsu da kuma tsinuwarsu har yake cewa bazai zauna da ita ba..

kalma yay mata sauki wajen tuhumarsu dake iyayen nata bawai 100% christians bane dukansu mutane da suke matukar girmama al'adansu da belief dinsu ta gargajiya musammn ma baban ta

Shiyasa Suke da tsautsauran ra'ayi irin sosai din nan basa ji kuma basa gani..

Dacan da yaransa basu wani girma ba shine kusan chief prosecutor na lamarin duk wani laifuka da y'ay'an mutanen comunitynsu suke aikatawa, baban adiahan yay kaurin suna wajen dabbaka believes dinsu na al'ada saidai musuluntar da mahaifyar sa tayi shine ya fara ruguza masa rayuwarsa gabaki daya kafin nan na Adiaha yazo ya dada dagargaza masa zuciyarsa.

Adiaha ta bushe idonta tafara amfani da hakan wajen kiransu marasa imani da tausayin rayuwarta.

She told them dat Ahmed din dai take so, da ace suna kaunarta fiye da yadda suke dabbaka Al'adansu aida bazasu tsaurara mata akan dan ta aureshi a haka ba. She started blaming them for eveything. Tace sune ma suke hanata zaman lafiya agidan mijjinta cos they dont like her.

Ahmed ya zame kanshi ya bar wajen ya kyaleta da su tanata kai sudai iyayen nata basu ce mata komi ba.

Har ya shiga motar ya zauna ya dauki biro da paper zai rubuta mata saki can sai yaji zaman bazai masa ba haka ya fito da papern a hannu ya jingina kansa da jikin motar yana tunanin abunda zai rubuta..

He felt remoseful sabida duk da baizo nan ba da hakan bai faru ba.

Jim kadan yaji ihu yafara gauraye cikin compound din gidan.

Da sauri ya dago kai cikin firgita da tsorata ya taho ta gate dinsu aguje jin muryan maman adiaha tana kiran sunan yarta agigice.

Da sauri da sauri ya wuce ciki sai ganin Adiaha yay da wuka a hannun ta tana kkrin yanke jijiyar hannunta ta danna wukar akai har jininta na zuba.

Abunka da iyaye duk sai da suka rusuna suka dawo lallabatta akan krta kashe kanta.

Tana kuka tace sam mutuwar yafi mata tunda sunci nasarar tsorata Ahmed har yanacewa zai saketa bataga amfanin rayuwarta da iyayen da basa son farincikinta ba.

Jikinshi atake ya fara rawa ya karaso da zafin nama yanamai ce mata ta aje wukar suyi magana acikin hankli.

Amma sam taki.

Sai cewa take If he dare come close to her she swear wll take her life.

Tace Karya kakeyi kace baka sona while im carying ur baby..I love u. I cnt breath witout you isit dat hard for u to understand?..

Ahmed ya lumshe idanun sa cikin lallami yace pls listen to me,ki aje wukar dont hurt urself anymore toh meya amfanin aure da kuma soyayyar da babu kwnciyar hankli aciki ehhhh?ure not happy and i am not ur parent are not..

Cikin datsar numfashin sa tace masa "i am happy with u.. aure na dakai akwai riba tunda cikinka ne ajikina. Ure just scared of them sabida sun nuna sun tsane aurenmu amma ni bazan taba yarda su cuceni ba. Indai har zaka sakeni anan banga amfanin rayuwata ba lemee just kill myself sai dukanku ku huta iyayenta duka da hawaye acikin idanunsu, Baban dake ji da zafin rai yace komae zata fada bazai taba accepting dinta acikin ahalinsa ba and she wll be forever cursed maman nata ne batace komi ba sabida tausayin yarta daya gumeta.

Adiaha if u dont want to listen to us atleast listen to ur husband wann auren naki babu amfani cos is hurting alot of ppl

Tace i dont care about oda ppl mama, i only care about myself tunda kunce soyayyata da aurena basu da muhimmanci agareku den fine zan kashe kaina amma kusani baxan taba yafe muku ba da kukaci nasara wajen wargaza ma mijina tunaninsa akaina da har yake cewa zai rabu dani sabida ku.

Tana fadin hakan ta danna wukar akan jijiyarta sai kyat ta yankashi jininta ne ya fara tsiyaya tsuuu kmar an kunna bakin famfo mahaifyarta ce tay sauri wajen tarota jikinta tanata kuka tana kiran sunanta..

Hayaniya suka fara ji na engine mashuna alaman matasan anguwa sunyi zuga suna zuwa..

Kan Ahmed ya kulle baisan me zaiyi ba kuma ga hayaniyar matasan sai dada tunkaraso suke

Maman ta kalle Ahmed badon ranta yaso ba tace u have to take her out of this place befor she dies.

Tunda haka ta zaba nida babanta mun barta da zabinta, pls take her with u, we dont care if she bcome a burden to ur heart, kar kayi sanadiyar da yarmu zata mutu oo dan inhar ta mutu kaima kasani saimun kashe ka.
Pls take my doter out of here tun kafin youth su karaso is not safe for the both of u.

Ahmed yaji kmar ya tsaya kawai shima akashe shi cos dis girl has become a serious problem ma rayuwarshi yanxu.

Maman sai rokonsa take akan ya tafi da yarta suje asibiti koma subar garin dan karta musu mutu anan.

Baban da bakin ciki ya dame sa hakanan ya juya ya bar wajen yanamai tura wheel chair dinsa ya koma cikin falonsu yanata zubda hawaye bai iya ce musu komi ba.

Hakanan ya dauketa ya sakata a mota suna barin kofar gidan saiga youth da adduna da sanduna suna neman wanda ake tuhuma.

Daga nan Asibiti direct Ahmed yakaita aka fara bata taimakon gaggawa bayan an cirota a danger
Ko wani xama basuyi ba ya amshi tickets guda biyu na emergency plight aka dawo dasu garin Abuja.

...asibitin dayake aiki ya wuce da ita aka dora mata drip shikuma ya koma office dinsa banda sallahn azahr da yay bai iya zama ba sai jeka ka dawo yake acikin tsananin damuwa da rashin sanin abunda zaiyi da lamarin nan.

Take Yafarajin kmar yay tsuntsu yagansa akasar canada gaban abokinsa Banji yana cikin jeka ka dawo cikin zullumi can saiga BANJIn ya kira.

Kai tsaye ya dauka ko zama baiyi ba yafara maida masa maganan Adiaha jikinshi na rawa idanunshi sunyi jaa kamr zaiyi kuka yarasa me ke masa dadi.

Shikansa banji saida yaji kmr kwakwalrsa ce ta toshe..

Aransa yanata mamakin irin son da Adiaha take ma Ahmed son da baiya ganin komi, snn baya iya bambamta daidai da ba daidai ba. Ko shikansa banjin so yay da ace sun rabu kawai kowa ya huta amma dayaji batun abunda tay bayan ga karamin ciki ajikinta sai kuma jikinshi yay sanyi.
Chapter 113 · 0% Book details