← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 157

Sashe 27

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Danta Ahmed kuwa bata
Samu damar tattaunawa dashi ba harsai washe gari lokacin komi ya lafa agidan sosai.

Da yamma lis yazo gaisheta unxpectedly ta zaunar dashi ta fara masa nasiha cikin nuna masa kulawa da gata sosai, dan tun yana jinta daga zaune harya kishingida ya kwantar dakansa akan kafafunta tareda lumshe idanuwan sa yanajin dul abunda take gaya masa masu ratsa zuciya sosai.

Kusan rabin nasihar ta akan matarsa ne, duk sai da ta tuna mashi yadda matsayin Adiaha yake dayaje ya daukota agarinsu, tace masa ta cancanci ya tausaya mata cos she is soo helpless,hopleless,vulnerable and very much afraid and depressed duk dan saboda shi.

Duk datace masa inhar yarsa ce Take cikin wann halinda Adiaha take ciki arayuwarta zaiji dadi aransa idan aka mata hakan? sai yay mata shiru bai iya bata amsa ba, Shikansa baisan tana lura da komi ba saida tafara bude masa komi dalla dalla.

Aransa bai tabajin tausayi da nadaman abunda yakeyi ma Adiaha ba saiyau dan kuwa wasu maganganun harsun fara sawa yanaji aransa kamar Allah ma zai iyayin mummunan fushi dashi akan yadda yake treating din aurensu da Adiaha.

Tsillin hawayensa daya zubo masa a ido na tausayi da nadama ya share yay mata alkwarin cewa zai gyara halinsa.

Bayan ta gamsu da dukkan nasihar data dasa zuciyoyin yaranta ne tafara tunanin nata rayuwar, gobe ne take shirin maida sister zainab gidan mijinta bayan nan tana son tafara shirinyin tinani akan future dinta na nan gaba dan batajin zatayi zaman hada kafada agidan tare kafaya.

Daren ranan gabaki daya a cikin tunanin rayuwa Ahmed ya karesa.

A fannin Adiaha kuwa izuwa yanzu harta fara cire ranta ta barwa Allah komi dan tasan kwanan nan kafayat zata fara gane irin zaman auren da takeyi da Ahmed na walakanci da kaskanci wanda ko kayan sawa isassu bata dashi duk kayan kwalliyarta ma datazo da su dik sun kare.

A fannin kafayat din kuwa duk sai ta rude ganin ta kasa gane kankowa agidan, tana lura da su tun jiya da akayi rikicin nan bata kara gane kan mood din kowa ba.

Su basu fushi snn basa murna, and she have no idea dat hajy khadijatu tay musu nasiha duk sun shiga hayyacinsu kowa ya nitsu.

duk ta sake baki ta dauka
Borin da mahaifinsu ya musune yake damunsu aransu. Dan Dama kuma tana da babban shirinta datake tay akan sister zainab musammn ma dataji labari awajen alaji bello cewa mijin zainab din yana fushi da ita akan zuwa gidansun datay.

Washe gari juma'a da sassafe yaune ranar da hajiya zata maida sister zainab din gidan mijinta danta bawa mijin nata hakuri .

Da asubahi tun basu farka ba Kafayat ta sace jiki ta taho kitchen din hjya khadija ta bude fridge dinta ahankli ta dauki wani goran ruwa,.

Duk wani logon su ma gidan ta sani dan haka take da cikakken masaniya akan irin ruwan da ake bawa yaron sister zainab yana sha kowani safiya inya farka a barci, hannu tasaka agaggauce ta ciro bottle din ruwan ta bude ta barbada wani irin gari aciki snn ta mayar ta rufe ta koma dakinta ta je ta kwanta tayi lumui.

Aranta babu abinda takeyi sai kyalkyalewa da dariyar mugunta cos she just cant wait taga yadda sister zainab zata shiga uku awajen mijinta akan rashin lapyar yaronsu shafiu inhar ya sha ruwan nan...
[6/10, 1:33 PM] SURAYYAHMS: Murmushin mugunta Kafayat ta dingayi snn ta dauki wayarta ta boye layinta tasaka private number snn ta fara rubuta text messge mai zafi ma mijin sister zainb ta tura masa.

Ba komi ta rubuta aciki ba face dan ta sanar da shi cewa ga matarsa nan tay neglecting dansu garin masifa yaronsu yanata jin kishir ruwa har yagaji yasha poison dan haka yazo da wurwuri ya dauki gawar dansa...

bata dade da tura tex din ba sai gashi nan ya mata reply anan ma ta kara harhada masa magana tace tun da matarsa tazo gidan masifa takeyi bata kulawa da yaronsu gashi har wani mummn abu yaje ya sameshi..

yayi yayi yasan wayene yake turo masa wnn sakon amma taki sam ta gaya masa snn saita nuna masa cewa damuwa datayi da rayuwar dansun yasaka taji tausayinsa ta kira babanshi danshi yazo yay ceton ran dansa dakansa cikin gaggawa.

Bayan ta hada gurmin ta kashe wayarta tare da rungume pillow da jikinta a cikin wann yanayin nishadin jin ta kammala haɗa bomb saura kawai ya tashi ayi rikici ayayin da take kwance lumui cikin jin dadi.

wani irin juyi tayi tanamai kara mirginawa tareda rungume bayan Alhaji bello gam gam bata wani jima acikin wann yanayin ba baccin bazata ya kwasheta..

Yau din jumu'a ne dan haka da sassafe Adiaha ta fito dan ta fara haɗa breafast cikin gaggawa.

Tun jiya cikin dare Ahmed yake lura da ita dan duk ya rasa ta yadda zai yi ya fara aproaching dinta da wata magana akan yanayin zaman auren nasu...

jikinshi yay sanyi, Aransa Yasan bai kyauta mata ba ko kadan, amma cikin zuciyarshi haryau gani yake kamar bazai taɓa saukar dakanshi down to her level ba, wani bin yakanji aransa kamar ya wuce ajinta nesa ba kusa ba managing dinta kawai yakeyi saboda yanayin daya tsinci kansa aciki.

Tun jiya cikin dare yake fama da irin feeling din nn nason yaje dakinta ya lallabeta ya bata hakuri amma sai yaji kamr bazai iya aikata hakan ba sabida baijin kmr zai iya mata hakan,wani irin guilty concience ne yake cikin aranshi amma kwata kwata bayason ya sauke mata kanshi acikin sauki kuma a fili dan baison ta fara fassara abun da niiisa bare tazo ta fara rainashi..

Aranshi baya ma jin sha'awar yin soyayya, shidai kawai yasan ko zai bata kulawa, zai batane ne a bisa hakkinta na aure,Ba soyayyar Adiaha yake son ya cusawa ransa aynzu ba, he just reliazed his mistake,Aure bautan ubangiji dan haka dole ne ya bawa aurensa kulawa, to cut the part of cruelty and abuse and be normal with her, kuma yana hoping ta fahimce hakan daga gareshi acikin sauki.

bayan ya dawo daga masjid ya shiga room dinta bai ganta ba sai kawai ya dawo nashi dakin domin yay wanka dan kar ya batawa kanshi lokaci sosai.

Wajajen karfe bakwai da minti sha biyar Adiaha ta kammala komi ta fara rabawa sashe sashe abincinsu kmr yadda ta saba. Sashen su kafayat ta kai wajen shiru kmr ma babu motsin kuwa aciki.

Yawanci inhar taje wajen anty adizat ta gamu da ita ko danta sulu sai sun kuntata mata acikin wasa suna ambatar ta da house girl, haka yayanta duk suke mata kallo,.

Anty adizat tariga ta lura da cewa hakan cin fuska ne kuma Adiaha bata son wasan daga yanayin fuskanta amma dake taga tana ganin girmanta bazata iya dakatar mata ba sai ta dawo da abun cin fuska acikin wasa duk yaranta a matsayin housegirl kawai suke kallon Adiaha basu san ma cewa matar kawunsu bace tsabar yadda uwarsu tasaka suka raina mata wayo sosai suna mata kallon jaka jaka.

Anty nurat kuwa inda kasan ta taɓa siya wa Adiaha kayansawa haka take hantarar yanayin shigarta kullum cikin mata burga da kayan sawa da kuma goranta mata sabida ita bata da shi.

A kullum yaumin itace ke tunawa Adiaha cewa bata cika mace ba and how unkept she look acikin gidansun.

unapologetically, zata zage snn ta gatsala mata baqar magana bata wani sakayawa dan gani take ta fi karfinta har abada,,

Daga yau tace mata kazama acikin salo sai gobe ta zageta tace mata bakauyiya ko kuma matsiyaciya acikin salon habaici dan kawai taga bata da isashen kayan sawan da za'a iya nuna ta dashi, kullum acikin memeci take, akan haka duk tabi ta hana yaranta raɓar Adiaha, ranar ma haka kawai taji tana ce musu wai su nesanta kansu daga jikinta karta koya musu saka house uniform,ma'ana wato dabi'ar maimaita kayan sawa. ..

Hakan bakaramin ci mata tuwo a kwarya yakeyi ba amma bata da yadda ta iya sai hakuri gashi tanajin matukar tsoro da kunyar kiran grand ma dinta awaya dan batason ma kowa yasan halinda take ciki ayanzu.

Ahankli take tafiya harta iso cikin bangaren hajiya khadijatu dauke da babban tray din abincin safensu ita da sister zainab a hannunta.

Isowarta sashen kenan bada jimawa ta tafara jiyo hayaniya ta ciki, tana matsowa kurkusa ta soma jin kukan yaron sister zainab, shafi'u. Tahowa take kanyi da tunanin ko irin rikicin nan ne ta yara dan tasan yaron fitinanne ne akwaishi da son kuka bana kadan ba.

Tana buɗe kofar abazata taci karo da sister zainab ta bankade ta ta fito fuuuuuuu kamr iska hanklinta a mugun tashe ta fito waje tana kuka sosai kmr ranta zai fita.

Tsorata tay ta aje tray din abincin akasa dan bata taɓa ganin sister zainab tana kuka har haka ba.

Bakinta na rawa rawa tazo gareta cikin nuna damuwarta afili tace Sister zainab meya faru "what is wrong? Kuka kawai sister zainb takeyi tanamai daura hannunta aka cikin tashin hankli sosai.

Tun kafin Adiaha ta kammala rife bakinta tafara jin motsi can saiga fitowar hajy khadijatu da yaron a hannunta duk ya sandare yana convulcing bakinsa yanata fitar da farin kumfa.

A mugun razane Adiaha ta matso kusa tace mumy meyasame shi haka?..innalillai..why is he convulsing like dis meya faru mummy?

Hankli tashe hjy khadijatu tace nima bansani ba reema,da safen nan ya tashi kalau muna tare da shi harna koma bacci, daga baya ne zainab ta tasheni tace min daga shan ruwa fa shikenan sai ya fara tari daganan kuma shine har yanzu bamu gane kansa ba.

Adiaha zatay magana cikin katseta tace reema Kiyi sauri mana ki sauƙa kasa Ki kiramin kazim zamuje asibiti dashi yanzun nan kar wani abu yaje ya sameshi.

A hujajan Adiaha ta sauka ta koma sashen su anty adizat tafara buga musu kofa acikin tashin hankli sosai

Bayan ficewarta ba da dadewa ba yaron yafara fidda jini jini ta hancinsa numfashinsa ya fara hauhawa can sama yana shakar iska da kyar yanamai neman daukewa cak.
Chapter 27 · 0% Book details