← Book details Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 157

Sashe 138

Kishiyar Kabila Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai a wnn karon ne yake fahimtar cewa kudi kyau da ilimi ba shine weak point din wasu matayen ba. Kuma tabbas ba kowace macene zata so shi shima ba.

Ganan dai matarsa Adiaha datake masa bauta tana tarairayrsa
Agaban iyayensa amma harga Allah wann gatan awajen yasrah kawai yake son yaga ya samu wanda ayanzu baisan me zaiyi mata ba. Dn yay na lallamin yay na hakurin amma babu abunda ya sauya kawai saiya dan ja baya ya dena tankata yafara nuna mata kamar baidamu ba.

Kwanan biyun idan yazo mata dakin ta suka fara irin faɗarsun sai ya rubuta takarda mai tattare da kalamai masu tsananin dadi ya aje mata akan table wanda yake mugun ci mata tuwo akwarya.

Haka kawarta maryam zatay ta tsokanarta inta zo mata ziyara taga letter amma yasrh kam dagske takeyi na son taga ta rabu dashi har acikin ranta.

Ranar asabar Ahmed baya nan Karan Alarm ne ya cika dakin tan gaba ɗaya, kwance take tana bacci har sai da Karan ya kusa katsewa tukunna ta bude ido ta Janyo wayar da hannun ta, ko kallon fuskar wayar bata yi ba ta saka hannu ta katse karan tukunna ta maida wayan ta ajiye shi, sai da ta mike ta zauna daga bakin gadon tukunna ta bude idonta a hankali wayar ta sake sauka taga 8:10am.

tafi minti biyar a zaune daga bisani ta mike.

gashinta ta tattare shi waje guda ta isa inda bathrobe dinta ke rataye ta cire kayanta dake jikinta ta saka bathrobe din ta shige toilet, sai da tayi brush tukunna tayi wanka, gaban mirror ta zauna bayan ta fito daga wanka ta shafe duk jikinta da mai,ta fesa body spray tukunna ta je saka kaya, closet dinta ta bude ta ciro wata grey colour abaya mai Babban hannu da adon golden daga jikinshi.

sai da ta saka kayanta tukunna tayi inda jakunkunanta ke rataye ta jawo daya daga ciki ta zuba tarkacenta na tafiya gasarta a ciki sannan ta yafa gyalen abayar a kanta sannan taje ta saka shoes har ta fita ta tuna da wani abu ta karasa can ta sauko jin kmr babu kowa a gidan shiru. tasan hala Adiaha ta tafi makarantar su na islamiya tunda weknds ne kokuma mayb tanakan bacci.

Fita tay har ta zauna zata fara cin abincin datay oder sai taga time zai kure maza ta mike ta yi hanyan waje batare da kowa yasan ina ta nufa ba,sai da ta taje dab bakin kofa zata fita Taji muryan Adiaha ta fito kenan daga dakinta da hijab din islamiyarta tana murmushi mai sanyi ayayinda take ce mata amarya yasrah harkin fito,kallon abincin tayi tace, kin kyauta siyan abinci a waje yauma ko ? Nide Nasha fada miki babu kyau kiyi hkri mana kinacin namu kema fa nan gidanki. Har ta karaso daf da iya tana kan mata maganan cikin lallami kmr yadda suka saba.

Yasrah na shiru har sai da ta gama maganan datakeyi tukunna ta juyo da kirkirenn murmushi a fuskanta ta dubi Adiahan tana karasowa cikin parlourn, cikin basrawa snn ta ce "kin tashi lpy anty reema, Ina kwana".

Amsa ta tay bayan ta zauna kusa da ita, tuna maganan da Taji ahmed yanayi ne awayarsa da abokinsa banji da yadda yake expressing din damuwar sa akan yanayin zamansun da yasrah jiya yasaka ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tace yasrah ina son magana dake.

nitsuwa tay duk dama tana sauri tafara saurarar zancen Adiaha.

Nasiha tay mata akan ta dawo hayyacinta tafara kulawa da mijinta kodan karda Allah ya kamata.

Snn ta gaya mata yadda matayen yayunsa suke dora mata laifi na cewa ita tay sake da bata nuna ma yasrahn Al'adansu na gidan ba. Koda takai ma Ahmed maganan jiya kusan abunda yake nuna mata kenan ayanayinsa duk dama bai taba fada mata a fili ba amma shima nuna mata yakeyi itace bata kkri wajen shawo masa kan yasrah. Saidai aranta gani take kmr so ake alaƙa mata laifi ace itace take daure ma yasrh gindi tana guje masa agidan sabida dan bata korarta koda ta zo kwana ko takiyin wani aiki a matsayinta na matar gidan itama.

Itama yasrah gani take kamar Adiaha bata san metake cewa ba datake son cusa mata lamarin Ahmed amma for sake of respect ta amsa mata tace tazata gyara .

Adiaha taji dadi sosai tace zata bi kasuwa da ta siyo musu kayan abinci domin yasran tay girkinta na shiga dakin miji a daren farko kodan maganganu da gulmace gulmace akansu ya ragu .

Bayan nan suka rabu can da yamma Adiaha ta dawo da kayan miya su alaihu da sauran tarkace yasrah batayi musu ba ta dafa lafiyayyen abinci har suka ci suna hirar rayuwa.

Cikin hirar suke jefa ma junansu ra'ayinsu.

Adiaha tana mai fahimtar da ysrh cewa ta hanyar bautawa miji shine kadai riba da kuma jin dadin zama tare dashi.

Yasrah kuma tana gaya mata cewa bataga abun so ajikin mijin nata ba.

Haka sukayi tay kowa na fahimtar kowa inda Adiaha ta wuni tana mamakin yadda yasrh taki jinin aurenta da Ahmed bacin ita babban burinta na rayuwa kenan snn gashi tasamu amma bata cikin jin dadi tare dashi.

Bayan ta dawo haka ta tayata girkin sunata hirar rayuwa su biyunsu kamr yan uwan jini, adiahan ce ta rakota ta kawo masa abinci a shirye akan plates dayaga hakan sosai yaji dadi aransa duk ya dauka ta shawo masa kan matarsa ne.

Tun shigowarsu da Abincin ya kure yasrah da lumsashun idanunsa baiya ko kiftawa.

Nan Adiaha ta koma dakinta tabarsu tare da tunanin ko itama zata huta da irin bahaguwar kallon da ake mata akan rashin nuna wa yasrah hanya.

yasrah na xuwa ta aje mashi snn tay zaune a falon ta zubawa tv ido ta basar dashi, duk wani maganan dayakeyi ba jinshi takeyi. Duk yadda yay zaton ya iya shan qamshi da kyaliya yau saida yasrah ta kure masa tunani, Yana bude abincin kuwa ya daka tsalle ya tashi ganin mutacen bera ne akai data saka masa yay tumbul da abincin izuwa kasa ya ƙona masa kafafu saida wajen yay wani jajazir a take.

Baiyi tsammani ba yaga har ta miƙe tana cewa kadan yagani inbaidaina tursasa mata zamowa matarsa na dole ba.

Sosai ransa ya baci da ita yaukam idonsa suka kada sukayi jaaa yanayin yadda tace masa kadan din nan yagani

Firgitan da yay yaska Adiaha ta fito daf lokcin yasrh taja tsaki ta nufi room dinta, shima a fusace ya bar wajen ya koma room dinsa ya rufe kofar da wani irin takaici ayanayinsa.

Dukansu Adiaha tabi da kallo Nannauyar ajiyar zuciya na kufce mata tahau share wajen ta kimtsa tsaf tare da jinjina ma tsaurin idon yasrah aranta..

Har Washe gari Ahmed yana cikin fushi da ita baisauko ba amma bata damu ba,trout sunday din baima nemeta kuma yaune karo na farko dataga yay hakan.

Washe gari Monday nayi ta fita sassafe batare da tagayamai ba ta wuce wajen trip din gasarsu na tsakanin makarnta da makarnta.

Kusan ince ma itace tafara isa bus stop na schl inda zasuje essay camp,snn babu wanda yasan da cewa bata fadawa kowa ba ta fito sai maryam kawarta.

Haka Su Ahmed sukata neman ta agidan har dare duk wayoyinta a kashe inran Ahmed dubune to duk sun tashi aranar. Adan dolensa ya nemo lambar Maryam yay ta gwadawa baiyi ba Adiaha tanata tayashi amma bawai ganin kkrinta yakeyi ba.

Wasa wasa har dare bai samu sukuni ba yanata zaga gari bai ganta ba sai da safiya yay ya dawo ya zo ya sameta a daki da alaman ta dawo.

Ransa sosai ya baci ya mata masifa sosai hartay kuka ganin yadda take ce masa ita ba matarsa bace shiyasa bazata nemi izini awajensa ba bakaramin damunsa abun yakeyi ba.

Yau baram baram suka rabu ko ajikinta washe gari ma ta kara ficewa sassafe abunta har yamma yayi sann ta dawo tazo ta samu an aje mata farin takarda akan gado.

Hannu ta miƙa ta dauka ta karanta tana jan tsaki sai kuma tay murmushi sosai tace Alhamdullhi.

Wadrob ta bude tahau kwasar Kayanta ta debe su kaf gurguje tayo dashi waje ko tsayawa batay ba ta wuce.

,.taci sa'a kuwa ko Adiaha ma batasan da ficewarta ba dake ta nakan sallahn magrib ne snn batare da ta lekata ba taja troley dinta da kyar bata tsaya koina ba sai airport, after some min ta iso katsina abunta xuciyarta tasss, direct sashen hajy maimunatun ta fara isa tanajin dadi aranta ita kuwa mamki ne ya rufeta sosai ganin yasrah ita kadai da kayanta acikin dare.

Tambayarta ta dingayi akan meyafaru ta taho ita kadai amma batace mata komi ba harsaida suka samu nitsuwa.

Nan kuwa batay wata wata ba ta bude zip din jakarta tare da miƙa mata takardan saki daya wanda ya nuna cewa Ahmed ne ya rubuta..
[7/27, 11:43 PM] SURAYYAHMS: Faɗin irin tashin hankli da kaɗuwr da hajiya maimunatu ta shiga dataga takardan sakin yasrah bazai iya fassaruwa ba, musmmn ma da taga ta kasa samun wani gamsashen bayanin sakin daga gareta saidai tace mata itama ahaka tagani akan gado ya aje mata..

Tun adaren ranar ta nemi mahaifyarsa hjya khadijatu snn ita kuma ta nemesa tare da fayyace masa komi wanda ya zame masa kmr labarin almara.

Baiya cikin garin abujan amma a mugun birkice Sassafe sai gashi nan yayy sammako zuwa garin katsina yabiyo bayan labarin sakin inda ya tarar da takardan da rubutunsa da komi sai dai baisan taya zai kare kansa ba dan kuwa tuni yasrah ta fayyace masu hajy maimunatu irin halayyarsa na fushi da cin zarafin aure da basu taɓa saninsa da shi ba ta daureshi dashi.
Chapter 138 · 0% Book details